Showing 36001 words to 39000 words out of 159134 words

Chapter 13 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

27 Sep 2025

9726

yatsar ta,tana faɗin kash,ganin a maimakon ya faɗi sai wucewa yayi cikin tafiyar nan nashi na kasaita,

Kallon shi tayi ta kalli wurin,to kodai ba ta saka da kyau bane,
Cikin hanzari ta karasa wurin domin dubawa,sai dai tana saka ƙafa sai ji tayi tayi baya zuuuu ta zame sai gata tayi zaman yan Bori,
Ba ƙaramin zafi taji ba wanda yasa ta saki ƙara,kokarin mikewa take yi,sai dai ta kasa mikewa dan data yunkura sai santsi ya kuma kwasanta,
Jin motsi a bayanta ne yasa ta juya,sai ganin shi tayi tsaye rungume da hannu yana kallon ta,
Hannu ta shiga miƙa mai,alamun ya taimake ta,
Takowa ya fara yi a hankali har ya iso in da take,kallon sakon biyar ya mata da hannun da take mika mashi ya kada kai ya wuce abin shi,
Yaune karon farko da bakin ta ya fara furta sunan shi a gaban shi,"Suraj! Suraj,yaya Suraj! "Sai dai ko juyowa ya kalle ta bai yi ba ya yayi wucewar shi,
Faɗi take" Mugu,waiyo Allah mazaunai na,"ta faɗa tana dafa duwawun ta,da rarrafe ta samu ta bar wurin,tana masa Allah ya isa,dan bai faɗi ba shine yasa ita ta shige,ta faɗi.
Haka ta koma kicin ta kuma hado ruwa ta zo ta goge wurin kar wani ya kuma zamewa tunda wanda ta haɗa ma gadan ya tsallake,amma wallahi bawai ta hakura bane sai ta rama,dan yanzun suka fara,
Dafe ƙwanƙwaso tayi tana fadin wash tare da yamutse fuska.

Da yamma da kyar take iya mikewa a haka tayi girki,har Ammi na tambayar ta ko lafiya me ta same ta ne,sai cewa tayi zamewa tayi a banɗaki,

Nafisa ce ta zo shiyan su wai Kaka na kiran ta,dama lokacin shirin wanke-wanke take yi,dan haka Ammi tace ta tafi ta bar wanke-wanke Amira zata ƙarasa,

Suna fitowa,taga yanda aka ƙawata harabar tsakar gidan harda Docuration akai mai da su Balan_balan kore da Ja,wurin yayi kyau saboda ya samu wadataccen haske, haɗu da su Hadiza tsaye ita da Zainab sun sha kwalliya yanda kasan wadanda zasu gidan biki suka yi,
Ko kallon banza basu ishe ta ba,suka wuce abin su,sai ma Nafisa ce data gaishe su,ita ko kallon arziki basu ishe ta ba,
Kallon Nafisa tayi"yau me za'ayi a gidan nan ne?

Dariya tayi "ai yau karin shekaran Yaya Nurudeen da kuma Aunty Maijiddarh,dan a wata irin daya aka haife su,shi yasa suke yi a tare"

Cikin mamaki tace"dama gidan malamai haka ana celebration na Birthday?

"To su dai suna yi sai dai ba ko yaushe ba,suma da kika ga zasu yi kangara gare su,kuma iyayen su sun daure masu gaba da baya shiyasa,"

Taɓa baki tayi"shi yasa naga waɗancan masu kama da Ungulun sun sha kwalliya "
Dariya sosai Nafisa ta fashe dashi,domin ba karamin dariya abun ya bata ba,wai masu kama da Ungulu,

A zaune take saman kushin tana kallon wa'azi a TV,zama tayi kusa da ƙafafunta a ƙasa,"barka da dare Kaka "
Juyowa tayi"shine yau baki shigo kin duba ni ba ko Habiba,ko dai fushi kike da ni?

Ɗan dariya tayi"A'a Kaka,dama ina shirin na kammala aiki na na shigo ne sai ga kiran ki"

"Allah yasa da gaske ne"
"Sosai ma"
"Kaka to ya naga ke baki shirya ba?
" Shirin me kuma"
"Na zuwa party mana"
Dariya tayi "raba ni da shirme"

Nafisa ce ta shigo tana tambayar Kaka"a saka kayan yaji a ruwan shayin dake kan wuta?

