Showing 24001 words to 27000 words out of 129098 words

Chapter 9 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

20

umurce ni da na kawo sa inda muka bari yanzu, da kuma bani wani abu da na fesa masa, ni kuma naga da kai yakamata munƙar-ƙare aikin, saboda kai masoyi nane kuma abokin cin Mushe shi yasa na janyo ka ciki".

A jiyar zuciya ya sauke da jin batun ta yana ƙara cewa, "cab gaskiya my beb son kuɗin ki yayi over, nifa da kika min bayanin aikin na ɗauka wanda kika sani ne, kamar yadda aka saba, irin na mutumin da ya baki aiki akan ki ɓata wa Hajiyar aikin su suna, da dai sauran abubuwa da muka sha yi, ashe gaibu kika kama, to amma ya akayi kika samu abunda kika fesa masa mai ƙarfi haka, taya suka baki ba tare da kin ga waye ba?"

"Bayan mun rabu da guy ɗin ne, suka sanar da ni inda zan ɗauka" Cewar Zilla ya kuma cewa, "ok, amma ina ce kina da numbern su, ki kira mana su kiji ya batun kuɗin, in muka samu kuɗin nan ai mun warke" dariya Zilla tayi sannan tace "Shege my love maganar kuɗi ba wasa" "a kinga laifi na?" "To nidai ko na kira numbern baya shiga, sai in sun kira" "gwada kira yanzu" yace mata dan shi har ya fara kasafta kuɗin a ran sa, saboda yasan Beb ɗin sa Zilla n'a ji dashi sosai, yasan tare zasu amfana kuɗin.

Tana dialing kuwa ya fara ringing, da murmushi irin nasu na Bariki tace "duba ya shiga" "yauwa shiyasa nace ki gwada" Cewar Nass cike da murna dan ji yake kamar kuɗin ne suka zo, 50 millions ba wasa ba.

Saida wayar ta kusa tsinkewa aka ɗaga, kan tayi magana taji ance, "à sauka lafiya" cikin wata irin murya mai kauri, "a sauka lafiya kuma?" Sai dai kafin ta kai ga ƙarisawa, hasken wata babbar mota ya dalle su, zaro ido su kayi kamar idon zai fito waje, sabida mutuwar da idon su ya gane musu, na yowa kansu, sai dai kafin Nass ya nemo tinanin yadda zai kauda motar, babbar motar ta bi ta kansu, --sai dai muce Allah yaji ƙan rai.

Fannin masu Fararen kaya kuma, kutsawa cikin dajin suka fara yi, yadda kasan da rana suke tafiya, --ban samu damar ganin hanya da kuma shiga Dajin ba, sai anan gaba zaku ji--.

09:00am

Shocking ɗin wuta da ya ratsa duk wata kafa ta jikin sa ne yasa shi farkawa cikin tashin hankali mai ɗauke da à zaba, hannun sa ɗaure da sarƙa, haka ƙafafun sa, sai Igiyoyin wuta dake kewaye da jikin sa,, zazzare ido ya fara yi a cikin duhun wurin domin kuwa, babu alamar haske ko kaɗan, "waye a nan? Ka fito mana" shine abunda Baba yake ta nanatawa a bakin sa, an ɗau lokaci ba tare da yaji ko motsi ba, sai shocking ɗin da ake kunna mai lokaci lokaci, à zaba yake ji a gaba ɗaya ilahirin jikin sa, idon sa duk ya ƙan-ƙance saboda wahala, sai is kar wahala daya ke furzarwa a bakin sa.

Lokaci ɗaya ƙwan Fitila da ke daidai saman kan sa ya ɗau haske, ya bayyana a daidai inda yake, rintse ido yayi yayin da hasken ya haske masa Idanu, takun ta kalmi ya fara ji a hankali har izuwa inda yake, buɗe ido yayi a hankali, jin alamar mutumin na tsaye akan sa yasa shi ɗaga kansa dan ganin Mutumin?.

Mutumin sanye yake da riga da wando cort Fari, irin manyan mutanen nan ne, ga jiki ga tsawo, sai dai baiga Fiskar Mutumin ba sabida kan sa na saman ƙwan Fitilar, "who are you?" Baba yayi masa tambayar da ƙyar, dariya ya ƙyalƙyale da shi sannan yayi shiru kamar bashi yayi dariyar ba, ya fara magana cikin isa.

