Showing 27001 words to 30000 words out of 129098 words

Chapter 10 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

21

tayi, tana faɗin, "taya zai zama kwana biyu?" Nan kuma ta ƙara tina lokacin tafiyar ta sa, "Allah ya baka nasara akan Ƙungiyar POSPA Aboki na, dan Allah duk abinda ake ciki ka rinƙa sanar da ni" "tabbas haka naji Uncle Tukur ya ce masa wancan ranar" . Cewar Amna a fili sannan ta ƙara cewa "ya kamata inje in samu Uncle yanzu ya faɗamin abinda Baba na yaje yi Kaduna" ta ƙarashe faɗi tana share hawayen ta, ta fice daga ɗakin.

Ba tare da ta sanar da su Mamma fitar na ta ba, ta fice daga gidan ko glass bata sa ba, kai tsaye gidan Uncle Tukur ta sake nufa, tana shiga suka fara mata kallon tausayawa, sabida sun san abin da ya faru, sai dai sunyi mamakin ganin ta ba tare da tabarau ba, koda yake tashin hankalin da take ciki ai zata iya mantawa da komi.

Wannan karon bata gaishe su ba, kawai tambayar su Uncle Tukur tayi, uwar gidan sa ce ta sanar da shi zuwan Amna, yayin da ta tadda shi shima yayi tagumi sabida tashin hankalin mutuwar abokin sa, dama yanzu yake son zuwa gidan su Amnan.

"Kice ta zo" kawai ya furta ba tare da ya kalle ta ba, fita tayi ta sanar wa Amna, ai kan ta ƙara sa, Amna ta yi hanyar ɗakin na sa, yanayin yadda ta shigo ne yasa shi saurin miƙewa, kallon ta yake yi cike da tausayi, da kuma ganin yanayin fiskar ta da bai taɓa gani ba.

"Amna kiyi...!" katse sa tayi da faɗin, "Uncle please tell me, ka faɗamin gaskiyar abin da na gani yau, kace min ƙarya ce haɗawa kawai a kayi, ai kasan Baba bazai aikata hakan ba ko?" Tana ƙarashe faɗi ta durƙusa tana zubar da hawaye masu zafi.

#Chakwakiya, ina tausayawa su Amna na rashin jigo da su kayi🥺.

To amma anya babu wani abu a ƙasa kuwa? Tabbas a kwai abinda ke faruwa wanda sai nan gaba zaku fahimta.

______________________________________________________________________________________________

Part 2️⃣9️⃣▶️3️⃣0️⃣

"Uncle please tell me, ka faɗamin gaskiyar abin da na gani yau, kace min ƙarya ce haɗawa kawai a kayi, ai kasan Baba bazai aikata hakan ba ko?" Tana ƙarashe faɗi ta durƙusa tana zubar da hawaye masu Zafi.

Zuwa kusa da ita yayi cike da tausayawa yace "ni kaina naji mutuwar Aboki na har cikin rai na, kiyi haƙuri Amna, ke musulma ce kin san cewa mutuwa da rayawa duk na Allah ne, addu'a yake buƙata a halin yanzu, bawai kuka ba", shima ya faɗi idon sa nason kawo ƙwalla amma ya daure.

Miƙewa tayi tana share hawayen ta tana faɗin, "nasani Uncle, nasan cewa dole kowa zai mutu in lokacin sa yayi, amma dalilin mutuwar mahaifi na ƙarya ce, kuma nasan kasan hakan". Cikin mamaki yace, "ƴata me kike son faɗa ne? Ni bansan komai dangane da mutuwar sa ba".

"Dan Allah Uncle Tukur kar kace haka, ka sanar dani dalilin zuwan mahaifina wannan garin, mutuwar sa ba ta Allah da Annabi bane, akwai abinda aka ƙulla masa, cewa fa su kayi wai kwanar sa biyu da rasuwa, bayan kuma ko jiya munyi magana da shi" ba tare da yayi magana ba ya wuce inda kujerar falon take ya zauna, itama binsa gurin tayi dan jin me zai ce.

