Showing 66001 words to 69000 words out of 129098 words
Chapter 23 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
sace Ammu, kuma sunce baza su sake su ba har sai na bi umarnin su idan ba haka ba zasu kashe su, shine sanadiyyar zuwana gidan nan, kuma gashi tunda na iso gidan nan ko saƙo basu turomin ba, Ammu ina matuƙar ƙaunar ahali na bana son abinda zai taɓa lafiyar su ko ya yake kuwa, anyiwa mahaifina ƙazafi bayan ya amsa kiran Mahaliccin sa, inada burin yin bincike dan gano mugayen da suka aikata masa haka, amma yanzu duk bani da wannan damar, saboda kasancewa ta anan, amma dan Allah karkiyi tunanin nazo ne domin wata mummunar manufa kinji?"
Amna ta faɗi tana kallon Ammu fiskar ta cike da damuwa, sai dai ƙolla bai fita ba, miƙa mata hannu Ammu tayi da ƙyar alamar ta matso, bata ƙi ba domin matsawan tayi, rungume ta Ammu tayi tana zubar da ƙolla, itama Amna bada haɗin kai tayi gurin rungumar ta, saboda ji tayi kamar mahaifiyar ta ta runguma.
BAYAN LA'ASAR.
Amna ce tsaye a harabar gida tana kallon ko ina a gidan, da kuma yin nazarin labarin Safna da Raheena ta bata da safe, sannan kuma da tinanin yadda zata ɓullowa su Hajiya, ana haka sai ga Marwan ya shigo da motar sa, ko kallon inda yake batayi ba tana cigaba da tinanin da takeyi.
Tsayawa yayi yana kallon Safna yau babu hijabi ko kuwa wani ƙaton mayafi, "Ashe dai tana da kyau" ya faɗi ƙasan leɓen sa, ɗayar zuciyar sa tace masa, "dama tana da kyau kawai dai tsanar da kayi mata ne ya hanaka ganin hakan" a fili ya ce, "Hakane kuma fa" tahowa yayi gaban ta yana ƙare mata kallo up and down, "keh!" Ya furta bayan ya matso kusa da ita kuma ko da gefen ido bata juya kan sa ba.
Juyowa tayi tana kallon sa ba tareda ta amsa ba, "ni kike kallo haka? To maza kizo muje ɗaki na akwai kayana kala biyu ki wanke min" ya faɗi yana kafe ta da wani kallo, "wato kaine mesa Safna tsallen kwaɗo guda dubu ko? Ta kanka zan fara, to amma fa M.R ya gargaɗeni da yin haka, koda yake ma to taya zai san nayi shi ba aljani ba, dan haka maganin mutanen nan zanyi hankali kwance, ba sunce wai Safna ta dawo da aljani ba? To zan tabbatar musu da haka" duk da zuciyar ta take maganar.
"Toh Marwan muje" ta furta, har ya yunƙura zai tafi sai kuma ya dakata jin ta ambaci sunan sa gatsai.
Yanzu wasan zai fara.
______________________________________________________________________________________________
Part 6️⃣7️⃣▶️6️⃣8️⃣
"To muje Marwan" ta furta, har ya yunƙura zai tafi sai kuma ya dakata jin ta ambaci sunan shi gatsai.
Sai dai yana juyawa yaga wayam babu Amna, zaro ido yayi ya fara waige-waige, "yanzun nan fa take nan, to ina ta shige?" Yayi tambayar wa kansa yana juyawa amma baiga ko alamar ta ba, nan yafara ambatan sunan ta amma shiru, da sauri yabar wurin yana yin hanyar shiga ciki.
Tarar da ƙofa yayi a rufe, yana nuckin sau ɗaya Amna ta buɗe ƙofar, tsayawa yayi yana kallon ta da tinanin wani abun daban, "keh ba yanzu nagan ki a waje ba? Ya akayi kika kasance a nan kuma?" Yayi mata tambayar, cikin mamaki ta fara yin magana a hankali kamar Safna ta ce, "ni kuma? Nida nake zaune a falo, rabona da waje ai tun da safe".
