Showing 75001 words to 78000 words out of 129098 words
Chapter 26 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
musu, "saida na tabbatar da masu aiki sun kammala kai musu abincin dining, naje na buɗe gaba ɗaya kulolin na zuzzuba maganin sa zawon da na siya ɗazu a hanyar dawowar mu ni da ƙawar Safna, kafin su zo harna bar wurin, shine fa bayan sun zauna nima nazo da niyyar zama suka hanani, saboda tsabar ƙiyayyar da suke wa Safna basu san ni kawai zuwa nayi dan neman tsokana ba, amma na so ace Alhajin nan bai ci ba, saboda shi mutumin kirki ne, amma dai ba matsala tunda kaɗan ya ci duk shima zai ɗan ji jiki, yauwa ina faɗa miki Ammu bayan sun gama ci suna miƙewa dan barin wurin magani ya fara aiki, to dama shi maganin sha yanzu magani yanzu ne, sai kinji yadda kowa ke sakin ta sa tusar"
Tsayawa da maganar tayi tana dariya ta kuma cewa cikin dariya "suna can kowa na fama da jikin sa" Ammu kallon ta kawai take yi, da zata samu dama da itama ta yi dariya sosai yau, taso ace abun a gaban ta ya faru, lokacin da take ƙarama itama ba ta ɗaukar reni ko kaɗan idan anyi mata abu bata cika haƙuri ba, domin ko zaman da sukayi da Hajiya à baya kafin ko mai ya sauya, to fa ba ta lamuntar abinda Hajiyar zatayi mata, nuna mata take ba ta jin tsoron ta, hakan yasa a baya Hajiya ba ta yin mata abu a gaban idon ta, kuma yazo mijin ta ne babba, amma yanzu da taga ba ta da kataɓus sai take yi mata duk abinda take so, Safna kuwa halin Mai daraja ta ɗauko, à halin mahaifin ta kaɗan ne t'a baro.
Buɗe bakin ta tayi ta fara yiwa Amna murmushi haɗi da ɗaura hannun ta a kan ta.
#MU HAƊU A NEXT PART IN ALLAH YA KAIMU GOBE. DON JIN YADDA SU HAJIYA ZASU ƘARE DA MUGUNTAR DA AMNA TAYI MUSU.
ALƘALAMIN TAKU HAR KULLUM... KU ƘARASA MIN😊
____________________________________________________________________________________________
Part 7️⃣5️⃣▶️7️⃣6️⃣
Tsaye gaba ɗayan su suke à falo inka ɗauke Amna da bata cikin su, fiskokin su harya rame saboda zawayin da sukayi babu ƙaƙƙautawa, fiskar Dady ne mai ɗan dama-dama da kuma Marwan amma sauran kam ba'a magana, bare ma Ruki yadda idon ta suka firfito waje domin tsayuwar m'a ta kasa yinsa, zama tayi a ƙasan kapet ɗin falon.
Dady ne ya ɗago agogon dake hannun sa yana kallon time ƙarfe biyu na dare, lallai wato awanni suka shafe suna fama da cutar bayan gida kenan?
Mai da hannun n'a sa yayi yana kallon ko wannen su, sannan ya ce, "what is the reason for this happening? Taya za'a ce abu irin wannan ya faru da mutane dayawa haka?" "Dady That's what I was thinking too" "anya ba tsinannun 'yan aikin nan bane suka sanya mana wani abu a cikin abinci? Saboda n'a tabbatar da cin sa ne ya sanya mana lalacewar ciki" Cewar Ruki hakan yasa gaba ɗayan su suka shiga nazarin maganar na ta, Hajiya da har yanzu take jin cikin ta ba'a daidai ba ta ce, "a ah bana tunanin zasu yi hakan, wa'yanda ba sa ƙaunar kalmar kora? Daga ka furta zasu fara roƙe-roƙe, kaga kuwa ai basa yi abinda zai sa akore sun ba"
"A koi wanda nake zargi" cewar Saleem yana kallon su duka, "kai banason shashanci, wa kai kuma kake zargi?" Faɗin Dady tare da kafe sa da ido, "Safna!" Saleem ya bada amsa, "what are you saying?" "Yes Dady zata iya aikata hakan, saboda tun da ta..." Hajiya tayi saurin rufe bakin Ruki daga ƙarashe maganar, ta san cewa zatayi tun da Safna ta dawo daga yawon ta, shi kuma Alhaji ya tambayi wani yawon?, daganan kuma magana ya dawo wani zancen daban.
