Showing 69001 words to 72000 words out of 129098 words
Chapter 24 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
da sakin marayun kukan sa.
Ita ko a hankali ta jawo Igiyoyi biyun ta haɗe su ta riƙe, a hankali ta lallaɓa ta bayan sa ta wuce, dan dama ba ta gaban sa take ba. Tana isa ɗaki ta zauna kan kujera ta fara dariya amma mara sauti gudun kar tsautsayi yasa aji ta, "kaɗan ka gani ma wallahi, ba ku kunce mara sa imani ba? To ni nan zanyi maganin ku, musamman ma waccan 'yar uwar ta ka hmmm, da Zainab ɗin nan zasu ji jiki a hannu na" ta faɗi tana cigaba da dariyar ta. Daga baya kuma taje ta kwanta.
Marwan ya ɗau lokaci yana tsallen kwaɗon, tun yana irgawa har ya daina, saboda ɓacewar lissafin da yayi, kuka yakeyi sosai kamar ƙaramin yaro ƙafafuwan sai rawa su keyi kamar rawar disko yake da su, saboda yadda suka gaji sosai, domin yanzu jinsu yake kamar ba nasa ba, gashi ba damar tsayawa kada aljanu su mai dashi ƙwallo, domin kuwa yasan in har suka aikata haka, tofa ƙasusuwan sa baza su taɓa miƙewa ba, idan sun barshi da ran ma kenan.
Taɓa bayan sa da akayi ne yasa shi wuntsulawa gefe, tareda sakin tusa wanda da kaji tusar ma kasan ta bala'i ce, domin kuwa yadda ta fito kamar fitar bom, "dan Allah kuyi haƙuri wallahi, na rantse bansan ya akayi na koma yi a hankali ba, amma yanzu da sauri zan yi wallahi" yayi maganar a firgice, saboda a tunanin sa aljanun ne suka taɓa sa, harda rintse ido wai dan kada yayi tozali da jinnu.
"Na shiga uku na ni Zainabu, Marwan me nake gani haka?" Cewar Hajiya tana kallon yadda Marwan ya zama dan fitilar falon a kunne, jin muryar mahaifiyar sa ne yasa shi buɗe ido, cikin muryar kamar zai yi kuka ya ce, "Hajiya me yasa zaki min haka? Why why Hajiya?" Durƙusawa cikin ruɗani tayi tana kallon Marwan da kuma zantukan da yake yi, "me yasa me ka ne Marwan eh? haukacewa kayi ko me?".
Sai da ya fashe da kuka sannan ya ce, "kin rusamin ƙoƙari na yanzu dole na in sake daga farko, Hajiya kin cuce ni wallahi, duk wahalar da nayi ya tashi a banza, me yasa ma kika zo kika taɓa ni" yayi maganar yana sa ke fashewa da kuka, domin ba ƙaramin haushi Hajiya ta bashi ba, saboda babban kofsi ta masa. Ita ko ga la la tayi da baki tana kallon sa jin abinda yace, "yau n'aga ta kaina, Marwan ko dai gamo kayi ne?" Tayi masa tambayar tana ƙoƙarin ɗaga shi, amma ya ƙi, a ƙarshe ma dai komawa gefe yayi ya fara tsallen kwaɗo yana sake irgawa daga farko kamar yadda aljanun suka basa umarni.
Hankalin Hajiya ne ya fara tashi ganin abinda Marwan ke yi, tayi-tayi ta ja sa amma yaƙi, ya ce wai ta rabu dashi sai ya gama, saboda kada su hukun tashi.
Ihun da Hajiya ta fara yi na neman taimako ne ya tasar da Amna da kuma Ammu, "akan me zata tasar da mutane suna barci?" Amna ta faɗi tare da sauka daga kan gado, Ammu ma Allah dai yasa lafiya ta faɗi cikin zuciyar ta.
