Showing 54001 words to 57000 words out of 129098 words

Chapter 19 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

35

saba, duk saurin ɗaga wayar da Amna tayi sai da ya rigata yin magana, domin harta buɗe baki amma sai ta rufe jin ya fara magana.

"Barka da hutawa 'yar ahalin ta, da'alama kina jin daɗi kasancewar ki cikin daula" wani haushine ya cika Amna hakan ya sata fara magana, "wani irin daɗi? kun sani zama cikin gida mai kama da kango, babu wani bil'adama a ciki sai ni kaɗai kamar mayya, ko hayaniya bana ji kusa da gidan kamar a cikin daji" shiru yayi mata hakan yasata jin ta kofsa fa, ita da zatabi komai ahankali saboda familyn ta, kome zasu faɗa mata yaci ta danne zuciyar ta.

"Am kaga yallaɓai ka gafarce ni, bawai na faɗa maka da wani manufa bane plea..." katse zancen da take yayi da cewa "M R. My name, ba surutu nakiraki muyi ba, ki ɗaga katifan gadon da kike kwana akwai ƙaramar kwali a wurin" ba tareda ta amsa mai ba ta ɗaga da hannun da badashi ta riƙe wayar ba, daukan ƙaramar kwalin tayi tana cewa "eh naganshi gashi na ɗauka" "open it" ya furta, saƙale wayar a kafaɗar ta tayi tana buɗewa.

Memory ne aciki, tana fiddo shi taji maganar sa yana cewa, "je kiyi connecting ɗinshi da.T V" hakan yasata fita daga ɗakin zuwa falo, kamar yadda yace takeyi har ta shiga gurin hotuna, "tana kama dake ko?" Yayi mata tambayar daidai lokacin da ta shiga wani hoto, sai da ta kusa sakin wayar dake kunnen ta sakamakon abinda idonta ya gane mata, buɗe wa'ennan manyan idanuwan ta tayi, kamar yadda take indai taga abin mamaki ko kuma tashin hankali.

A hankali take tafiya har ta isa gun TV, hannu ta tasa tana shafa hoton da ta gani haɗi da ƙa re masa kallo, sai kuma ta fashe da dariya harda kama ciki. Sassauta dariyar tayi da faɗin "raina min hankali kuke son yi ne wai? Taya zaku samu hoto na kuyi editing sannan ku tambaye ni wai muna kama, a tinaninin ku nayi kama da masu hankalin kaza ne? Kai amma fa wanda yayi edit ɗin nan na musamman ne ya mayar da hoto kamar gaske" ta faɗi tana cigaba da dariyar ta.

"Ba ke bace" ta tsinka yi maganar shi cikin dariyar ta, "bani bace? K..." ya kuma katseta "ki shiga hankalin ki, niba abokin wasan ki bane" lokaci ɗaya dariyar da take ya tsaya jin yadda mutumin kokuma tace M R yayi magana, wanda maganar ya nuna ba wasa, "I'm sorry" kawai ta furta, ya cigaba da cewa "sunanta SAFIYYA, wacche ake kira SAFNA, 'ya ga ABUBAKAR MAI DARAJA da kuma MARYAM ƘANIN ARƊO" haɗiye nyawun mamaki tayi, tana ƙara ƙura idonta kan hoton wanda akace ba ita bace.

Kuma ga kamanninta dake fiskar yarinyar, sai 'yan bambanci ƙwaranni da bai wuce biyu ba, na farko shine ƙwayar ido na yarinyar ya kasance baƙi saɓanin na ta daya kasance ash colour, sai tabo dake gefen bakinta cycle baƙi wanda girmansa yayi banbanci da kalan wanda kuka saba gani, kuma itama tana da exactly irin sa amma a gefen wuya "amma wannan wani irin kamane? Kamar wanda Hausawa ke cewa kamar antsaga kara? Ajiyar zuciyan mamaki ta sauke.

"Kiyi gaba" taji ya faɗi haka, babu ɓata lokaci taje next photo, wannan Mai daraja kenan wato mahaifinta" haka dai ya rinƙa sanar da ita sunayen sauran mutanen gidan su Safna har ma da ma'aikatan gidan, "to me amfanin nuna min hotunan mutanen da bani da wata alaƙa dasu? ban taɓa saninsu ba, sanin na su amfanin me zai min?" Tayi masa maganar bayan ya kammala sanar da ita sunayen su da kuma matsayin kowa a gidan.

