Showing 108001 words to 111000 words out of 129098 words
Chapter 37 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
haka.
Kusan daidai suka dawo, sai dai Shuraim ne ya shiga da fari ka na daga baya ta shigo itama, tarar da Hajiya tayi a falo, har zata wuce sai kuma tazo ta zauna akan kujera tana faɗin, "barka da yamma Hajiya, ya hidimar biki da aka fara? Duk da ba'a samu a ciki ba" dariya mai haɗe da tsoro Hajiya tayi tana faɗin, "lafiya ƙalau Safna 'yar albarka, wai ai dama ana kammala komai sai a sanar da ku, amma ina mu ina ƙin sanar da ku?".
"Wow Hajiya, yau kin kirani da sunan albarka" cewar Amna tana ƙaramar dariya, "yo to Allah na tuba, duk abubuwan da nake faɗa miki da ɗin ma, ai saboda baki taɓa tambayata ma'anar su bane, amma ba masu ɗaci bane" "oh haka abun yake kenan?" "Ee wallahi!" Hajiya ta faɗi tana ƙarashewa da ya ƙe, "hmm ko wani surkulle za a haɗa ni dashi gobe in naje gurin boka? Sai nayi maganinki, da ni kike zancen, ba kin hanani sukuni ba?" Hajiya ta tambayi kan ta a rai, don gobe zata je gurin sabon malamin Ladingo, tare da jagorancin ita da kanta Ladingon.
"Toh Allah ya kyauta" Amna ta furta hakan haɗi da tashi tana taɓe fiska, ganin Hajiya na raina mata wayo, upstair ta nufa tun da yanzu sun koma 'yan sama, tana shiga haɗaɗɗen ɗakin ta tsaya kallo, kamar yau ne ta shigo sa, kallon abubuwa na alfarma ta keyi, har ta isa gaban Ammu dake zaune kan keken da Amna ta kawo mata sabo, mai ɗauke da na'urori a jikin sa, ijje jakar hannun ta tayi à ƙasa tana durƙusawa gurin Ammu, ta ce, "Ammu ina fatan kina samun farin ciki a cikin wannan ɗakin, don kin san ɗakin da Hajiya ta zauna dole shima zai ɗauki mugun halin ta, sai daga baya zai zama mai natsuwa kamar ke Ammu" ta ƙarshe maganar cikin raha.
Murmushi Ammu tayi mata, haƙiƙa wannan yarinyar alkhairi ce a wurinta, ina ma duk wannan canjin da aka samu Safna na nan, da tayi farinciki sosai, Amna ta ƙara cewa, "sannan ina fatan Jummala na kulamin da ke sosai?" Ammu ta amsa mata da ido, "yauwa haka nake so, domin ita da Hambali mai gadi ne kaɗai nake ganin suna da kirki cikin masu aikin nan, shiyasa na bata wannan aikin" ta faɗi tana wa Ammu murmushi, ta gane amsa mata da Ammu tayi, domin shi da murmushi ne take iya gane su yanzu.
Kuma cewa tayi, "Ammu ni na rasa a wani mataki nake, wannan MR ɗin ya bani aikin sawa Dady ido, amma banga abunda zansa masa idon da shi ba, dama zaki iya bani shawara akan abin da yakamata inyi da naji daɗi, saboda yakamata in samu mai bani shawar-wari" tayi maganar cikin damuwa, hannu Ammu ta ɗaura a kan hannun Amna da ke kan ƙafar ta, yanzu Ammu ba ta shan wahala kafinta ɗaga jikin ta sosai kamar baya, magan-ganu take yi wa Amna amma ba ta ganewa, kuma magan-ganu ne masu muhimmanci.
DARE.