"A'a barshi kinsan Surajo baya son yaji ko kaɗan,har balle barkono,idan ya nuna kawai ki tace sai a saka a fulas"
Da to ta amsa tana wucewa,

Hiran su suka cigaba dayi tana danna mata kafa,
Daga bisani tace ma kaka bari ta je tayi fitsari,tana shiga dakin Nafisa ta same ta a ciki tana ninke kaya,dan haka fita tayi ta zagaya ta kicin,
Ganin karamin fulas mai kyau yasa ta buɗe,ganin shayin ne a ciki yasa da sauri ta shiga dudduba durowoyin kicin ɗin,ganin garin Barkono yasa da sauri ta diba ta zuba a kofi,sannan ta zuba ruwa,yana dan kwantawa ta samu karamin lariya ta tace,sannan ta buɗe karamin fulas din ta zuba kusan rabi a ciki sannan ta mai da komai ta ajiye ta fito,
Dawowa falo tayi ta zauna ta cigaba da danna ma kaka ƙafa,

Ba jimawa sai kuwa gashi ya shigo shida Salman yana rike da wani karamin jakka a hannun shi,
Sai da ya gaida kaka kafin ya zauna,
"Kai kuma jakkan waye a hannun ka?cewar Kaka tana kallon Salman,
Mai da jakkan gefe yayi" Na yaya Suraj ne"

"Salmanu shiga kicin ka dauko ma yayanku ƙaramin fulas da kofi ka kawo mai"

Murmushi yayi"yauwa dama shi yasa na biyo Yaya dan in sha "ya faɗa yana shigewa kicin,
Ba jimawa sai gashi ya dawo harda kofuna guda biyu a hannun shi,
Budewa yayi ya fara zuba ma yayan shi sannan ya miƙa mashi,
Ajiye wayar dake hannun shi yayi ya karba kofin yana faɗin " Thank "

Kai Kofin bakin shi yayi yana shakan ƙanshin shayin idanun shi a lumshe,sai kuma ya buɗe ya juyo yana fuskantar Kaka,
Da sauri ta kauda kai daga haɗa idon da suka yi tana cigaba da matsa ma Kaka kafa,
"Waye ya dafa shayin?

" Khadija na saka tayi haɗin komai,sai kuma Nafisa dana saka ta tace shayin ta zuba a fulas"

Ajiye kofin yayi,ya kalle Salmanu dake ƙoƙarin kai kofin bakin shi"je ka kiramin Khadijah "

Ajiye kofin yayi ya fita da sauri dan Allah_Allah yake ta dawo ya shaya shayin ahi,
Ba jimawa kuwa sai gashi ta shigo cikin yanga tana wani juyi cikin wani dogon riga na material data saka mai bala'in daukar ido,gashi ta sha makeup sosai,

Zama tayi gefen shi dan nisa da shi kaɗan,sai dai kuma ko kallo bata ishe shi ba,dan bai ma juya ya kalli inda take ba "Yaya Suraj gani"

Ba tare daya juyo ba yace"kira Nafisa "
Ta gane wa yake nufi dan haka a bakin kofar dakin Nafisa ta tsaya ta faɗi mata,
Tana dawowa tana kokarin zama ya nuna mata gaban shi,"dawo nan ki tsaya"

Nan take gabanta ya yanke ya faɗi,ganin yanda yayi maganar a dake,babu alamar fara'a a fuskar shi,ko wasa,to me tayi,domin ta san duk wanda zai ce ma ya tsaya a gaban shi to ba alkhairi bane,tambayar kanta ta fara tana tunanin abinda tayi a yinin yau,
Cikin sanyi jiki ta tako ta tsugunna a banshi tana karanto duk addu'ar dake bakin shi,
Kallon Nafisa yayi wacce ta iso tana kokarin dukawa a gefe ya nuna mata gaban shi kusa da Khadija,alamun ta tsaya a wurin ita ma,

Sake ƙafar Kaka tayi ta juyo tana jiran taga meke shirin faruwa,

Gani tayi ya juyo kanta kafin su haɗa ido da sauri ta kauda kai gefe,amma duk da haka sai da yace"ke ma dawo nan"

Da sauri ta juyo tana waro mai dara_daran idanun ta tana buɗe su a kanshi,tare da nuna kanta"Ni?

