Showing 27001 words to 30000 words out of 159134 words
Chapter 10 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
kayan kamashin da ake goge kushin tayi ta mika mata tare da soso,
Karba tayi ta koma ciki ta fara goge sabon kushin din da bai yi komai ba,
Cikin mintuna biyar ta gama jika kushin ɗin nan sharkaf da ruwa,domin ruwan dake cikin Bokitin sai da ta tabbatar da kushin din ya kusa shanye shi,kaɗan din daya rage garin mikewa ƙafarta ya ture Bokitin ruwan ya zube,
Ba tare da damuwa ba ta dauki Bokitin ta fita dashi ta bar shiyan....
Kuyi haƙuri mura ya saka ni a gaba,..
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*19*
*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*
Ihun da taji ne yasa ta zabura da sauri daga saman sallayar da take ta fito,
Khalid ne rungume a jikin Zainab yana rusa ihu tare da rike ƙafa,
"Lafiya,me ke faruwa? Ta tambaya tana karaso wa wurinsu" Me ya same shi?
"Mama,wai waye ya zubar da ruwa ne haka,gashi Khalid ya zame,ni kuma na daura takardu na a saman kushin kalli yanda suke jike kamar na zuba a ruwa"
Kallon kafar tayi wanda nan take ya kumbura,ta kalli yanda kushin din ya jike,"kira likita ya duba ƙafar nan "
"To Momy"
Amsar shi tayi tana ta lallashin shi,har likitan ya zo,nan ya duba shi ya kuma tabbatar da yayi targade,
Nan ta ba da baƙi kuwa aka gyara ma yaron kafa wanda take jin kukan shi har cikin zuciyar ta,domin shine jikan ta na farko yaron Aunty Hajo,
Ganin yayi barci ne yasa ta fita da kanta tayi shiyan Ammi,wacce ita harma ta shige daki dan lokaci kusan tara saura
Tana shigowa Amira ta samu zaune tana daddana laptop,ganin wacce ta shigo ne yasa ta mike tsaye tana mamakin me ya kawo Momy Rahama Shiyan su,dan tasan bata shigowa sai da dalili mai ƙarfi,
"Ina ne dakin me aikin ku"
Yanda taga tayi magana a dake ne yasa ta nuna mata da hannu,
Kai tsaye dakin ta shige,
Sai dai bata same ta a ciki ba,jin motsin ruwa a banɗaki ne yasa ta ɗan dakata,
Mintuna biyu tsakani sai gata ta fito daure da tawol wanda ya saukar mata har guiwa,suman kanta a jiki wanda yake ja,dan ba za'a saka suman kanta a jerin baƙaƙe ba,yana da tsayi dan ya sauko mata har kafaɗa duk kasancewar shi a jike,
Sam bata lora da ita ba,dan hankalin ta na kan wayar ta da taji yana ƙara,
Jin saukar abu me nauyi a kanta ne yasa ta dafe wurin tana rintse ido,dan wani irin zafi taji ya ziyarce ta wanda yasa ma ta kasa ihu,
Kafin ta dawo haiyacinta ne taji saukar duka a jikin ta na igiyar caja da ke ajiye a wurin,
Wannan karan kam ihu ta saka domin zafin ya mata yawa,kun san yanda duka yake ga jikin da yake jikakke,abun babu sauƙi,
Saukan bulala kawai take ji a jikinta babu kakkautawa,
Tsabar gigicewa yasa ta rasa wake mata irin wannan hukuncin,dan abun yazo mata a ba zata ne,gabaɗaya ta ruɗe,
Cikin ikon Allah ta samu sa'a ta hankada Hajiya Rahama wacce take jibgegiyar mace,domin ba karamin ɓace,shi yasa ta samu sa'a ta saka ta a tsakiya,
