Showing 6001 words to 9000 words out of 129098 words
Chapter 3 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
a makaranta".
Saurin ɗago kai tayi, tana kai dubanta gareshi cike da mamakin tambayar tasa, daidai shigowar Hajiya ɗakin riƙe da plate ɗin shayi, mai mai ta tambayar yayi à karo na biyu, kan Safna tayi yunƙurin magana Hajiyar tace "Alhaji kenan" ta faɗi haɗi da miƙa masa cup ɗin shayin tana cigaba da cewa,
"Alhaji kenan to tunda har tagaji da makarantar kawai ka rabu da ita, tunda ita tafaɗi da bakin ta" zuciyar Safna ne yafara zillo kenan abunda Hajiya ke shirin yi mata kenan.
#
EN UWA NA, HAR YANZU BAMU SHIGA LABARIN KA'IN DA NA'IN BA FA, INA FATAN KUNA FAHIMTAR LABARIN.
LABARI NE ME CIKE DA SARƘAƘIYA, SAI KUN CIGABA DA FOLLOWING ƊINA SANNAN ZAN WARWARE MUKU KOMAI.
ALKALAMIN TAAKU
Aisha G Umar ✌🏽
______________________________________________________________________________________________
Part 0️⃣7️⃣▶️0️⃣8️⃣
Sai da ya kurɓi tea ɗin sannan yaƙara faɗin "hakan kikeso Safna?" Kanta yunƙura dan yin magana, ya shigo ko sallama babu, tun kan yayi magana idonsa ya faɗa kan Safna, "what are you doing here?" Ya furta haɗi da haɗe fiska, "hee Yazeed, she's my daughter, zata iya shigowa lokacin da takeso kamar dai kai" Dady yabasa amsa. "Amma ba a ƙasa take yin magana dakai ba?, yau meya kawo ta?" Ya ƙara tambaya.
"So take ta bar school, shine na keson naji masalar" "barin school kuma?, to tayi me a gida? rabu da ita dad ba tinani mai kyau bane" Yafaɗi yana hararar inda take, kanta na ƙasa yayin da zucuyar ta ke motsawa haɗi da tsoron abunda dady zai ce.
Ƙara faɗin "baza kibar zuwa school ɗin ba, maza kije ki shirya ki wuce" Yazeed ya faɗa, saurin tashi daga inda take tayi, ta fice, ranta fal farin ciki, koba komai taji daɗin zuwan sa, zata cigaba da zuwa school ɗin ta, Yazeed yafi raga mata akan sauran yaran, hakan yasa koda wasa bata son shiga harkar sa.
"Dad ai da baka saurare ta bama" Dady yace "well dama so nake naji dalilin ta, amma ni kaina ai nafison taci gaba da karatun" Yafaɗi yana miƙewa yayi musu sallama zuwa company.
Bayan yafita, cikin takaici da haushin ɗan nata, tace "kai Yazeed!, wai menene matsalar ka da yin Makarantar Safna ko rashin sa ee?" "No momy she's a little girl shiya sa zatayi tinanin hakan, taya za'abar ta tabar school ta zauna tayi me a Gida?, file ɗin dana baki ajjiya nazo amsa, jirana ma ake"
Cike da haushin maganar sa ta ɗauko mishi file ɗin, batare da sake yin magana ba ya fita.
Binsa tayi da kallon takaici, yadda ya rusa mata ƙaramar plan ɗin ta, ita tama rasa gane kan Yazeed, tsana ya ke nunawa ƙasƙas-tacciyar yarinyar nan kokuwa kula da ita yake?,
Bayan isar ta ƙayataccen makarantar irin wanda ake kira sai ɗan wane da wane, nufan ajinsu tayi, tun kan ta ƙara sa ciki Aminiyar ta ɗaya tilo Raheena ta taho haɗi da yimata oyoyo, ta kama hannun ta har izuwa mazaunin su suka zauna, Raheena tace "ya akayi kikayi latti besty? najira ki, har nayi tinanin tahowa kikayi" ciro littafin ta tayi ba tare da tace mata komai ba.