Ruki ma ta tashi domin ba ƙaramin ƙara Hajiya takeyi ba, su kan su masu aikin marasa nauyin barci sun farka, zuwa falo Amna tayi lokacin Ruki ma ta sauko, "wai shi wannan har yanzu yana anan?" Cewar Amna a zuciya domin ita tama manta da abinda tayi, afili kuwa tambayar Hajiya tayi, "Hajiya what's wrong?" Harara Ruki ta aikawa Safna ta matso kusa da Hajiyan ta ce, "Hajiya me yasa ki ihu haka? Me marwan yake haka kuma?" Sai lokacin Hajiya tayi magana da cewa, "auta na wan ki yahaukace na shiga uku" tayi maganar cikin tashin hankali, "Hajiya haukacewa fa" cewar Ruki tana ya mutsa fiska domin bata ɗauki maganar Hajiya a gaskiya ba.
Marwan kuwa bama ya jin abinda suke cewa, shi dai ya cika sharaɗin mutanen ɓoye kawai, Hajiya da Ruki ne keta ƙoƙarin hana sa abinda yake amma sun kasa, Amna ce ta ce, "hakan na iya faruwa da wasu mutane, ƙila kiɗima ne yayi masa yawa, Hajiya wani a cikin ku ya lapka mai mari zai dawo hankalin sa" kallon ta Ruki tayi itama ta ce, "keh har ke wace daza kice mu mare..." "a ah Ruki yanayin da yake ciki zaki duba, ba nuna ƙiyayya a kaina ba" Amna ta katse abunda take son cewa da faɗin haka.
Ƙaramin tsaki Ruki ta ja kafin nan Hajiya taje gaban sa, kamar yadda Amna ta ce Hajiya tayi, amma Marwan bai bar abinda yake ba, itama Ruki tayi na ta nan ma haka, "bari ni na gwada" Amna ta faɗi haka tana zuwa gurin Marwan, da gewa tayi ta watsa masa mari lafiyayye, mutumin ku da yaji saukar mari a kumatun sa kamar wuta, ai baisan lokacin da yayi zaman 'yan bori ba, gaba ɗaya hannayen sa ya sa a fiskar sa, domin ya kasa tan-tance gefen da akayi masa aika-aikan, mummurzawa kawai yake kansa a ƙasa, domin yadda idanuwan sa suke gane masa duhu-duhu.
"Kun gani ko? Nawa ne ya shige sa" ta faɗi hakan, su kuwa durƙusa kansa kansa sukayi, jijjiga shi Hajiya ta farayi sai da ya ɗau mintuna kafin idon sa ya fara washewa, a hankali ya ɗago idon yana ganin su Hajiya kamar wanda bai san su ba, yayinda dukkan su suke ta ambatan sunan sa. Amna kuwa wucewa tayi ta ƙyale su domin barci ne a idon ta sosai. Da ƙyar Hajiya da Ruki suka samu nasarar jan sa zuwa ɗakin sa, mutumin ku yana samun gado ya la fe akai, barin ɗakin su kayi suna tinanin abinda yasa shi hakan.
WASHE GARI.
Amna na idar da sallah ta fita daga ɗakin Ammu, zuwa falon tayi ta jisa shiru, "har yanzu barci suke wato, babu mai tashi yayi sallah" ta faɗi cikin ranta, komawa ɗakin tayi ta kuma ɗauko kofin nan na jiya, hayewa matattakala tayi saboda sake zuwa ɗakin Marwan, shiga ɗakin da ta samu a buɗe tayi, tana shiga ta fara zare ido tana kallon haɗuwar ɗakin, Ruki ta gani a kwance bayan ta ƙarasa shiga kuma ta samu fitila a kunne.
"Lallai! Yanzu wannan yarinyar ma anƙa wata mata ɗaki amma su Ammu aka bar musu na su kamar a jeji, lallai!" Ta faɗi a zuciyar ta tana fita, gefen hannun damar ta tayi, can ma ta samu wasu ɗakuna a jere guda huɗu, "wato samar ma ɗakuna ne birjik kenan?" Tayi wa kanta tambayar, bata tsaya jira ba ta shiga guda ɗaya a ciki, "wato su a buɗe suke barin ɗakunan su kenan? Harda fitila ma Hahh" ta faɗi tana shiga ɗakin, tako yi sa'a na Marwan ɗin ne, nanma taga ɗakin ba ƙaramin haɗuwa yayi ba.