Fiddo Ido yayi fiye da na ɗazu cikin ruɗani, "keh karki rainamin wayo ni sa'arki ne shegiya?" ya kuma faɗa, "zakaga shegiya!" Cewar Amna a zuciya à fili kuwa tace, "to me amfanin yi maka ƙarya? Ni babu inda naje" "zo muje ɗaki in baki kaya na ki wanke min, da toh ta amsa masa yana tafe tana binsa baya, yana cikin tafiya yaji ankira sunan shi cikin muryar fitar iska.
Da sauri ya juya, yanzu ma yaga wayam bayan sa babu Amna, rikicewa yayi yafara dube-dube, "kai, kai! No yarinyar nan ne take raina min hankali kawai, dan haka bari naje na same ta" yana faɗi ya juya zuwa falo, bai same ta ba ya kuma fita waje nan ma bata nan.
Hajiya da ta sauko daga upstair ne taga yaron ta a wani irin yanayi, zuwa kusa dashi tayi ta fara cewa, "kai Marwan ina ka tsaya ne wai? Ina can ina jiran ka amma sai zuwa nayi na sameka a falo, ya naga kana wani zuru-zuru da idanu kamar wani ɓarawo?" "Haba Hajiya! Keda zaki tambaye ni menene silar kasan cewa na haka amma kike wasu zantuka daban".
"To yo ba tambayar na ka nayi ba? Sai ka bani amsa" "hmm Hajiya ina faɗa miki yarinyar nan ne ta dawo aljana" "ehh! Wace yarinyar?" "Hajiya wa zan kira shegiya idan ba wahalalliyar nan ba? Shigowa na fa nagan ta har nayi mata magana a waje, amma ina juyawa sai naga babu ita, koda nazo falo sai na ganta, nanma da nace tazo inbata kaya na tayi min wanki nan ma ta ɓace bangan ta ba" saida Hajiya ta ja tsaki sannan ta ce, "wani irin magana kake cewa ne? Kuma wani kayan zata wanke maka bayan jiyan nan kasa aka wanke maka?".
"Haba Hajiya ba ƙarya nayi ba fa" Hajiya ta kuma cewa, "Alhaji zai dawo gobe, shiyasa nake son magana da kai, ba wai maganar shirme ba, shiyasa nake son Yazeed, da shine da tini yazo babu jinkiri, ya kusa dawo wa in huta, ina jiran ka yanzu" tana gama maganar ta wuce, shi kuwa haushi ne ya cika shi, jin maganar da tayi kan Yazeed, ita Hajiya baza ta taɓa daina nuna banbanci tsakanin sa da Yazeed ba, duk abinda zai mata kuwa.
Da kallo ya bi Hajiya har ta haye sama sannan ya sauke kai ƙasa, abinda ya faru ɗazu ne ya dawo masa, nufan side ɗin su Ammu yayi dan yin maganin ta kan abinda tayi masa, "wannan renin wayo ne ai, ni zata yiwa wasa da hankali?" Ya faɗi a cikin ran sa.
Tunda ya girma zai iya cewa bai taɓa zuwa ɗakin da Ammu take ba, koda kuwa ace taɓa ƙofar ne, sai yau, tura ƙofar yayi ya shiga yana wani yamutsa fiska shi nan ɗakin bai masa ba, sai dai a mamakin sa sai ganin Amna yayi kwance kan gado, kuma kayan dake jikin ta ba na ɗazu bane. A razane ya juya dan fita, sai da yayi gore da ƙofa sannan ya wuce, sai tura wuya yake kamar raƙumi saboda saurin da yake yi, yana tinanin kodai gamo yayi da aljani ne? Kuma yake ɗaukar masa siffan Safna?.
Bai koma ɗakin sa ba gurin Hajiya ya nufa, à can ya samu Ruki, tattaunawa suka farayi akan dawowar Dady gobe, duk da dai shi kam hankalin sa ba'a tattare dashi yake ba.
Amna kuwa Marwan n'a fita daga ɗakin ta tashi ta fara dariya, domin taji ƙarar goren da yayi, ɗaga Ammu dake gefen ta kwance tayi tana ci gaba da darawar ta, "Ammu mutumin ya rikice fa" ta faɗi bayan ta zaunar da Ammu, yayinda ita kuwa Ammu babu abinda take yi illa binta da ido, domin bata san me tayi ba, waye ya shigo ma bata sani ba, tunda kanta gefe yake, kawai dai Amna kwantar da ita tayi, tace mata wai tayi kamar tana barci.
