Showing 117001 words to 120000 words out of 129098 words

Chapter 40 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

46

ya bar doctor da ke ta girgiza kai cike da tashin hankali.

Komawa kan kujerar sa yayi da zaman daɓas, yana mai jin wani irin abu na yawo cikin zuciyar sa, "yanzu ya zaiyi? Tabbas abun da na aikata ya zame mini annoba a rayuwata, shin idan gaskiyar sirrin da nake ɓoyewa a zuciyata ya bayyana ni da su baza mu hallaka ba?" Ya faɗi jikinsa n'a rawa, à da yayi tunanin rayuwarsa ta fara daidaita bayan tsawon lokaci, ashe dai ba haka bane. Da fe kansa yayi yana kuma zurfafawa cikin tunanin abun da Alhaji Jamilu ya sanar da shi.

AMNA.

Zaune take kan kujerar gefen Ammu, ta tsura mata ido kamar mai kallon wani sabon halitta, yayin da Ammu kuwa idonta yake a rufe, allurar bacci na ɗawainiya da ita. Tunanin tashin hankalin da ta shiga ɗazu tayi, har wani fargaba taji lokacin da doctor ya fito daga gurin Ammun. Zubar hawaye taji kan hannunta, kallon hawayen tayi sannan ta saki murmushi ta share na idon na ta sannan ta cigaba da kallon Ammu ta fara magana.

"Ammu hawaye ne ya fito daga ido na" Ta sauke numfashi mai haɗe da murmushi, ta matso kusa da Ammu haɗi da kamo hannun ta sannan ta cigaba da cewa, "Ammu ni da kike gani na ko? Ba abu kaɗan bane yake sa ni shiga damuwa fiye da kima sosai, ko tausayin da zai sani har nayi kuka, saboda ni ba mace ba ce mai karyayyiyar zuciya, wanda da na ke ɗaukar hakan da kowa ma irina ne, sai dai daga baya na fiskanci ni ce da wannan zuciyar, don ban taɓa cin karo da mutum mai irin halina ba, lokacin da nake da yarinta, nakan yi mamaki idan naga mutum yana hawaye akan abun da bai taka kara ya karya ba, saboda ni ko ciwo aka ji min baya min zafi sosai, duk da haka kuwa sai na rama akan wanda ya min hakan, shiyasa ba kowani yaro bane yake mugun wasa da ni, saboda ina da zafin zuciya, ban san ko ina ƙarama sosai ba, amma zan iya irga sau nawa nayi kuka a rayuwata, domin duk abun da ya sani kuka hawaye ya zuba daga idona ɗaya na bin ɗaya, to abu ne babba, babban babba ma".

Sai da ta ja numfashi sannan ta ƙara faɗin, "abun da zan iya kotanta shi da mafi girma da na shiga tashin hankali, shine rasuwar mahaifina! A wannan lokacin na shiga halin da da ace za a kawo min wanda ya aikata masa wannan abu gaba na, tabbas zan iya hallaka shi, saboda yadda zuciyata ya ke a wani mugun yanayi. Sai kuma ɓatan ahalina. Sai dai yau n'a shiga tashin hankali akan abun da ka iya faruwa da ke Ammu, hawaye ya fito idanuna akan ki, ba ma yau kaɗai ba, harda wasu ranaku à baya, hakan yasa nake mamakin kaina sosai akan hakan".

Ta faɗi tana kuma share wani hawayen, "wani mamaki kike yi 'yata?" Dady da shigowan sa kenan yayi mata tambayar jin kalmarta ta ƙarshe, saurin miƙewa tayi da tsoron kar dai ya ji maganar ta? Ba tare da ya jira amsarta ba ya ƙaraso yana cewa, "bai kamata ki kuma sa kanki à damuwa ba 'yata, komai ya wuce, zata tashi" murmushin ya ƙe ta sakar masa tare da miƙewa don ta ba shi guri ya zauna.

WASHE GARI. Da safe.

