Showing 24001 words to 27000 words out of 159134 words
Chapter 9 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
ya girgiza kai"A'a Ammi zuwa ajima zamu fita da Abbu ne sai dai ko Suraj"
Jiyowa yayi ya kalli yayan nashi yana bata fuska,wanda shi kuma da sauri ya kauda kai,
"To hakan ma yayi,kaga sai kuje kaida Amira ku gaida su"
Ba zai iya ci mata musu ba ko kaɗan,kuma ma bancin haka zai so ganin karshen mai ƙarya,"insha Allah Ammi,sai dai kimin hakuri zuwa bayan sallar la'asar sai mu je "
"Hakan ma yayi Allah ya kalmu"
"Na gode sosai Mam Allah ya biya ki,Allah yasa kifi haka"
"Amin kar ki damu,ɗauki ga bakin leda can ki kaima Kaka"
Ɗaukar ledae tayi ta fita tana sharan hawaye,
Girgiza kai Ammi tayi"yarinya abin tausayi"
Duk cikin su ba wanda ya bata amsa.
Tana fita kai tsaye shiyan kaka ta shiga inda ta same ta a zaune saman Babban darfuma ta mike ƙafa Nafisa na ja mata,
Cikin girmamawa ta gaishe ta tare da ajiye mata ledar a gefe,
"Ɗauka ki kai min ɗaki Biba"
"To Kaka" Ɗauka tayi ta shiga ɗakin,
Tsayawa tayi sake da baki tana kallon ikon Allah,wai dama har yanzun akwai irin wannan Gadon na mutanen da Mai Runfa,lah,ita da labarin shi kawai take ji bata taɓa gani ba,
Dakin gabaɗaya tsarin shi da kayan dake ciki duk na mutanen da ne,sai dai komai a tsare yake,kuma a tsaftace,
Akan wani teburi ta ajiye ledar ta fito tana murmushi,
Zama ta yi a gaban kaka tana tankwashe kafa,"Kaka nikan dakin ki yamin ƙyau sosai "
Kallon yarinyar tayi itama ta tana sakar mata murmushi "me ya burge ki a dakin tsohuwa?
Cire hannun Nafisa tayi daga kafar Kaka ta shiga matsa mata a hankali tana dannawa" Komai da komai,kinga ni kam har balle wannan gadon naki mai runfa,da kwanunaka,harda kyaryan mai kamar kwanu,kinsan wani abu?
Girgiza kai tayi tana jin daɗin matsar ƙafar da take mata,dan har tafi Nafisa iyawa,ta kuma san dai_dai inda yake ma mutum ciyo,"A'a saikin faɗa "
"Inda ace mijin da tan aura zai so irin waɗannan kayan ko,da nazo kin ɗan min naki na tafi dashi,ɗan Allah idan kin tashi kyauta da wannan gadon ki bani ina so kinji" Ta fada tana marairace fuska.
Dariya sosai Kaka ta saka ganin yanda ta wani marairace fuska ita a dole tana roƙo"in banda ke me zaki yi da kayan tsohuwa"
"Ni dai ina so kinji kaka,kuma kullun zan dinga zuwa ina danna maki kafa ina kuma tuna maki dan kar ki manta"
Dariya take tana jinjina wauta irin na yarinyar wacce cikin lokaci kankani ta shiga ranta,
Abbu ne suka shigo tare da Abba,suma da fara'a a fuskar su jin dariyar tsohuwar tun daga ƙofar falo,
Sallamah suka yi tare da shigo bayan kaka ta amsa,
Ganin sun zauna kusa da kaka ne yasa ta matsa tana gaida su,
Abba ne yace"wacece wannan "ya fada cikin sakin fuska dan shi yana da son wasa da yara.