"Kana son sanin ni waye? Sanin waye ni ba shida amfani a gare ka, Ɗan Jarida mai ƙaramin Ƙoƙolwa, amma karka damu zan sanar da kai kafin ka wuce garin da ba'a dawowa" ya faɗa hakan haɗi da jawo kujerar da ke kusa ya zauna.

Duk da har yanzu hasken na hana shi damar ganin fiskar sosai, amma ya daure ya ɗaga idon sa kan mutumin, baƙi ne irin wuluk ɗin nan, wanda yake kyautata zaton cikin zuciyar sa ma haka take, sai ƙananun idanuwan sa Jawur "ko kasanni ne?" Mutumin ya faɗi haka ganin yadda Baba ke kallon sa.

Ya cigaba da cewa "Kai wawan Ɗan Jarida ne, ba tare da wata wahala ba sai ga ka a hannu na, na ɗauka kama ka zai zama kamar kama Kare ne, ashe ko Mage baka kai ba" ya ƙarashe da dariya.

"Bincike akan Ƙungiyar mu kamar wasa da rayuwar ka ne, kokuwa ince ka yi wasa da rayuwar ka, ko bataliyan Sojoji basu isa sukawo ƙarshen kungiyar mu ta POSPA ba bere kai Kiyashi, babu wanda ya isa ya ga Sirrin Shugaba ZABBA BA, koda kuwa mu ne, bere kai ƙaramin alhaki".

Ba ƙaramin nauyi Bakin sa yayi masa ba, da ƙyar ya iya buɗe bakin sa ya fara magana cikin rarraunar murya "kenan ba kai bane Shugaban? Ku wasu irin marasa imani ne? Kun lalata tarbiyyan al'umma da dama, kun kashe wasu da dama, kuma har yanzu kuna kai, saboda tsaban hatsarin ku kuke kashe duk wanda yayi yunƙurin fito da gaskiya a kan Ƙungiyar ku".

Shocking ɗin da ya ƙara ziyar tan Baba ne yasa shi yin shiru, jinkin sa yahau karɓar shocking ɗin sai rawa yake, hatta leɓen Bakin sa, ba tare da tsayar da matsa madannin Igiyoyin ba Baƙin mutumin yace "dogon lokaci babu wanda ya sake fito da maganar POSPA sai kai yanzu, tun daga lokacin da sunan ƙungiyar mu ya yawaita ta akan binciken ka Idon mu ke kan ka, mun ɗauka a iya maganar ƙwayar zaka tsaya, amma neman inda kungiyar take dan ka ruguza ta babban kuskure ne"

Tsaida maganar yayi da cire hannun sa kan madanin, a jiyar zuciyar wahala mai ƙarfi Baba ya sauke, lokacin da shocking ya sake shi, da ƙyar yake fitar da numfashi, har ƙolla ido sa yayi sabida a zaba, "duk abinda kuke yi Allah na kallon ku, yadda kuke cutar masa da Bayi, tabbas ku jira yi na ku sakamakon nan bada daɗe wa ba" Cewar Baba cikin murya ƙasa-ƙasa dake ɗauke da raɗaɗi.

Cigaba da magana Baƙin mutumin yayi, "gode min za kayi da na zaɓan maka mutuwa mai sauƙi, yau zaka baƙunci lahira idan kaje sai ka haɗu da wa'enda su kayi kuskure irin na ka" Yana ƙara she maganar ya miƙe haɗi da matsa madannin shocking ɗin, take ta cigaba da aikin ta a gaba ɗaya jikin Baba.

Dariyar mugun ta ya sake kwashewa da shi, ya nufi hanyar fita.

AMNA.

Dukkan su hankalin su ya tashi ganin cewa tun yamma ba Baba bai kira su ba, bayan tun da ya tafi hakan bai faru ba, sannan wayar sa ba ta shiga.