A asibiti suka kwana, Dady da Shuraim ne ke ta yin nan da can gurin harkokin da ya dace

Ammu ce ta fara buɗe idonta, tana sauke su a kan Amna da ta miƙe tana murnan Ammu na farkawa, murmushi Ammu ta sakarwa Amna, itama ta maida mata da martani, "sannu Ammu, sannu kinji? Yi à hankali, akwai inda kike ji yana yi miki wani yanayi?" Ta yiwa Ammu maganar cikin sanyin murya, murmushi Ammu ta sake yi mata a karo na biyu.

HAJIYA.

"Hajiya me ya sameki ne wai? Jiya na tambayeki kin ƙi sanar da ni, bayan yadda kika dawo abun tambaya ne, domin da ace à hanya na haɗu da ke ƙila da ƙyar in gane ki, sannan na faɗa miki ankai uwar maƙiyarmu hospital ba tada lafiya amma baki ce komai ba, kuma ina ganin ki kika matse ƙafafunki da ruwan zafi" cewar Ruki tare da zama kan kujera, kallonta Hajiya tayi tana cewa, "kinzo ɗaki na ne don ki ƙara min damuwa ko me? Ruki don Allah ki rabu da ni inji da abunda ke addabar zuciyata, kin san yawan asarar da nayi jiya kuwa? Hmmm".

Hajiya ta faɗi tana ƙara jin haushin abun da ya faru jiya, gashi da ƙyar take tafiya don ƙafafuwanta sun ƙara tsami, ko hawa upstairs ma da ƙyar ta samu ta haye jiya ɗin, don ba ta jin zata kuma sauka ƙasa idan ba daidai taji ba, duk da ita asarar dukiyan da tayi ya fi damunta akan jikinta ma, duk da yanzu ma so take ta je ta kuma matse su da ruwan ɗumi. Cikin halin ko oho Ruki ta miƙe don barin wurin ta furta, "shikenan ni na tafi!".

Da kallo Hajiya tabi Ruki, wato ko zata mutu bai dami autar ta ta ba, tuna ɗanta Yazeed tayi, domin idan da shine da bazai taɓa barin wurin ba sai ya kwantar mata da hankali, duba wayarta ta fara yi, sai ta tuna ai ɓarayi sun sanƙame mata shi jiya, miƙewa tayi tana tafiya da ƙyar a zuciyarta tana kuma tunanin hanyar da zata ɓullowa lamarin Safna, domin har yanzu fa ba ta jin zata saduda akan neman mafitar ya kice Safna cikin rayuwzrta. Haka har ta fice daga ɗakin, tsayawa à matattakala tayi tana ƙa re masa kallo, domin ba ma ta son taka su don zasu ƙara mata ciwon ƙafa, kwalawa Ruki ƙira tayi don ta bata wayarta ta kira Yazeed.

AMNA.

Kallonta yayi yana cewa, "C.E.O ya kamata ki tashi a wurinnan ki bar Ammun ta huta, kina damunta" "to kai me ruwanka?" Ammu kuwa kallon su kawai ta ke yi, Nurse ce ta shigo haɗi da cirewa Ammu ruwan da suka sa mata, sannan ta miƙa musu takardar sallama, "ya akayi takardar sallama da wuri haka? Bayan tana buƙatar kulawa a wurinku? and we don't need to see doctor Salis first?" Shuraim yayi tambayar da mamaki, nurse ta bashi amsa, "doctor Salis ya bar aiki a sibitin nan, sai.." "whatt? Barin aiki? on what grounds?" Cewar Shuraim, Amna ma mamakin abun tayi sosai, nurse ta ce, "ban da masaniya gaskiya, amma dama ai jikin madam babu wata matsalar da ya rage".

Nurse ta faɗi tare da ficewa. Da mamaki suka raka bayan nurse da kallo, sannan suka dawo da kallon junan su, Shuraim ya ce, "what did you understand?" "Me kuwa zan fahimta? May be matsala ya samu da hospital ɗin, gaskiyarsu yanzu Ammu ta samu sauƙi, let's just go home"

BAYAN SUN KOMA GIDA. Amna ce ta tara masu aiki duka, sannan ta ba kowa aikin da ya dace da shi, amma kula da Ammu à ko wani lokaci shine babba akan duk wani aikin su, sannan ta ce idan da akwai wanda aikin bai masa ba zai iya yin gaba, sai ta samo wasu, sannan duk wanda yayi wasa da kula da Ammu to abakin aikin sa bayan hukunci.