" Sunan ta Biba ina jin baku taba haɗuwa bane,amma a dakin Ammin yara take,bayan tafiyar Abbu Sufyan ne na daukar ma Ammi ita saboda tsautsayin daya same ta"
"Godiya muke Uwar ƙwarai" Cewar Abbu yana murmushi,
Cikin jin na'uyin dattawan tace"Kaka na tafi sai anjima"
"To Ƴar Albarka sai na ganki,kar dai ki manta da Alƙawarin mu"
Dariya tayi kasa_kasa"ba zan manta ba"
Tana fita Abbu yace"to wani Alkawarin kuma aka yi"
Tana dariya ta sanar dasu yanda suka yi da Biba,aikuwa suma ba karamin darawa suka yi ba,daganan suka shiga hira kamar yanda suka saba duk Juma'a,a haka itama Goggon yara tazo ta same su,sai daf da sallar la'asar sannan suka fito shiyan su mazan suka tafi masallaci....
Tana fitowa shiyan kaka komawa tayi shiyan su,a kicin taga abinci a kula ta diba iya cikinta ta shige daki.
Sai da taci ta koshi sannan ta mike,juye_juye ta hauyi akan gadon,haka kawai ta rasa meke mata daɗi,ta rasa natsuwarta,komawa ƙasa tayi ta kwanta,sai dai nan ma haka ne,ji take kamar tayi ihu,abinda bata so tayi dai shi ne dole zata yi dan samun kwanciyar hankalin ta,in ba haka ba ji take kamar ta tube kayanta tayi yawo tsirara,
Jakkan kayanta ta ciro ta zazzage shi gaba ɗaya,daga can tsakan jakkan naga ta ciro wani dan sacet din magani wanda banga suna a jikin shi ba,guda daya naga ta cire tare da ballashi gida biyu ta saka rabi a baki ba tare data damu ba akan ta kora da ruwa,
Har wani jan numfashi take da saukewa tana wani lumshe ido yanda kasan wacce keshan wani abin daɗi,
Maida sauran tayi a kasan jakkan shi kuma ballin ta samu leda ta daure shi,harfa ta kusa gama mai da kayan kamar wacce aka tsikara ta kara zazzago kayan ta ciro ballin ta wurga abaki ta tattaune shi,goran ruwan da taci abinci shi ta dauka tasha sannan ta kara mai da kayan,
Komawa tayi kan gadon ta kwanta tana kallon sama yayin da taji wani natsuwa da kwanciyar hankali na sauko mata,a hankali ta fara lumshe ido tana budewa,ganin yanda dakin ya fara juya mata a hankali a hankali,
A haka ta kasance ita dao ba'a sume ba ita ba'a farke ba,har lokaci ya tafi.
Ganin an idar da sallar La'asar ne Ammi tace Amira taje ta sanar ma da Biba akan ta shirya yanzun Suraj din ya mata waya su same shi a bakin get.
Koda ta shiga dakin a kwance ta same ta,dan haka karasawa tayi inda take kwance tana tada ita"Biba,Biba,ki tashi wai Ammi ki shirya Yaya Suraj na get yana jiran mu"
A hankali ta buɗe idanun ta,waɗanda ba karamin nauyi suka mata ba,da kyar ta iya haɗo ɗan sauran hankalin daya rage mata"to ganinan zuwa"
Juyawa tayi ta fita ba tare data lura da halin da take ciki ba,
Ita kuma ganin ta fita ne yasa ta tashi da kyar ta shiga ban ɗaki,ruwan sanyi na fanfo ta kunna ta tara kanta,sai da ta gama jikewa sannan ta fito,ita gaba ɗaya jinta taje a 140 komai daidai,
Jakkanta ta jawo ta ciro jallabiya baki ta saka,ta tauko zanin Atamfa ta daura asama,sai karamin Baby hijab ta daura a sama,wanda ana ganin bakin jallabiyar da yake da dogon hannu,kuma ta kasan ma zanin bai gama sauka ba,ana ganin baƙin jallabiyar,takalmanta masu kyau ta saka ko nace masu ɗan dama dama acikin wanda A'i ta saka mata,
