Showing 72001 words to 75000 words out of 129098 words
Chapter 25 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
Dady wa Amna, hakan yasa ta miƙewa ta nufi sashin Ammu, sakin dariyar da ta ƙunshe tayi, domin tasan Marwan ya dakata da maganar ne saboda abun da tayi masa jiya.
Dady kuwa gyara zama yayi yana kallon su da kyau sannan ya ce, "abun da nace haka za'ayi" sannan ya juya gun Hajiya ya ce, "Hajiya nasan kin san komai, dole ne Safna tayi aiki cikin wannan kamfanin, because a rubuce yake, so bai kamata hakan ya zama abin damuwa ba" yana faɗi ya miƙe ya wuce ɗakin sa.
Hajiya kuwa miƙewa tayi cike da takaici, Haka Marwan ma zarya ya fara yi a cikin falon, Ruki da Saleem kuwa sosa kai kawai su keyi cike da baƙin ciki a kan Safna, "Hajiya don Allah ki zaunar da Dady ki hana shi abinda yake son yin nan, tun yaushe nake tambayar sa ya maida ni ko manager a cikin wannan company amma yaƙi, and now one time yace wai Safna zata zama C.E.O na M D company? Impossible".
Hmm kawai Hajiya tayi ba tare da ta ce komai ba ta wuce ta haye sama, domin ita kaɗai ta san yadda zuciyar ta yake a halin yanzu, samun guri Marwan yayi ya zauna cike da damuwa, Saleem ne ya ce, "wai akan wani dalili ma Dad zai aikata haka?" "Nima tunanin da nake kenan, ni fa Dady bai taɓa min maganar zai sani aiki a company ba, amma sai gashi wannan mayyar zaisa ta jagoranci M D company" Ruki ta faɗi cike da damuwa, tana sake cewa, "wallahi ji nake kamar naje na shaƙeta ta mutu mu huta, duk ta hana kowa sakat".
"Ke ki daina kiran ta da wa'yan nan sunayen marasa daɗi" faɗin Marwan yana kallon Ruki, cikin mamaki ita da Saleem suke kallon sa jin abin da ya ce, "to akan me?" Cewar Ruki, Saleem ya ce, "ko kaima zaka dawo Yazeed ne?" Miƙewa yayi tare da jan tsaki yana ƙara cewa, "ni dai na faɗa muku, dan babu ruwana" ya faɗi yana wucewa, Kallon-kallo tsakanin Ruki da Saleem, kowa na tinani daban cikin konyar sa.
AMNA.
Zuwa tayi ta tasa Ammu gaba tana sanar da ita abinda Dady ya ce, murmushi Ammu tayi domin ta san lokacin hakan dama yayi, sai dai wannan she's not her daughter, amma tana roƙon Allah yasa komai ya tafi daidai, Amna cikin damuwa ta ce "to yanzu Ammu faɗamin what I'm doing now, wai shin Safna ta amshi ta kardun sakamakon jarabawar ta ma kuwa?" "A ah ba ta amsa ba".
Saurin juyawa ƙofa Amna tayi jin maganar da akayi ta wurin, miƙewa tayi tana washewa Raheena da ta gani baki haɗi da cewa, "Raheena ke ce? Your welcome ƙaraso" ta faɗi cikin murya kamar na rashin gaskiya, ba tare da ɓata lokaci ba Raheena ta ƙaraso tana zama gefen Ammu, "am besty karki ɗauki maganar da nake a wata sufa" cewar Amna dan kawar da tinanin da Raheena zata iya sawa a ranta, murmushin da bai gushe daga fiskar ta ba ta cigaba da yi ta ce, "na sani itama Ammu wasan kike mata ko?" "Hah yes-yes so nake na rinƙa ganin ta cikin farin ciki koda yaushe".
Ta faɗi tana ci gaba da dariyar ya ƙe. "Dama ke ɗin ta musamman ce, tabbas kina matuƙar ƙoƙari gurin saukar da haƙƙin ki na 'ya, ina roƙon Allah ya cigaba da baki lafiyan da zaki kula da ita, ya kuma kawo ƙarshen ciwon dake tattare da Ammu" cikin jin daɗin maganar Raheena ta zauna haɗi da kama hannun Raheenar tana faɗin, "ameen summa ameen, shiyasa kike burge ni, akwai ki da fahimta sosai" tayi maganar tana murmushi.