Tsayar da dariyar da take tayi da faɗin, "na manta ashe ban faɗa miki ba, Ammu kin san me nayi? A ah koh? Ba su Hajiya ɗazu sunce wai 'yarki ta dawo da sheɗanu ba? To shine nake son na nuna musu hakan" mayar da kanta gefe tayi ta kuma cewa, "a hankali zanyi maganin su dukkan su, shine na fara a kansa" murmushi kawai Ammu ta yi mata, domin taga yarinyar ta cika wauta. "Zan rama muku duk abinda suka aikata muku ke da 'yarki, sai sun kasa ko harara idan suka ganku, duk da cewa ban taɓa ganin 'yarki ba sai a hoto amma ta birgeni da ƙawarta taban labarin ta".
Ta faɗi tana sakin murmushi bayan ta dawo da kanta ga Ammu, sai kuma ta bar murmushin da take tana ƙara cewa, "amma fa ta ban takaici sosai, yaushe zata tsaya ana zaginta ko kuwa duka, cab wallahi inda ace nice a matsayin ta ko? Sai na musu abinda bazasu taɓa yiwa ko dabba haka ba bare ɗan Adam" tayi maganar tana cizan yatsa.
Kallon ƙwarin guiwar da yarinyar take dashi take, tunowa da ɗaga kujerar da Amna tayi ɗazu tayi ɗazu tayi, a ɗazun tayi mamaki sosai, domin wannan kujeran yana da matuƙar nauyi, domin katakon sa na da ne, da badon haka bama da ya daɗe da zagonyewa, kujerar da ake kama-kama kan a gusar dashi gefe shine ita ta ɗaga shi har ya kife, abinda ko shara Safna zatayi a wurin sai dai ta share gefensa domin bata ma koda gwada matsar dashi. Tabbas yarinyar tana da abin mamaki, dukda tanajin wani yanayi idan tana kallon Amnan, wanda take ji tun ranar da tazo, amma a lokacin sai ta ɗauka kawai dai dan 'yarta ta koyo wasu ɗabi'u ne.
"Ammu ya kamata kema inbaki labari na koda kuwa kaɗan ne" Amna ta katse Ammu da zancen zucin da take, "ni sunana Amina mahaifina yamin laƙabi da (Amna) ina da kaka mace mahaifiyar Babana Mamma, sai mahaifina da kuma mahaifiyata mu biyu kaɗai mahaifan mu suka samu ni da ɗan uwa na Mubarak, ni bansan wasu mutane a matsayin 'yan uwan mu ba sai wannan ahalin, kum..." kan ta ƙarisa burin ƙoilarta dake drawer yayi ƙara, da sauri taje ta ɗauko shi ba tareda ta tsinke ba, yayin da Ammu ke mamakin yadda wani lokaci take magana ko numfashi ba ta tsayawa yi.
Ɗagawa da hello tayi, amsa mata yayi sannan yace, "na kiraki ne dan insanar miki abinda za kiyi a gaba" ta ce, "toh M R amma baka tambayi lafiyata ba ko kuwa kaji ya Na kasance cikin gidan" murmushi a can gefen yayi ba tareda ta san yayi hakan ba ya cigaba da cewa, "gobe alhaji Jamilu zai dawo daga ƙasar instambul, dan haka abinda zakiyi shine, muna da buƙatar kisa masa ido sosai, duk wani motsinsa ya kasance kin sanshi".
"Zanyi ƙoƙarin hakan..." "ba ƙoƙari ba yi zakiyi da gaske" ta ce, "insha Allah, yasu Mamma suke? Dan Allah inason inji muryar su koda kaɗan ne" ya amsa mata, "ba jin muryar su kaɗai ba, har ganin su zakiyi, amma ba yanzu ba" yana faɗi ya kashe waya.
Jiki a sanyaye ta koma kan gado ta zauna, tana mai jin tsananin kewar su, "dole inyi dik yadda zanyi saboda ku dawo gare ni" ta faɗi cikin zuciyar ta, ta ba Ammu tausayi hakan yasa tayi ƙoƙarin ɗaga hannunta zuwa kafaɗar Amna.