Mai bata amsaba shima sai madaidaitan adanunshi daya sauke a kanta,alamun tabbatar wa,

Ita dai Kaka tana kallon ikon Allah,
Ganin yanda ya jera su a gaban shi duk su uku......
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*25*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Kallon Salman yayi "ɗauko wani kofin a kicin"
Tashi yayi ya dauko mai yana mamakin me zai yi da wani kofi kuma,"dauko shayin ka"

Nuna ma Khadija wanda ke cikin kofin yayi,"ɗauka"

Cikin sauri ta dauka babu musu,
Ɗayan kofin da Salman ya kawo ya nuna ma Nafisa "juye na cikin fulas ki ɗauka"ita ma haka tayi,

Shi kuma Salman cikin girmamawa yace"yaya gashi"

Nuna Biba yaya,domin shayin kofin Salman yafi nashi yawa"bata"

Kallon yayan nashi yayi ya kalli shayin shi da ya kwallafa ma rai,sai dai ba damar tambaya in ba haka ba ya ja ma kanshi,mika ma Biba yayi,
Sai dai sam taki karɓa sai ma kauda kai da tayi,kara mika mata Salman yayi amma taki kula shi,

Ɗan murmushin gefen baki ya saki wanda lokacin yayi dai-dai da dago kai da tai ta kalle shi,bata san sanda ta furta masha Allah ba a zuciyar ta,tunda take ganin shi bata taba tsayawa ta mai kallo koda sakon goma ba ne sai yau,idan ana maganar kyau da gayu aka zo nan an kai iyaka,fari ne shi sosai irin tas ɗin nan,idanun shi matsakaita ne farare tas dasu,sai dai kuma bakin cikin idanun ba baƙi bane brown ne mai matukar daukar hankali irin wanda ba kowa bane ke iya jure haɗa idanu da shi,
Giran shi a cike yake gazar_gazar baki kirin,sai dai ita tunda take bata taba ganin namiji mai tsayin giran ido mai matuƙar jan hankali ba irin nashi,idan yana kallon kasa zaka ɗauka idanun shi a rufe suke kamar dai yanzun da duk umurnin da yake basu hankalin shi nakan wayar da yake dannawa,idan kuma aka gangaro kan Lips din shi,ji tayi tsigar jikin ta na tashi kallon su kawai da tayi,domin gasu yan kanana jawur da su,har wani maiko suke na daukar hankali yanda kasan ya shafa masu man baki,
Gaskiya ba shi ba babban baki yanda kasan na mata,zuciyar ta ne ya raya mata ko dai mace Allah ya so ya halicce shi,sai kuma aka yi shi namiji,
Sai dai kuma suman kanshi ba mai laushi bane,ko irin mai kwantawar nan a'a,mai ƙarfi ne dan a tsaye yake yashe kyara an aske gefe_da gefe sai kyallin maiko yake yi,gashi baki kirin yanda kasan ta saka bakin abu,

Nan take taji kishi ya kamata,wallahi wannan ko tantama bata yi yafita kyau nisa ba kusa ba,haba dan Allah ai dole yayi yanga ya kuma wulakanta mata,
Tun ranar farko da ta fara tsayawa kusa dashi take maitan ta gano wani kalan turare yake amfani dashi,sai dai ta kasa gani wani irin kanshi ne wannan,
Domin kamshi ne dake fita a hankali_a hankali yake mamaye wurin da yake,sabanin wani turaren da tun mutum na nisa da kai zaka fahimci zuwan shi saboda kamshin turaren shi,amma nashi sai ya iso daf da daf sannan kamshin zai fara tashi yana mamaye wuri har balle idan ace ya zauna ne to ba'a magana,a takaice kamshi ne mai kashe zuciya da saka nasuwa,
Ji tayi cikin sanyin muryar nan nashi wanda baya fita da hayaniya yace"idan kin gama ƙare min kallo ki amsa abinda ake baki"
Lumshe ido tayi sannan ta buɗe a hankali saboda sai da ya ɗan matso kusa da ita kaɗan sannan yayi maganar,yayin da daddadar ƙanshin dake fitowa daka bakin shi ya dake fuskarta,
Ba tare data ce komai ba ta amsa kofin da Salman din ke mika mata,kanta a duke saboda tsare ta da ido da yayi,

Nurudeen ne ya shigo da sallamah yana faɗin "Kaka ina kayan dana baki ajiya?