Murmushi mai sauti Raheenan tayi tana maida kan ta gurin Ammu ta gaishe ta, Ammu ta bata amsa da murmushi, "dama fa abinda ya kawo ni kenan ince miki gobe muje mu amso results ɗin mu, saboda nima kaina tun ranar da muka rabu dake ban ƙara zuwa ko gefen makarantar ba" cewar Raheena, Amna ta ce, "toh badamuwa Allah ya kaimu, da safe zamu je ne?" "Eh da safe, a nape zamuje koh? Ko kuma inzo mana da mota?".
"Ga mota kuma mu hau nape?" Cewar Amna cikin ran ta, a fili kuwa ta ce, "ki taho mana da mota dai" miƙewa Raheena tayi tana ƙara washe baki jin yau Safna ta ce zata hau mota saɓanin da, "dagaske? Da gaske kike besty? Yau zaki hau motar mu muje school da shi? Wow I'm so happy" mamakin abinda Raheena tace tayi, ganin kuma tana murna da hakan sosai, wato da Safna ce baza ta yarda ba kenan?
Raheena ta ƙara cewa, "shikenan gobe zan taho da shi amma karki canza shawara fa" "bazan canza ba" Amna ta faɗi tana murmushi, "yauwa! Keh naga Dady ya dawo, koba komai zaki samu sauƙin wani abun wurin su Hajiya yanzu" faɗin Raheena domin ta ji daɗin dawowar da Alhaji yayi don ƙawarta.
Ta kuma cewa, "to ni zan tafi Momy na jira na" "toh shikenan sai goben" "shikenan abun da zaki ce sai gobe?" "Toh akwai wani abin da zance ne?" 'Yar harara Raheena tayi mata ka na ta ce, "eh mana, da kina cewa in gaishe da Momy, amma yanzu baki faɗi hakan ba, jiya ma haka" sai da Amna tayi alamar mantuwa kafin ta ce, "na fa riga da na faɗi hakan a raina, kawai dai ban sanar da ke bane, amma ai bazan manta da Momyn ki ba" "Momy na?".
Bugan goshin ta tayi jin ta kuma kofsawa sannan ta ce, "no Momyn mu nake nufi, baki na ne kawai ke kuskure yau" bugan kafaɗar ta Raheena tayi tana dariya tayiwa Ammu sallama tana wucewa, sai kuma ta ƙara juyowa ta ce, "baza amin rakiya bane?" "Dole ma" Amna ta faɗi suka wuce suna dariya.
#Alhaji ya dawo, to ko yaushe Yazeed ma zai dawo?
Kuna ganin Amna zata yi wannan aikin? To idan zatayi ya zai kasan ce? zata ƙyale Marwan haka ta koma kan su Saleem ko kuwa?
____________________________________________________________________________________________
Part 7️⃣3️⃣▶️7️⃣4️⃣
Hajiya bata samu damar waya da mashawarciyar ta ba, saboda bawa Alhaji kulawa dan dawowar da yayi, ko ba haka ba ma maganar ai bazaiyu a waya ba, da so samune ma Ladingon tazo, to amma ta sanar da ita itama akoi abinda ke damunta, yaron ta babban ya ƙara aure amma matar ta fi ƙarfin ta, domin kuwa duk wata kuturɓar da ta haɗa ba ya aiki, gashi yaron yanzu kuɗi yake samu ba ƙarami ba.
WASHE GARI.
Gaba ɗayan su babu mai sukuni, kowa da maganar Alhaji ya kwana a ransa, musamman Hajiya da kuma Marwan, jiya Hajiya ke sanar wa da Yazeed hukuncin da Dadyn sa ya aiwatar, amma sai ce mata yayi, "Hajiya wannan ai tunani mai kyau ne, kinga ƙila hakan ya taimaka mata ta wani fanni..." katseshi tayi da faɗin, "da'alama har yanzu soyayyar yarinyar nan yana rufe maka ido ko? Idan ba rashin hankali ba ce maka akayi fa shugabar kamfanin zai bata ba wai ƙaramin matsayi ba, amma Kana min wani zantuka daban?" Dan haushi kashe wayar tayi ba tare da ta kuma sauraron zancen sa ba.