Tagal_tagal tayi sai gashi ta faɗa kan gado,
Da gudu ta samu ta fito fallon tana ihu tayi waje,har tana banke Amira wacce take tsaye ta bakin kofa tun jin ihun Biba na farko,
Ta juya ne kenan dan zuwa kira Ammi sai ga Biban ta fito da gudu tayi waje yayin da Momy Rahama tabi bayan ta ita ma da gudun wanda take yi kamar zata kifa,dan in da akan ɗan ta ne ko jikan ta babu wanda take jin zata iya ragama,
Tana kaiwa tsakiyar gidan ta tsaya cikin tsananin kuka tana kalle_kalle dan ta rasa ina zata je ta tsira a wannan lokacin,ɗan irin raɗaɗin da kanta da jikin ta ke mata bana lafiya bane,dan tunda take a rayuwar ta bata taba fuskarta abu makamancin haka ba,
Idonta ne ya tsaya a shiyan Kaka,tana juyawa baya ta hango Momy Rahama saura kaɗan ta cimmata,
Zaune suke sun tasa kaka suna zolayar ta wacce take cin naman gasasshiyar Rago,Aunty Maijidda,Yaya Ibrahim,Sulaiman,Bilki,da kuma Suraj wanda yake tsaye ta bakin ƙofar shigowa yana amsa waya,
Bata iya gudu sosai saboda jirin data fara gani,ba dukan data mata bane matsalar,abinda ta buga mata akai shine matsalar,
Ji yayi an faɗo jikin shi da ƙarfi,sai kuma aka zagaya ta bayan shi aka kankame shi,cikin kuka da kuma murya mai tattare da tsananin tsoro take"Help me! Help me please! "
Gabaɗaya hankalinsu ne ya dawo kansu,mamaki suke wacece wannan ,daga ina kuma take haka,domin dai sun ga mutum daga ita sai tawol,duk jikin ta a buɗe yake,
Ganin shigowar Momy Rahama tana haki ne yasa suka maida akalar kallon su kanta,
"Yauwa Suraj miko min makiran yarinyar nan,yau sai naga ubanda ya ɗaure maki kafa a garin nan"
Jin abinda tace ne yasa ta sake shi da sauri,ta juya tana nufan wurin da Kaka ke zaune,
Komawa bayanta tayi ta tsugunna ta rike rigarta ta baya "ɗan Allah kaka karki bari ta matso inda nake,kashe ni zata yi,she is a monster"
Cikin hasala tace "kam bala'i,ni kike kira da monster?
Ta faɗa tana karasowa cikin tsakiyar falon.
Da sam bata gane taba,amma jin muryan ta ne yasa ta kira sunan ta dan tabbatarwa" Habiba"
Kara rike rigarta tayi da karfi "ɗan Allah gata nan zata zo,ki ce ta tsaya ɗan Allah ki taimake ni"
Ranta ne ya baci sosai "wannan wani irin rashin hankali ne Rahama,Me haka zaki biyo yarinya da gudu kamar sa'ar ki,ashe har yanzun baki da hankali ban sani ba"
Cikin daga murya tace"Mama amma kinsan abinda yarinyar nan tayi kuwa,ruwafa ta zubar da gangan dan na sakata goge kushin Khalid ya zame yayi targade sai da aka mashi kyaran kashi"
"Sai me dan ya faɗi yayi targade,yanzun so kike ki kasheta dan ta saka jikanki yayi targade saboda bakida kunya baki San daraja taba,ace yarinya har ta gudu ta zo shiyana amma ki biyo ta har gabana zaki daka,lallai baki ganin daraja ta"
Shiru kawai tayi tana huci,
Jawota tayi daga bayanta,ita kuma tana girgiza mata kai tare da kara boyewa,
Jawota tayi"is ok,fito "
Jawota tayi ta tura mata ita gabanta "gata nan dai sai kashe ta tunda ta taɓa jikanki"
