Showing 120001 words to 123000 words out of 159134 words

Chapter 41 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

27 Sep 2025

9745

bata ciki na tabbatar zata ji daɗi idan tasan anan kuka sauka,ni ma kuma zanfi samun natsuwa"

Kallon juna suka yi suna sakin murmushin farin ciki,domin kan lallai sun yarda yanzun Ummu Salma tayi aure kuma ta samu miji,

Bin bayan shi suka yi har cikin babban falon gidan.

Duk zaunawa suka yi a falon suka kara kallon gidan,

"Ya su Mama " Ya tambaya,

"Kamar yanda ka roka akan kar mu faɗa masu tukunna shi yasa basu san mun zo nan ba"

"Dama nafi bukatar ku fara ganin halin da yar uwar ku ke ciki saboda ku zasu fi su iya jurewa"

Abdulmalik ne yace"kani ni kam kana min kama da wani malami bari dai ka gani"nan ya ciro wayar shi ya kunna video din wa'azin Young ustaz mika ma Abdulrahman yayi"kalla ka gani kamar har ta baci "

Amsa yayi ya kalli na wayar ya kalli shi yanda yake zaune yana kallon su hankali kwance,
"Shine mana,kanin mu ai kai ne ko? Ya tambaya domin son tabbatarwa

" Ni ne"

Mamakin su ne ya saka boyuwa ikon Allah,"To Babban Malami irin ka a ina ka haɗu da Biba gashi har kunyi aure"

Dan murmushi yayi"is a long Story,idan ta tashi zata faɗa maku"

"Allah yasa ta manta da komai ta yafe mana"Abdulmajid ya fada cikin damuwa,

" Karka damu Allah ya bata lafiya "
Duk da Amin suka Amsa,

Tambayar shi suyi game da bayanin likita akan lafiyar ta,

Bai ɓoye masu komai ba ya sanar dasu har kuma da irin aikin da take buta,

"Abbas Mama ta faɗa mana lokacin Salma na da shekara biyar a duniya tayi fama da ciyon koda sosai wanda sai da cire Mama daya aka saka mata"cewar Abdulmalik

"In dai har Salma zata samu lafiya a shirye muke damu bada Kodar mu domin a saka mata" Kanin mu,dan Allah ka mai da mu Asibiti likita ya gwada mu ya gani a cikin mu duk na wanda ya mata a shirye muke damu bada har ta da jinin da take bukata"

Shiru yayi dai ba tare daya basu amsa ba tamkar dai mai nazarin kalaman su.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*73*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*



Sai zuwa yamma sannan suka kara komawa Asibiti domin a gwada su,dan lokacin da Dr ya basu kenan.

Abdulrahman ne ya fara shiga aka gwada shi,su kuma suna zaune a babban ofishin likita suna jira,sannan da aka kammala yi masu gwaje-gwajen daya kamata sannan suka koma gida dan sai zuwa gode sakamako zai fito,

_______A gidan kuwa,suna barin shiyan Kaka part din su suka shiga,
Zama tayi sharaf saman kushin tana sauke numfashin takaicin mahaifiyar nata,

Itama zama tayi kusa da ita"yanzun ya zamu yi"

Cikin jin haushi ta juyo tana fuskantar ta"akan me kenan?

"Akan wannan yaron mana Suraj,nasan kin San me nake nufi"

Ji tayi ranta na ƙara ɓaci "yanzun ni Momy me kike son in yi ne,ina ce tun farko sai da na faɗa maku ina son shi haka nan,amma ke da Aunty Atika babu irin zagin da baku mai ba,har da Marina sai da kika yi,bayan ni na hango ma kaina irin rayuwar da baku hango ba,gashi a karan banza kun saka wata yar aiki cikin daula,sannan yanzun kina tambaya ta akan me zamu yi? Mekewa tayi ta bar falon tana faɗin "sai ki san yanda za ki yi"

Da kallo ta bita baki buɗe "ki zo mu samu mafita" Sai dai ko kulata ba tayi ba tayi shigewar ta,

Dan shiru tayi tana nazarin maganar Kaka,in dai kuwa haka ne to dole ne Yusuf ya janye dan ko ana ha maza ha mata wallahi ba zata bari wannan daular ta wuce su ba.