"Koda mutane sun yarda da ya aikata hakan, bazai dame mu ba, saboda mu munsan halin sa ai" "a'ah Uncle, taya bazai da memu ba bayan anayiwa mahaifin mu mummunar zato"? Ta faɗi tana hawaye, Ta cigaba da cewa, "ranar da Baba zai tafi naji kuna maganar wata ƙungiya mai suna POSPA, Baba ya sanar damu cewa ziyara zaije amma abun ba haka yake ba, kuma kai kaɗai ne kasan sirrin sa, dan Allah ka faɗamin"?

Miƙewa yayi kamar ya shiga cikin damuwa yace "a'ah 'yata bakiji da kyau ba ne" ya ƙarashe maganar da roƙon Allah yasa karta ƙara yi masa wannan maganar, saboda mutuwar abokin shi ya zame masa izina, kamar yadda hausawa ke cewa, "in kaga gemun ɗan uwan ka ya kama da wuta, to ka shafawa na ka ruwan sanyi".

SU MAMMA.

Shiru basu ji motsin Amna ba, dubawa su kayi nan ma basu gan ta ba, suna kiran wayar ta sukaji ƙarar ta ɗakin Ummee, wannan yasa hankalinsu yaƙara tashi akan ina taje? Ta ina zasu fara neman Amna?

AMNA DA UNCLE TUKUR.

"Na roƙe ka dan girman Allah kar ka ɓoyemin komi, kasanar dani abun da mahaifi na ya ɓoye mana, karkayi sanadiyyar ɓatanci a gare shi bayan ya mutu, tun da har kana da hanyar kuɓutar da shi daga hakan", ta ƙarashe maganar tana fashewa da matsanan cin kuka, Amaryar tasa ta shigo sabida jin kukan Amna da tayi.

"Baban Asma'u lafiya kuwa?" "Bakomai jeki kawai" shine abinda ya ce mata, sannan ya ɗanyi ajiyar zuciya yace, "ƴata ki daina kuka, tashi ki koma kan kujera, ta shi kinji"? Ya faɗi mata shima yana zama akan kujerar, miƙewa tayi tana sharar hawaye ta zauna, ashe tsawon lokacin da tayi ba tare da ko ɗigon ƙwalla ya zuba daga idanuwan ta ba, rashin abin kukan ne.

Ƙura masa ido tayi, sai da ya ni sa sannan ya fara magana, kamar haka, "tabbas mutuwar sa shiryayye ne. mahaifin ki mutum ne mai kishin ƙasa kuma mai taimakon al'umma, kamar yadda kika sani ne yayi taimako da dama a cikin aikin sa na Jarida, sai dai tun da ya fiskanci wata babbar matsalar da take faruwa a ƙasar sa na shaye-shaye kuma samari da 'yan mata dayawa sun lalace sanadiyyar wata ƙwaya, ya fara bincike, a kai, saboda ƙwayar tana zama kamar jaraba ce ga wanda ya fara shan ta, ya shiga tashin hankali lokacin da yaga abinda ƙwayar take haifarwa mutane sosai, domin kuwa har hawaye yayi lokacin, nan ya fara tinanin ta yadda zai kawo mafita a kan lamarin, nan ya ƙara faɗaɗa binciken sa a kan Ƙungiyar POSPA, da kuma shugaban su ZABBA BA, sai dai tun da ya fara binciken sa akan wannan Ƙungiyar nake hana shi amma ya ƙi, ni da kaina nayi masa binciken bayan ya roƙe ni da nayi masa, na sanar dashi hatsarin su da kuma abubuwan da suka aikata amma yaƙi janyewa". Ya dakata da maganar yana tina lokacin da akayi hakan.

Ya cigaba da cewa "zuwan sa Kaduna yayi ne sabida ya gano reshen Ƙungiyar, saboda alamar zargi da yake akan wanchan garin, ya faɗamin cewa ya haɗu da wata 'yar bariki, ya samu information akan ta, tasan duk wata ƙwaya sabida babu wanda ba ta sha, dan haka zai bi hanyar da zata masa bayani akan ƙwayar, in dai tana shan sa to tabbas ta wata boyayyiyar hanya take samu, ranar da na yi magana dashi na ƙarshe ya sanar min da ya samu damar magana da ita, dan kuwa da kan ta ta amince masa".