Ɗaukar wayarta tayi tana kallon sa, kamar mai jiran kiran MR, sai kuma ta ɗau babban wayar, tayi dialling number Raheena, babu ɓata lokaci Raheena ta ɗaga, nan suka fara hira sosai gwanin sha'awa, domin a yanzu ita ce kaɗai a bokiyar hirar ta, "Raheena ina fa jiran ki goben in Allah ya kaimu, saboda ina son ya zama kina taimaka min a companyn nan, kuma kema kya samu ragin zaman gida ai ko?" "Insha Allah zan zo kamar yadda na ce miki, su Momy sun amince, duk da ni ina jin matsayin da kika bani yayi yawa, ina laifin ma ko ki bani mataimakiyar mai tarban baki na farko? Amma a ce zaki sa ni a makusantar office ɗin ki?".
Cewar Raheena, "sai kinzo kawai ina jiran ki" Amna ta faɗi da kashe wayar, murmushi Raheena tayi, wani lokaci tana ɗan ganin wani halin Amna kamar na Safnan, idan ba ta son wani magana sai ta katse shi da canza magana ko kuma tayi shiru.
Amna kuwa sauke wayar tayi tana tunani, ta dawo ɗakin nan ne musamman don ta sawa Dady idon, sai dai ita bata ga abun sa idon ba. "Ya fita ɗazu, na tabbata bai dawo ba, to ko naje ɗakin na sa nayi bincike ne?" Tayiwa kanta tambayar tana miƙewa don zuwa ɗakin na sa.
A hankali take tafiya tare da ankarewa har ta isa ƙofar, duk da cewa tana jin tsoron kar a ritsa ta, amma ta sa hannu don jin ko a buɗe yake, a buɗe ta tadda shi, a hankali ta shige ciki haɗi da tura ƙofar, ta shiga ɗakin ne ba tare da tasan abin da zata bincika ba. zuwa tayi ta buɗe walldrop ɗin sa, kaya ne kawai a ciki, nan ta fara dube-dube har hannun ta yakai kan wasu takardun files cikin drawern Dadyn.
Ciro su tayi ta fara dubawa, buɗe ɗaya tayi don taga na menene? Karanta rubutun saman ta farayi, "ya nake gani kamar takardun mallakar dukiyoyi?" Ta faɗi cikin mamaki, tana kuma sa idon ta don ta ƙarasa karantawa, sai dai kanta ƙara duba wani taji takun ƙafar mutum, da alama wannan ɗakin aka yo, don takun ta yi ƙara sosai, "Dady!!!" Ta furta a tsorace, tare da fiddo Ido tana miƙewa.
Ƙara jin takun tayi yana sake ƙaratowa sosai, "innalillahi wa inna ilaihi ya zan yi?" Ko ƙarasawa bata yi ba saboda tsoron da take ji, idan har Dady ya kamata cikin wannan ɗakin me zata ce masa? Dame zata kare kan ta? Bayan ga shi har files ta ɗauka, rasa abun da zatayi tayi, da sauri ta durƙusa, hannu na rawa na tsoro ta fara maida files ɗin cikin drawern.
Shigowa ɗakin Dady yayi kansa na kan wayar sa yana duba wani abu, sai kuma yayi saurin ɗago kan sa, fiskar sa alamar tsantsar mamakin abun da idon sa ya gane masa.
'Ƴan-uwa shin zuciyar ku ta ɗarsa muku wani abu akan kalaman da Shuraim yayi na cewa, yanzu ya tabbatar da haka? Domin kamar ya taɓa sanin ta.
Shin ko me Amna zata faɗawa Dady idan ya ganta?
Me zai faru?
___________________________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣0️⃣1️⃣▶️1️⃣0️⃣2️⃣
Shigowa ɗakin Dady yayi kansa na kan wayar sa yana duba wani abu, sai kuma yayi saurin ɗago kan sa, fiskar sa alamar tsantsar mamakin abun da idon sa ya gane masa.
Ɗayan wayar sa ne ya gani a ƙasa, sauke numfashi yayi yana faɗin, "ashe na faɗar da wayan ban sani ba" ya faɗi haɗi da ɗaga wayar ya maida ta kan gado, shi kuma ya wuce toilet.
