Showing 126001 words to 129000 words out of 129098 words
Chapter 43 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
ni zaki koma" cewarsa yana dariya ya yayi gaba, hmmm ta yi da da baki, sannan ta bi bayansa don su koma tare, saboda bada driver tazo wurin ba. Shiga mazaunin kusa da driver tayi, shima ya zagaya ya shiga, a hankali ya fara sarrafa motar cikin ƙwarewa, bai mata magana ba ganin itama gimtse bakinta tayi.
Sauke numfashi mai sanyi tayi ka na ta ce, "ina da wata tambaya" sai da ya kalli fiskarta ta wurin gilashin madubin gabar motar sannan ya ce "yau ranar tambayarki ce 'yanmata, ki tambayi sarki da ɗansa" sai da ta juya ta dube shi yadda yake murmushi ta ce, "to yanzu, me abu na gaba, wato abun da ya kamata mu maida hankali akansa?" "Abu na gaba a wurinki babu shi yanzu, sai dai ƙara maida hankali akan company, wanda kuma shima tare za muna yinsa" ya faɗi mata tare da sake maida hankalinsa a kan hanya. Haka har suka kaiga isa gida.
DARE.
Su Dady ne zaune a kan kujerar dining, kowa na kai wa ciki haƙƙinsa ba tare da barin bashi ba, "na tambayeki ɗazu baki bani amsa ba, me ya faru na ga kina ɗingishi?" Cewar Alhaji yana kallon Hajiya, Marwan da Saleem suma suka maida hankalinsu kanta, ban da Shuraim da hankalinsa yake kan abinci da kuma wayarsa, kan ta nemo amsar da zata bashi wayarsa ya fara ƙara, numbern Yazeed ya gani akan screen, tsayar da cin na sa yayi da murmushi sosai akan fiskarsa, ya kuma duban Hajiyar yana cewa, "ɗanki ne yake kira na, kuma na san akan maganar dawowarsa ne" murmushi na farin ciki tayi, domin ta san tayi kewan ɗan na ta, babu abin da take buƙata fa ce Ganin dawowarsa.
Ɗaga wayar Dady yayi, "my son how kana lafiya? Ya Australian?" Yazeed daga can gefen ya basa amsa da faɗin, "Fine Dad" "well, ya maganar tasowarka ɗin? Zaka haƙura sai next week or?" "No Dad! Nifa na ce maka zan ta so tomorrow, na gaji da garin nan, kuma ina da abubuwa masu mahimmanci da ya kamata na yi su, sannan ga auren Marwan, ko ba komai ya kamata ace ana komai a gaba na".
Dady ya ce, "shikenan Allah ya kawoka lafiya" da Ameen Yazeed ya amsa sannan ya katse wayar, sauke numfashi yayi yana jin ina ma ya riga da ya isa Kaduna, domin ba ƙaramin ƙosawa yayi ba, "zan yi tozali da kyakykyawata, tunanina, Safna ke ta dabance a rayuwata, kuma kina da matsayi sosai a cikin zuciyata, zan dawo na ganki" ya faɗi a hankali tare da murmushi mai haɗe da son ganin Safna da yake son yi, shafo gashinsa da ya sha gyaran turai yayi ya kuma cewa.
"shin kamanninki ya canza ne? Ko kuwa kina à yadda na sanki? A ah na ma san baki canza ba" ya faɗi tare da sauke hannunsa yana kwantawa kan lallausar kujerar da yake zaune a kai, "koda ma ace kin canza ɗin, na san kyau ne kika ƙara. Allah ya dasa min sonki cikin zuciyata Safna, kina kasancewa a duk wata kafa ta numfashina ako wace rana, ranar da zan isa garin Kaduna! Rana ce ta farinciki a gareni, kuma bayan barinki da nayi, bazan sake yarda nayi ni sa dake har haka ba, shin zaki aureni Safnah? Tambayar da zan fara miki kenan bayan nayi fiska da fiska da ke, kuma na san zaki ce, eh zan aureka".