Suna zaune tsakar gida kamar kullum in za suci abincin safe ko Dare, sai dai yau ga abincin amma kowa ya kasa ci, Amna ce ta kira numbern Uncle Tukur a bokin Baba, take tambayar sa ko yaji labarin Baba, amma yace "a ah nima tun safe bamuyi magana da shiba, amma ku kwantar da hankalin ku, tayu wata 'yar matsala ce ta hana shi kira".

Amna tace "Uncle mun kira wayar sa baya shiga" "to ƙila ko wayar ba caji ne, amma mujira zuwa gobe" "toh Uncle nagode Allah ya kaimu" Amna ta faɗa masa tare da yi masa sallama.

"Allah yasa lafiya, dan ni hankali na yaƙi kwan tawa" Cewar Mamma cikin damuwa, Mubarak yace "insha Allah Mamma yanzu dai kuci abinci, Domin kunsan Baba baya son rashin cin abincin ku, idan yaji kunƙi ci zai yi fushi" Ummee tace "hakane to muci ko".

Amna kuwa shiru tayi kamar mai tinanin wani abu, sai da Mubarak ya taɓo ta tukunna ta farga da tinanin.

#To Ƴan-uwan arziƙi, kun dai ji yadda ta kasance da Zilla ashe saka ta akayi.

ta tafka zunubai da yawa, ta yi sanadiyyar sa mutane da yawa cikin matsala, duk akan kuɗi, sai gashi ajalin ta yazo cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da ta tuba ba.

Ya Allah ka kare mu da aikata abun da ka hanemu da yinsa, wa'enda suke da hali irin na Zilla, Allah ka shirye su.

Ga Baba kuma cikin Uƙuba, shocking zai kashe sa ko kuwa?

Me yasa Mutanen nan sa kaya Fari?

Nasan kuna nan kuna wasu tambayoyi a zuciyar ku,

To ku cigaba da kasan cewa tare da Alƙalamin taku {Mrs Umar}

______________________________________________________________________________________________

Part 2️⃣7️⃣▶️2️⃣8️⃣

WASHE GARI.

Abu kamar wasa basu ji kiran Baba ba, Mamma ce tayi tinanin kiran wani daga cikin 'Ƴan-uwan Takori, sakamakon wayar da sukayi yasa su shiga cikin tashin hankali, domin kuwa an tabbatar musu da cewa Baba bai je ba, ko alamar sa ma basu gani ba.

Amna da kamar ta fara fahimtar wani abu ta je ɗakin Ummee, ta jira Ummee ta idar da Sallan Azahar, sannan taƙarisa dab da ita ta ce, "Ummee inason zuwa gidan Uncle Tukur". "Me za kije yi"? Ummee tayi mata tambayar daidai shigowar Mubarak.

Zama yayi a gefe shima, lokacin Amna ta ce, "Haka kawai Ummee please ki bar ni inje, ba daɗewa zan yi ba" ta ƙarashe faɗi haɗi da marai-raice fiska, dan so take taje sabida wani dalilin ta, "muje tare" cewar Mubarak, "a'ah ba inda za ka, kaida kake fama da jikin ka" Amna ta faɗa mai haka, Ya ƙara cewa, "naji sauƙi ai yanzu".

Maida kallon ta tayi gurin Ummee tana ƙara roƙon ta, "kije amma karki daɗe kamar yadda ki ka ce" "toh Ummee na gode sai na dawo" ta faɗi tana miƙewa tafita a falon, Mubarak yana mata maganar tare za su, amma ko juyowa bata yiba, saboda ba ta son rakiyar ta sa, 'yar ƙaramar shiri tayi, sannan ta sa glass ɗin ta, sai wayar ta a hannun ta, shiga Napep ɗinda ta tara tayi.

A ƙofar gidan sa aka sauke ta, da sallama ta shiga, gaishe da matan sa guda biyu tayi, suka sanar da ita bai dawo ba yana office, babu ɓata lokaci ta fita daga gidan ta kuma taran wani napep ɗin zuwa gurin aikin Tukur.