"Ya kika rufe mata baki?" Alhaji ya faɗi hakan, Hajiya ta ce, "Alhaji na rufe mata baki ne saboda nima akwai tunanin da nayi" "wani tunani?" "Maganar yaron nan da kwai ƙamshin gaskiya fa, tabbas na san yarinyar nan ta ci abincin, idan kuwa hakan ya faru, to ya kamata itama cikin ta ya dame kamar na mu, dan haka muje mu duba mu gani, idan har ya kasance babu abinda ya same ta to itace tayi mana hakan, idan itama ya faru da ita tofa daga masu aiki ne, sai mu bincike su".
Dady ya ce "Akan me zaku sa tinanin nan à kan ku? Safna baza ta taɓa yin makaman cin hakan ba" "Dady muje mu tabbatar kawai" cewar Saleem, domin ɗazu bayan ya fito daga toilet ya fito ya tsaya a step yana kallon falon ba tare da ya sauko ba, riƙe ƙarfen yayi da ɗayar hannun sa ɗaya kuma a cikin sa, a nan ne ya hangi Amna kamar tana cikin annashuwa, hakan ya ɗar sa masa kokonto a ran sa, duk da dai yasan Safna ba tada mugun hali amma tun da ta dawo yake karo da ita cikin wani yanayi, hakan yasa bai yarda da ita ba.
Nufan hanyar da zai sa da su daga ɗakin su kayi, Hajiya na roƙon Allah yasa Safnan ce ta aikata musu haka, ai kuwa da yau sai ta tantance kiɗi da karatu a hannun ta, Dady kuwa ba don yaso ba yabi su, domin ya san 'yar sa Safna baza ta aikata kotan-kocin hakan ba, haka har suka isa ƙofar, Ruki ce gaba zata buɗe ƙofar, amma kanta sa hannu dan bude ɗakin suka fara jin sautin ƙaran ta.
"Waai wai ciki na, wayyo zan mutu, ciwo" abinda su kaji Amna na cewa kenan, cikin tashin hankali Dady ya shige ɗakin yana nufan inda take can gefe a durƙushe, ta riƙe cikin ta tana ci gaba ƙara, suma sauran shigowa su kayi cikin rashin kulawa suke kallon ta, Marwan ne kaɗai bai mata wannan kallon ba, "yata kema cikin n'a ki ne ke ciwo?" Cikin nuna bata san hakan ya faru da su ba, ta ce, "Ddady kumma hakan ya same ku ne?" Tayi maganar da muryar da ke nuna ba ta daidai.
"Saleem jeka ɗaki ka ɗauko akwatin neman agaji da sauri" cewar Dady ba tare da ya dube sa ba, haɗe fiska yayi jin wai shi ne wanda zai ɗauko akwatin neman agaji, kuma Safna za'a wa aiki da shi, ko motsi daga inda yake baiyi ba ya ce,
"Dady forget her, muma babu abinda muka sha, kuma ba munji sauƙi ba?" "Tinanin hakan ne bai zo muku ba" cewar Amna ƙasar leɓe, "kinyi magana 'yata?" Faɗin Dady jin kamar yaji sautin fitar magana daga bakin ta, rintse ido tayi tana ci gaba da matse cikinta daga bisani ta ce, "Dady cewa nayi cikina ya fara lafawa" "da gaske?" Ya faɗi yana ɗan sake fiska, ya kuma juyawa gun Saleem ya ce, "jeka mana".
Sai da Saleem ya ja tsakin sa ciki-ciki kan ya wuce, Ruki sai tattamuƙe fiska take, Marwan da Hajiya kuma suna kallon Amna, yayin da Hajiyar ke ji ina ma zata samu hanyar rabuwa da yarinyar nan, ai da ta huta.