AMNA
Bayan me kunnuwan jaki ya gama lecture suka fito shan iska waje, zaune suke kusa da wata bishiyar Limis, a kan wasu daga cikin bencin makarantar, suna cin gurguru, su na hira, su huɗu, Amna, Zara, Nabila, da kuma Walid. Zuby ce tazo wucewa itama da ƙawayen ta, Jamila, zaliha.Tsayawa tayi tafara binsu da kallon tsana, wanda bakowa bane ya haddasa wannan tsanar face Amna.
Zuby yarinya ce mai matuƙar ƙoƙari, saidai tauraron ta ya dishe ne sanadiyyar zuwan Amna ajin su, saboda Amna ta take ta ƙoƙari matuƙa, bata taɓa zuwa na ƙarshe aduk abu na karatu, itace ta dawo ɗaliba mafi hazaƙa a jin su, duk da kuwa bata ɗaukar raini ko kaɗan, itafa Amna bataƙi su daku da kowaye ba, indai yashiga harkar ta,
su karan kansu samarin makarantar basa gigin zuwa mata da maganar banza, bare ayi maganar SO, ai basu samu wannanr fiskar ba, saboda daidai take da uban kowa, Hakan kuwa baƙaramin tsana ya haddasa mata, a cikin wasu daga cikin ɗaliban makarantar ba, musamman Zuby da ƙawayen ta, da kuma wasu maza biyar da ba a ajin nasu suke ba.
sunyi matuƙar sa mata ido akan glass ɗin da take sawa, har wasu na tunanin ko tana da matsalar ido ne, so suke kawai wata rana suga idon da take rufewa,Amna ba tada girman kai fannin karatu, wasu da dama sukanzo wurinta tayi musu bayani akan Subject ɗin da basu gane ba.
"Keh Amna duba yadda Zuby ke mana wani irin kallo" Zarah ta faɗi tana taɓo kafaɗar Amna, ahankali ta kai idon ta izuwa inda su Zubyn suke, sai da ta taɓe baki kana tace, "rabu da ita babu abinda zata iya sai kallon ai" kasan cewar babu tazara a tsakanin su yasa maganar ta shiga kunnen Zuby.
Takowa Zuby tayi izuwa gaban su ta dubi inda Amna take sannan tace "ke Makauniya! ki kiya yeni niba kalarki bace, don haka kishiga taita yinki bafa tsoronki muke ba!" "Lallai Zubi, ke har zaki cewa Wanke hannu ka taɓa Makauniya, to kishiga taitayin ki, da alama baki san me ake kira da Danger ba ko?" Wali ya faɗi hakan,
Murmushin gefen baki Amna tayi, Jamila kuwa cewa tayi, "don Allah rufa mana baki, dubeka ko kunya ba kaji namiji ɗaya cikin mata" kwashewa da dariya su Zubi suka yi, a hasale ya miƙe, dakatawa yayi yayinda Amna ta daga mai hannu, ta miƙe ta fara takawa izuwa gaban Jamila, ta fara magana.
"Jamila kike ko Jumla?, inace ke kin taɓa ɗanɗana jan layin kinsan yadda yake, toh zaifi miki salama ki sawa bakinki kwaɗo" riƙe kumatu Jamila tayi yayin da ta tuna marin da Amna ta taɓa yi mata, komawa gun Zuby tayi, ta cigaba da faɗin "ke kuma!, ni nafi ƙarfin in kiyaye ki sai dai in ƙyamace ki, saboda baki fara wanka ba bare har kifita inga abun kiyaya a tattare da ke" tafaɗi tare da juyawa.
Zuby bata iya cewa komi saboda ba ƙaramin gamawa da ita Amna tayi ba, sukuwa abokan Amna dariya suka farayi har da ƙyalƙyalewa, da kyar suka tsaya da dariyar suka furta, "da kyau!". Nabila tace, "wow Amna kinyi wallahi" murmusawa kawai Amna tayi ta furta, "let's go" suka wuce su kabar Zubi da tawagarta.
Kiran Mubarak ne ya tsaidasu, yana faɗin "ashe ta nan kuke" "Aboki na ya akayi yau kun daɗe a class" "bari kawai wali yau dogon karatu mukayi" murmushi dukan su sukayi, Zarah tace "Mubarak anyi abu baka nan" "wani abu?" "gani ya kori ji naso ace kagani" Nabila ta faɗi hakan, Mubarak yakuma faɗin "hmm nasan bai wuce Amna ce ta buga game ba, saboda nasan ta" dariya sukayi.