Murmushin ƙarin farinciki yayi yana kuma cewa, "idan kuwa har kika bani wannan amsar, to babu wanda ya isa ya hanani aurenki sai dai mutuwa, koma me za a ce min babu abin da zai rabani da ke, domin soyayyarki da ga cikin zuciyata take", ya ƙarashe tare da sauke numfarfashin shauƙi na soyayya.
Fannin su Hajiya kuwa, cike da murna Hajiya ta ce, "ɗana zai dawo, wayyo daɗi, Alhaji wai bakayi kewansa ba ne? Tsawon lokacin da yayi baya nan amma kake maganar ya ƙara wasu kwanaki?" Saleem ya ce, "ai shi ba dawowarsa ba, kawai takura da zaiyi wa mutane, baka isa kayi ko wace irin magana agabansa ba sai kaji ya kai maka mazga a baki" "ya dai fi ku ai," Hajiya ta faɗiwa Saleem haka, cikin rashin jin daɗin abun da mahaifiyarsa take faɗi lokuta da dama Marwan ya ce, "Hajiya haka ko da yaushe kike cewa, daman na san kinfi son sa akanmu".
"Ba shakka! To dama bazan fi son sa ba? Ya fi ku kula da ni, ku kun maida ni ko oho a wurinku" Saleem ya ƙara faɗin, "amma dai Hajiya kawai faɗa kike yi, in ba haka duk abun da Yazeed yake amma ki ce ya fi mu?" "Komai ya wuce yanzu tun da zai dawo, sannan ku kuma! Na sha faɗamuku abun da kuke yi a tsakaninku ba dai dai bane, ku 'yan'uwa ne, bai kamata a rinƙa samun saɓani tsakanin ku ba" faɗin Dady bayan ya dakata da cin abincin, Marwan ne ya kula cewa, "hmm Dady shifa haka yake ne, don ni na san sai dai don wani abun ne zai sa ya dawo ba din aurena ba, domin ba ɗauka ta yayi wansa ba".
Da jin maganarsa Hajiya ta ce, "sau nawa nake faɗa maka ne Marwan? Akan wani dalili Yazeed zai ƙi zuwa aurenka? Ɗana ba zaiyi hakan ba" "shikenan ai! Dama son da kike masa ba zaisa ki ga aibunsa ba ai" Marwan ya faɗi yana barin wurin, shima Saleem miƙewa yayi harda tura plate ɗin abincin da yake ci gaba. Shuraim da tun da suka fara magana bai sanya musu harshe ba, sai ma lallatsa wayarsa da ya cigaba da yi shima ya miƙe daga zaunen da yake, ya furta musu, "good night" cikin girmamawa Dady da Hajiya suka yi masa sallama ya wuce.
"Wai ina Autana ne?" Dady yayiwa Hajiya tambayar, ta bashi amsa da cewa, "ta ce min zata je wani walima da suka haɗa ita da abokanta, ƙila suna can suna fama" "amma da dare haka? Ki daina barin yarinyar nan tana fita a irin wannan lokaci" "ai ina ga ma tana hanya" cewar Hajiya.
Bayan Hajiya ta koma ɗakinta cikin ɗingishi, domin ƙafafuwar har yanzu da ɗan sauransu, zama tayi gefen gado tana faɗin, "Oh ni Zainabu, haka za ayi wannan hidimar ƙafata yana kamar bolon-bolon?" Ta faɗi tana tunano abun da ya farun, tsakin takaici ta ja haushin Safna na sake karaɗe mata zuciya, tana farin ciki da ya kasance ɗanta Yazeed zai dawo, sai dai a gefe ɗaya tana tunanin bayan dawowarsa, domin ta san tabbas za a ɗaura ne daga inda aka tsaya, domin ta san ba makawa yana dawowa zai kawo mata magana akan Safna, gashi ita kuma har yanzu ba ta da kataɓus, "yanzu wani abu ya kamata inyi ne?" Ta faɗi tana ƙoƙarin tuno dabarar da ya kamata, sai kuma ta bar tunani da sakin wani shu'umin murmushi, murmushin da ke ɗauke da makirci.