Amna batayi yunƙurin yi ma su Hajiya wani abu ba jiya, domin itama da kanta ba isashshen barcin tayi ba, kusan rabin kwana tayi itama da tinanin maganar Alhaji.
Kamar yadda Raheena ta sanar mata, gurin ƙarfe tara tazo da mota, da tinanin kada ƙawarta ta canza magana, amma hakan bai faru ba, ta fiya sukayi suna hira gwanin sha'awa, har suka isa makarantar.
Ko daga nesa ka hange makarantar ka san babu talaka da zai samu zarrar zuwa da sunan wai karatu, idan ba ya samu wata hanyar ba, domin yadda makarantar ta haɗu, A.A royal university, kai daga jin sunan sa ai kasan na 'ya'yan masu hannu da shuni ne, ba ƙaramin kallo Amna ta keyiwa wannan makarantar ba, saboda ko da wasa ba tajin ta taɓa ganin makaranta mai kyawun wannan, "wannan wai makaranta ne?" Ta faɗi a zuciyar ta, yanayin yadda Amnan take ne yasawa Raheena wani kokonto a ranta.
Hakan yasa tayi mata tambaya da cewa, "besty ya kike kallon makarantar kamar yaune mafarin shigan ki? Ko ya sauya miki ne?" Juyowa Amna tayi tana kallon ta, a ranta tana faɗin, "Amna ya kike haka ne? Ai ko gurin zinari za'a kaiki bai kamata ki yi abun da kikayi yanzu ba, haba ba sai a raina ki ba, bare kuma kinsan basaja kikeyi fa",
Ta ku gaba tayi ba tareda ta ba Raheena amsa ba, hakan yasa Raheena itama a ranta tana faɗin, "kar dai na taɓo 'yan Safnan da suke kanta, ta dawo kamar da, ni da nake murnan ƙawata ta canza" a fili kuwa tafiya tayi ta cin ma Amna tana murmushi ta ce, "kai besty ni fa ba maganar haushi na faɗa ba" "to ni cewa nayi kin yi maganar haushin?" Cewar Amna ba tare da ta kalli Raheena ba, "To me yasa kika yi min shiru?" Tsayawa Amna tayi ta juyo tana kallon ta yanzu fiska a haɗe, itama Raheenar tsayawa tayi tana kallon Amna.
"Matso in sanar da ke abinda yasa nayi shiru" faɗin Amna, matsowa rayi tana cewa, "faɗa min" jaƙul-ƙuli Amna ta fara yiwa Raheena haɗi da faɗin "shine wannan" da sauri Raheena tayi baya tana dariya kamar yadda Amna ma abinda take kenan, haka dai suka ƙarisa ciki.
Akan hanyar su ta dawowa bayan sun samu damar amsan dukkan takardun su, Amna ta hangi wani ƙaton chemist, umartan direban tayi da ya tsaya, tsayawa yayi kamar yadda tace Raheena na yi mata kallon mamaki, "kar dai kice baza ki ƙarasa gida a mota ba?" "Not that inason inje chemist ɗin can ne" "to amma what.." Amna bata bari ta ƙarasa ba ta buɗe ƙofar ta ce da ita, "akwai kuɗi a wurin ki?".
"Eh akwai" Raheena ta faɗi tare da buɗe hand back ɗinta ta, "kamar nawa kike so?" Ansan jakan hannun Raheenar kawai tayi tana faɗin, "ban sani ba amma bari na tafi da jakar duka, duk kuɗin da yaci shikenan, in mun koma gida inmayar miki".
Tana faɗi ta wuce, zuwa tayi ta siya abubuwan ta, daga bisani ta dawo, tana shiga motar ta cewa direban Raheena, "zamu iya tafiya" ba tare da ta sanarwa Raheena abin da tayi da kuɗin ba.
Direba ko ya tada motar suka cigaba da tafiya.