Barin kallon ɗakin tayi tana yin sanɗa zuwa bayan kujerar ɗakin ba tare da tsoron komai ba, kallon sa tayi yadda yayi shame-shame akan gado da kayan jiya, waigawa tayi dan neman abinda zata buga mai dan ya tashi, dan ta san yadda yake wannan barcin idan tayi magana bazai tashi ba, pillown dake kan kujerar ta ɗauka ta wulla kansa tare da saurin yin ƙasa dan ɓoyewa.
Shi kuwa jin anwulla mishi abu kansa yasa shi tashi firgigit, dai dai lokacin da Amna ta fara yi masa magana sigar muryar aljanu, hakan yasashi shiga situation irin na jiya, "Mu zaka karyawa alƙawarii? Kaƙi ƙarasa tsallen kwaɗon da muka sa kaa?" Kan ta kamo wata maganar ya fashe da kuka yana faɗin, "Wallahi ba laifina bane na rantse muku, Hajiya ce ta katse ni ina cikin yi".
"Wannan ba matsalar mu banee" ganin ƙofar a wangale ne yasa shi tunanin ya fe ce kawai domin tsira da ransa, wannan wani irin masifa ne? Ace duk ƙoƙarin da yayi jiya basu gani ba? Suka ƙara biyo shi da safe? Amma fa ƙafafuwan sa ba ƙaramin tsami sukai masa ba, ba ma ya jin zai iya taka ƙasa dassu, to amma fa idan yatsaya yasan babu makawa aljanu zasu hukunta shi.
Wani irin dauriya ne ya tsatso daga jikin sa domin idonsa na gani bazai tsaya aljanu suyi ram da shi ba, a hankali ya sauka daga gadon, wani irin gudu da yayi kai kace ansa guragu gasar tse re, dariya Amna ta kwashe dashi domin taga yadda ya zura da gudu, amma sai ta bar dariyar tana fita dan saurin komawa ɗakin Ammu, can gefen hagu na saman ta ganshi yana ta dagewa da gudun sa, ganin ba kowa ne yasa ta saurin bin hanya ta sauko daga upstair tana yin sashin Ammu.
Tana isa ta kulle ƙofar ta fara dariyar da bata samu damar yi ba, har tana kama ciki saboda yadda take ƙyal-ƙyalewa.
Marwan babu inda ya tsaya sai ɗakin Hajiya, fa ɗawa yayi ciki yana rafkawa Hajiya kira, "kai me haka zaka fa ɗo min ɗaki da sanyin safiyar nan Babu neman izini?" Ta faɗi bayan ta tashi, ni kuwa nace ta manta da hakan ɗabi'ar su ce ƙila.
Zama saman kujerar ɗakin ta yayi yana sauke nishi kamar wanda ya kwana yana gudu, jin bai bata amsar ba ne yasa ta tashi tana kallon sa yanzuma kamar jiya kokuwa tace ya fi jiya yanayin da ta ganshi, zama gefen sa tayi tana ƙa re masa kallo ta ce, "Marwan me ya faru kuma?" Cikin muryar fitar nishin yadda zuciyar sa yake a tsinke ya fara magana.
"Aljanun jiya ne, suka kuma zuwar, mini yanzu, saboda ban ƙarasa frog jump ɗin da suka sani ba, Hajiya dan Allah a kira masu ruƙiyya su zo gidan nan inba haka ba wallahi aljanun nan baza su rabu da ni ba" ya faɗi yana sharɓar hawaye, hakan yasa itama ta fara yarda da maganar sa, har tsoro ta fara ji tana waigawa bayan ta, "Marwan da gaske kake?" "Wallahi kuwa Hajiya".
#Amna sannu da aiki 😃 saura na gaba.
____________________________________________________________________________________________
Part 7️⃣1️⃣▶️7️⃣2️⃣
Shirye-shiryen dawowar Alhaji ake gadan-gadan domin ya faɗa musu a gida zaiyi la'asar, masu aiki kowa aikin sa yake, Amna kuwa tana ɗaki ta zauna sai sharara wa Ammu surutu take, da badon Ammu bata da lafiya ba da tabbas yau tasha dariya, amma duk da haka ta sha murmushi, wanda har haƙoran ta suka ɗan bayyana, wani irin ihu Amna ta saki lokacin da taga haƙoran Ammu waje, "Ammu haƙoran ki sun fito, laa, hakan na nufin kin fara samun sauƙi, domin tun da nazo dai banga hakan ba" ta yi maganar cike da nuna murna, itama karan-kanta Ammun taji daɗin hakan.