Kauda kai tayi"nifa Mama ba haka nake nufin ba,naga duk kin canja maganar "ta faɗa tana barin falon cikin jin haushi tare da kuɗin idonta idon Biba sai ta karya ta,
Ganin ta fita ne yasa ta zame tana zama a wurin tare da saka kuka sosai,
Ammi ce ta shigo tare da Amira cikin sauri,
Gabaki ɗayan su yanda kasan wadanda aka ɗinke ma baki,sai binta da ido da suke yi cikin tausawa,domin ga shatin bulala nan a jikin ta,wanda ya fito rado_rado a jar fatan ta,
Da sauri Nafisa ta matso inda take tana kokarin ɗaga ta"Biba tashi muje ki saka kaya,jikin ki abude yake"
Fisge hannun ta tayi daga cikin nata"ki ƙyale ni! Bubu inda zanje,yau bazan kwana a garin nan nan ba,"
"Haba Biba me kike faɗa haka ne? Ga bashi kaka ta hanata tabaki ba,ai ta wuce,tashi muke"
Cikin kuka ta ce "baki ga yanda jikin na yayi ba,kalli hannuna,! She is wicked women! What did I do to her! Me na mata,ni ba zan ƙara kwana a gidan nan ba,"ta faɗa tana dafe kanta tare da ɗan rintse ido" Ance gidan malamai akwai tsoron Allah,suna kyautatama kowa,ba suda zalunci,Ashe duka karya ne,su masu son kansu ne,na tabbatar da a wani wurin nake aiki da babu wanda zaimin haka,tunda nake a rayuwata ba'a taba marina ba,sai a gidan nan,ba'a taba duka na ba sai wannan so calling gidan malamai,Nafisa kalli yanda ta bata min jiki na,shikenan na zama mai tambo a jiki,ba zan zauna ba,na gama aikin I am out"
Gabaɗaya jikin su ne yayi sanyi,domin tabbas ba'a kyauta mata ba,kuma a yanda sunan su yayi kauri bai kamata a samu irin wannan shaidan daga cikin gidan su ba,
Ji tayi an yafa mata abu a jikin ta,wanda ya rufe ruf jikinta gaba ɗaya,
Dago ido tayi ta sauke a kan Ammi wacce ke tsugunne a gabanta,
"Idan har an zalunce ka,kana da damar da zaka faɗi abinda aka maka,amma suturta jikin ki ya zamo shine abu na farko daya kamata kiyi"ta faɗa tana share mata hawayen dake sauka saman fuskarta,
Aunty Maijidda ce cikin tsoro tace " Ammi jini"
Duk kallon inda ta nuna suka yi,farin hijabin da Ammi ta yafa mata ne ya fara jikewa da jini wanda yake ɗigowa daga cikin kanta,
Ammi na kokarin kai hannu saman hanta ne,taji saukar lallausar hannun shi biyu saman kanta wanda hakan yayi daidai da lunshe ido da tayi tana ganin wani duhu na gifta mata,
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*20*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Salati Kaka ta saka cikin tsoro,domin ko kaɗan bata son tashin hankali tana da saurin rudewa,"inna'lillahi'wa'inna'ilaihi rajiun,ya Ubangiji ka rabani da ganin bakin rana a rayuwa ta,yau me zan gani,kisan kai a gidan nan,"gaba ɗaya ta ruɗe tana kuma kokarin ruɗa su da kalamanta,
Ganin bata numfashi ne yasa cikin tsoro ita ma Ammi tace"Shamsuddeen bata numfashi fa"
Koƙarin ɗaukarta yake yace "Ammi ki kula da Kaka"
Ɗaukarta yayi yana ƙoƙarin barin Falon da ita,
Da sauri Nurudeen ya dakatar dashi ta hanyar faɗin "ina kuma zaka kai ta,baka ganin halin da take ciki?