Tana fitowa ƙafarta na gurdewa da takalmin kasancewar sa mai ɗan tudu,
Ammi bata falo dan haka tayi wucewar ta,dan ma ko tana falo ba ganewa zata yi ba,
A bakin kofar gida ta iske Amira a tsaye wacce tana ganinta ta karasa in da mota ke fake ta buɗe gidan gaba ta shige,
Ita ma tana zuwa gidan gaban ta buɗe tana ƙoƙarin zama a kan Amira,
Ganin da gaske zauneta zata yi ne yasa da sauri tace"ke Biba baki gani na ne zaki zaune ni"
Dakatawa tayi,cikin wani irin yanayi tace"Ke Amira baki gani na ne da ba zaki ce min akwai mutum ba,ni fa bana son iskanci,
Ta faɗa tana buɗe ƙofar baya ta shiga ba tare data kulle kofar ba,
Kallon juna sukayi ita da Yaya Suraj wanda ya kauda kai,
"Mu tafi mana wai me muke jira ne,nifa zafi nake ji,
Juyawa tayi ta kalle ta sai gani tayi kofar motar a buɗe," Oh My God,Biba nifa ina da abinyi dan Allah ki kulle ƙofar motar mu tafi "
Kallon ƙofar tayi,cikin mamaki tace "wani kofar zan kulle bayan wanda na kulle,ko dai baki gani ne?
Kallon yayan nata tayi" Is she ok?
Kara kauda kai yayi gefe kamar bai ji ta ba,
"Ya ilahi" Ta fita ta rufo kofar da karfi cikin jin haushin Biba wacce tayi wani shiri kamar mai shirin yin Surfe,
Jan Mator yayi suka hau kan titi yayin da babu mai yi ma ɗan uwan shi magana kowa da abinda yake sakawa a ran shi,
"Ta wani Get zamu shiga" Ya fada a hankali ganin sun kusa isa.
Jin ba'a tanka mashi bane yasa cikin jin haushi Amira tace"wai ba da ke ake magana ba Biba?
Kamar me magagi cikin ihu wanda sai da ta kusa tsorata su daga shi har Amira tace"ta kofa zamu shiga"
Juyawa baya tayi " Biba wannan wani irin hauka ne,ba sai ki yi magana a hankali ba"
"Kaji min yarinya,bancin a hankali nayi magana,so kike nayi ihu ne,ni da ban iya ihu ba,a hankali nafi iya magana sai dai ki yi haƙuri,"
Da karfi ta dafa kujeran da yake zaune"kai Direba kayi gudu damu mana kamar kana tuki,wai ko dai kanada tsohon Basir ne "
Kiran sunan Allah ya fara domin kuma ya tabbatar daga dukkan alamu yarinyar nan da wuya in tana da hankali,
Ba wanda ya kulata har suka isa cikin Asibitin suka faka mota in da ake ajiyewa,
Suna fitowa da kyar ta samu ta tsaya,dan wallahi zuwa lokacin ƙwayar data ci ya gama jukuwa,
"Ta ina zamu bi? Cewar Amira tana kalle a cikin Asibitin,
Ihu tayi da gudu taje ta rungume wata mata suna dariya tare,
Jawo matar tayi ta takawota gaban su" Yaya ga Aunty Jasmine,Malamarmu ce"
Gaisawa suka yi da matar cikin mutunci,
"Ɗan Allah yaya Kuje bari ingaida yayar ta da aka kwantar zan karaso"
Jinjina mata kai kawai yayi,
Jan hannun ta malamar tayi suka wuce,
Shi tsoron yima yarinyar ma magana yake yi Allah ya gani,balle yanda ta wani kame tana daga hanci,
Badan yaso ba yace "mu je wurin Mamar taki"
Gaba tayi shidai yana binta a baya,da haka suka shiga cikin Asibitin,shi dai yaga sai wuce bangarori daban-daban suke suna tafiya,wani wurin ma sau biyu suke zagaye shi,
Shikan ya gaji da wannan zagayen dan ya lura kamar ma tafiya kawai take yi,
"Ke tsaya"
Juyowa tayi ta kalle shi,
"Wai ina ne wurin"
Cikin kallon rashin fahimta tace"ina ne ma za mu je?