_______karfe tara na dare ne suka kara komawa Asibiti tare domin jin sakamakon gwajin da aka yi.

Yanzun ma kamar dazu ne sune zaune a ofishin Babban likitan,sai dai wannan karon bashi kaɗai bane su uku ne,
Dan haka cikin kwantar da murya suka shiga yi masu bayani akan an samu jinin Abdulmalik zai dauki nata,batun koda ma haka na Abdulmajid zai mata,
Wannan bayanin ba karamin farin ciki ya saka su ba,

"Dr yanzun zuwa yaushe za'a gudanar da aikin?ya tambaya,

" Nan d kwana biyu,domin zuwa gode kayan da kayi mana oder zasu iso,dan haka sai mun tsaya mun kwada su yanda ya kamata"

"Babu damuwa Allah ya kaimu"

Da Amin suka amsa,

"Sai dai batun STEM Transplant zuwa gobe da yamma za'a yi mata shi,domin mun duba cigaban da aka fara samu ta wannan ɓangaren" Cewar ɗayan Dr ɗin.

"Babu damu a shirye muke a ko wani lokaci"

Daga nan suna fitowa gida suka koma domin Ammi ta kira akan ita ma tana hanya domin zuwa ta gana dasu.

Tun a harabar gidan suka shaida isowarta dan ganin baƙuwar mota a wurin parking,

A falon kuwa suna saka ƙafa wani daddadan kamshi na musamman ya ziyarci hancin,
Kalle_kalle yake a falon ganin yanda ko ina yayi fes,duk da falon a kyare yake a ko wani lokaci domin ma'aikatan gidan na ƙoƙari,amma gyaran mace dana namiji ba daya bane,
Fitowa tayi daga cikin hannun ta ɗauke da wasu hadaddun kuloli yayinda Bala ke biye da ita a baya shima yana dauke da sauran kayan,
Da sauri ya amshi kayan dake hannun ta yana murmushin farin ciki "Ammi sannu da zuwa"

"Yauwa har kun dawo"

"Umm" Ya faɗa yana ajiye kulan a table,

Cikin girmamawa suka shiga gaishe ta,
Amsawa tayi cikin dakin fuska tana nuna masu wurin zama,
"Ya kuka tsaya a tsaye,ku zauna mana"

Zaunawa sukayi "Ammi mun same ku lafiya"

"Lafiya qlau,ya iyayen naku"

"Suna nan lafiya"

"Ya jikin Baban naku,da sauƙi kuwa ko har yanzun sai a hankali"

Wannan karon kallon juna suka yi cikin mamaki,ya akayi tasan da jikin Baban su har haka,

Ganin sun dan shiga yana yi na mamaki ne yasa ta kuma cewa"karku damu hakan ba abin mamaki bane,domin na San iyayen ku shekaru ishirin da biyu data wuce"

Wannan karon ko Abdulmajid kasa ɓoye mamakin shi yayi"Ammi a ina kika san iyayen mu,sannan gashi kuma Ummu Salma tana auren danki,amma kuma baƙi taba niman itayen ta ba,ko dai dama kin riga kin San ko ita din wacece?amma baki nime mu ba?

Wannan karon kam murmushi tayi domin tambayoyin yaron sun mata,tana son mutum me confidence,"batun sani iyayen ku ba abu ne daya shafe kuba,wata kila nan gaba kadan ku na iya sanin a ina muka san juna,ita kuma Salma tun farko nasan ita din wacece,sannan maganar kiran ku ko maida ita gida kuma kun san ba abu bane da zai yu a wancan lokacin,domin zuciyarta bata gama karɓar kaddaran daya same ta ba,yanzun kuma da ta ji tana iya yafe maku ta karbe ku a matsayin ƴan uwa shine ta haɗu da wannan tsautsatin,shi yasa ma har Ɗa na ya kira ku domin ku ganta"