Wani mugun kallo ya watsa mashi sannan ya kuma saka kai,
Kaka ce tace" Shamsuddeen dawo da ita nan Nura ya duba ta"
Cikin tsananin jin haushi ya dawo da ita ya ajiye ta a saman kushin ya juya ta bar falon,
Duk da kallo suka bishi,to me shi kuma ya bata mashi rai haka,
Kiran sunan shi da kaka tayi ne yasa shi dawo da kallon shi kanta"Sujaro zo ka dauke ta ka kai ta dakina"
Kallon wacce ake cewa ya ɗauka yayi yanda take wance babu numfashi,a hankali ya tako in da take kwance ya dauke ta ya shigar da ita dakin kaka,saman karamin gadon kaka ya kwantar da ita,
Aunty Maijiddarh ce data biyo shi a baya ta yaye gabaɗaya hijabin da Ammi ta rufa mata wanda ya gama baci da jini"Yaya Suraj ka dafe kanta inda yake fitar da jini"
Kauda kai yayi daga kallo ɗaya da yama jikin ta,dan sai lokacin yake ganin irin yanda fatar jikinta yayi,jin muryar Nurudeen yana ƙoƙarin shigowa ne yasa yaja zanin gadon ya rufa mata jikinta gaba ɗaya dashi,
"Ki danne mata wurin" Abinda ya faɗa kenan ya bar ɗakin,
Kai tsaye in da su Kaka suke ya tsaya ya mata magana,sai kuma ta kwalla kiran sunan Nurudeen wanda ya shiga dakin ko yana ƙoƙarin zame zanin da aka yafa mata,"Fito ga Hauwa'u ta zo,sai ta duba ta"
Yi yayi kamar bai ji me tace ba,sai da Maijiddarh tace"Kaka na magana "
Tsaki yaja ya fito falon yayin da ita kuma wacce aka kira da Hauwa'u ta shiga dakin,
Maijiddarh ita take ta taimaka mata har ta gama mata treatment sannan ta rubata Allurai da magunguna,
Duk suna zaune suna jiran fitowar ta,
Kai tsaye wurin da yake zaune ta nufa tare miƙa mashi ƙaramin takarda "yallabai an samu nasaran tsayar da jinin sannan na mata duk abinda ya kamata,wadannan magunguna da Allurai ne da za'a siya zan dinga zuwa na mata na kwana uku ne,sannan shatin jikinta ma zai tafi idan tayi amma da cream din dana rubuta,"
A maimakon ya karba sai kauda kai da yayi ganin duk yanda suka zuba mai ido,
Ganin bai da niyar karba ne yasa Ammi tace"kawo takardar "
Miƙa mata tayi cikin girmamawa,
"Allah ya maki Albarka yarinya,Bilki zo ki ɗauko kuɗi a daki na ki sallame ta mun gede sosai"cewar kaka,
Cikin rawar jiki Bilki ke kokarin tashi,sai ji suka yi matar tace" A'a Kaka ki barshi tsakani na da Suraj yafi nan,babu matsala Allah ya bata lafiya "
Da Amin suka amsa kafin ta masu sallamah ta fita,
Tashi suka ga yayi yabi bayan ta,
Ammi ne da Kaka suka shiga dakin,
Allah sarki baiwar Allah,a hankali take sauke numfashin wahala,gabaɗaya ta gama basu tausayi,
"Ki yi ƙoƙari ki bada a amso maganin da Alluran"
"To Kaka,bari na saka a kawo mata kaya saboda idan ta tashi"
"Haka ne"
Fitowa falo suka yi,
Salman ne yace"wai me ya haɗa ta da Momy Rahama?
Balki ce ta bashi amsa"wai rashin kunya tai mata,ai ni wallahi ba karamin birge ni tayi ba,dan yarinyar sam ba ta da kunya,haka fa taima goggo rashin kunyar nan,bata San Momy ba kyale ta zata yi ba"ta fada tana mikewa "tunda an gama game bari na ƙara gaba" Haɗa ido suka yi da Nurudeen wanda ya zuba mata harara,kasancewar ta raina shi shiyasa ko akai bata kawo shi ba saima dariya da tayi tana barin falon,
Kafin suma su watse,
Ranar a shiyan Kaka ta kwana tare da Nafisa,cikin dare ne wani irin zazzafar zazzaɓi ya taso mata wanda jikin ta har wani gab_gab_gab yake yi,yanda kasan wacce zata tashi,
Hakan ba karamin tsorata Nafisa tayi ba,gashi bata son ta tayar da kaka saboda ta san tana da hawan jini idan tana barci ba'a tashin ta,
Gabaɗaya ta rasa mafita, ta kuma san tabbas idan bata nime taimako ba komai na iya faruwa da Biba,
Wani shawara ne ya fado mata,dan haka da sauri ta shiga dakin kaka ta dauko wayar ta,
Tama rasa wata number zata kira dan Allah ya gani ba tayi Boko ba,ba zata iya tantance waye ta kira ba ko wa zata kira,
Dan haka number data gani a farkon wurin kira ta latsa ma kira,tana kallon Agogo,a lokacin ƙarfe biyu na dare,
Kira biyu aka ɗauka,jin muryar wanda yayi sallah ne yasa cikin rawar jiki ta kira sunan shi"Yaya Suraj kai ne? Ta tambaya domin tana buƙatar tabbatarwa,
Bai damu da bata amsar tambayar data mai ba sai ma jeho mata nashi tambayar da yayi"ina kaka?