"Ni ce fa Zainab, wannan wanda matsalarta baya bata wahalar warwarewa, nayi abubuwa da dama a baya kuma na ci nasara, to me zai sa wannan ƙaramin abun ya dameni? Inaa bai kamata na sa wannan tunanin a raina ba, kamar baya! Zan sake magance wannan matsalar ma cikin sauƙi" ta faɗi tana kuma murmushi.
WASHE GARI.
Amna ce cikin shirin zuwa company, doguwar rigar nan dai yauma ta sa kamar kullum, abaya ce mai tsada cikin wanda tayi siyayya, red colour ne amma ba mai haske sosai ba, ya kasance mai ɗaukar ido kaɗan, sannan ta yafa gele ruwan hoda da kuma takalmi, shima jakar ruwan hodar ne ta ɗauka , tayi kyau sosai, tsayawa tayi tana kallon masu aikin da suka shigo yanzu durƙushe a gabanta, "keh ce wacche a baya nakewa magana ba kya kula ni ko? Har da kalamai masu ɓata min rai bah?".
Baki na rawa cike da da na sani Hanne ta ce, "don Allah kiyi haƙuri ki min afuwa Hajiya" dariya mai ɗan sauti Amna tayi ka na ta ce, "ba wai in miki afwa ba, ina son ku kula da Ammu sosai kada wani abun ya sameta, idan kuwa na ji saɓanin abin da na faɗa muku to fa baza muyi zancen yafiya ba! Ta faɗi tana kallon gaba ɗayan su, "insha Allah zamuyi yadda kika ce" suka ba ta amsa ita kuma ta wuce zuwa gaban Ammu da ke kwance jikin har yanzu baya motsi sam, a cikin zuciyarta tayiwa Ammu addu'a tana yi mata kallon tausayawa sanna ta fice.
Tambayar drivernta tayi ko ya ga fitan Shuraim, amma ya ce a ah Shuraim bai fita ba, hakan yasa ta bashi amsa da cewa, to ya je daga yanzu ba da shi zata na zuwa company ba, cike da damuwa da tsoro ya ce, "Madam ko nayi laifi ne?" A ah ba laifi kayi ba, hasali ma zaka cigaba da aikin ka a gidan nan, amma zuwa company da dawowarsa ba da kai zan rinƙa zuwa b..." shiru bakinta yayi bayan ta hango Shuraim na doso inda suke, cikin shigarsa ta wando da riga masu kyau sosai, na baku zaɓin colour da kanku.
Kallonsa takeyi sosai, domin ya matuƙar tafiya da hanaklinta, "woooow" ta faɗi amma bata fitar da sauti ba, shima Shuraim ɗin tsayawa yayi bayan ya kusa isowa dab da ita, shima ta burgesa, kallon kallo suke wa junan su cikin wata farsaba daban, ko wanne kallon haɗuwar ɗaya yake, driver kam wucewa yayi ya barsu à wannan duniyar kallon kallon.
Mota ce tayi perking a ƙofar gidan, cikin motar Ruki ce da wani saurayi, har Ruki ta sa hannu zata buɗe murfin motar don fita, ya katse ta da buɗe bakinsa da yake baƙi alamar shan taba yana faɗin, "karki manta! Amsarki zuwa gobe kaɗai take da tasiri, idan ya wuce to kin rasani, just think about it" ya faɗi mata yana kallonta da jajayen idanuwan sa, "dont worry my man, ba zai ma kai gobe ba, zaka ji matsayata akan maganar" murmushi yayi mata yana kuma cewa, "ok sai na ji kin" itama murmushin tayi masa tare da ficewa daga motar, ita kuma cikin shigar riga da skirt baƙi masu kolliya na kanti, sun matseta sosai domin gaba ɗaya halittarta sun fito a ciki.
Tun jiya da ta fita bata dawo ba, a gurin partyn ta kwana da wasu abokanta, shigewa tayi cikin gidan kasancewar ba da mota ta dawo ba, domin dama ba da shi ta je ba, jiyan ma shi yazo ya ɗauketa.