Miƙa mata magani Dady yayi bayan Saleem ya kawo akwatin, amsa tayi tana kallon sa a zuciyar ta ta ce, "mutumin nan yana da kirki sosai, amma me dalilin da yasa M.R ya ce in sanya masa ido?" A fili ta ce, "ba damuwa Dady akwai ruwa a nan zan sha dashi" cewar ta cikin muryar shan wahala daga raɗaɗi, dan taga alamun kamar so suke ta sha a gaban su, to ita da babu abinda yake damunta kuma me zatayi da magani?.
Fita su kayi suna komawa falo, ita kuwa tana jin takun su ya tsagaita ta kuma fitowa tana sanɗa, gashi idan tana sanɗa baza kaji alama ko kaɗan ba, da dabara take aikata komai.
"You see? Nasan 'yata baza tayi haka ba, tana da tarbiyya" "Alhaji ya kamata kasan Safna fa ba 'yarka bace, domin ina ganin kamar kana mantawa, taya zaka ba taa yarda haka? Wani lokaci kamar kana nuna kafi sonta akan wa'yan da ka haifa da cikin ka" Hajiya ta faɗi hakan don hakan ba ƙaramin sosa mata rai yake ba, samun guri Dady yayi ya zauna kan kujera, wani irin murmushi ya saki yana bin Hajiya da kallo yana cewa.
"Idan ba 'yata bace 'yar waye ne? Ita ce kaɗai 'ya ga yaya na Mai daraja, a yanzu kuma baya nan, to idan ban ba ta kulawa ba waye zai mata hakan? Ko tana da wanda zata ɗauka matsayin uba bayan ni?" Shiru Hajiya tayi ba tare da ta kuma magana ba, "hakan na nuna cikin masu aikin nan ne aka samu wanda ya aikata, dan haka tomorrow a taramin su inyi magana da su" cewar Dady, nan kowa yayi hanyar makwancin.
Jin jina kai Amna tayi jin maganar da Dady ya faɗa, nan girman sa ya ƙaru à idon ta, da alama mutumin babu abinda yake a ransa sai taimako, komawa ɗakin Ammu tayi tana zama gefen gado haɗi da sauke ajiyar zuciya, "wato su in anbarsu wannan dabara ce koh? Azo a tarda ni à ɗaki don agane ko nice n'a zuba magani" Ta faɗi tana sakin dariya, sai kuma ta tashi don cire kayan basajar ta.
WASHE GARI.
Bayan Dady yasa an tara masa masu aikin girki, nan ya fara tuhumar su, jikin kowacce a cikin su kyarma yake yi, sai rantse-rantse suke, Amna kuwa ganin ana shirin ɗaurawa wasu laifin da tayi ne yasa ta zuwa wurin ta gaishe da Dady, amsawa yayi tare da tambayar ta ya jiki? Ta amsa mishi da yayi mata sauƙi sosai, sannan ta ɗora da cewa.
"Dady ina ganin da kayi haƙuri ka rabu da su, tun da hakan bai taɓa faruwa ba, ta yu sunyi amfani da kayan dafa abincin da gurɓatacce à ciki, saboda wani lokaci yin amfani da abunda ya fara ɓaci ko kuwa rashin wakewa da kyau yana iya haddasa makaman cin haka, me zai hana baza'a yafe musu ba? Inyaso sai à gargaɗe su na gaba" jin jina kai yayi da maganar da ta sanar dashi ya gamsu, amma à gefe ɗaya kuma abinda ba ta taɓa yi masa bane tayi masa yau, wato ta kalleshi ido da ido tayi magana da shi, ba tare da rusunar da kai ba, da kuma nuna kunya. Sai dai bai damu da hakan ba.