Duk shiru suka yi domin sun kasa tabbatar da manufar wannan matar,sai dai koma menene zasu jira har sanda ƴar uwar su zata farfado,

Nuna masu abincin dake gabansu tayi"kuci abinci kar yayi sanyi"

Cikin natsuwa suke cin abincin har suka kammala,
Mikewa tayi tana kallon su"ku kwantar da hankalin ku insha Allah ƙanwar ku zata samu lafiya,sannan ku dauka tamkar a nan gida kuke"

Haɗa baki suka yi wurin faɗin "mun gode"

Sallamah ta masu yayin da Suraj ya rakota har bakin mota inda Direbanshi dama ya dauko ta shi kuma zai maida ita,

Buɗe jakkan dake hannun ta tayi ta ciro wani dan karamin Kit fari ta miƙa mashi"na riga na gama haɗa komai na cikin wannan so yanzun kana iya haɗa shi da sauran"

Amsa yayi yana buɗewa,wannan farin abun ne daya ciro a cikin idon shi wanda ta bata a wancan ranar,a takaice Cameran ido"to Ammi"

Ajiyar zuciya ta sauke tana shafa fuskar shi "Allah ya albarkaci rayuwarka,"

Lip din shi ne kawai ya motsa wanda ke nuna alamun ya amsa,

Sai da ya tabbatar sun bar cikin harabar gidan sannan ya koma ciki.

Har sun shiga dakin da ya basu,

Ƙofar dakin ta naga ya buɗe ya shiga,
Dakin a gyare yake fes kamar akwai mutum a ciki,
Sif din kayanta ya buɗe wanda yake babba ne sai ba sosai ba amma mutum zai iya shiga ciki ya tsaya tsaf,
Kallon kayanta dake jere yayi,sai kamshi suke yi,lumshe ido yayi yana buɗewa,
Hannun shi manna a jikin sif din wanda nan take muryar naga wurin ya kawo haske yayin da muryar computer ya fara magana "welcom maste" Scanning tafin hannun shi wurin yayi,kafin kuma lokaci ɗaya naga kamar an tura kayan cikin sif din gefe shi kuma inda nan take yayi kasa,ma'ana wurin Elevator ne,
Tafiyar mintuna biyu sai gashi ya tsaya tsaf,bude ƙofar yayi ya fito, wanda wurin wani kayataccen wuri ne mai ƙunshe da nau'ikan na'ura na Cumpute kala-kala,komai na dakin fari ne sol mai matuƙar jan hankali,gashi a gyare shi ma wurin yake,
Buɗe wani kofar da akayi aka shigo ne yasa na mai da hankali wurin,
Bala ne ya shigo hannun shi rike da jug dan madaidaici mai matukar kyau wanda zaka iya ganin ma abinda ke ciki,

Murmushi ya saki ganin uban gidan nashi"barka da shigowa Yallabai "

A hankali ya taka har gaban waɗannan computers ɗin,wani soket ya dannan nan take gabaɗayan su suka kawo wuta,"ya iyalanka?

"Suna nan lafiya yallabai"

Zaunawa yayi a saman kuyera yayin da ya buɗe dan akwatin da Ammin shi ta bashi ya ciro wannan abun idon ya Daura a wani kwalba,ya jima yana danne_danne cikin kwarewa da sanin kan na'uran,sai da ya gama sannan ya shire ya mai dashi cikin akwatin,danne_danne yaci gaba dayi na tsayin lokacin wanda a ƙalla yayi kusan awa biyu,
Kallon agogo yayi wanda ya nuna ƙarfe sha ɗaya na dare,
Mikewa tsaye yayi yana miƙa tare da lanƙwasa wuya jin yanda ya riƙe masa,
Daukar jug din shayin da Bala ya ajiye mashi yayi yana tsiyayawa a ƙaramin cup,
A kan wasu jerin kushin masu matukar kyau da tsaruwa ya zauna yana mike kafa,cikin natsuwa yake kurban shayin yana dan lumshe ido yayin da yake kallon Screen din computer dake haska video cikin gidan tun daga ranar da yayi tafiya har zuwan su Pa da dauko wasikar da tayi ɗayan dakin,a takaice babu abinda bai gani ba har zuwa ranar da suka bar gidan,
Lumshe ido yayi a karo na ba adadi kamar mai jin bacci yana sauke su a kan hotonta,wanda take tsaye a harabar gidan dan daga dukkan alamu bata san da hoton ba,
Na ranar da taje taron wa'azin matan manyan malamai ne,