Juyowa yayi ya dubi Amna da itama kallon sa take yi, amma tana sa maganar sa a mahangan tinanin ta yace "abinda na fiskanta shine, tabbas sun bibiye shi ne, suka haƙa masa rami ya afka ba tare da ya sani ba, ni kaina yanzu ina tinanin ƙila suna bibiya na ba tare da na sani ba, dan haka Amna kema ina roƙon ki da kibar wannan maganar kamar yadda nayi shiru kema kiyi, ki kiyaye dan Allah saboda da ace aboki na ya ji magana ta a wancan ranar da duk hakan bai faru ba".

A jiyar zuciya Amna ta sauke haɗi da lumshe ido tana buɗewa, yayin da wani ƙullutun baƙin ciki da kuma alwashi ya bugi ran ta, "thank you so much Uncle, da ka sanar dani wannan sirrin insha Allah zan kiyaye kamar yadda kace" ta faɗi cikin shaƙaƙƙiyar murya dake nuna maka tabbacin zakanyar Baba ta sha kuka.

Sallama tayi musu akan zata wuce gida, Uncle Tukur ne ya kai ta saboda ya kamata ya duba su Mamma, suna shiga gidan Mubarak yayo gun Amna da sauri cikin murnan ganin ta yace, "Amna ina kika je ne? Kin ƙara samu cikin damuwa".

Ta'aziyya ya ma su Mamma da kuma ƙara basu haƙuri sannan ya tafi.

Wannan daren babu wanda ya rintsa cikin su, Amna tinani biyu tasa a ran ta, 1- tinanin mutuwar Baba, 2- tinanin sanadin mutuwar ta shi.

WASHE GARI.

Yau wa ma yake maganar zuwa wani wai School, mutane da yawa suka zo gaisuwa, yayin da wasu da yawa gulma suke akan abinda ya kashe shi, gulma su ke kai kace 'yan ƙauye ne, --- kun san dai ƙauye da gulma---.

SAFNA.

Kamar kullum sai da ta kintsa mahaifiyar ta sannan tayi shirin zuwa makaranta, a daidai gate ɗin shiga layin ta tsaya, ba'a jima ba saiga Raheena a napep tazo, dama haka suke, ko Raheena ta jira Safna a ƙofar shiga first GRA ko kuwa Safna ta jira zuwan Raheena da napep, inkuma akayi rashin sa'a ɗaya ba lafiya, kokuma wani dalili ya hana ɗaya zuwa makaranta, to sai fa sunyi latti, dan duk wacce tazo gurin ɗaya bata samu damar shigowa ba, to fa jira za tayi, sai idan jiran yayi yawa sannan ta wuce.

Suna zaune ita da Raheena bayan an fitar musu lecture, Raheena take cewa, "Besty nifa bikin Salma bai wani min armashi ba, ko dressing ɗin su bai yi min kyau ba" "Dama zuwa wurin biki kikayi ko zuwa kallon dress ɗin su kikayi? Kin san dai sa'ido babu kyau ko?" Safna tayi mata maganar tana murmushi.

"Nifa na kasa gane kanki wani lokaci malama wani lokaci miskila" Raheena ta faɗi tana dariya, itama Safna murmushin take.

Bayan antashi suka yo hanyar gida, kamar kullum Safna aka sauke, bayan sunyi sai gobe aka wuce da Raheena, ita kuwa Safna tayo gida, a hanyarta ta shigowa falon Ruki ta taɗe ta sanadiyyar sa mata ƙafa da tayi a hanya, fa ɗi ƙasa tayi tana jin zafin buguwan da ƙafar ta yayi.

Dariya ta kwashe da shi tace "kwana biyu kin samu free a gidan nan, kina yadda kika so abinki, to watan ci gaba da kasancewa cikin wahala fiye da baya ya tsaya miki, dan haka ki shirya" ta ƙarashe faɗi da sakin wata dariya, ta yi waje ta bar Safna a ƙasa, sai lokacin ta fara ƙoƙarin tashi.

Bata san da cewa Ruki ta zuba man gyaɗa a hanya a kusa da wurin ba, tana miƙewa ta ɗauki jakar ta, taku biyu kawai tayi ƙafar ta ya taka gurin maiƙon, zamewa ƙafar ta tayi a wurin, baya-baya tayi zata faɗi taji an riƙe ta, idon ta a rufe dan ta gama sadaukarwa ƙasa za tayi, a hankali ta fara buɗe idon, ganin wanda yayi mata wannan taimakon, domin kuwa tasan da tayi ƙasa tabbas ƙafar ta ne zata karye.