DA DARE.
Laɓewa tayi tana ganin lokacin da Marwan yayi parking ɗin motar sa, duba agogon wayar ta dake hannun ta tayi, ƙarfe goma sha biyu da 'yan mintuna na dare, "musamman naƙi yin barci saboda kai, ɗan iska zanyi maganin ka yau, ba ni zaka cewa in biyo ka ka bani kayan ka na wanke ma bah? Alhalin ƙarya ne baka da wasu kaya masu datti, wato kai ga ka ka samu banza ko?" Ta faɗi a ƙasar bakin ta harda ƙofa, saboda taji lokacinda Hajiya tayi masa maganar an wanke masa kaya.
Saurin zuwa falo tayi ta nufi bayan kujera mai uku ta ɓoye a bayan sa, haɗida ɗaga kofin robar da ta samu ɗakin Ammu tana sawa a bakin ta, tare da jiran sanda zai shigo.
Marwan kuwa shigowa yayi kansa tsaye kamar kullum, saida ya garƙame ƙofa yana juyowa ya fara jin wani irin sauti a kunnuwan sa kaɗan-kaɗan, sai dai burus da hakan yayi dan ya ɗauka kunnen sa ne kawai ya ja jiɓo masa, sanya ƙafa yayi yana cigaba da tafiyar da yake, saidai ya dakata da hakan, ya kuma ƙame ƙam, yayin da jikin sa ya fara yi masa na mazari, idanuwar nan sai wuwwulasu yake kai ka ce ɓerar da mage ta titsiye, sakamakon jin sautin da yayi yanzu da ƙarfi, kuma na ban tsoro.
Magana Amna ta fara yi masa cikin wannan kofin ta irin wata murya da tayi ƙoƙarin sarrafawa ta ce, "Marwaaan ka aikata mana babbar laifi, shiyasa muke bibiyar ka cikin siffar mace" maganar yayi amsa-kuwa cikin falon, sakamakon kofin da ke bakin ta. Shi kuwa ba ƙaramin rikicewa ya ƙara yi ba, jin muryar Aljani haiƙan cikin kunnuwan sa, kuma ya rasa ta ina yake jin hakan, sannan kuma wai ya musu laifi, cab ɗi, aro jarumta yayi yana yin tafiya a hankali zai wuce, ƙarar faɗuwar kolban flowern da yaji acan gefen ne yasa shi ƙara dakatawa, cikin tsoro ya juya yana kallon inda kolbar ta fashe.
Amna da ta faɗo da abun sanadiyyar igiyar da ta haɗa da jikin kolban ce ta fara magana cikin muryar ɗazu tana cewa, "hahhh kai bil'adama mu zakawa wayo? To karka manta mu ba jinsun ku bane, idan ka ɓata mana rai zamuyi rawa a kanka, ta yadda za'a shafe tarihin ka gaba ɗaya" sai da ya saki wayar hannun sa ta faɗi ƙasa, saboda tsaban tsoro, raga-raga wayar tayi, baki da jiki na rawa ya fara magana fiska kamar zaiyi kuka, "no-no-no-no kuyi haƙuri kar kuyi rawa a kaina, ku yafe min".
Sai da Amna ta kusa yin dariya saboda yadda yayi maganar, "yadda yake tafiya cikin isa duk a banza, ashe mashahurin matsoraci ne" ta faɗi a zuciyar ta a fili kuwa ta ce, "mata kaiii uku kake da kafin muyi tinanin haƙiƙanin hukuncin da za mu aikata makaa, kuma idan har ka kuskure ɗaya a ciki, to fa taka ta ƙare, domin aika ka zamuyi can wata duniyar aljanun" tayi masa maganar cikin ƙatuwar murya saɓanin wanda tayi masa ɗazu.
"Na shiga uku! Wallahi aljanin ba ɗaya bane" cewar Marwan a zuci, sannan ya ce, "na tuba zanbi duka matakan" ta amsa mishi da, "da ka huta kuwaa, number one" sai kuma tayi shiru domin ganin shi da tayi ta saƙon kujeran alamar mamaki jin tace number one, "kaaii ba abun mamaki bane dan munyi yaren turawaa, saboda aljanu babu inda basa zuwaa, dan hakkaa, saurari abin da zance".