Tana gama isar musu da wannan maganar ta wuce ta barsu à wurin. Gaba ɗaya 'yan aikin suka shiga taitayin su, dole suyi abun da Hajiya Safna ta faɗa, domin sun fahimci yanzu ita ce shugaba a gidan, domin ko abu tasa ɗaya daga cikin su, inya haɗu da Hajiya ta sa shi aiki, idan ya ce Safna ce ta sa shi to da sauri Hajiya ta ke cewa ya wuce.

Labari Ruki ta ɗauka ta kaiwa Hajiya, wani ƙarin baƙin ciki ne ya kuma shigewa zuciyar Hajiya, kai wai ita me ya kamata tayi ne?

DARE.

Ƙishin ruwa ne ya farkar da ita, hakan yasa ta tashi daga kwancen da take, kai dubanta gefen Ammu tayi yadda take sauke numfashinta a hankali, murmushi ta saki tare da sauka daga gadon zuwa gurin kofin ruwa, sai dai babu ruwan domin ɗazu ita ta shanye kuma bata sa ko wani ba, tun da suka dawo yau bata je dining ba, a ɗaki ta ci abinci ita da Ammu, saboda kasancewar Ammu majinyaciya. Ta kula da Ammu sosai, domin ba tayin nisa da ita sosai.

Nufan hanyar ƙofa tayi daidai kiran MR na shigowa wayarta, dawowa tayi ta ɗaga wayar tana tunanin kiran da yayi mata cikin dare, duk da ba wai daren sosai yayi ba. Kara wayar a kunnenta tayi tare da fita da kofin glass ɗin don zuwa kitchen ta ɗibo ruwa, "ya jikin mahaifiyar Safnan?" MR yayi mata tambayar, ta ce, "a yanzu na ɗauketa tamkar Ummee na, zaka iya cewa ya mahaifiyarki?" Ta faɗi domin ta lura da yanzu MR baya yi mata magana cikin kausasawa, murmushi MR yayi sannan ya kuma cewa, "da kyau! Yanzu kenan ba ki buƙatar ahalinki su dawo? Cause kin samu another family".

"A ah taya kuwa zan so hakan, kawai dai na faɗa maka ra'ayi na ne" ta faɗi a hankali kasancewar dare ne, bayan ta fara sauka daga upstair tana yin kitchen, MR ya kuma cewa, "me zai kaiki kitchen à wannan lokacin? Ko yunwan dare ne ke damunki?" Dakatawa da tafiya tayi da tsananin mamaki, "ya akayi kasan hakan?!!" Tayi masa tambayar cike da mamaki, dariya MR yayi ta can gefen yana cewa, "na faɗa miki muna sane da motsinki duk inda zaki je" "Ikon Allah! Amma MR kuna tsafi ko?!" Ta kuma yi masa maganar, MR ya ce, "eh amma a kan ki kaɗai".

Ƙarasa shiga kitchen ɗin tayi don ta sha ruwan domin maƙoshinta ya fara neman a gaji, ya fara zama kamar kafaffen kogi, sha tayi sannan ta zuba ruwa a kofin jug ɗin sannan ta fice daga kitchen ɗin, sai a lokacin MR ya kuma cewa, "har kin gama abun da zakiyi?" Cikin ɗaukar maganar sa hasasowa kawai yake a zuciyarsa hakan kuma yake yin daidai ta ce, "gaskiya ka iya hasashe sosai ranka ya daɗe" Murmushi ya kuma yi Amna ta kuma cewa, "ban san wace rana zaku nuna min inga family na ba, ina cikin kewan su sosai".

Bai amsa mata ba har ta shige ɗakin su, "sai da safe" kawai ya faɗi sannan ya katse, à jiyar zuciya kaɗan ta sauke sannan ta ijje glass jug ɗin gurin zamansa, damuwa ne yayi mata shige a zuciya, sai taji gaba ɗaya barcin ma ya tafi, hakan yasa bata hau gadon ba ta juya kawai ta fice don ta je ko falo ne ƙila ta samu sauƙi.