Wali yace "Kasan sistern ka she doesn't take affence" "it's ok" Amna ta furta ta sa hannu a jakan ta fito da gurgurun da yake daure a leda yaji madara, tana ƙara faɗin "ga naka dan na kusa cinyewa ma" "aiko da kinbiya" Yafaɗi bayan ya ansa, shima ya fito mata da chocolate yace,
"kinga chocolate ɗin da na siya miki, amma bazan baki ba" kwacewa tayi "basai ka bani ba na ƙwata" gaba ɗayan su suka sa dariya. Mubarak bai da Abokai, hakan yasa Abokan Amna ne nasa.
YAU ASABAR RANAR HUTU,
Gari ya waye tangararan, zaune gaba ɗayan su suke akan tabarmar Ummee suna karin kumallo, Amna tace "Ummee me zaki dafa mana da rana" "ko gama cin na Safe bakiyi ba amma kina tambayar na rana" "eh ɗin ina ruwan ka" mubarak yakuma cewa "akoi ruwana ai Ummee na kika tambaya" dakatar dasu Mamma tayi da Fadin
"kai kai so kuke ku ƙware ne?, to bari kuji bamai kawo muku ruwa in ku ka ƙware kuna abu kamar ƙananun yara" dariya Ummee da Baba sukayi, Amna ce ta dubi Mubarak tace, "laah Mubarak da kai fa Mamma take" "a ah dake dai, dan Mamma ɗaukar ki take ƙarama"
Bugu ta kai masa a cinya, tare da hararar sa, "wai Allahna wannan hannun ƙarfen naki kika samin?" Darawa su Mamma suka yi, mamma tace "Ƴan rigima" "yakamata ace Amnata ta fara girki tunda batason akira ta da ƙarama ko?" Baba Yafaɗi hakan yana kallon Amna, Ummee tace
"aikuwa dai gata ta tsani ko zuwa kitchen bere girki itafa kawai a dafa abata" "cab Ummee to ai in mutum yaci Abincin Amna wllh sintirin bayan gida zaiyi ranar, kofa riƙe ludayi bata iya ba" turo baki tayi tana faɗin "Mamma kin ganshi ko!" Dariyar suka ƙara yi, Ummee tace, "yaran nan in ka biye su, baza kaci abinci ba har yayi sanyi,
KADUNA Safna
Ba ƙaramin ruwa akayi ba jiya da dare gari ya ɗau sanyi sosai, hakan yasa bacci yazama mai Daɗi a wurin masu gata, amma Safna kuwa, kasan cewar yau Asabar babu Makaranta, hakan ya zame mata dole da ta tashi tayi dukkanin aikin cikin gida, koda kuwa saukan ƙanƙara ake. Sanin hakan yasa tunda suka tashi asuba sukayi sallah su kayi karatun Alqur'ani, batayi gigin komawa bacci ba.
Lulluɓe Ammu tayi da lallausan bargo, ido suka haɗa da Ammu, ganin yadda ta keyi mata kallon tausayawa yasata tsayawa, ta shapa kan Ammu tana ƙirƙiro murmushi a fiskarta cikin sassanyar muryar ta tace, "my Ammu na kinsan mene ne?, yau tashi nayi da karsashi a jikina sosai, koda ace duk gidan nan akace na gyara zan iya"
Ganin yadda tayi maganar sai itama ta maida mata murmushi, acikin ranta kuwa, tasan Ƴarta so take kawai ta cire ta a damuwa, domin tasan wahalar dake tattare da aikin gidan, aikin da mutane shidda keyi, su ɗin ma suna daɗewa kafin sugama, amma ace mutum ɗaya zaiyi, saboda rashin imani duk ranar asabar da lahadi Safna ce meyin aiki a gidan in aka cire girki.