Amna da ta ɓoye a bayan labule ne tayi saurin fitowa daga wurin, ganin Dadyn ya shige toilet, saɗaɗawa tayi tana fita kasancewar a buɗe ya bar ƙofar, nufan ɗaki tayi da sauri, tana shiga ta kulle ƙofar ta fara sauke numfashi, "oh rashin gaskiya dai baiyi ba wallahi, yanzu da ya kamani fa? Duk abun da ya zargeni da shi ya tabbata, ban isa in musa ba, tun da à ɗakin ya tadda ni tsamo-tsamo ba tare da sanin sa ba" ta faɗi tana kuma sauke a jiyar zuciya, da kuma tunanin yadda zata bar wannan bincikan na babu gaira babu dalili, sai dai amma tayi ta tunanin wannan file ɗin da ta fara karantawa, taso a ce ta gama karanta shi ko me nene abun da ya ƙunsa?.
WASHE GARI.
Bayan tayi shiri ta fito, a harabar gida ta tadda Dady da wani mutumi suna tattaunawa, kasancewar suna nesa da ita bata jiyo abun da suke cewa ba, har zata wuce sai kuma ta ga bai kamata ta wuce ba tare da ta yiwa Dady sallamar ta tafi aiki ba, tun da har ta ganshi, kuma shima ya ganta, duk da cewa gani take kamar ya san da zuwa ɗakinsa da tayi. Ƙarasawa inda suke tayi ta gaishe da Dady da kuma wanda suke magana da shi.
Sai dai wani irin kallo ta ga Wanda yake tare da Dadyn yayi mata, wanda bata gane na mamaki ko tsoro, ko kuma wani abun daban ba, da adawo lafiya Dady ya bita sannan ta wuce da tunanin ko ƙila wani abun mutumin yake saƙawa a ranshi.
COMPANY.
Tsayawa tayi tana kallon Shuraim da ke maƙale da waya a kunne, da alama cike da nishaɗi yake yin magana a wayar, tana iya gani gurin da tayi masa nushi jiya, gurin ya kumbura kaɗan, kuma yayi ja abunka da farar fata, ji tayi à ranta bata ji daɗi da ya kasance ita tayi masa hakan ba, ƙarisawa inda yake tayi, don ta bashi haƙuri, duk da cewa zuciyarta na hana ta yin hakan, zubar da ƙimarta ne ma ai, tun da shima ya ta ɗe ta ƙasa kuma taji zafi, amma kuma ai kamar shi fa Shuraim baya wani shakkanta ko kaɗan.
"eh masoyiyata, komai a nan yana tafiya dai dai, sai dai zan so ace kina kusa da ni, da nafi jin daɗin haka" abunda Amna taji ya faɗa kenan bayan ta ƙarisa inda yake, kuma wani abun ma da sanyin murya taji yayi maganar, wadda ita da kanta sai da taji wani iri cikin ranta, haɗe fiska tayi da tunanin ma da bata zo ba, ko da yake ai da budurwar sa yake wayar, then what?.
"Ok bye miss you more heart beat" ya kuma faɗi bayan ya juyo da duban sa kan Amna, ƙara haɗe fiska tayi ta juya don wucewa, ya tare ta da cewa, "madam C.E.O you want my help? Na ga kinzo wuri na" "ni na ce maka wurin ka nazo? That's may company, zan iya zagayawa inda naso" ta faɗi cikin haushi ta wuce office. Tana shiga ta zauna a kan kujera ta kwantar da kanta, yadda take idan tana jin ƙunci, ko tunani, shigowa yayi yana kuma faɗin.
"Madam C.E.O hope your alright?" Yayi maganar cikin nuna damuwa, don shi yayi tunani yayi ko akwai abun da ke damunta, "me ya dame ka idan ba a daidai nake ba? Just leave me alone!" "Okeyyy! Ko dai sauraye sun cize ki ne jiya? Suka sa miki haushin mutane? Ko da yake dama haka Safnah take, every time cikin fushi da mutane, na faɗi gaskiya?" Ya faɗi yana murmushi.