Gurin ƙarfe uku na yamma Alhaji ya iso gida, da murna da kewa su Hajiya suka tarbe shi, zama su kayi a falo suna ɗan taɓa hira, juyawa Dady yayi gun Saleem ya ce, "kai tun da na tafi ka kasa tuntuɓata ko sau ɗaya, baka damu da ni bane ko?" "No Dad aiki ne yayi min yawa" "wani aikin kai da ko office ba ka zuwa?" Cewar Ruki tana harar sa, cikin haushi ya ce, "be careful with me wallahi, 'yar iyayi kawai waya tambaye ki?".
"To ba gaskiya ta faɗa bane? Kaida ko a gidan nan yaushe rabon ka da ka zauna? Ka fita da sassafe kana dawowa kuma ka shiga ɗaki sai barci, bare ayi maganar zuwa aiki" fiska a haɗe ya ce, "Hajiya to kunsan abinda nake fita yi ne, ba duk aikin bane?", Dady ne ya fara magana, "ya'isa! Dama kai baka maida aikin ka a bakin komai ba, abunda mutane da dama ke nema, amma kai ka samu amma Kana sakaci dashi".
"Toh Dady me zan yi da wani sana'a? Kana da kuɗi fa, koda dukkan mu zamu zauna ba tareda da aiki ba, nasan har mu tsufa muna cin wanda ka tara" Saleem ya faɗi hakan, murmushin takaici Dady yayi daga bisani ya ce, "who told you that? Idan zaka mayar da hankalin ka gwara kayi hakan, ka cire wannan tunanin a ranka" tura baki Saleem yayi, yayin da Alhaji kuma ya maida kallon sa gun Hajiya yana cewa, "ina Marwan kuma?" Ta amsa masa da, "ban sani ba kam amma nasan bazai daɗe ba, sanin ka dawo".
Maida kansa ya kuma yi gun Ruki ya ce, "where is my daughter?" Ya mutsa fiska Ruki da Saleem suka yi domin sun san Safna yake tambaya, a yamutse Ruki ta ce, "tana ɗakin su" "call her for me" ya kuma faɗi, Hajiya kuwa da kallo kawai ta bisa.
Badon taso ba taje dan kiran ta, "ana kiran ki a falo" kawai ta faɗi tana juyawa bayan ta shiga ɗakin su Ammu, "Zan sauke miki abinda ke maƙale a cikin kankin nan" cewar Amna tana tashi dan fita, ba tare da ta ɗaura himar ko gyale a saman riga da zanin da ta sanya yau ba, domin tun da tazo bata taɓa sanya riga da zani ba, sai dai da skirt ko kuwa doguwan riga da basu da yawa a ciki, kuma duk sanda zata sanya to fa sai ta ja tsaki.
Gyara ɗankwalin ta tayi tana ficewa, karka so kaga tafiyar Amna cikin zani, domin kuwa yadda zanin gefe ɗaya yai tsawo ɗaya kuma gajere, bayan kuwa sai nannaɗewa yake yana yin sama, tafiya kam kar ayi maganar sa.
Tana isa falo ta tsaya tana bin Dady da kallo haɗida yin wani tunanin can, ta ji hayaniyar dawowar sa amma bata fito ba sai yanzu, katse mata tunanin yayi da faɗin, "ya kika tsaya can 'yata? Taho mana" ya faɗi duk da yayi mamakin ganin ta haka, abinda bai taɓa gani ba, tahowa a hankali tayi tare da samun wuri ta zauna kan kujera, ba tareda an bata umarnin hakan ba.