Miƙa mashi hannu tayi" Kaga zo ka taimaka min na shiga ciki,tunda an gama wa'azin "

Kallon su yayi ya Suraj dake zaune ya daura kafa daya kan daya,nuna su yayi"su kuma waɗannan fa kamar masu niman gafara "

"Aikin ɗan uwan ka ne,ni zo ka daga ni"

Kallon Biba yayi,sannan yaje ya taimaka ma Kaka ya kai ta daki,sannan ya fito dakin riƙe da leda a hannun shi,
A maimakon ya wuce sai niman wuri yayi ya zauna yana kallon su,

Kiran sunan ta yayi"Khadija "
Da sauri ta amsa"Na'am Yaya"
"Ajiye kofin ki wuce,'ya nuna Nafisa" Ke ma tashi ki tafi"
Cikin sauri duk suka ajiye kofin suka mike,
Ganin haka yasa itama ta ajiye kofin tana kokarin mikewa,
Wani irin tsawa daya daka mata sai da taji hanjin cikinta ya kaɗa,"who the hell are you to stand up ?

Ba ita kaɗai ba har su kansu basu san sanda suka koma suka tsugunna ba,
Domin ba zasu iya tuna randa yayan nasu yayi irin wannan tsawar ba,
Lallai yau an tabo shi,
Mugun kallon daya sakar masu ne yasa ba shiri suka ƙara mikewa suka bar shiyan gabaɗaya,har ita Nafisa da Salman,domin sun san yau kan Biba sai kuma ta Allah.
Nuna mata kofin dake gaban shi yayi"ɗauka ki shanye "

Duk da a tsananin tsorace take dashi karo na farko,amma hakan bai hana ta zaro ido ba tana girgiza kai,

Cikin sanyi da son sulhunta komai Nurudeen yace"Bro pls kayi haƙuri koma me ta maka ka yafe mata"

Nan take ya saki fuska harda sakin dan guntun murmushi yanda kasan ba shi ya gama tsorata su ba yace"is ok ni Bani da damuwa,kawai in kana son na haƙura ta ɗauki shayin nan ta shanye "

Kallon Biba yayi wacce tuni ta fara hawaye,saboda ta san Me a cikin shayin wanda gashi har tururi yake na zafi,
"Ok zata sha,badai shayin bane matsalar?to zata sha"

Ɗaga kafaɗa yayi"ok then"

Cikin muryar lallashi ya kira sunan ta"Biba "

Allah sarki jikin ta har bari yake ga hawaye duk ya wanke fuska ta juyo tana kallon shi"is ok ya isa,ki kwantar da hankalin ki I am with you,shayi ne kawai zaki sha,dan haka ki ɗauka ki sha sai ki wuce"

Da sauri ta girgiza mai,
"Me yasa ba zaki sha ba" Ya tambaya

Cikin kuka tace"bana shan shayi"

Nuna mata kofin dake gabanta yayi"amma wannan ba kalan shayin da kika saba sha ba,wannan yana ƙara lafiya dan haka ki daure ki sha a wuce wurin"

Girgiza kai take yi"dan Allah kar ka bari ya saka ni in sha mutuwa zanyi,dan Allah ka taimake ni"

"Is ok Baby I will help you"
Maida kallon shi kan Suraj yayi wanda gabaɗaya ma hankalin shi bai kansu yana kan aikin da yake yi a waya,

"Suraj wai me yasa kake son ka tilasta mata ta sha,tunda bata ra'ayi kamata tayi ka bar ta, ba kowa ke da ra'ayin shan shayi ba har balle irin wannan"

Ko kallon su bai yi ba,
"Suraj pls ka ajiye wayar nan muyi magana mana," Ya faɗa cikin roƙo dan yasan halin shi idan har yace zai mai garaje yana iya hassala shi,

"Me kake buƙata? Ya faɗa ba tare daya ajiye wayar ba,

" Dan Allah ka saurare ni dai"

Ajiye wayar yayi yana fuskantar shi"ok ina jin ka"

"Dan Allah ka bar ta ta wuce"

"Idan kana hada ni da Allah kana ƙara ja mata ne"
"Sorry na fahimta to ka bar ta ta wuce"

"Me yasa dana ce kowa ya dauko shayin ya ɗauka ita taki karɓa?