Fara aikin tayi, gurin ƙarfe bakwai ta saki aikin, taje ta kaiwa Ammu breakfast, sai dai ita bataci ba saboda so take ta gama aikin cikin lokaci, don ƙarfe goma ne time ɗin da hajiya tasa mata lokacin gama aikin, kuma ta san ta kamar yunwar cikin ta, gashi aikin kuwa da uban wuya, tana rokon Allah ya kiyaye mata ciwon baya, saboda yadda take aikatuwa a wannan ranakun.
Karfe tara da en mintuna ta gama aikin cike da gajiya ga yunwa, tana gamawa ta nufi kitchen dan ɗaukar abincin ta da ta ijje, sai dai tana buɗe inda ta ijje abinci yace ɗauke ni inda kika ijje ni.
Dube dube tafara yi acikin kitchen ɗin dan samun abinda zata kashe yunwan cikin ta dashi, tunanin ta ne yatsaya ganin kret ɗin Ƙwai, ɗaukar biyar tayi, ta soya atake, ɗaukar bred din da ta gani a gefe tayi, haɗi da godewa Allah. Zama tayi da bismillah ta fara antaya wa acikin ta.
"Kai ka kai bred ɗina?" Saurin sakin bred ɗin tayi ta miƙe à rarrabe ta furta, "Ru....Ru....ki...dama....na.. ki..ne?" Ta ƙarasa à tsorace, sai da Ruki ta ƙaraso gaban ta, cikin ɗagun murya tace, "mayunwaciya yanzin abun da na ijje zaki ɗauka?, harda soya Ƙwai, wato kin samuri ko?" Juyawa tayi ba tare da tsayawa jin abinda safna zata ce ba, tayi hanyar falo, binta Safna tayi à baya tana bata haƙuri,
Tsayawa Safna tayi ganin an shiga falo, sannan ga Hajiya a falon.
______________________________________________________________________________________________
Part 0️⃣9️⃣▶️1️⃣0️⃣
"Hajiya! Hajiya!" Juyowa Hajiya tayi tana duban autar tata jin yadda ta kira ta, "Ruƙayya ya akayi kike yimain wannan kira", "Hajiya ni dan Allah adai na kirana Ruƙayya se kace sunan wacce tafito daga Ƙauye?" Ta faɗi cikin muryar shogoɓa.
"To naji Ruki menene?, gashi naga wannan abar a biye dake" ta ƙarasa faɗi tana nuna Safana da ido, Ruki tace "hajiya Sata ta fara yi, bread ɗin da nace miki na ijje a kitchen, shi ta ɗauka kuma Hajiya harda soya Ƙwai kusan rabin kret".
Kallon Safna tayi, sannan tace, "What a binda ta fara kenan?" Tun isowar su falon jikin ta ke rawa, tasan yadda Hajiya keson Ruki sosai A matsayin ta na Auta, kada kuwa tsinke Ruki ta ijje ita kuma ta dauka, Hajiya zatayi maganin ta.
da sauri ta iso gaban hajiya haɗi da rage tsawo, tafara magana cikin sanyin muryar ta kamar koda yaushe, "Hajiya bansan nata bane wallahi" zazzafan mari Hajiya ta sakar mata daya sata zama daga durƙushen da take. "Mutum ya ijje abu ke kiɗau ka, gaki mai hannun Ɓera ko?, bakyacin Abinci ne ko me?".
Murmushi jin daɗi Ruki tayi, Share hawaye Safna tayi ta ƙara faɗin, "kiyi haƙuri Hajiya, Abincin da na ijje ne ban gani ba kuma banyi break fast ba shiyasa, naji yunwa sosai" kai mata mari ta kuma yi a karo na biyu, "ok wato bakiga naki ba, shiyasa kema kika ɗau na wani, da kyau"
Ita kuwa Ruki murmushin mugunta take yi, yayin da idon ta ya sauka akan jus ɗin dake cikin jug a kan teburin glass, sai ta ɗauko shi tareda cire marfin sa, nufo kan Safna tayi, ji kake shaaa ta juye mata shi a jikin ta, jan numfashi mai ƙarfi Safna ta ja tare da lumshe ido, yayin da take jin saukar sanyin ruwar jus ɗin a jikin ta, Daidai fitowar Alhaji.
taka upstair ɗin da sauri da sauri yake, da alama akoi aiki mai mahimmanci da yake son fita yi, idon sa kan abinda Ruki tayi wa Safna, ƙarasa sauko wa yayi, "what's going here?." Juyawa su biyun sukayi suna kallon sa yayin da yake takowa inda suke. Safna kam zafafan hawaye ne ke fita daga idon ta.