Ba tare da ya kula tambayar da tayi masa ba ya cigaba da faɗin "Mai daraja hamshaƙin mai kuɗi ne, ya rasu shekaru ashirin da biyu da suka gaba ta, bayan ya rasu ya bar manyan kamfanoni guda biyar, Safna ta ɓace wata ɗaya da ya wuce, dan haka zaki koma gidan amatsayin ta, kuma zaki kula da mahaifiyar ta da take da ciwo mai kama da paralise" ai yana ida maganar Amna tace "ehhh! Yallaɓai, am sorry M R me kake faɗane? Ta yaya zan koma matsayin wata? Kuma wai zan kula da mahaifiyar ta me ciwo kamar paralise, nakashashshiya kenan, wato baiwa kuke ƙoƙarin mai da ni ko me?".

"Kehh!" Ya daka mata tsawa, hakan yasa ta yin shiru ganin bakinta yaƙi sa linzami, ya cigaba dacewa "da'alama kin fara maida lamarinnan wasa ko? Shikenan inaga gwara na kawo ƙarshen komai kawai, dan haka zuwa anjima zan sanar dake inda zaki samu gawan s..." "a'ah a'ah dan Allah dan Allah kayafemin, karka musu komai dan Allah, daga yanzu bazan ƙara yi maka magana na makamancin wannan ba na rantse, zanbi dukkanin umarnin ka ba musu" tayi saurin katseshi da faɗin haka cikin tashin hankalin abinda yake, harda durƙusawa alamar roƙo kamar tana gaban shi.

Ba tareda ya faɗa mata ya yafe mata ba ya dasa da cewa, "gobe bayan sallahr azhar zaki fita gidan nan dan komawa gidan su Safna da zama, zaki rinƙa sanya black eye color da kuma irin baƙin abunda ke gefen bakinta, ta yadda zaki sa je kizama ita sak, duk wa'ennan abubuwan suna cikin hand bag dake ƙarƙashin gado, kayan da zakisa ma yana gefensa, sannan akoi abinda zaki kiyaye, maganar ki zai zama a hankali mai sanyi, kuma tafiyar ki ya zama a natse" "wai me sanyi da da zafi nake magana? Kuma wai tafiya a natse sai kace wacce ke tafiya bazar-bazar kamar ankoro shanaye?" Tayi maganar cikin zuciyar ta.

"Kalar kaya kuwa daga atamfa shine wanda zaki fi sawa, koda zakisa wani kuwa sai dai doguwar riga abaya ko makamancin su, kuma duk abun ɓacin ran da za'a miki dole ki daure koda kuwa marinki akayi wannan shine halin Safna" "cab wallahi ba'a marenin bane hi'im" ta kuma faɗi cikin zuciya, "sune abinda zaki kiyaye, duk abinda zai zo daga baya, zamu sanar dake domin komai daki-daki muke binsa" "to M R zanyi yadda kuka ce amma dan Allah karku taɓa min iyali na" ta faɗi bayan ya gama mata bayanin, sai dai kan ta ƙarisa maganar ma ya katse, "wannan dai dama bahago ne" ta furta a fili,

Zuwa tayi inda yace ta ɗauki kayan tana faɗin "daga ƙasan katifa sai ƙasan gado, gaba kuma waya san a ina zasu ce inɗauki wani abun?"

WASHE GARI.

BAYAN SALLAHR AZHAR.

Amna ce ke fitowa daga cikin falon sanye da riga da skirt atamfa pink white and maroon colour, sai hijab white daya kusa kaimata ƙasa, sannan plat shoe sanye ƙafan ta, hannunta riƙe da hand back ɗin, fiskar ta kuwa ya dawo tamkar fiskar Safna, domin duk wata banbancin dake tsakanin su ta cike shi, tafiya takeyi tamkar zata faɗi, saboda rashin sabon da batayi ba kan sa skirt, saboda ita ko tamfar zata sa tofa sai doguwar riga, ta kalmi kuma tafi sa mai ɗan tsawo, sannan ga himar wanda bata cika sashiba sai a gurin sallah dole.