Haushi ya ƙara bata don haka ta ce, "ina ganin kai ne shugaban masu ƙa-ƙabe na London, kuma kayi karatu mai zurfi fannin iya baƙar magana" dariya ya kwashe da shi har da zama akan kujera yana faɗin, "kuma you know what?" "A ah" ta bashi amsa, "zauna to in faɗa miki" zaunawa tayi ba musu, tana sauraron sa, don tayi zaton zai bata tabbacin abin da ta faɗa ne, "nima fa ina mamakin da ya zama hakan", cewar Shuraim.
Cikin ƙara maida hankali ta ce, "wani mamaki?" "Mamaki da ya zama ki ka ce wai ina da baƙar magana, bayan ko shiga cikin mudun iya maganarki ma ban isa ba, ke ce fa C.E.O, kinga kuwa ke ce shugaba a ko wani fanni, harda baƙar magana, girman kai, ji ji da kai, da ma komai" "ohh! Hakane? Amma in tambayeka mana? Me yasa a gida kake nuna girman kai kamar wani sarki, ni kuma kake addabata?" Tayi maganar riƙe da ƙugu, "Oh girl, amma a baya kin ce ina da girman kai, amma yanzu kin nuna kamar ke ba na yi miki hakan" ya faɗi da murmushi.
Sai ya cigaba da cewa, "but still i will tell you why" kallon sa Amna kawai take sai taji ya ce, "saboda ke kamar mai bani nishaɗi ce that's why" haɗe gira tayi tare da buɗe baki, sannan ta ce, "kaaii! Ni ɗin ne mai baka nishaɗi? Wato ga babyn roba ko goi-goi ko?" Ta faɗi tare da tashi a kan kujerar don ƙarasowa inda yake, tsayawa tayi a gaban sa ta cigaba da zubo bala'i, "wato shiyasa kake min haka? Kuma ma ni ɗin, amma fa ka mai da ni ƙaramar yarinya" "to da ke ɗauka kike ke babba ce?".
Ƙara buɗe baki tayi irin ƙarawa kayi? "hiiiinn" ta faɗi da jan numfashi sama ta kuma cewa, "harda ƙarama ka maida ni kenan? Ta tabbata a babyn roba ka ɗauke ni, to aikuwa..." garin magana tana ciccilla hannu, kawai hannun ya hankaɗa wayar Shuraim da ya ijje a kan table ɗin ta.
Saurin durƙusawa tayi don taro shi kan ya kai ƙasa, yayinda shima Shuraim abin da yayi ƙoƙarin yi kenan ya tarosa kafin ya amsa kiran tayis. Hannun sa ƙasa na Amna sama ta samu damar tare wayar, sai dai hannun n'ata da ya haɗu da na Shuraim kawai sai taji shocking ya kamata, ko kuma ince dukkansu ma, hakan yasa Amna sakin wayan Shuraim ya kuma saurin tarboshi.
Miƙewa su kayi dukkansu Amna na nutsawa tunani, wannan abun kamar ya taɓa faruwa da ita, tabbas a kwai wanda hakan ya taɓa faruwa ita da shi, ƙarewa Shuraim kallo take sosai sannan ta furta, "kaima kaji shocking?" Bai amsa mata ba, ganin tana ƙoƙarin zurfafa tunani, shi kuma dama ba da niyyar zama ya shigo office ɗin ta ba, sakamakon akwai aikin da zai gudanar, ijje mata papern da ya ciro daga aljihunsa yayi, yana faɗin, "ga wannan kiyi nazari a kansa, and next don't forget, ki rinƙa sa maganin sauro kafin ki kwanta barci, na tafi ya kamata in ƙara jin muryar masoyiyata, tun da à ko da yaushe ba à buƙatar taimako na, kin ga sai inna rage lokaci gurin hira mai daɗi tare da ita" yana ida maganar ya fice yana murmushi.
wani irin haushi ya kuma cika ta, amma haushi mara dalili, "wato ina barin sa free har ya samu lokacin soyayya ko? Me ma yasa ba na sa shi aiki ne?" Zuciyarta ta bata amsa, "ke da bakinki kika ce ba kya buƙatar taimakonsa" sauke ajiyar zuciya mara dalili tayi, ta koma kan kujerar ta ta tana bin ƙofa da kallo. Lokacin massage ya shigo a na'ura, taɓawa tayi don jin saƙon, "madam akwai wacche ke son magana da ke sunanta Raheena" "she can enter" kawai ta basu amsa.