DARE YAYI.
Hajiya Marwan da kuma Salim da Ruki suna zaune kan dining, Amna ta taho tana shirin zama, bata gama sallamar da jikin ta kan zama a kan kujerar ba Hajiya ta miƙe haɗi da janta gefe, jan da tayi mata ya haɗa da haushin da ta kwana kuma ta wuni da shi na Amna, kan maganar Alhaji.
Kallon ta Amna tayi kamar bata san abinda tayi ba, cikin ɓacin rai da tsana Hajiya ta fara magana, "na ga alamar iskancin na ki ƙaruwa yake ƙara yi ako wace rana, wallahi kar ki ƙure ni idan ba haka ba, sai insa Marwan da Saleem su lakaɗa miki duka yanzun nan" "Saleem dai don ni bana ciki" Marwan ya faɗi haka kansa a ƙasa.
domin babu abinda zai sa ya ko taɓa Safna bare ayi maganar duka, domin kuwa bai manta alƙawarin da ya ma aljannu ba, ƙafafuwan sa har yanzu Jan su yake basu daina yi masa zugi ba, domin ko jiya zuwa yau, yayi tsammanin ƙara ji daga garesu amma yaji shiru, yana kyautata zaton ko sun yafe masa ne, tunda ko kallon banza baiyi wa Safnan ba ƙila shiyasa, domin kuwa har girma yake ɗan bata idan yayi tozali da ita, to akanme yanzu kuma zai ɓata rawansa da tsalle? Abinda bazai saɓu ba kenan.
"Akanme Saleem kawai? Kenan kai baza kabi umarnin uwar ka ba kenan?" Cewar Hajiya gaba ɗaya suna kallon sa, saboda Ruki ta fara shafa mata cewa Marwan n'a wasu ɗabi'u akan Safna yanzu, amma rashin nutsuwa da bata yi bane yasa bata bibiyi lamarin ba, gashi kuwa hakan na tabbata, kardai furucin da suke yi mata na mayya ya kamata, zata lamushe mata ɗa a banza domin kuwa ta san tun fil'azal Marwan ba son Safna yake ba, gwara da Yazeed ne ma.
"A sha re zancen kawai Hajiya ki zauna mu zuba abinci muci shine maslaha" cewar Marwan yana janyo plate domin dama basu fara cin abincin ba suna jiran fitowar Alhaji. Saleem barin kallon da yake wa yayan sa yayi ya maida kan Amna ya ce haɗe da ɗaure fuska, "get out of here, dama anan kike cin abinci ne? In banda iskanci" suma Hajiya da Ruki wurin Amnan suka juya da kallo, kowa ya buɗe baki zai ƙara yi mata wani magana ta ce.
"Kar ku damu yanzu zan wuce ma, babu buƙatar wahar da bakin ku" tana faɗi ta wuce tana murmushin da ita kaɗai ta san dalilin hakan, ba ɗakin Ammu ta nufa ba, zama can gefe tayi inda baza su gan ta ba.
Su kuwa Hajiya Dady na zuwa a ka fara ba ciki haƙƙin sa na dare, Dady kaɗan yaci ya tashi ya koma ɗakin sa, sakamakon kiran da ya shigo wayar sa, Hajiya da zuri'ar ta kuwa sai da suka yi hani'an sannan kowannen su ya miƙe, "wayyo Hajiyaa! Ciki na" cewar Ruki haɗi da riƙe cikin ta yayin da ta fara ji tamkar ana yamutsa mata kayan cikin.
Hakan yasa Hajiya saurin riƙota tana faɗin, "me ne...?" Sai dai bata samu damar ƙarasawa ba saboda kamar Ruki ta harbe ta, domin kuwa itama ji tayi kamar ana muƙur- ƙusa mata kayan cikin ta, su Marwan zaro ido su kayi suna kallon abinda ya faru da Hajiya da Ruki, ai kan suyi wata ƙwaƙƙwaran motsi ko wanne a cikin su shima ya kama cikin sa.