Tana buɗe idonta ta sauƙe su a kan Yazeed da ya saki ido sai ganin fiskar ta yake kamar yaune ganin sa na farko, mamaki ne ya cika ta da ganin yadda yake mata kallo kamar bai san meke wakana ba, alamar motsin da Safna tayi dan ya sake ta ne yasa shi dawowa daga duniyar da ya shiga.

Sakin ta yayi tare da wayan cewa, yana ƙwalawa direban sa dake kusa kira, da sauri yazo yana faɗin "na'am ranka ya daɗe" "ina masu goge-goge suke?" "Suna ɓangaren su ranka ya daɗe" "kiramin su" yayi masa maganar ba tare da ya bar wurin ba, Safna kam kallon ikon Allah take.

Juyowa yayi yaga ta ƙure sa da ido "Ke me kika tsaya jira anan dama ba shigewa ciki za kiyi ba? To maza bar nan salon san gulma ko?" jiki na rawa ta ɗauki jakar ta daya kuma faɗi ta yi hanyar ɗakin su, da kallo Yazeed ya raka ta.

Ita kuwa Ruki da ta laɓe a gefen ƙofa haushi ya cika ta, "kai Yazeed shishshigin ka yayi yawa wallahi, ina ruwan ka, nida har nake hasaso yadda tafiyar ta zai koma ɗingishi ko rarrafe," ta faɗi a zuciya tare da sakin tsaki a fili marar ƙara.

Masu aiki suna zuwa Yazeed ya hau su da masifa, "wani irin aiki kuke yi ne har da za ku zubar da mai a nan, me ya kawo maiƙo falo wani irin iskanci ne haka? To ku saurare ni daga yau kar na ƙara ganin hakan ya faru, this is first and last warning".

Ƙas kawai su Jummala su kayi da kan su, duk da cewa basu san ya akayi hakan ya faru ba, amma sun karɓi laifin sabida ko gaskiya suka faɗa ba yarda zaiyi ba, sai dai ma su ƙara wa kansu wani abun.

"Jira kuke sai na ce ku gyara?" Yayi musu maganar, ai da sauri suka tafi ɗauko kayan aiki, shi kuma ya wuce rai ɓace da bai zoba da wani abun ya samu yarinyar nan.

#A samu wa'ƴan da zasu raka ni zuwa yiwa su Amna ta'aziyya 😥 to amma kodai Baba......?🤭

Gashi dai an sanar da Amna komai, kuna ganin zata yi binciken itama ko ƙaƙa?

Menene tinanin ku a kan Yazeed?

______________________________________________________________________________________________

Part 3️⃣1️⃣▶️3️⃣2️⃣

BAYAN LA'ASAR.

Dogon rigan kanti tasa tare da dogon wandon roba, yayi mata kyau sosai, ɗaure gashin ta tayi da rinbom, kalar gashin ta ba baƙi wuluk, sannan ta sanya hula ta rufe gashin, ta ɗora madaidaicin gele a kai, fitowa da Ammu tayi waje yauma, ta fara mata hira dan ɗebe mata kewa.

"Ammu jiya nayi mafarki kin yi magana da muryar ki da na daɗe nake burin ƙara sauraro, kuma kinsan me kika faɗa"? Cewa ki kayi "my daughter akwai wani ɓoyayyen al'amari wanda da daga ni harke bamu san shi ba, amma nan gaba zai bayyana a gare mu insha Allah". "Ammu nah nayi ta nazarin mafarkin nan shin gaske ne kokuwa ƙaryan mafarki ne kawai, kuma abin mamakin ba wai ni kike faɗawa ba, ni a chan gefe na tsaya ina kallon ku, sai dai banga fiskar wacce ki kewa maganar ba domin ta bani baya, amma kasancewar muryarta da ta doki dodon kunne nane yasani fiddo Ido, sabida muryarta sak tawa".

Ƙure ta da ido kawai Ammu tayi, itama fiskar ta alamar nazari, sai dai babu abin da ta fahimta dangane da wannan mafarkin.