Tana tafiya tana magana cikin ɓacin rai, "dan Allah duba yadda na zama sai kace wata mashahuriyar malama, Hijab har ƙasa ko kyau banyi ba, yadda kasan ɓera yasha jumfa, gashi jin ƙafafuwa na nake a wani ta kure, kai kuma a haka zanyi zamar rashin 'yancin nan a maimakon Safna wai, ya Allah ka taimake ni" Tana gab isowa gate taji alamar buɗewa, ita tama manta gate ɗin a rufe, saboda haushin kayan da tasa yasata mantawa, tana fita taji ƙara message, tana dubawa taga adreshin gidan ne suka turo.

Ta fiya da ɗan nisa tayi kan ta ƙarisa kan hanya, napen farko da ta tara yace zai kaita akan dubu ɗaya da ɗari biyar, amma tace furr ita bata yarda ba wai yayi tsada ɗari biyar zata bashi, ai mai mashin yana Jin haka ya wuce ba tareda ya kuma mata magana ba, ta tari na biyu shi kuma ya ƙara ɗari uku akan kuɗin da wancan yace nanma taƙi, ganin cewa fa yawan ci masu napep ɗin ba mai faɗin dubu da ɗari biyar ɗin da mutumin farko ya faɗa kowa ƙarawa yake hakan yasa ta fahimtar gurin mai nisa ne, idan kuwa ta tsaya jira tofa lokaci ne zai wuce, hakan yasa ta shiga napep ɗin da ta ƙara tara, bayan yace mata dubu biyu zata bashi.

#AMMA SHIN MENENE MANUFAR MUTANEN NAN AKAN AMNA DA HAR SUKE SON TADAWO GIDAN SU SAFNA A MADADINTA?

YA AMNA ZATA YI RAYUWA A MATSAYIN WATA DABAN? SHIN ZAI YU?

YA KUKE GANIN HAJIYA ZATAYI IDAN TAGA SAFNA TA DAWO GIDA BAYAN DUK SHIRIN DA TAYI DON ƁATAR DA ITA?

______________________________________________________________________________________________

Part 5️⃣7️⃣▶️5️⃣8️⃣

Ganin cewa fa yawan ci masu napep ɗin ba mai faɗin dubu da ɗari biyar ɗin da mutumin farko ya faɗa kowa ƙarawa yake hakan yasa ta fahimtar gurin mai nisa ne, idan kuwa ta tsaya jira tofa lokaci ne zai wuce, hakan yasata shiga napep ɗin da ta ƙara tara, bayan yace mata dubu biyu zata bashi.

Suna cikin tafiya. Ɗaga hannunta tayi tana shafa gefen idon ta a zuciyar ta tana cewa, "kai da kanka idon Amna kaima ka samu rabonka, sai da fa na ƙoƙarta kusan sau biyar sannan na samu nasarar dai daita wannan ƙwayar idon roban" ganin mai adai-daita ya tsaya ɗaukar wani ne yasa ta dagatawa da maganar da takewa kanta tana cewa, "haba malam taya zaka ɗauki wani bayan zun-zurutun kuɗin da kace zanbaka? kanme baza ka kaini ni kaɗai ba?".

"Hajiya bazaiyu bafa, indai kina son inkaiki ke ɗaya to ki ƙaro kuɗi" yana faɗan haka kuwa bata kuma kulashi ba, tafiyan awa ɗaya ba minti ba kwai su kayi, tsayar da napep ɗin yayi daidai gate ɗin first G.R.A.

Miƙa masa kuɗi tati daga cikin jakar hannun ta yayi wucewar sa, saida ta duba adreshin da aka turo mata, bayan ta tabbatar layin ne hakan yasanya ta shiga cikin sa, tafiya take tana ganin gidaje na alfarma iri daban daban, "ikon Allah, irin wa'ennan tanƙama-tanƙaman gidaje jere haka" ta faɗi a fili, har ta wuce gidan sai ta ɗanyi ribas, ƙara shiga massage ɗin tayi dan sake tabbatarwa shin gidan da ta ganin ne koko wani, ganin cewa ko shakka babu gidan ne yasata zuwa gurin ƙofan dan ƙonƙosawa.