" Me kake nufi?

Ba tare daya kalle in da take ba yace"ka tambaye ta"

Kallon ta Nurudeen yayi"me yasa baki ɗauka ba?

"Bana shan shayi shi yasa"

"To kaji me take"

"Yauwa kai likita ne ai ko?

Jinjina kai yayi" Sosai ma kuwa"

"Zaka bari ta mutu a gabanka?ya faɗa yana nuna mashi Biba.

" Kai ina har abada,idan akwai hanyar da zan ceceta sai nabi dan ceto ta"

"That is good,dan haka ɗauka kisha yanzun kafin na nuna maki asalin waye ni ta yanda ba zaki taɓa manta hakan ba" Ya faɗa cikin tsananin daure fuska babu alamar wasa a ciki,

Kokarin magana yake amma sai cewa tayi"idan ba zaka iya jira a nan ta sha ba,ka jira ta a waje idan ta fito ka ceci rayuwar nata"
Jin abinda yace ne yasa yayi shiru kawai yana kallon su,
Yayin da ita kuma ta dauki kofi cikin kuka tana faɗin "i am Sorry" Sai dai ko kallon ta bai yi ba,

Kurba daya taima shayin ai da gudu ta mike ta shiga yarfe hannu ta rufe baki dan ta kasa haɗiye wa,
Duk da kallo suke binta,ƙoƙarin zubarwa take yi taji yace"idan har kika zubar zan ƙara maki wani "

Da kyar da rintse ido ta haɗiye,
Gaban shi ya nuna mata dole ta dawo ta tsugunna,a takaice ranar taga Azaban da tunda Allah ya halicceta bata taɓa tsammanin haɗuwa da irin sa ba,domin ko wani kurba daya ji take kamar zai tafi da numshinta da fatar bakinta harma da maƙoshin ta,
Tayi kuka tayi data sani tayi ban haƙuri amma bata taɓa tsammanin rashin imanin shi yakai nan ba,

Da Nurudeen ya nuna bacin ranshi sai cewa yayi idan ya kuma magana sai ya kara mata ruwan shayin domin ita da kanta ta haɗa abinda zai kashe ta,ko ƙarya na faɗa? Ya faɗa yana kallon ta yanda miyau ke dalala daga bakin ta,

Da sauri ta girgiza kai,Alamar haka ne,

"Dan haka idan ba zaka iya jira har ta kammala ba kana iya jira a waje"

Gaskiya ba zai iya ba,amma kuma ya tausaya mata,wata kila saboda bata san halin Suraj din bane shi yasa ta yi gangancin yi masa kutse,
Tashi yayi ya bar falon.

Bai damu da yanayin da take ciki ba sai da ya tabbatar ta shanye shayin dake cikin kofin tas sannan ya mike tsaye,dukowa yayi saitin kunnenta "ki tabbatar da ƙwarin gwiwar ki kafin aiwatarwa" Yana gama faɗar haka yayi ficewar sa ya bar ta nan tana fitar da numfashi da ƙyar,

Ko tashi bata iyawa sai da Nafisa da ke kofar gida taga fitowar shi shine ta shiga ta dagata,
Amma ina ko tashi bata iyayi,da talla_talla ta taimaka ta kaita shiyan su,dan ji take cikinta kamar ana busa mata wuta a ciki,
Ranar bata ga komai ba sai da daddare domin ranar a cikin bayi ta kwana,domin zawo mai azabar yaji ya kamata,tun tana yi tana iya fitowa har ta koma a banɗakun kawai take zaune,ko zaman ma sai dai tayi goho,tun tana iya hawaye har takai bata iyawa,domin abun sai ya haɗe mata ya zama Amai da zawo,
Kafin gari ya waye har ta zabge yanda kasan wacce tayi jinyar shekara,ko tashi bata iyayi,ita kanta Ammi data ganta da safe sai da ta tsorata,cikin gaggawa tasa akayi Asibiti da ita,a takaice sai da tayi kwana uku a Asibiti tasha ruwa leda Takwas,dan zawo tayi bana Arziki ba ko zama taba iyawa,
Duk numfashi daya cikin tsine ma Suraj take,in Allah ya yarda yace ta tabbatar da ƙwarin gwiwar ta kafin aiwatarwa to sai ta bashi mamaki,sai tasa yayi suman tsaye..
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login