A yanda yake zaune yana kallon hoton yana sauke numfashi a hankali zai tabbatar maka da yana cikin wani yanayi wanda kallon shi dai bai isa yasa ka tantance a wani halin yake cikin ba,kallo ne irin na wanda ake ma mutumin da aka dade ana tsumayen shi,ta ɗayan bangaren kuma kallo ne irin iya matukar kewar ki,idan kuma har ka kara natsuwa da kyau hankalin ka zai iya baka cewar babu daya acikin biyun waɗannan kallon,domin kallo ne da ina matukar jin haushi ki,koma dai wani irin kallo yake ma hoton shi kaɗai yasan sirrin dake cikin zuciyar shi.

Ganin ƙarfe daya na dare yayi ne yasa ya mike yana kashe komai na dakin tare da barin wurin ta hanyar daya shigo.

*bayan kwana biyu*

Alhamdulillah an samu anyi STEM Transplant din lafiya,kuma likitoci sunyi Observing dinta na awa Arba'in da kwas ba tare da wata matsala ba,sannan a yau suke saka ran ƙarfe goma na safe za'a mata kidney Transplant din.

Tunda ya tashi wanka kawai yayi ya fito tare da nufar shiyan Kaka,domin a nan gidan ya kwana yau ba a gidan shi ba dan su Abdulmajid suna tare da Abdulrahman a Asibiti.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*74*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Da sallamah ya shiga shiyan kaka wacce ke zaune tana gyangyadi,
Murmushi ne ya subuce ya juya ya fita dan baya son ya takura mata,

A hankali yake takawa cikin tafiyar nan nashi tamkar na mai tausayin taka kasa,
Har ya baro shiyan kaka yaji daga bayan shi ana kiran sunan shi wanda hakan ya tilasta mashi juyawa,
Da hannun take mai alamar da yazo,
Babu musu ya isa in da take tsaye tana sakar masa murmushi,
Cikin girmamawa wacce take ɗabi'ar shi yace"Momy in kwana?

"Lafiya qlau Suraj,hala fita zaka yi da safe haka?

" Umm"kawai yace yana mamakin tsayar da shi da tayi,dan gaskiya bai cika shiga lamarin Momy Saudat ba domin yasan a matsayin data ɗauke shi,ita da Momy Rahama.

"Kaga dama kuwa akwai maganar da nake son muyi dai in ba damuwa ko zamu iya shiga ciki?

Kallon ta yayi ya kalli kofar falon ta da take nuna mai yana mai da kanshi ga Agogon Azurfan dake hannun shi,ganin yana da dan sauran lokaci ne ta saka ya sauke ajiyar zuciya " Ba damuwa Momy "

Tana gaba yana biye da ita har cikin babban falonta wanda take a kyare tsaf,dan ita ma Momy Saudat mace ce mai tsafta,

Nuna masa kushin tayi"zauna bari na saka a kawo maka abun kari"

"A'a na gode"

Bata saurare shi ba ta shiga kwala kiran maijiddarh,wacce bata san yana ciki ba ta shigo tana tura baki da fadin"Momy lafiya k...

