Showing 51001 words to 54000 words out of 129098 words

Chapter 18 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

27

zaune take tayi ta gumi, ta rasa na kamawa sai hawaye take ta zubawa yayinda zuciyar ta ke nunamata fiskokin ahalin na ta, tana cikin wannan yanayin wayarta dake yadde waje yafara rurin neman agaji, kamar bazata tashi ba tafara tafiya zuwa inda wayar yake.

Kiran farko ya yanke kan ta ƙaraso a kira na biyu ta ɗaga wayar, baƙuwar number ta gani ba suna, karawa kawai tayi a kunnen ta ba tareda yin magana ba, dama indai numbern da ba suna ta kirata tofah ba ta magana har sai wanda yakira ɗin ya fara magana, idan kuma missed call ta tarar nanma ba ta kira har saisanda aka kuma kira.

"Fatan Amna ce ta ɗaga wayar?" Akayi mata tambaya daga cikin wayan, "yes is me" ta amsa cikin sassanyar murya, "mahaifiyar ki, kakarki, ɗan uwanki, duk suna hannun mu" mutumin da ya kira ya faɗi haka.

Hmmm suwa kuke tinanin sun kwamushe su Mamma? Koda dai ga maƙwamushin yayi magana to ko me dalilin sa nayin haka?

______________________________________________________________________________________________

Part 5️⃣3️⃣▶️5️⃣4️⃣

"Fatan Amna ce ta ɗaga wayar?" Akayi mata tambaya daga cikin wayan, "yes it's me" ta amsa cikin sassanyar murya, "mahaifiyar ki, kakarki, ɗan uwanki, duk suna hannun mu" mutumin da ya kira ya faɗi haka. Ƙolalo ido tayi sosai jin abinda ya faɗa, "ina suke, ina Ummee na ina Mamma ta ina Mubarak ɗina?" Ta faɗi har murya da jikinta na rawa.

Shiru yayi ba tareda ya bata amsa ba "hello hello" take furtawa haɗi da duban wayan ko tsinkewa yayi, ganin haryanzu mutumin na kan layi yasa ta ƙara cewa "ya kayi shiru? Me yasa kuka ɗaukan min family na? Nasan kune wa'ƴanda kukayiwa mahaifina sharri, kuma abinda yake faruwa a ƙasar mu kune sila, karku cutar min da ahalina, idan wani abu kuma ya samesu to nice ajalin ku, na rantse" tayi maganar tanajin ina ma mutumin na kusa da'ita da tayi masa wani irin sha ƙu a wuya, ta yadda sai yayi dana sanin aikata hakan.

Dariya mutumin yayi yana cewa "karsashinki ya burgeni yarinya, amma bazaiyi amfani anan ba, karki manta suna hannun mu ne fah, kuma duk ƙoƙarin da zakiyi dan ganin kin gano inda muke bazaki taɓa nasara ba, sannan koma dai menene kike tinani akan mu baidame mu ba, dan haka zaifi miki kyau ki da kata ki saurari abinda zance", huci kawai take fitarwa ba tare da tayi magana ba yace da ita.

"Ina da zaɓi guda biyu, kuma dolene ki zaɓi ɗaya daga cikinsu, na farko shine, dolenki ne ki amince kibi umarnin mu akan dukkanin abinda muka umurce ki da kiyi, idan ba haka ba kuma kinada zaɓi na biyu, shine ki tarar da gawawwakin ahalin ki, wanne kika zaɓa?" Cikin ruɗewa da abinda ya faɗi tace "please don't do anything to my family, sune rayuwata" tafaɗi tana matsar ƙwalla dan da'ayiwa ahalinta abu gwara ayi mata.

"Ba kida wannan matsalar dama zaɓi biyu kike da, dan haka choose first or second" "first" ta furta a taƙaice, "fine so now abinda zakiyi shine, kiyi wanka kici abinci ki sami hutu, ki samu cikakken nutsuwa zuwa anjima zan kira insanar dake abinda zakiyi" yana ida maganar ya kashe wayan, kallo tabi da wayan tana maijin ina ma duk wannan mafarki ne.

Kamar yadda yace mata wanka tayi sannan ta nemi ɗan abinda ta korawa cikin ta, amma ci tayi kamar wacce ke cin magani a ƙarshe ma dai sai barin abincin tayi, duk da rabonda cikinta ya ziyarci koda ruwa tun jiya before ta tafi school,

ƘARFE 11:00am.