Kowa da yadda yake sakin ihunsa, sai kuma suka fara jin kamar zawo na ƙoƙarin samun hanyar fita daga masubur-buɗan sa, Ruki ce ta fara sakin nata tusan sai Saleem ya amshe, haba wa ba sai Marwan ma yace baza ayi babu ni ba, dariya Ruki ta sa jin ƙarar na Marwan ɗin ya fito wani zuit dashi kai kace an cewa bodari gyara zaman ka, Hajiya kuwa maƙe na ta tayi domin kuwa koba komai ai bai kamata yaran ta suji ƙarar fitan na ta ba, wannan ai abun kunya ne.
Sai dai fa tusa ya ce, ba da ni ba Hajiya dole na antayo nima na shana akan me za'ayi babu ni?. Ƙafar da Hajiya ta sa dan wucewa ba sai ya ba wannan tusar damar fitowa ba, ji kake baaam kamar ƙarar fa ɗin nucléaire, haba saiga Hajiya apuja jan tana nufan upstair, su Ruki cika bakin su da iska su kayi suna kallon kallo, haba kawai suka fashe da dariya, sai dai fa dariyar na su baiyi tsawoba suma suka kama hanyar ɗakin su, domin samun sarari a toilet, sakamakon yadda cikin su ya ke sake wani ƙa ra ƙulu-lululuu, suna tafe suna sake boma bamai abin su kowa da kalar ta sa.
Hajiya tana isa ɗaki ta nufi toilet, sai da ta fitar da wannan cutar ka na taji sala ma, fitowa tayi ta zauna a bakin kujera tana sauke numffarfashi kamar wacche ke gasar numfashi, sai dai cikin nan bai kuma yi mata amana ba, domin ko wani gagarumin zawo ne ya kuma tahowa, "wayyo Allah na ni Zainabu! Wannan wace iriyar bala'i c..." bata ƙarasa kalmar ba ta ruga zuwa toilet ba tare da tayi shirin hakan ba. A ɓangaren ukun ma haka yake domin babu mai minti uku waje ba tareda ya kuma shigewa banɗaki ba. Marwan kuma abu ya haɗe masa goma da ashirin, ga cangala ƙafa ga kuma iftila'in yanzu.
Hajiya ce zaune kan carpet tayi ɗai ɗai, domin kuwa yadda ta zauna sai kace wacce akewa ruƙiyya, Alhaji zaune kan kujera ya tasa ta gaba yana cewa, "ke ko kunya bakya ji? Dubi yadda kikayi zaman nan, ba kyajin kunya ɗaya daga cikin yaran nan yazo ya tadda ki haka?" "Daga baya kenan wai an tambayi biri kana cin ayaba? Ni da nayi ƙatuwar tusa a gaban su, wanda ni da kaina saida fitar tusan ta bani tsoro, to me ya rage kuma" cewar Hajiya cikin ranta a fili kuwa ko sannu bata ce masa ba, saboda it kaɗai ta san yadda cikin ta yake murɗa har yanzu.
"Look toilet ɗin ma a buɗe kika barshi, ji yadda ɗakin nan yake wani tashin hamami, da girman ki baza ki iya fesa ko air..." sai dai fa shima Dady a halin yanzu bai samu nasarar ƙarisa wa ba, jin cikin sa na yi masa kukan ƙwari, da sauri-sauri shima yayi toilet ɗin Hajiyar da ɗazu yake binsa da kallon ƙyama, ɗakin ma yake son barin sa, sai ga shi yanzu ya shige ciki ba tare ya shirya hakan ba.
"Waya gaya maka borno gabas take, gashi kaima ka shiga layi, kaji inda daɗi" Hajiya ta kuma faɗi cikin ran ta.
Amna dake manne à ƙofar su Hajiya ce riƙe da bakin ta, tana danne dariyar da ke neman kufce mata, barin wurin tayi tana kallon ɓangaren su Marwan da ta baro yanzu tana kuma sakin dariyar ta ƙasa-ƙasa.
Bayan ta koma ɗakin Ammu take cewa Ammu, "kinji wani tusar da suka saki a jere ɗazu kuwa Ammu?" Ta faɗi tana ƙara tintsirewa da dariya, nan ta fara sanar wa Ammu abinda tayi