"Tana barci"
"Lafiya kika kira?
" Biba ce ba ta da lafiya "ta fada da sauri jin yana ƙoƙarin ajiye wayar.
Dan shiru yayi yana tunanin ma wacce Biba,
" Na sani"ya bata amsa dan sai yanzun ya tuna tunda yasan dai a shiyan mutum ɗaya ce ba ta da lafiya,shi baimasan sunan ta ba sai yau.
"Yaya wallahi jikinta rawa kawai yake sosai gashi yayi zau,na rasa me zan yi,tsoro nake ji kar wani abu ya same ta"
"Ki jika towel da ruwan sanyi ki dinga Gogo mata a jiki"
"Yaya nayi hakan amma abin ya fi karfi na dan kamar zata yi jijjiga"
Shi mutum ne mai tausayi sosai dan haka mikewa yayi tsaye daga zaunen da yake saman darduma ya fito,
Kai tsaye shiyan su ya nufa,sai da ya ƙwanƙwasa sannan tazo ta buɗe mai ya shiga,
Nuna mashi Biba tayi wacce take kwance an jibga mata zannuwan gado a jiki,Lokaci-lokaci kuma takan zabura,kai basai ka taba jikin ta ba,ko daga yanayin ta kaɗai ya isa ta shaida maka irin yanda zafin jikinta yayi sama.
Yasan ba shida wani taimako da zai iya mata tunda ba aikin shi bane,wayar dake hannun shi ya danna kira wanda sai da ta mai kusan miss call takwas sannan ya ɗauka cikin muryar Barci,
Ce mai kawai yayi"kazo shiyan kaka ina jiran ka"ya sauke wayar a kunnen shi.
Jin an ambaci sunan kaka ne yasa da sauri ya wastsake ya saka dogon riga ya fito,kai tsaye shiyan na nufa,a buɗe ya samu ƙofar dan haka ahiga yayi,yana ƙoƙarin nufar ƙofar kaka,dan ba karamin ji da tsohuwar suke yi ba,shi yasa lamari in dai nata ne basa wasa dashi ko kaɗan,
Ji yayi muryar Nafisa ta ce"Yaya Nurudeen nan zaka wuto "
Bin bayanta yayi inda ya taradda Suraj a tsaye,kallon shi yayi,sai dai kafin ma ta mai magana ya nuna mashi gado da ido,
Cikin sauri ya karasa inda take kwance tare da yaye bargon ya dafa goshinta,
Kallon Nafisa yayi cikin dan yanayin bacin rai tace"garin ya kika bari jikinta yayi zafi har haka,ba kisan tana ita shiga Fit saboda high fever ba"
Ita dai bata ce komai addu'ar ta daya Allah yaba Biba lafiya,
Yaye duka bargon da aka rufa mata yayi"kara karfin AC"
Dan waro ido tayi ganin yanda take rawar sanyi sannan ace ta kara AC"rawar sanyi fa take yi"
Wani irin kallo ya wurga mata da sauri ta yi yanda yace tana kallo ikon Allah,
Allah yasa dazu kafin Ammi ta tafi sai da ta taimaka ta saka mata dogon wondo da riga shima dogo har kasa mara nauyi amma na barci ne,sai hula,to garin zaburan da take yi ne hulan ya zame wanda nan take suman duk ya baje saman filo,ya rufe mata fuska,
Suman baki ne wuluk yanda kasan ta shafa mashi dayis saboda baƙi,ga tsantsi da laushi,
A hankali ya kai hannu yana kyara mata suman tare da shafawa yana kallon tushen suman don son tabbatar wa ko nata ne,
"Dibo ruwa da towel ki zo kina shafa mata,bari na dauko Alurai wanda zai taimaka mata" Ya karasa faɗa yana barin dakin da sauri,
Shi dai tana tsaye rungume da hannu yana kallon dun abinda suke yi,sai dai bai ce masu komai ba,
Ba jimawa kuwa sai gashi ya dawo da kayan aiki,cikin kwarewa ya