Sauke numfashi tayi tana cigaba da kallon ƙofa har Raheena ta shigo. Da mamaki ta ƙaraso inda Amna ta ke, tana faɗin, "besty ya naga kina min kallon biri da ayaba?" Tayi maganar sigar zolaya, Murmusawa Amna tayi, "wato kallon biri da ayaba nake miki? To waye birin wa kuma ayaban?" Itama ta faɗi cikin zolaya, "kece birin ni kuma ayaba, saboda na miki kyau sosai yau, shiyasa kike min kallon haka" faɗin Raheena, dariya suka saka, Raheena ta zo ta zauna Amna ta ɗora da faɗin, "to ba kyau kika min ba, mutumin nan ne ya ɓata min rai, ba shi da aiki sai yaga ya sa raina ya ɓaci" nan ta fara koraro da zantuka, wanda Raheena ba ta gane cikkaken ma'anar su, kasancewar da sauri take maganar.
"Wani mutum ne kike magana a kai ne?" Raheena tayi tambayar don tsaida Amna, sai a lokacin ta dubi Raheena da kyau irin mai shirin kawo labarun duniya ta ce, "kina shigowa kinga wani ya fice daga office ɗin nan ai" "Eh na ganshi wani kyakykyawa ba?" "Wannan ne kyakykyawa? Ko dai kina da matsalar ido ne?" Dariya Raheena tayi ganin yadda Amna tayi maganar ta ce, "ko dai ke ce mai matsalar idon ba".
Amna ta kuma cewa, "a ah ni garau nake, ni ban san me ne ne a kan sa ba, sai ya rinƙa yin abun da yaso, ko wace magana kawai faɗa min yake" "wait-wait-wait Amna, yi min bayani, kina magana da sauri" tsayawa tayi tana kallon Raheena, "ki daidaita natsuwar ki ƙawata, sai ki min bayanin abin da yake faruwa" daidaita natsuwarta tayi tana kallon Raheena, na ƙoƙarin zuba mata ruwan da ke cikin wani haɗaɗɗen glass cup mai haɗe da jug ɗin sa da ke wurin, miƙawa Amna tayi, ta kuma cewa.
"Faɗa min me yayi miki? Wace magana yake yi miki?" Kurɓar ruwan tayi sau ɗaya ta ijje kofin, sai dai itama baza ta iya faɗin ga takamamme abun da yasa ta jin wannan haushin ba, "just leave it, muyi magana akan aikin da zaki fara, zan baki komai da ya dace ki cika kafin fara aiki" Amna ta faɗi don share zancen, "ikon Allah, wannan sabuwar ƙawar tawa da ban mamaki take" Raheena ta faɗi tana dariya, Amna kuma na harararta.
HAJIYA.
Ladingo ta ce, "ƙawata wai me na sai kinje gurin malamin nan? Tin-tini na ce ki bar ni inje miki da kai na, ba girman ki bane, amma ki ka ce zaki je, kuma na faɗa miki aikin nan ba sai kin je da kan ki ba, zaki iya wakilta ni, don ni nama ɗauka zaki canza ra ayi yau" "kin ga Ladingo idan zaki kai ni to muje, haba har yaushe? Ce miki nayi ni da kai na zani, inga malamin ido da ido, sannan in tabbatar masa da ƙudurina, saboda gudun matsala, kuma ni kaɗai nasan irin abun da nake son in mata"
Ladingo rai bai soba don so take ta kuma samun rabonta, amma da'alama wannan karon hakan bazai samu ba, kallon Hajiyar tayi muryar banso haka ba ta ce, "to ai shikenan muje koh?" Hajiya ta ce, "yauwa to, muje driver na ne zai kai mu" "a ah ƙawata zai fi kyau dai mu shiga motar da ake zuwa ƙauyen da shi, don wallahi ƙauyen