"Sannu sananna baza ki iya zama a ƙasa ba sai a kan kujera? Gaki hamshaƙiya ko?" Cewar Hajiya tana kallon Amna kallon tsana kamar kullum, Dady ne ya ce, "rabu da ita, me a ciki dan ta zauna, ba ga Auta da Saleem ma suna kai ba?" Shiru kawai Hajiya tayi dan ta san shi, dama koda yaushe haka yake nunawa Safna kula, wanda ta yi ƙoƙarin hana hakan amma batayi nasara ba, da tana ganin ta rabu da alaƙaƙai da ta tura Safna wata duniyar, ko da ya dawo ma ta samu ƙaryar da zata shafa masa, amma sai ga shegiyar ta dawo.
"Welcome back Alhaji ya hanya?" Cewar Amna cikin girmamawa, "Thank you my daughter, but why you call me Alhaji? Dady kike kirana right?" Saurin cewa tayi, "oh sorry Dady, banji daɗi bane, shiyasa bana gane abubuwa sosai" "is okay, hope dai now your ok?" "Of course Dady I'm alright" tayi maganar tana wani jin banbaraƙwoi kiran sa Dady da tayi.
"Fine, akwai maganar da nake son yi dake" "ok I'm listing" cewar Amna, yayin da su Hajiya kuma suka tsura masa ido, duk da Hajiya bata gama gane abinda ya faɗa ba, Ruki dake kusa da ita ne ta fiskanci haka, shi yasa ta kuma matsawa kusa da ita tana mata magana ƙasa-ƙasa, "Hajiya Dady cewa fa yayi akwai maganar da yake son yi da ita" zaro ido kaɗan Hajiya tayi, Allah dai yasa ba maganar kamfani zai yi da Safna yanzu ba.
"Daad! Har yanzu kana falo baka huta ba?" Marwan ya faɗi haka bayan ya shigo cikin falon, haɗi da samun guri ya zauna, idon sa kan Amna, sai dai ko kallon banza bai mata ba, itama binsa tayi da kallo, "matsoracin banza" ta faɗi cikin zuciya tana ƙunshe dariyar ta.
Murmushi kawai Dady yayi masa ba tareda ya amsa ba, ya cigaba da yi wa Amna magana, "kin karɓi takardun kammala Universityn ki?" Shiru tayi tana yin gefe da idon ta domin batasan gaskiyar ba, nan ta fara kame-kame ta rasa me zata ce, kar tace ta amsa ya zama ba haka ba.
"Idan baki amsa ba to ki samu ki anso nan da kwana biyar, domin zaki fara aiki a company" ba Amna kaɗai ba hatta Hajiya da 'ya'yan ta suka haɗa baki gurin faɗin, "eehh!" Saboda mamakin da kowannen su yayi, amma fa ko wanne a cikin su mamakin sa daban, kallon su yayi dukkan su, sannan ya kuma maida kansa ga Amna ya ce, "kece zaki jagoranci M.D company a yanz..." kan ya ƙarisa suka sake katseshi, Hajiya da eehh! Sauran kuma da whaat! wannan karon Amna bata ciki.
"Dady me kake cewa ne?" Cewar Saleem Ruki ma ta ce, "Dady kana nufin wannan ce zata jagorancin big company?" Hajiya kuma ta ce, "haba dai Alhaji taya zakayi saurin yin wannan hukunci haka? Ya kamata ka dai yi tinani zai fi" Amna kuwa ko motsi ƙaƙƙarfa ba tayi jin wai ita zata jagoranci babban company wata sabuwa.
Ba tare da Dady ya basu amsa ba Marwan ya miƙe tsaye cikin haushi ya fara cewa, "haba Dady what's wrong with you wai? Akan me zaka ce wannan shegi..." ya faɗi yana nuna Amna da yatsa, lokaci ɗaya kuma ya dakata, kallon yatsar da ya nuna mata yayi, sannan ya kalle ta, sai kuma ya saki murmushin dole tare da saukar da yatsan sa, saboda tuno da abinda ya faru jiya da yayi.
Komawa yayi ya zauna su Hajiya kuwa kallon sa kawai suke, ya yunƙura yana magana amma kuma sai yayi shiru, amma fa basuyi tunanin yanayin da ya fara yin maganar wa mahafin sa ba daidai bane, "'my daughter you can go" Cewar