Tana zaune ta ƙurawa waya ido, tana jiran kiran mutumin, saboda ta gwada kiran layin amma a kashe, kira ne ya shigo wayar hannu na rawa ta ɗauki wayar, sai dai ba mutumin bane wannan karon Nabila ce.

"Amna ya bakizo ba lafiya? Ina ce Zarah ta sanar dake Wali ya rasu, kuma har anshirya shi yanzu za'a kaishi makwancin sa na gaskiya, kakarsa da danginsa sai kuka suke bakiga ba" cewar Nabila cikin kuka bayan Amna ta ɗaga wayar, saida ta rintse ido sakamakon yadda maganar ta sosa mata zuciya tace "ta faɗamin, amma ina cikin wani irin hali ne da zuwan da ƙyar yayu" "wani irin hali? Me yafaru ina fatan dai ba cutar bace ta kama wasu a gida?" Ta tambaye ta tana sassauta kukan na ta, "ba shi bane amma kekam koma dai me zakiji daga baya, ki daina kuka ki roƙan masa samun rahamar ubangiji, shine abinda yake buƙata a halin yanzu kinji?".

Share hawaye Nabilan tayi tace "hakane Allah yajiƙan sa yasa Aljanna ce makomar sa" "ameen Allah ya kyautata makwancin sa, Allah ya yafe masa laifukan sa" takai ƙarshen maganar tana miƙewa, ɗauko Alqur'ani donta karanta ko zata samu mafita cikin wannan halin da take aciki, kuma ta ƙara ƙwa rara kanta, saboda ya kamata ta ƙarawa kanta juriya, tabbas saita ruguza wannan ƙungiyar kuma saita kawo ƙarshen mara imanin shugaban nan nasu, sai ya ɗanɗani irin azabar da yake yiwa al'umma, to ta yaya?.

Wayar tane ya fara ƙara hakan yasa ta samun aya ta tsaya tana saurin ɗauka, tun kan tayi magana mutumin ya fara cewa, "kizama cikin shiri ƙarfe 03:30 daidai ya kasance kina ƙofar gida, za'azo a ɗauke ki, kayan da zakisa suna cikin koren jaka a ɗakin ɗan uwanki, bayan kin sanya kayan ki goya jakar a bayanki, sannan babu buƙatar ɗaukar komi bayan waya da kuma key ɗin gidanku da zaki kulle, kuma babu buƙatar sanarwa maƙwabta ko wani na kusa dake, magana na ƙarshe kuma, ko sannu karya shiga tsakaninki da wanda zai ɗauko ki, karki manta ahalinki suna hannun mu".

Yana ida maganar nan ma ya kashe, babban ajiyar zuciya ta sauke tana nazarin wa'annan wasu irin bil'adama ne wai? Me suke buƙata agareta? Amma dai dolene tayi abinda sukace karta sa ɓa musu gudun wata matsalar.

__Ƙarfe uku ta riga da tayi duk wani shirin da suka sa ta, t-shirt fari ne me hoton mota a jiki, sai baƙar wando jins mai laushi tare da riga mai kama da na sanyi dogo wanda yakai guiwa shima baƙi amma ba mai tudu ko nauyi ba, nidai na kirashi da fation, sai takalma fari irin sau ciki masu ɗan tsawo kaɗan inaga sune ake kira boots ko? To koma dai mene irin wanda kuka hasaso amma masu kyau ne, sai gele mai laushi da ta yafa a saman kanta, fiskarta kuma tasa mask, ido ma yasamu baƙin glass, yadda ko wanda yasanta ne tofa bazai ganeta ba, amma fa tayi kyau, jakan da ta ciri kayan a ciki ne saƙale a ɓarin hannun ta na dama__

Tana rufe ɗakunan tana duba lokaci dama ta kintsa gidan ɗazu, 03:28 ta fito daga gidan tana garƙame ƙofan gida tana ankarewa kada wani ya ganta, to dayake ma babu mutane sosai a waje, tana kai ƙarshen murza key taji tsayawar baƙin mota a bayan ta, juyawa tayi ta dubi motar sannan ta duba wayarta ƙarfe 03:30 daidai kamar yadda sukace, "lallai wato su basa African time" ta faɗi a zuciyar ta, fitowa direban yayi yana buɗe mata mazaunin baya, saida ta bishi da kallon mamaki sannan ta shiga shikuma ya rufe ƙofar ya koma mazaunin sa.