Wayar ta ce tayi ƙara, numbern abokin ta Wali ne akai, tana ɗagawa tace "Wali ya kake, sorry ina ɗan wani uzuri ne, inna gama i will call you back". "No Amna listen, wani abun tashin hankali zan sanar dake, nasan kinfi Mubarak dauriya shiya sa nake..." sai kuma yadakata, sabida abinda yake son sanar da ita shi kansa, ya shiga cikin tashin hankali da ganin sa, amma yana da tabbacin bata gani ba sabida Amna ba gwanar shiga internet bace.

"Wali faɗamin mana, meyafaru dan daga jin ƙarar kiran da ka mini na tsinci kai na cikin wani yanayi" cewar Amna haɗi da buɗe kunnuwan ta dan jiye mata abinda Wali keson faɗa, "Kin kalli labaran GT kuwa? kina ina ne?" Yayi mata tambayar, "a'ah, just tell me what you want to say"? "Bazan iya faɗa ba, saboda, amma dai ki shiga labaran GT dake wakana yanzu, sabida suna ta nanata lamarin, Gidan Radion nan na Kaduna".

Katse wayar tayi ba tare da ta yi masa wani magana ba, ta buɗe Data, dan ganin meke faruwa, tashin hankali ba'a sa maka rana, hoton Baba taci karo da shi an maƙala a kan labarun GT mai kawo rahoton yana cewa.

"Labarun GT kuke saurara, Assalamu alaikum Jama'a barkan ku da wannan lokaci, labarin mu na yau shine, yau an tsinci gawan wani bawan Allah anan garin Kaduna, ya mutu ne bayan yayi shaye-shayen sa yayi maƙil, a gefen titi aka tadda shi, a binciken hukumar, gawan ba na yau bane, a ƙalla zai yi kwana biyu, hakan yasa aka bada damar yi masa jana'iza ba tare da nemo iyalan sa ba".

Saurin fita daga wurin tayi ba tare da ta ƙarashe jin maganar ba, ta rintse Idanuwan ta da ƙarfin gaske, gaba ɗaya jikin ta ya ɗau kyarma, buɗe idanun tayi har sun fara canza kala, ambaton sunan Allah ta farayi cikin tashin hankali, ganin abinda ke faruwa yasa mai napep ɗin cewa, "Hajiya lafiya dai?" Baki na rawa tai masa magana da ya maida ta Gida, tare da sanar dashi sunan unguwar.

Tinanin zasu iya sake labarin nan a tashan labaran da Ummee take gani ako da yaushe tayi, hannun ta na rawa ta duba numbern Mubarak, yana ɗagawa cikin ɗimuwa ta ce, "Mubarak ina Ummee?" "Mamma na ɗakin ta, Ummee kuma i think taje kallon labaran duniyar da take gani da rana" ƙara shiga tashin hankali tayi ta ƙara cewa "yi maza kaje Kasan yadda zaka hana Ummee kallon labaran nan".

"Sabida me? lafiya kike kuwa? Ya naji voice ɗin ki haka?" "Stop asking, just do what I say" Cike da rashin fahimta yace, "ok" tare da nufan falon Ummee, sai dai mai afkuwa ya afku, domin kuwa daidai lokacin da aka kawo fiskar Baba ya shigo, yayin da mai kawo rahoto yake zubo maganganu.

Zaro ido waje Mubarak yayi yana faɗin, "a'ah, no, noooo" Ummee kuwa numfashin ta ne ke niyyar barin jikin ta, saboda tsaban shock da tayi da jin abinda aka faɗi a kan mai gidan ta, Mamma ce ta shigo tana tambayar "lafiya"? Sai dai itama idon ta ya gane mata, kunnen ta ma ya jiye mata.

A take shock ɗin Mamma ya fi, domin kuwa ita sakin jikin ta tayi, tayi ƙasa, tashin hankalin su ne ya ƙaru, ganin abinda ya samu Mamma, lokacin mai napep ya sauke Amna a ƙofar gida, sai dai fa yau duk wanda yayi tozali da idon Amna sai ya tsorata, sabida yadda fiskar ta yake ɗauke da tashin hankali muraran, duk da bata cire glass ɗin ba.