Tana shiga idonta ya faɗa kan Shuraim da Amna da sukewa junansu kallo, wanda ita ta ɗauki hakan da na soyayya suke yi, baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyarta.
Wayar Shuraim dake hannnunsa ne yayi ƙarar shigowar massage, hakan ne ya dawo da su daga duniyar da suke, gaba ɗayan su wayan cewa sukayi, domin kuwa dukkan su sun saki layi, borin kunya suka hau yiwa junan su kowa na wai gawa kamar yana duba wani abu, Shuraim ne ya dakata da waigawan da yake ya furta, "madam C.E.O na yi miki kyau ne?" Juyowa tayi fiskarta alamar tambaya ta ce, "waa? Wai kai? Ni ce ma nake son tambayarka, don na ga yadda kake kallona ya wuce tunani, har wani hangame bakinka kayi"
Dariya ya sa yana faɗin, "mamala tell the truth, amma ya naga kinzo inda mota ta take? Ko dai yau kina buƙatar taimakon ne?" "See malam, in zaka je muje, in kuma baza ka je ba to ka faɗamin, domin yanzu tare zamuna tafiya" dariya kawai yayi yana zuwa ƙofar motar ya buɗe tare da juyawa inda take, alamar ta zo ta shiga, daɗin hakan taji a ranta, amma bata nuna masa ba, shiga tayi shima ya shiga tare sa yiwa motar key.
Ruki na tsaye suka wuce ta, yanayin yadda ta gansu ya tabbatar mata da sun fara soyayya, hakan ya sa a zuciya ta bar wurin kamar zata fashe. Ɗakin Hajiya ta nufa kai tsaye, à kwance ta samu Hajiyar hakan yasa ta yin saurin zuwa inda take tana tashinta, cikin rashin daɗi Hajiya ta yi zaune tana kallon Ruki tare da mutsutstsuka idanu, "Auta na kin dawo ne? Amma me yasa kika kwana? Bayan kin san sai da nayi miki gargaɗi akan hakan? Kin sa Alhaji sai tambayata ya ke yi akan ina kike? Har na ma rasa amsar bayarwa".
Ruki da take ɗauke da haushin su Amna da ta gani ne t'a fara magana, "Hajiya duk ki adana tambayoyin nan n'a ki, ni wata mahimmiyar magana ce ta kawo ni, don da ba haka ba ma bazan dawo yanzu ba" ta faɗi tana zama gefen Hajiyar, gyara zama Hajiya tayi, tana fiskantar Ruki ta ce, "magana? To ko wani kuɗin kika samo mana ne?" "Hajiya ke da an taɓo ki kuɗi, kudi" Ruki ta faɗi tana kau da kanta gefe tare da tura baki, "to me aibun hakan? Ai kuɗi sune warakar duk wata matsala, kuma aljannar duniya ne su, su ke siyarwa mutum daraja, kiga ana binsa kamar sarki".
"Hajiya duk ƙyale wannan maganar, muyi magana akan abun da nake son sanar miki, lokacin da na shigo gidan nan kin san suwa n'a gani?" Hajiya ta bata amsa da cewa, "a ah faɗamin me kika gani?" "Shuraim ne da Safna, kuma sai kinga yadda suke wa junansu kallon ƙauna" ta faɗi cike da jin haushi, itama Hajiyar cikin takaici ta ce, "kallon ƙauna dai? Ba shakka yarinyar nan ta samu wuri tayi bake bake, wato Shuraim ɗin da nakeson ya mallakeki saboda dukiyar ubansa shine ita tayi masa kutse, sannan idan ɗana ya dawo in kuma samun ƙarin baƙin cikin, amma kar ki damu na riga da na shirya wani abun"
Ruki ta fiskanci Hajiya tana cewa, "dama na riga da na faɗa miki, wallahi wannan yarinyar ta fi ƙarfin mu yanzu, ta zame mana nan gani nan bari, kuma n'a tabbata a yanzu Shuraim ya faɗa cikin sonta dumu-dumu domin dama na fara ganin wasu alamu na hakan. Amma ni ko nayi masa magana baya tanka min, duk yadda zanyi masa don inyi hira da shi koda kaɗan ne baya bani dama, gaisuwan ma yadda kika san dole haka yake amsawa, amma ita ai kinga har surutu yake da ita, har da dariya cikin farin ciki".