Saidai kantasa hannu Baba Hambali ya buɗe, ganin Safna da yayine yasa shi washe baki yana faɗin "Ayyah 'yata ashe kina hanya? Nayi farinciki da dawowarki" Itama washe bakin ya ƙe tayi tana faɗin "Wallahi kuwa, to bara nashiga koh?" Tana faɗi ta shige, tsayawa tayi tana bin ko ina da kallo, harabar gidan ya matuƙar haɗu, take fadi a ranta, "to amma wani sashe zan tinkara matsayin wanda inda take zaune?" Ta faɗi a zuciyar ta tana kewayawa da idonta a gaba ɗaya gidan.

Tana tsaye taga ɗaya daga cikin masu aikin na wucewa, "ke hanne!" Ta furta da ƙarfi, juyowa 'yar aikin da ta kira hanne tayi, tana kallon Amna kamar kashi, "cab a lallai, su dama a nan masu aiki basa darja 'yan gida ne? Dubi yadda ta ke kallona kamar tana kallon kashi, hmm da badon sharaɗin wannan M R ɗin ba ai da sai na kusa tsole mata idon na ta, dubeta wata munes da ita" ta faɗi a zuciyar ta a fili kuwa tace, "dan Allah ɗan zo".

Wucewa hanne tayi ba tare da ta ce mata komai ba, daidai shigowar baba Hambali, "a ah 'yata baki ƙarasa ciki bane? Fatan dai lafiya?" Ta bashi amsa da "dama jiri-jiri nake ji ne shiya hanani ƙarisawa ciki" "ayyah sannu ƙila tafiyar da kika sha ne yasamiki hakan" ana haka sai ga jummala, itama cikin fara'a tazo gun Amna tana faɗin "maraba-maraba Safna'u kece tafe? Sannu da dawowa" wannan karon ma washewa Jummala baki kawai tayi.

Baba Hambali yana faɗamata ai jiri ne ke damunta ma, dan haka ta taimaka mata gurin shigar da ita ɗaki, hakan yasa Jummala kama hannunta dan kaita ɓangaren su, bin ko ina da kallo kawai Amna keyi tana kallon inda Jummala ta nufa da ita, tsayawa sukayi à ƙofar falon Jummala tana cewa "sai mun ƙonƙosa, kwanan nan Hajiya tasa arinƙa rufewa bayan munkammala duk aikin ciki, saboda tana zargin akoi wanda ke kula da mahaifiyar ki cikin mu".

Ba tare da Amna ta gama fahimtar me Jummala ta gaya mata ba tace "to badamuwa bari in ƙonƙosa, tana faɗi ta matsa jikin ƙofan ta fara nuckin ba ƙaƙƙautawa, Hajiya dake falo zaune taji ana nuckin ɗin ƙofa, hakan yasa ta fara kiran autarta dake ɗakin ta da tazo ta buɗe ƙofar, amma Ruki amsa kiran kawai tayi ba tareda tayi ko gezau daga inda take zaune ba, ganin Ruki bata zoba kuma anƙi daina nuckin yasa ta barin danne dannen da take a waya ta taso tana masifa.

"Wai waye a ƙofar nan ne?" Ta faɗi cikin ɓacin ran yadda ake ƙonƙosawa babu ƙaƙƙautawa, tana budewa ta ƙara faɗin, "baka iya ƙonƙosawa sau ɗaya ne haba?" Ta faɗi dai dai buɗe ƙofar, suna haɗa ido da Amna ta fara baya-baya tana nuna ta da yatsa bakinta na rawa tama kasa furta komi, cikin bayan da take ƙafarta ya zame nan ta faɗi ƙasa tiimm, duk da taji zafin faɗin da tayi, amma ta fara ja baya tana cigaba da kallon Amna, yayin da zuciyar ta ke faɗin mata ba gaskiya bane, kawai gizo take mata.

Amna kuwa mamakin abinda taga Hajiya ta yi tayi, "too ita kuma wannan lafiya take kuwa?" Ta faɗi a zuciyar ta tana shiga ciki, zuwa kusa da Hajiya tayi tace "barka da yamma Zainab" zaro ido Hajiya tayi jin tabbas maganar Safna ce ba tareda ta fahimci sunan da Amna ta kirata ba, wanda hakan yasa Amna tinawa fa da ainahin sunanta ta kira ta, to inta gane fa? Sai tayi saurin ƙara cewa "am Hajiya nakeson cewa" ta faɗi dai-dai saukowar Marwan daga upstair.