Jan motan yayi bai tsaya ako ina ba sai a airport, "airport kuma? To mezanyi anan?" Shine tambayar da tayiwa kanta, guri ya samu ya tsaida motar sannan ya fito, koda ta sa hannun ta dan ta bude ƙofar itama ta fito sai taji shi a kulle, domin saida ya kulle yadda baza ta fito ba sannan ya wuce, hakan yasata gyara zama kawai tana ganin ikon Allah. Mutane basu dayawa a wurin sosai.

Mintuna da baifi shidda ba ya dawo, buɗe mata yayi ta fito yayi mata alama da ta biyo shi ba tareda magana ba, binsa take a baya harzuwa gurin jirgi, juyowa yayi gareta yayinda itama ta tsaya tana kallonsa, ansan ƙaramar waya mai madanni airtel ɗin daya miƙa mata tayi, yana kuma yi mata alama akan ta miƙa masa nata wayar, har zatayi masa magana akan taya zai bata ƙaramar waya yakuma ansa nata babba? Amma sai tayi shiru da tatina maganar wancan mutumin.

Miƙa masa wayar tayi ya ansa yana yi mata nuni da harda jakar bayan ta ma, shima ta cire ta miƙa masa, ma'aikatan jirgin ne mata biyu suka taho gurin ta suna yi mata maga da turanci suna cewa "ranki ya daɗe lokacin tashin jirgin ki ƙarfe huɗu ne kuma ya kusa, zaki iya shiga yanzu, dan Allah ki biyo mu" saida ta juya ta kalli direban da ya kawotan sannan ta bisu kamar yadda sukace ba tareda ta san wani garine zataje ba.

Jirgin yana nan kamar babu mutane sai 'yan ƙwaranni sabida yadda garin ya zama, domin wa'ƴanda suke ciki manya ne sosai wato masu kuɗi shiyasa suka samu jirgi domin anfara ƙoƙarin hana zirga-zirga a gaba ɗaya ƙasar saboda abinda yake faruwa, domin ko ina maganar ake.

Bai cika awa biyu ba jirgin ta isa garin Kaduna, bayan ta fita ne taji ana musu barka da shigowa garin Kaduna, hakan yasata mamaki to meyasa zasu kawota garin? To yanzu ya zatayi ma? Gata dai ta sauka a ciki to ina ta nufa... ƙarar kiran ƙaramar wayar ne ya katseta daga tinanin da take, tana sawa a kunnen ta yace.

"Your welcome, ki bar inda kike tsayen nan kiyo gaba, gefen inda ake parking ɗin motoci" ba tareda ya kashe wayar ba tazo inda yace, "akwai mota wanda ke kama da irin wanda kika hau ɗazu, ki maida kallonki ɓangaren hagunki" nanma tayi kamar yadda yace "eh na ganshi" "to kishiga cikinsa" da toh ta amsa ta nufi gurin motar, kan ta ƙarasa nanma direban ya buɗe mata mazaunin baya.

Shiga kawai tayi ba tare da sunyi magana ba, tafiya mai tsawo kaɗan sukayi, motar bai ijjeta ako inaba sai a ƙofar wani haɗaɗɗen gida, bayan matuƙin yayi parking a tsakiyar gidan ya fito ya buɗe mata ƙofa ta fito itama tare da bin gidan da kallo dan ya haɗu sosai, makulli kawai ya bata ya koma cikin motar yafita daga gidan, yana fita ya kulle gate ɗin da key, taji ƙarar rufewar da yayi amma bataji wani abu makamancin tsoroba.

Massage ne ya shigo wayar ta hakan ya sata shiga gurin saƙo "makullin da aka ba ki na ƙofar shiga ne je ki shiga" tafiya takeyi tana dube-dube har ta'isa ƙofar falo, key ɗin tasa tabuɗe ƙofan, a hankali ta tura ƙofar tana binbaya, "kaaiiii!" Batasan lokacin da bakin ta ya furta hakan ba, saboda yadda tsaruwar falon yake ba magana, nan ma batayiwa idanunta rowa ba dan hangamesu tayi suna wuwwulawa kota ina.