Maganar ta tsaya ne a ƙasan maƙoshinta dalilin ganin wanda bata yi tsammanin gani ba musamman zaune a falon su,

"Kawo ma Yayan ku abun kari"

Da sauri ta juya tana fadin to,
Cikin mintunan da basu wuce biyar ba sai gata ta shigo dauke da tire ta ajiye a gaban shi,
Sannan ta nime gefen ta zauna tana satar kallon shi kasa_kasa,
Sai take ganin yau ya ƙara mata kwarjini sosai musamman da yake cikin shigar jampa na wani farin yadi mai matukar laushi fari tar wanda daga ganin shi kasan ba na karin kuɗi bane musamman yanda ya lafe a jikin shi,
Ta gefe ɗaya kuwa suman shi har daukar ido yake tsabar baki da ƙyalli da yake yi yanda kasan wanda ya shafa ma dayis,
Sai hakan ya ƙara fito da ainahin kyawun da Allah ya masa da wani irin ƙwarjini mai cika wuri irin na wadanda suka rike sallah da Salati,

Ganin har mintuna biyar sun ƙara shuɗewa babu wanda yace komai,shi kuma yana zaune tamkar wani hamshaki,

"Suraj kaci abinci mana"

Ƙara duban Agogo yayi "Momy bana karin safe da wuri"

"To ko ruwa ba zaka sha ba" Dan kauda kai yayi domin shi tunda yake su tayin abinci kamar na yau bai taɓa haɗa su ba,dan haka ba tare da ya kuma ce mata komai ba ya dauki koran ruwa ya buɗe ya tsiyaya a kofi yayi Bismillah yayi kurba daya ya ajiye.

Ganin yana shirin mikewa yasa da sauri tace"ya jikin matar taka?

"Da sauƙi" Ya faɗa ciki_ciki dan zaman sa anan din ya fara gunduran sa,

"Emmm dama a ina batun lamarin ka da Maijiddarh ya tsaya?

Wannan karon kallon ta yake sosai" Kamar wani lamari kenan? Ya mai da mata da tambayar,

Ganin yanda ya zuba mata idanu ne yasa ta danji zuciyar ta na rawa,amma idan ta tuna me take son tayi sai taji ta kuma samun kwarin gwiwa,"ina nufin lamarin auren ka da Maijiddarh,kaga tunda ka dawo kuma komai ya wuce to me zai hana a maida saka ranar na,kaga mu ko yanzun ka shirya a yau ɗin nan ma ana iya daura maku aure,ko me ka gani?
Ta fada tana da sare shi itama da nashi idanun.

Wani irin laulausar murmushi ya saki,irin mai tsayawa a rai,ya mike tsaye,juyawa yayi in da Maijiddarh take zaune kafin ya dawo da ɗuban shi kan ta"gaskiya Momy is not a good idea haɗa jini da jinin yahudawa,,sannan na ma matata Alkawarin ba zan taɓa mata kishiya ba,kin san wani abu kuwa?

Shiru kawai tayi tana kallon shi cikin tsananin mamaki domin bata taba tsammanin zai iya maida mata magana har haka ba,

Ci gaba yayi da faɗin "na kuma faɗa mata idan har a shekarar auren mu na farko ta haifarmin Baby to duk abinda na mallaka ya zama nasu,and I tell her that I Love her ita kaɗai,kinga Momy yin maganar Maijiddarh yanzun kamar cin amanar ta ne,wanda haka baya daya daga cikin hali na,dan haka ina mai baku haƙuri Allah ya bata miji na gari"yana gama fadar haka ya juya yayi fitarsa yayin daya barsu nan zaune tamkar wadanda aka zare ba jijiya,

Yana fitowa falon ya saki wani ɓoyayyen ajiyar zuciya tare da shafa kanshi yana busar da iska ta bakin shi,sai kuma ya saki murmushi tuna irin halin da ya baro su a ciki,tabe baki yayi lokaci guda yana fadin a ranshi when did I tell her that I Love her oho,ko ta yaya ma zan iya haɗa jiki da wannan yarinyar har ta haifa mashi ya'ya oho ya ba kanshi amsa yana daga kafaɗa da faɗin "aure zan yi "

Tunda ya doso wurin parkin din security din shi suka mike tare da buɗe ma shi kofar wani lafiyayyen farin mota a cikin gerin mitoci uku dake jire suna jiran shi.

*____________Asibiti*

Kira ne ya shigo wayar Abdulmalik wanda tun jiya ake ta dun shi da kira amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login