Sallamar su yayi daidai saukowar Hajiya daga step, "Alhaji taya zaka sallame su da wuri haka? Ba tare da an hukun ta su kan abinda ya faru ba?" Ƙarar wayar da akayi masa yasa shi tashi ya bar wurin bai ba ta amsa ba, da kallo Amna ta bishi, "me yasa baya son amsa waya à cikin mutane?" Tayiwa kanta tambayar, sannan ta juyo da kallon ta kan Hajiyar da itama da kallo ta bi shi, "Hajiya antashi lafiya?" Da à rashin lafiya kika ganni?" Cewar Hajiya harda harara, "Allah ya baki haƙuri" Amna ta faɗi itama ta wuce.
Amna yatsan ta 'yar manuniya take bubbugawa gefen goshin ta tana tunanin abinda zata aikata a gaba, ƙyafta yatsun tayi tana murmushi haɗi da furta, "iihiiiim" wato dai ta samu idea.
Saleem na zaune kan kujerar garden yana shan iska haɗi da latsa wayar sa, yaso ya fita amma Dady ya hanashi hakan ya sashi zuwa yana chat da budurwar sa, feshin ruwa kawai yaji a jikin sa, saurin miƙewa yayi yana neman ta inda wannan ruwan ya taho amma baiga alama ba, taya hakan zai faru? Ya tambayi kansa, ƙarar shigowar masage ɗin da budurwar shi ta tura masa ne yasa shi komawa ya zauna yana karan tawa, Amna da ke laɓe cikin flower ta fara magana irin muryar da tayiwa Marwan.
"Kaaiiii ƙaramin ɗan tatuuul!" Ƙara miƙewa yayi take jikin sa ya hau kyarma, "maza ka rufe idaniyar kaaa" bai bari Amna ta kammala ba ya rintse idon sa ƙam, "idan ka kuskura ka buɗe don ka gammu to tabbas zaka makan ce" "bazan buɗe ba na rantse" "Ashe shi wannan mata maza ne, gwara Marwan ya ɗan fi sa dake wa, koda yake shi babba ne" cewar ta a zuciya, a hankali ta zo ta bayan sa ta daure mai ido, nan ta fara wawwanka masa maruka a fiska, tare da faɗin, "idan ka ƙara yiwa Safna wani abun to tabbas zaka yankawa kanka kazan tashin hankali".
rantsuwa ya fara yi, yana faɗin bazan ƙara ba tare da sakin kukan tausayi, domin ji yake kamar ana zuba masa wuta a fiskar, ihu ya cigaba da yi yana faɗin, "wallahi bazan ƙara yin ko magana da ita ba bare na faɗi wani abun" ihu yake sosai hakan ya jawo hankalin mutane, aka taru ana kallon sa har su Hajiya suka fito, bai tsaya da kukan da yake yi ba, kuma babu kowa a wurin, dan shi baiji cewa an daina marin sa ba.
Cire masa farin ƙyallen da aka rufe mai ido da shi Hajiya tayi, ganin sunyi masa magana amma yaƙi yin shiru, bere su sa ran zai sanar da su abinda ya same shi, sai da Alhaji yayi masa wawan girgiza kafin hankalin sa ya dawo jikin sa, kallon su yake tare da dakatawa da kukan da yake, rungume Dady yayi yana faɗin "Dady wallahi da alhjanu à gidan nan" ya faɗi yana kyarmar tsoro, haƙoran suma sai kyarmar suke, dukda fiskar sa baƙa ce amma sai da tayi ja, har wani kumburi yayi".
"Me ya cize ka à fiska?" Dady yayi tambayar, a ruɗe yace Dady me fiskar tawa tayi? Na canza kama ne?" Sai kuma ya fashe da kuka, dan yasan wannan zafafan marukan da yasha ai dole ya canza kamanni, Marwan kuwa can gefe yake jikin sa na rawa kaɗan-kaɗan, tsoro ya fara shihgan sa, da alama dai mutanen ɓoyen nan ta kan Saleem suka biyo yau kuma. "Kowa ya koma yin abinda yake" cewar Hajiya wa masu aikin.