Natsuwa yayi sosai dan sauraron abinda jinnu zai faɗi, "na ɗayaa, zaka fara yin alƙawarin bazaka sake yiwa waccan yarinyar da kuka maida mara galihuu, koda kuwa kallon banza nee, ita da mahaifiyar taa, na biyuu, fiskar ka zakayi ta tafkawa mari har sai munce ya'isaa, na ukuu, zakayi tsallen kwaɗo guda dubu biyuu" muƙut Marwan ya haɗiye nyawun na banu bayan Amna ta tsaya da maganar ta.
Tsawa ta daka masa cikin ƙatuwar muryar da tayi masa ta ce, "baza kayi banee?" "I will wallahi I will, nayi alƙawarin daga yau bazan ƙara yiwa shegiyar yarin..." "shegiyaa?" Ta ƙara daka mai Tsawa kan ya ƙarisa, "no Safna bazan ƙara yiwa Safna kallon banza ba bare wani magana mara daɗi nayi alƙawari" ya faɗi cikin rawar murya da sauri, harda hawayen sa. "To idan ka karya wannan alƙawarin kuwa, zaka ga yadda zamuyi da kai, Kama ka zamuyi mu cukur-kuɗa ka, sai mun mayar da kai ƙwallo" ta kuma faɗin haka.
#Hhhhhh su Marwan saura na gaba.
______________________________________________________________________________________________
Part 6️⃣9️⃣▶️7️⃣0️⃣
"Hakan baza ta faru ba ma" ya faɗi cikin rawar murya, magana ta cigaba da yi masa cikin muryar da ta fara yi masa da fa ri, "kai ka sani kumaa, muje abu na gaba". Hannun sa yasa ya fara marin kan, ganin yadda yayi marin a hankali ne yasa ta cewa, "ƙaramin yaro akace ka mara ne ko ko ƙato? Ashe baka yarda da maganar mu ba kenan?" Ai bai bari ta ƙarasa ba ya fara marin fiskar sa da ƙarfi, yana rintse ido saboda yadda zafi ke ziyar tan sa.
Sai da ya ɗau minti kusan ashirin sannan ta tsaida shi, fiskar nan tsamo-tsamo da hawaye, "Ashe idan mutum ya mari kansa haka zaiji zafi?" Tambayar da yayiwa kan sa kenan, amma ya samu amsa ai, tunda ya riga da yaji hakan.
"Yauwaa to maza muje na ƙarshe, tsallen kwaɗo guda dubu biyu, kuma masu kyau ba aikin jeka na yika ba, sannan idan ka kuskure ka tsaya koda sau ɗaya ne to fa zaka dawo baya" "na roƙe ku kuyi haƙuri ku ragemin frog jump ɗin nan, ina laifin nayi ko sau goma, amma idan har nayi sau two thousand to wallahi ƙafafuwa na bushewa zasuyi, kudube ni da idon rahama" ya faɗi bayan jin maganar aljanu cikin muryar kuka.
Sake jan ɗaya igiyar tayi, hakan yasa wata kwalbar flowers ɗin faɗi, saurin durƙusawa yayi fitsari na shirin kufce mishi saboda tsaban tsoro, da'alama dai ya ƙara ɓatawa aljanun nan rai, tunda gashi sun kuma fasa wata kwalbar, "wayyo na shiga uku, kuyi min rai wallahi zanyi, yanzunnan ma" yana faɗi ya fara tsallen kwaɗo da sauri da sauri, yayinda Amna kuwa take dariyar ta ciki-ciki, yi yake yana irgawa har yayi guda hamsin da ɗoriya.
Bacci take ji sosai yanzu, dan haka sai tayi masa magana cikin ɗayar ƙatuwar muryar ta ce, "ya naga ka fara yi a hankaliii? So kake ka dawo baya kenaan?" "A ah wallahi zan cigaba dayi da sauri" Marwan da ya gaji sosai ya faɗi hakan yana kuka, "to kaci gaba da yi har sai ka kai adadin da muka cee" "toh-toh" ya faɗi yana cigaba da yi da kuma ci gaba