Hajiya kuwa kame kame ta fara yi, kafin ta canko abinda zata ce masa, Ruki tace, "dady abuna ta cinye" ta fadi cikin muryar ta na shagwaba, "abu kuma?," "eh dady bred" "yanzu a kan bread kika yi mata haka Autah na?" Ruki ta ƙara cewa, "Dady naje ɗauka nefa na tarar ta cinye, kuma koɗayin sa nakeyi" "haba my Autah" ya faɗi yana girgiza kai, saboda baiji daɗin abinda tayi wa Safna ba.
Yakuma juyawa inda Safna take, yace "my Daughter I'm sorry tashi ki tafi" miƙewa tayi tace "Nagode Dady" haɗi da sharar ƙolla a karo na babu a dadi. Bin bayan ta Ruki tayi da kallon banza sannan ta haye sama.
"yanzu a gaban ki hakan ya faru amma baki iya cewa komi?" yayi tambayar wa Hajiya da ke tsaye, "Alhaji kasan yara ba'a rasa su da irin ƙananun faɗa shiya sa" "hmm" kawai yace yana ƙoƙarin fita, ta tsai dashi da tambaye, "Alhaji ya naga kana shirin fita lafiya? Yau fa Asabar!" Sai da ya duba à gogon dake hannun sa yace.
"Eh akoi abinda zanje yi ne" kawai Yafaɗi ba tare da ƙara sauraron ta ba ya fice. Cikin mamaki tabishi ta kallo tana tambayar kan ta, "to wani irin aiki alhaji zai je yi? Shida nasan ranar asabar da Lahadi baya fita, sai dai in zaiyi tafiya?" A ɓangare ɗaya kuwa, cike take da haushin Safna, "shegiyar yarinyar nan, kwanan nan so nake na kamata da laifuka, ta yadda zan bata wuya da hujja, amma komai taka tsantsan take dashi" ta furta harda jan tsaki....
Sai da ta tsaya a bakin ƙofa ta share hawaye, sannan ta sa kai cikin ɗakin, a kan Kujera ta samu Ammu, murmushin ƙarfin hali ta sakar mata da suka haɗa ido, shiga toilet tayi, tafara kukan da bata samu damar yin sa ɗazun ba, ciki ciki take yin sa gudun kada Ammu ta ji.
Saida tayi mai'isan ta, sannan tayi wanka ta fito, doguwar Riga marar nauyi tasa, inda Ammu take ta nufo haɗi da zama a gefen ta, ganin alamar kuka a idon gudan jinin nata, cikin damuwa tayi mata tambaya da ido, "babu komai Ammu na, ƙwaro ne ya faɗa min ido, am bari in haɗa miki ruwan wanka kema" ta faɗi haɗi da miƙewa gudun kada ta ƙara yi mata wata tambayar.
Haka dai Safna ta ƙare wannan weekend ɗin.
Tana zaune akan kujerar falon tana kallon tashar daɗin kowa, Ruki da Saleem suka shigo. Kashe TV Ruki tayi, "waike Safna wace irin Mutum ce? Uban wa yabaki damar zama a falon nan? Ko baku da ɗaki ne?" Ruki ta faɗi.
Kallon ta kawai Safna ke yi da tinanin, wannan wani irin bala'ine? Kenan zama a falon ma bata da iko ko me? Zafin marin da ya ziyarci kumatun ta, yasa ta barin tinanin tare da saurin riƙe kumatun ta, yace, "da kika zauna baki ji abunda aka ce miki bane?"
"Yauwa Saleem ƙara mata, ni wallahi na tsani Safna, amma na rasa gane dalilin da yasa dady yabar su a gidan nan daga ita har Mayyar Uwar ta" saurin miƙewa Safna tayi cikin ɓacin, ta fara magana, "Ruki karki zagan min Ammu na, tun da batai miki komai ba"
Ruki ta cigaba da cewa, "Ashe kar na zagar miki Uwa, to in ban da ke me zakiyi da irin Uwar nan taki,