Tantara-tantaran ƙarar shigowar masage cikin burin ƙwailar da aka bata, "nasan ke jaruma ce, baza kiji tsoron kasancewar ki ke ɗaya acikin gidan nan ba, dan haka zaki zauna har izuwa lokacin da zamuje maudu'i na gaba, duk abinda kike buƙata akoi aciki, baza ki ƙara jina ba sai lokacin" saƙon da aka turo mata kenan.

"Amma family na fah?" Tayi saurin tura mai saƙon "suna cikin ƙoshin lafiya" tana karanta saƙon da ya maido mata sai ta tsinci kanta da yarda da maganar, bata tsaya jira ba tacigaba da ba idonta abinci, tana kewayawa gaba ɗaya kusurwar dake ciki, babu abinda babu hatta kaya akwai a walldrop, kayan abinci nau'ika daban-daban a kwai a ciki, sai wanda ta zaɓa.

Ta kwana ranar tana tinani, na familyn ta da kuma na mutuwar abokin ta da kuma lamarin da ya faru a gari. Kwana ɗaya kwana biyu, sati ɗaya sati biyu duk tayi a gidan ba tareda taji labarin kowa ba, ita kaɗai a cikin gidan sannan shi mai kiran ma bai kira ba, har gajiya tayi da hakan, dukda cewa gidan ya tara kayan alatu aciki amma bai sanyata jin daɗin kasancewa ciki ba, sabida kaɗaici, dukda akwai ƙaton plasma a ciki, wani lokaci ma a waje take wunin ta in kaɗaici ya mata yawa.

AFTER ONE MONTH.

A haka har wata ɗaya yayi, izuwa lokacin kuwa Nigeria ta matuƙar amsawa domin garuruwa goma sha shidda ne abun ya faru da su, amma yanzu komai ya ɗan fara daidaita kaɗan.

HAJIYA.

Tara masu aikinta tayi tana tambayar su wayene ke kula da Ammu? Domin ta lura da akwai wa'ƴanda suke kula da ita, tsawon watan nan yaci ace ta mutu saboda yunwa, kai ko sati mutum yayi baici abinci ba ai da ƙyar ya kai labari, bare ita har wata, kuma duk sanda zataje duba ko ta mutu sai ta tarar da ita ƙalau, to hakan yasa mata kokwanto cewa tabbas akwai mai kula da ita a bayan idon ta.

#Toh fah wata sabuwa, gadai Amna garin Kaduna, to ko meyasa wa'ennan mutanen suka kawota garin? Kuma menene maudu'in gaba?

Allah sarki Wali ma ya tafi, ku miƙo ta'aziyya in isar muku a wurin iyayensa da kuma abokansa🥺

Ga kuma Hajiya uwayen son duniya, ko zata gane wanda ke kula da Ammu acikin masu aikin? Dan nima nasan akoi a dila mai kula mana da Ammu cikinsu, dabadon haka ba da munji mummunar labari.

______________________________________________________________________________________________

Part 5️⃣5️⃣▶️5️⃣6️⃣

Masu aikin suna tsaye gabanta a jere kansu ƙasa yayinda Hajiya kuwa take binsu da kallon ƙas-ƙanci, sai tambayar su take kowa na ce mata bashi bane, "ba shakka, wato so kuke kumayar dani mara tinani ko? Ni zaku renawa hankali? Kowa da ya buɗe ruɓaɓɓen bakin sa sai yace ba shiba? To bara kuji idan har kuka sake na gano wanda yake kula da sheɗaniyar matar nan sai na hukunta shi kan na koreshi daga gidan nan, maza kuban wuri talakawan banza kawai maƙas-ƙanta" a hankali suka bar wurin, dukda basuji daɗin maganar da tayi musu ba, to ya suka iya? Ai talaucin ne yakawo su.

ƘAWAYEN AMNA.