"Ah Lallai ba shakka", cewar Hajiya da tayo wurin buguzun-buguzun kamar wacce za ta tashi sama, a tsorace Safna ta juya tana kallon ta, yayin da zuciyar ta keyin ɗar-ɗar, Ammu kuwa kanta na inda 'yarta take sabida ba damar juyawa, itama tana tinanin da abinda Hajiya ta zo yi yanzu, dan zata iya tina kallon ƙarshe da tayi wa Hajiya tun wani lokaci da jikin ta yayi mugun ta shi, a hanyar fita da ita dan zuwa Asibiti ne tayi tozali da ita, ko lokacin ma harara ce kawai Hajiyar ta rakata da shi.

Kamar yadda ta daɗe bata ga Marwan da Saleem ba, sabida ita Ruki kodan ta tsokani Safna tana zuwa ɗakin, sai shi kuma Yazeed da yake zuwa gaishe ta lokaci-lokaci.

Da Hajiya ta aika musu da kallon ƙas-ƙanci sannan cikin ɗagun murya ta ce "wato kamar yadda bayani ya iskeni hakan take kenan? Tunda kika ga kwanan nan ban samu zama ba shiyasa kika samu damar fito da nakashashshiyar uwar nan ta ki waje ko? Dan munafurci harda samun keken guragu, fito da ita ki kayi dan muma ta lamushe mu kamar yadda ta lamushe uban ki?".

Yauma maganar ta ƙara dakan mata zuciya. wato kenan maganar da Ruki tayi mata rannan a bakin Hajiyar taji kenan? ɓangaren Ammu ma hakan take sai dai ita bai wani dame ta ba saboda ba yau bane farkon fitar mummunar kalmar a bakin Hajiyar a gareta ba.

"Tambayar ki nake kin min shiru ga mahaukaciya na zuba zance ko?" Cewar Hajiya tana ƙara hayayyaƙo mata kamar zata rufe ta da bugu, "ranar da tayi rashin lafiya ne doctor yace a rinƙa fitar da ita tana shan iska, kuma Dady ne ya bani damar hakan" Safna ta faɗi hakan cikin tsoron furucin Hajiya na gaba.

"Allaaaaah! Ba shakka wuyan ki ya isa yanka Safna, iyeeee! Wato ni kike cewa Alhaji ya baki dama, to shi Alhajin uban ki ne? Nace shi uban ki ne?" girgiza kai Safna ta hau yi mata ganin fa yau da en muguntan a gaban goshin ta ƙarara. to kari ta kaiwa Safna da ƙafa daya sa ta saurin sauka daga inda take zaune.

"Kiyi haƙuri Hajiya, wallahi ban fito da Ammu dan wata manufa ba" hamɓarin da Hajiya ta kai mata baki ne yasa ta gunmtse bakin na ta tare da ɗaura hannayen ta biyu duka akai, tana bin Hajiya da kallon tsoro.

Jikin Ammu ne ya fara rawa saboda ƙoƙarin miƙewa da take son yi, a hankali ta fara ƙoƙarin tashi daga keken guragun ta, dan so take tayi ido huɗu da Hajiya da bata san idon uwa ba, sai dai kan ta ƙarisa miƙewar Hajiya ta sa ƙarfinta ta ture ta, nan Ammu tayi ƙasa daga ita har keken.

Da sauri Safna ta yunƙura dan taro Ammu, sai dai ta riga da tayi ƙasa, durƙusawa tayi tana ƙoƙarin ɗaga ta, hawayen takaici na fitowa daga idanun ta, saida ta komar da Ammu kan keken sannan ta juyo tana yiwa Hajiya wani irin kallo wanda bata taɓa yi mata irin sa ba, ita ma dakan ta bata san tana yi ba.

Zaro ido dan mamaki Hajiya tayi, yau Safna ke yi mata irin wannan kallon? Kallon da ke nuna zalla rashin tsoro a idanuwan ta? "Safna ni kike wa kallo haka? Ba shakka dan na taɓa ruɓaɓɓiyar uwar nan ta ki? To bari in illa ta ta, kinga sai ki nunamin cikakken manufar abinda idon ki keson isarwa". Ta faɗi tana ƙoƙarin ƙara ture Ammu a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login