Amna ma tsaye take cikin su kamar bata san komai ba, "Dady wallahi aljanu ne, na ji maganar su" Saleem ya faɗi hakan, babu wanda ya yarda da maganar sa sosai illa Marwan, tunda shima hakan ya faru dashi. Kwantar masa da hankali sukayi sannan suka maida shi ɗaki don ya samu nutsuwa.
A jiyar zuciya kawai Dady yayi lokacin da suka zauna à falo, su uku Hajiya da shi sai kuma Amnan, kallon ta yayi yana faɗin, "me yasa baki sanar dani kin amsa takardun ba? Ni da nake buƙatar su dan fara gabatar da wani abun? Da nace miki kwana biyar a zato na abun zai yi wahala ne" sai da ta risinar da kai ta ce.
"Eh Dady tun da na karɓo ban samu damar haɗuwa da kai ba, naga kamar kana busy, shine nake son yi maka magana lokacin cin abincin dare, koda nazo kuma sai aka hanani zama" "waya hanaki zaman? Kenan da abun mahimmanci sosai ne na rasa shi kenan?"
Ya faɗi cikin ɓacin rai, shiru Amna tayi, ta gefen ido ta hangi Hajiya na zizzilla ido, "to daga yau tare zamu rinƙa cin abinci at any time" ya faɗi cikin nuna tabbatar da abinda ya ce, ganin haka yasa Hajiya cewa, "Alhaji kana baiwa yarinyar nan dama da yawa fa" "cin abinci daren ne dama? Abinda ya kamata tuntuni ana hakan?" Godiya kawai Amna tayi masa ta wuce ɗaki dan ta samu hutu.
____________________________________________________________________________________________
Part 7️⃣7️⃣▶️7️⃣8️⃣
Ɗaki su kayi ita da ƙawar ta, nan Hajiya ta kwashe abinda ke damunta ta sanar wa da Ladingo, "ƙawa ta kice kina cikin tsananin damuwa? To ina ganin ko zamu komawa boka mai tafasa ne?" Ladingo ta faɗi hakan cikin nunawa Hajiya ta damu da ita, jin hakan yasa Hajiya cewa, "ba shakka Ladingo! Da alama dai kin manta abun da bokan na ki yayi mini? Kuma kema fa kina da ta ki matsalar amma bai magance miki ba, dan haka ba na son wannan batu, babu ɗan iskan da zan sake ba Kuɗi na wallahi, yanzu da wa'yan nan kuɗin na nan da Allah ka ɗai yasan a muhallin da suke a halin da muke ciki yanzu, haka kurum?" "To yanzu dai Zainab ya kike so ayi?" .
"Kawai dai ki ban shawara ta yadda zan ɓullowa lamarin, tun kafin akai ni a baro, wallahi ni narasa kataɓus ɗin da zanyi, Alhaji ya tabbatar da Safna ce zata jagoranci wannan kamfanin, na san kuma bazai fasa ba, idan har na bari wannan abun ya faru to ba ƙaramin cin baya zanyi ba, sannan Yazeed yana dawowa shima zai bijiro min da maganar auren ta, akan hakan ta afku wallahi na gommace in ƙa re ƙarshen rayuwa ta a gurgunce kamar yadda nake faɗa ako da yaushe, gashi kece kika ban bahaguwar shawara akan na nuna masa ina bayan sa, yana can ɗin ma ya addabe ni da maganar ta to ina ga ya dawo? Da na biye ta tashi ma da tuni a cikin wayar tawa suke soyewar su, dan haka ni dai yanzu ki bani shawara mai kyau" Hajiya ta faɗi tana mai jin haushi cikin ran ta.
"Ita ba a taɓa ba ta shawara idan aka samu matsala sai ta ɗaurawa mutum laifi, amma baza ta iya aikata komai da kanta ba, dole sai ta tuntuɓe ni" Ladingo ta faɗi cikin zuciyar ta, a fili kuma sai da ta matso kusa da Hajiyan ta ce, "toh ƙawata idan har Safnan ta ce ba ta da buƙatar aikin fa?" "Yarinyar da ta riga ta amince da hakan, har ta kardunta ta damƙa masa fa" Ladingo ta kuma cewa, "Idan