Nabila da Zarah ne tsaye ƙofar gidan su Amna, Nabila tana cewa "tsawon lokacin nan muna zuwa ƙofar gidannan amma muna samunta a garƙame, kuma layin su baya shiga, daga Amna har Mubarak ɗin, wai meyake faruwa ne?" "Nima abinda yake ƙullemin kai kenan, saboda rashin zuwan Amna jana'izan Wali nasan ba banza ba" cewar Zarah, jinjina kai cikin damuwa Nabila tayi ka na tace "hakane kuma ranar da za'a kaishi makwancin sa na kira ta, sai dai maganar da ta faɗamin nasan tabbas da matsala, amma koda na tambayeta bata sanar dani abinda ke wakana ba".

Zarah tace "Allah dai yasa lafiya, yauma haka zamu koma kenan Nabila? Amma inada wani tinani, tunda muke zuwa fa bamu taɓa tambayar kowa ba, inaganin muje gidan maƙwoftan su Maman Abdul ko zamu samu wani information ɗin" "hakane to muje" cewar Nabila suna nufan gidan, bayan gaisuwa da sukayiwa matar suka zauna kan tabarmar da ta shimfiɗa musu.

Zarah tace, "Mu ƙawayen su Amna ne" "yauwa koda naji ganin fiskarku yamin kamar na sanku" cewar matar gidan tana tsaka-tsakiyar murmushi, wato dai sese-sese fiskar ta yake, Nabila tayi murmushi tace "eh ai zaku sanmu sosai ma, domin muntaɓa shigowa da Amna wani lokaci da aka aike ta" matar takuma cewa "hakka, to yanzu dai zan'iya sanin abinda ya kawo ku? Ko su Amnan ne suka aiko ku?" Kallon-kallo Zarah da Nabila sukayi jin tambayar da matar tayi, anya zasu samu abinda suke so kuwa?.

"A ah ba su bane suka aike mu, muma tambayar su muka zo yi, sabida lokuta da dama muna zuwa amma a rufe muke samun gidan" faɗin Nabila, "to gaskiya muma bama ce ba, amma dai iyayen tane suka fara ɓata, dan har ita Amnan na tazo neman su gidan nan, to daga bisani itama bamu ganta ba domin a kulle muka tadda gidan, kuma ko sallama batayi mana ba" abinda matar tace musu kenan, haka dai suka fito daga gidan suna tinanin abinyi, inma suka ce zasu sanarwa 'yan sanda to me zasu ce? Tunda suma basu da tabbacin abinda yafaru, addu'a kawai suka rufe bakin su dashi suka kama hanyar gida.

Uncle Tukur shima ana sa ɓangaren ya rasa abinyi akan ɓatan su Ummee, koda zuciyar sa tafi karkata akan wannan ƙungiyarce tasa cesu, ƙila so suke su kawo ƙarshen iyalan abokinsa, kashe shi ɗin da sukayi bai ishesu ba, idan kuwa hakane shima kansa yasan dole su nemeshi, saboda ya ba Baba gudunmawa sosai gurin bincike akan su, to kuwa shima baiga ta zama ba.

RAHEENA.

"Haba my daughter me yasa kike sawa ranki damuwa ne harhaka? Dube ki har kin rame fa!" Cewar Momyn Raheena haɗi da zama kan kujera gefen ɗiyarta ta, sai da Raheena ta sanya kanta a kafaɗar Momyn tace "Momy wallahi hankali na ya ƙi konciya akan rashin dawowar Safna duk sanda zanje sai Baba Hambali yace min bata dawo ba, zuciyata taƙi samun natsuwa" "ki daina sa muggan tinani cikin ranki, duk sanda zuciyar ki ta kawo miki wani mummunar tunani akan haka, ki kawar dashi da salati ga annabi, sannan ki yawai ta yi mata addu'a insha Allah 'yata Safna tana cikin ƙoshin lafiya" tayi mata maganar tana ɗaga kanta dake kafaɗar ta tare da faɗin "kinji koh?" "Insha Allah Momy".

AMNA.

Saman gado take zaune kanta jingine da katakon kan gadon, tana kallon sama kai ka ce irga silim ɗin ɗakin take amma inaa, nazari ne take tayi cikin ƙoƙwalwar ta domin a lissafin ta yaufa ta shafe one month a cikin shirun gidannan, tana cikin wannan yanayin wayarta dake gefen ta ya fara ruri, da waigawar ta da kuma ɗaukar wayar sai ka rasa waya riga wani tunda dama kiran take jira, kamar yadda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login