Bayan ta fito daga ɗakin Ammu ta hangi kamar giftawan mutum a kasa, sauka daga upstair tayi ahankali don ganin waye ne yake a waje haka? babu haske mai ƙarfi sai wanda ake bari me colours na dare, hakan yasa ko dare ne zaka iya yawo inda kake so a ciki ba tare da ka kunnen mai hasken ba.



Hangan Shuraim tayi a tsaye ta hanyar ɗakin sa,

nufan inda yake tayi don taje taji me ya sa shi tsayuwa a waje da dare haka? lura tayi da ya sauke waya a kunnen sa, hakan yasa ta tunanin ƙila can da budurwar ta shi yake magana, sai kuma ta ji wani abu na rashin daɗi ya faɗa a ranta, kunna wayarta ta keson yi da niyyar ta haske shi.

Kawai hannun ta ya shiga gurin call, ba tare da idon ta ya kai ba, don ita so take kawai ta kunna tochi, hannunta ya taɓa numbern MR ya shiga dialing.

MR kuwa da ya manta bai sa numbern ta a inda yake sawa ba kawai yaji kira ya shigo wayar sa, yana dubawa yaga numbern Amna, "oh I'm forgot" ya faɗi bakinsa cikin mask, sannan ya amsa don yaji me dalilin kiran sa?.

Sai dai jin muryar sa ya fito kamar à waya biyu ne ya sa shi sake faɗin hello? Don ya tabbatar, ai kuwa da gaske akwai wata waya a bayansa da yayi amsa kuwwar.

Amna, bayan ta kira ba da sanin ta ba, kawai taji wayar Shuraim tayi ƙara, kafin tayi wani tunani taga ya sanya wayar a kunnensa, sai kuma taji kamar magana daga wayar dake hannunta, dubawa tayi ta ga ashe MR ne t'a kira, sawa akunnenta tayi, kawai idonta ya kai inda Shuraim ya ke, wani irin mamakin tunani ne yazo mata, hakan yasa ta yin sanɗa ba tare da ya sani ba ta matsa kusa da shi.

Idan ba kunnuwanta ƙarya suke jiye mata ba, tabbas kamar maganar da Shuraim ke yi ne ya ke fita daga wayar, sai dai muryar ta sa a sauye, sanya handspring ɗin wayar don ta tabbatar da abin da tunaninta ya kawo mata tayi, lokacin Shuraim ya kuma maida wayar kunnensa bayan ya ji shiru, sai dai ta ji muryar amsa kuwar maganar sa ta amsa gida biyu.

Juyowa MR yayi idon sa ya faɗa cikin na Amna, da take yi masa kallon tuhuma da mamaki da kuma zargi, zaro ido yayi yana kallonta sosai, "ya akayi nayi sakaci haka?" Ya yiwa kansa tambaya a cikin zuciya. a hankali Amna ta fara takowa har izuwa gabansa, jikinta yayi wani irin sanyi, zuciyarta ya tsaya cak, kanta ya kulle, da ƙyar ta iya buɗe bakinta ta furta, "me!? Me haka!?" Tayi masa tambayar ba tare da ta kau da kallonta garesa ba, tana kuma cewa, "MR!? Kuma Shuraim!? Me hakan yake nufi!?".

TOOFAH👀 ko menene doctor Salis ya aikatawa su Dady? Da alama babban laifi ne, kuma wani sirri ne a ɓoye cikin zuciyarsa? Zai bar gari kamar yadda Dady ya basa umarnu?

Hajiya ta ƙi saduda fa, to ko wace hanya zata nemo kuma? Ko zata koma gurin ƙawarta Ladingo bayan baran-baran ɗin da suka yi?

Hummm sannan ga shi Amna ta gano ashe Shuraim shine MR. Ko me dalilinsa na sace ahalinta da kuma sa ta dawowa gidan su Safna? Sannan me dalilinsa na wannan basajar?🤔

Mu haɗu a next part idan Allah yayi mu cikin masu rai.

Alƙalamin✍🏼 taku ɗin nan dai {Mrs Umar} sabon inkiya [Gimbiyar Fasaha]👸🏽

Daga ƙungiyar Fasaha.