Ganin yadda Hajiya takewa Safna kallon mamaki yayi, hakan yasa shi ƙarasowa inda take, Amna kuwa juyawa inda Jummala take tsaye tayi tana faɗin "Jummala zo ki ƙarasa ladan ki, kikai ni ɗaki har yanzu jirin nake gani" ta faɗi domin haryanzu bata san ɗakin da zata dosa ba, da toh Jummala ta amsa domin tsoro take kar hakan yazama laifi a wurin Hajiya, dukda ta ga yanayin data shiga da ganin Safna, to ko me dalili?.

Bayan su Amna sunyi ɓangaren su Safna, Marwan ya durƙusa gun Hajiya yace "Hajiya ya akayi naga kamar kinawa shegiyar nan wani irin kallo? To wai ko baki gane ta bane? Naga ba canzawa tayi ba" Ba tareda ta amsa mishi ba ta miƙe tana bin bayan Amna da kallo, "kai kai kai" take ta furtawa idonta abayan su Amna, Marwan yace "Hajiya nine Marwan fa, ya kike ta kiran wani kai?" Juyo da kallon ta tayi gun sa tana furta "maranni" cikin mamaki yace "Hajiya kamar mari fa kikace?" "Eh nace ka mareni ingane abinda na gani gaske ne ko ƙa ƙa" "to shikenan".

Yana furta wa ya kaiwa Hajiya lafiyayyen mari daga ƙaton hannun sa, "ba shakka! La'ilaaa Dan ubanka ni zaka mara?" Cewar Hajiya da ƙarfi riƙe da kumatu tana bin ɗanta da wani irin kallo, "Hajiya kece fa kikace inmare.." kan ya ƙarisa Hajiya ta kai masa bugu cikin ɓacin rai, kaucewa yayi yana nufan ƙofar falo, yana fita yana juyawa ganinta yadda take fitar da numfarfashin ɓacin rai, ƙasa-ƙasa yake cewa, "lafiyan Hajiya kuwa? Lokaci ɗaya yanayin ta ya sauya, cewa fa tayi in mare ta bayan nayi hakan kuma tanunamin ɓacin rai? Allah dai yasa ba gamo tayi ba".

Saida Hajiya ta ɗauki wayar ta dake kan kujera ta nufi ɗakin ta sai huci take kamar ɗan zaki, ɓangaren Amna kuwa Jummala na kaita ƙofan ɗaki tayi mata godiya tace zata'iya tafiya, bayan Jummala tabar wurin ta cigaba da bin ko ina da kallo, hannunta tasa kan hannun ƙofar tana murɗawa a hankali haɗi da shiga ɗakin tana rufewa, sai dai a duhu ta sami ɗakin babu alamar haske ko kaɗan, tafi tinanin ko kashe gloff ɗin akayi, hakan yasa ta fara laluba bango inda take tinanin ko tanan madannin yake.

Cikin sa'a hannun ta ya taɓa madannin da take da tabbacin madannin gloff ɗin ne, tana dannawa haske ya gauraye ɗakin hakan ya bata damar kallon ko ina a ɗakin, "duk kyawun gidannan amma ace ɗakin cikinsa ya zama haka?" Ta faɗi saboda arba da tsofaffin kayan da idon ta ya gane mata, domin katakon da aka buga gadon ya tsufa sosai daɗadɗe ne, dabadon kayan da da ƙwari ba da tuni katakwayen sun zagonye.

Kapet da pentin ɗakin kai duk abinda ke cikin ɗakin su Ammu tsohone, kujeran dake ɗakin ma jikinsa har ya fara yagewa alamar daɗewa, banda ma haka ga alamar fari-farin datti dake kan kapet ɗin "oh my God! Daga zuwa na zan hau aiki kenan?" Ta faɗi cikin takaici, jin alamar buɗe toilet ɗin ɗakin taji hakan yasata maida idonta gurin dan ganin wake fitowa.

A daddafe Ammu ke fitowa daga bayan gidan tana nishin wahala, "ohooo! Wato itace kenan?" Ta furta a fili tana cigaba da bin Ammu da kallo, ba tareda tayi yunƙurin taimaka mata ba, Ammu kuwa jin kamar muryar abunda tafi ƙauna à duniya tayi tamkar a mafarki, take jikinta ya hau kyarma tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login