Tun daga Ƙofar gida take jin ƙarar Ummee da Mubarak, yadda ta iske Mamma sai ya ƙara ɗora ta cikin wani tashin hankalin, ba tare da ta ƙarasa ciki ba, "Muje Asibiti, mu kai ta kada wani abun ya same ta" Cewar Ummee cike da fargaba sai kuka take, Mubarak kuwa duk da cewa namiji ne shi, amma hawaye ne ke ta zarya a kumatun sa.

Da sauri ta ƙarasa inda Mamma take tare da cire glass ɗin idon ta, tayi wulli da shi "Ummee ku dai na kuka ba sai an kai ta hospital ba zata tashi" ta faɗi bayan ta taɓa kai da wuyan Mamma, ita kaɗai ta ɗaga Mamma ta mayar da ita ɗaki zuwa kan gado, ta lulluɓe ta da bargo ta koma gurin su Mubarak, sai dai har lokacin ko ɗigon hawaye bai fito daga cikin manyan Idon ta ba, sai launin ja da ya kewaye farin, yayin da zuciyar ta kuma ke cike da tashin hankali, amma gwara ta daure taji da na familyn ta.

A yadda ta barsu ta dawo ta same su, "Mubarak ɗin Baba ka daina kuka ka ji, kaida yakamata ka rarrashi Ummee amma kake kuka?" Ta faɗi tana riƙe masa hannu alamar rarrashi, komawa gurin Ummee tayi, tana bin ta da kallon tausayawa, tace "Ummee nah ki daina kuka..." katseta Ummee tayi da faɗin.

"Amna cewa fa su kayi Baban ku ya mutu ko baki ji bane? kuma wai sanadin....!" sai kuma ta fashe da kuka, ana haka sai ga shigowar wasu daga cikin maƙoftar su, jin kamar da matsala a gidan, nan suka fara taimakawa Amna gurin rarrashin su Ummee.

Lallai gaskiya Amna jaruma ce, irin wannan jarumta haka, yadda ta daure ta ɓoye duk tashin hankalin dake zuciyar ta--

Komawa ɗakin Mamma Amna tayi, lokacin kuwa Mamma ta fara motsi, wucewa kitchen tayi da sauri ta ɗibo ruwa a glass cup ta dawo, a hankali ta ɗago ta haɗi da gyara mata zama ta bata ruwan ta sha, hawaye masu zafi Mamma ta fara fitar wa, tana faɗin, "shiyasa na hana shi zuwa amma yaƙi, me yasa zai min ƙaryan zuwa ziyara, ashe abinda zai je yi kenan".

"Dan Allah Mamma nah kar kice haka, kece mutum ta farko da zaki ba da labarin Baba, kinsan ko à mafarki bazai aikata hakan ba" kuka Mamma ta sa tana ƙara cewa "nasan haka, amma me dalilin sa nayin ƙarya?" "abinda yakamata in sani kenan" cewar Amna a cikin zuciyarta.

Su Wali, Zarah da Nabila ne suka zo suma, dan su rarrashi abokan na su, kusan magriba suka koma, Ummee da Mamma ko magana babu sai ido kawai musamman Mamma, suna zaune gaba ɗayan su a ɗakin Mamma, Amna ce ta tashi kamar antsikare ta, ta wuce uwaɗɗakan Ummee, tana shiga ta durƙushe a ƙasa, sai a lokacin take ji kamar yanzu ne abin ya faru.

Kukan da ta jima bata yi ba ne ta fara sakin sa mai ratsa zuciyar mai sauraro, kuka take sosai kamar ran ta zai fita, komawa gefe tayi, ta haɗe ƙafafuwan ta da hannu guri guda, tana ci gaba da kuka, idon ta ya canza kala, gashin ta da ya warware daga ƙullin da tayi masa tun da safe, sai ya barbazu a kan fiskar ta.

"Me nene yake faruwa ne? Baba menene yasa ka ƙi sanar damu dalilin...?" ba tare da ta ƙarashe maganar ba ta miƙe tana tinanin wani abu, sai kuma ta ciro wayar ta dake cikin aljihun wandon ta, da sauri-sauri take ƙoƙarin ƙara kamo labarin, zama tayi tana ƙara sauraron abinda suke cewa a ciki daidai wurin da, "a binciken hukumar, gawan bana yau bane, a ƙalla zai yi kwana biyu".

Tsaidawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login