"Na ce ki kwantar da hankalinki Auta na, domin tuni n'a kamo hanyar da zanyi maganin komai" Ruki ta ce, "Hajiya duk bar komai yanzu, na riga da na yanke hukunci, zan auri wannan saurayin nan nawa Jaiz kawai, idan ba haka ba zanyi biyu babu, kuma gashi ya bani zaɓi, idan har ya kai gobe ban amince da aurenshi ba, to shi kenan zamu rabu" zaro ido Hajiya tayu jin maganar Autar ta ta, sannan ta ce, "ke me kike faɗa haka? Kuma me yasa zai ce miki nan da gibe?".
"A gidansu ne aka ƙiyasta masa hakan, idan har zuwa gobe bai fitar da mata ba, to fa zasu yi masa auren dole, shi kuma yana sona sosai, shiyasa muke so idan har komai yayi kawai ayi auren lokaci ɗaya da na Marwan" juyar da kai Hajiya tayi tare da tunanin abinyi sannan ta juyo haɗi da matsowa kusa da Ruki ta ce, "ke m'a kin san hakan da wuya, yaufa saura kwana shida fa ayi wannan auren, ko dan kinga ba na yin shirye shirye ne shiyasa? To abin da yasa na ƙi tara mutane shine, domin na san kashe kuɗi zamuyi sosai, saboda kowa baje ƙafa zaiyi ya kwashi garaɓasa, din haka nake so sai saura kwanaki uku zan fara hidimar, sunanan suna ki ra na, Hajiya akwai abun da za azo ayi ne? Hajiya na jiki shiru ko an ɗaga bikin ne? Haka suke tambaya ta, ke kuwa da jin haka kin san kwaɗayi ne zai kawo su, shiyasa nayi wanna dabarar".
Hajiya tayi maganar cikin maƙon zuciya, sannan ta kuma cewa, "amma kiyi maganar haɗa aurenki rana ɗaya da na Marwan sai ka ce a duniyar cinnanku?" Ruki ta ce, "Na san kwanakin da ya ragen Hajiya, domin nima dama ina shirye shirye yadda tarona zaiyi ni da ƙawayena, kawai abin da nakeson ki fiskanta Hajiya, wannan bawan Allahn in har na rasa shi to wallahi munyi gagarumar asara, har fa cemin yayi idan akayi aurenmu da kamar wata biyu zai mallaka miki wadu kadar..." "keee 'yannan kice haka yake ɗan albarka? Wayyo Allah daɗi! To amma abun dubawa shine Alhaji, na san da ƙyar ya amince".
"Hajiya ki dai duba tagomashin da zamu ɓarza a wannan lamarin, kar hakan ya wuce mu, domin na san Shuraim kam ba so na zaiyi ba, kuma babu tabbacin zan samu wani kamar Jaiz, sannan uwa uba yana matuƙar sona" sai da Hajiya ta ɗan zurfafa tunani ka na ta ce, "shikenan! Kwantar da hankalinki, zanyi duk yadda zanyi inga anyi wannan auren rana ɗaya da wanki" cike da murna Ruki ta ce, "yauwa Hajiya shiyasa nake godiya da ya zama ke ce uwata", murmushi Hajiya tayi suna rungumar juna.
Yazeed.
Kamar yadda ya ce, tun da safe ya taso ƙarfe shidda na safe jirgin ya ɗaga. Hoton Safna yasa yana kallo haɗi da murmusawa, shima yayi kewan familynsa sosai, amma yana ganin kamar don ita kawai zai dawo.
Bayan kwanakin da yayi yau dai Allah yayi ya iso, Dady da kansa ya tarbesa à airport, cike da murna ya rungume Dady, yayin da Dady yake masa maraba, shiga mota su kayi driver ya ja, jikin Yazeed har wani kaɗawa