___________________________________________________________________________________________________________

Part 1️⃣0️⃣9️⃣▶️1️⃣1️⃣0️⃣

"MR!? Kuma Shuraim!? Me hakan yake nufi!?". Ta faɗi tana kuma ƙure da idon sosai, yayin da zuciyarta ke tsananta bugu kamar ganga, ganin bashi da zaɓi yanzu da tun da ta riga ta harboshi hakan yasa ya cire mask ɗin fiskarsa, tare da sake maida hankalinsa gareta suna cigaba da kallon kallo sannan ya furta, "Safnah! Ki tsaya ki fahimce ni da kyau! tabbas ni ne MR wanda yayi silar zuwan ki gidan na..." "meyassa! Akan wani dalili? Wani abu ni da dangi na muka yi maka? Da har zaka yi wasa da rayuwarmu haka?" Ta katse shi da faɗin hakan cikin ɗagun murya da ɓacin rai.

Saurin dakatar da cigaban maganarta yayi da cewa, "Amnah listing to me, ki daina ɗaga murya yanzu dare ne, za a iya jinki, mu bari zuwa gobe, zan sanar dake komai" "a ah, a ah! Komai a yanzu zaka sanar da ni, akan me ka keyin wasa da rayuwata?". Ta faɗi domin yanayin da take ciki na kullewar kai baza ta barshi ba sai ya sanar da ita dalilinsa na yin mata haka.

Matsowa inda take yayi cikin tausasa zuciyarta ya ce, "Please Amnah, just tomorrow nayi miki alƙawari, jinin wannan alfarmar" sauke ajiyar zuciya tayi tare da kawar da idon ta da ya fara ƙanƙancewa gefe, saida ta haɗiye wani nyawun baƙin ciki sannan ta juya ta wuce ba tare da tayi masa magana ba, shima numfashin ya sauke, na rashin daɗin faruwar hakan, domin bai so abun ya kasance da wuri ba.

Amna na zuwa ɗaki ta nufi kujera, zama tayi tare da ɗaura hannayenta duka biyu a kai, domin har yanzu babu abunda zuciyarta baya saƙawa mata, tambayoyi ne birjik cikin ranta, babu abin da take buƙata fa ce amsoshin tambayoyinta, ta ɗau tsawon lokaci a haka, ka na daga bisa ni ta miƙe ta koma gado ta kwanta, duk da cewa ba ta tunanin zatayi barci cikin nutsuwa.

Shuraim ma tunane-tunane ne yake a nasa ɓangaren, duk da cewa ba wai ya razana da ganewar da Amna tayi masa bane, sai dai ba yanzu yaso faruwar hakan ba, amma tun da hakan ya faru, to gobe zai sanar da ita komai da komai.

WASHE GARI. Asuba.

Ba wani barcin kirki tayi ba, sabida tunanin da tasa a ranta, zuwa kusa da Ammu tayi tana kallonta, "bari in taimaka miki kiyi sallah Ammu", ta faɗi tana ƙoƙarin ɗaga ta, sai dai yauma kamar jiya, jikin Ammu baya motsi sam, zuciyarta ya bada razananniyar bugu, domin jiya ɗauka tayi da ko don jikin na ta bai gama dawowa bane, amma gashi yau hakan ya sake faruwa, wani tsoro ne ya shige ranta, na kada wani abun ya kuma samun Ammun.

"Ammu me yasa jikinki baya motsawa, don Allah ki motsa jikinki ko kaɗan ne inji daɗi kinji?" Tayi maganar kamar me shirin yin kuka, kallonta kawai Ammu take ko murmushin yaƙi fita yanzu, "don Allah Ammu ki motsa min koda hannunki ne" ta kuma yin maganar tana yin ƙasa da kanta idonta ya ciko da hawaye.

Miƙewa tayi don zuwa ɗakin Dady, saida ta share hawayen sannan ta fara ƙwankwasa ɗakin, bata izinin shiga yayi mata sannan ta shiga da sallama, zama a kan kujera tayi tana gaishesa, amsawa yayi da tambayarta me yake damunta haka? "Dady dama akan jikin Ammu ne na zo,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login