Wannan karon ko dafe goshinshi yayi,yau Ammi ta haɗa shi da aiki,da ba dan babu yanda za'ayi ya koma ba tare daya cika umurnin ta ba da tun a titi data kira shi da suna Direba yayi wulli da ita,,
Cikin bacin rai yace"gaida mahaifiyarki "
Dafe kai ita ma tayi"Oh ashe haka ne,nama manta,"yatsarta ta saka abaki tana juye juye"ta ina ne ma hanyar "dan gani take gabaɗaya hanyar ya rarrabe mata,
Dan hanyar ya kasu kashi uku ne ko wanne da bangare da zai kai ka,
Hannun hagu ta nuna tana dariya " Yauwa,Ustazu nan ne hanyar"ta faɗa tana yin gaba,
Ba yanda ya iya dole ya bita har kofar wani daki,
Sai da ta ƙwanƙwasa sannan ta cire takalmi ta shiga da sallamah,juyowa tayi ta kalle shi "shigo mana"
Babu musu yana hamdala a zuciyar shi koba komai yayi barka ya rabu da Tambelen ta,
Dan haka shima da sallamah ya shiga sai dai bai cire takalmi kamar ita ba,
Kasa karasa sallamar yayi ganin a inda suke,wanda ba ko ina bane da ya wuce banɗaki,
Yanzun banɗaki yarinyar nan ta kawo shi,
Cikin tsananin masifar da ba zai iya riƙe kanshi ba awanni lokacin yace"wai ke wata irin mara hankali ce,dama Mamar taki a banɗaki take,sh...........
Kafin ya karasa fadar a binda ke bakin shi ta yanka ihu mai ƙarfi tare da fadowa jikin shi tana kankameshi,wanda ba karamin tsorata shi tayi ba dan saura kaɗan su zube ƙasa da ba dan yayi saurin dafe bangon ba,dan a rayuwar shi babu abinda ke saurin tsorata shi irin ihu, ita kuma wannan shedaniyar kamar ta sani sai tsorata shi take........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*18*
*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*
Kokarin ture ta daga jikin shi yake yi amma taki bashi dama,sai ihu take yi tana kuka wanda haka ne yaja hankalin mutanen dake wurin tare Nos,
Da sauri ya maida face mask din data cire mashi dan baya son ko kaɗan a san waye shi,wannan ma yana iya zamar mashi abin kunya,
Nos din data iso inda suke ne cikin faɗa_faɗa tace"wai meke faruwa anan ne"
Da sauri ya cire ta daga jikin shi yana tura ma nos ɗin ita wacce ganin zata faɗi yasa ta rukota jikin shi,
Ita kuma cikin gushewar hankali ta cakumi wuyar matar tana nuna mata shi"wannan ne,wallahi shi ne,ya.. Ya...
Ganin da gaske shirin zubewa take yasa wata mata dake kusa da ita ta jijjiga ta,dan suna tsoron ko wani mugun abin ya ta"je buɗe idon ki,me ya maki "
Ƙara nuna shi tayi da hannu "Mama ta,Mama ta ya sace"
Duk mutanen dake wurin cikin tsoro suka zubo masa ido,wanda shima kanshi cikin tsoron yake kallon ta ganin tana shirin jawo masa masifa,
Juyawa yayi da shirin barin wurin ta kwalama security kira,
Jin an kira security ne yasa ya tsaya,
Zuwa lokacin babu abinda yake yi sai kiran sunan Allah a zuciyar shi, domin sam baya buƙatar a san koshi waye,
Cikin yanayi na fitar hankali ta kuma cewa"Ku duba min shi,tana nan cikin Aljihun shi ya saka ta,ku caje min shi da kyau"
"A'a anya kuwa wannan kanta daya kuwa,Madam Merry ina ga fa kamar mata cikin hankalin ta,ji yanda take magana"
Duk kallon ta suka yi domin tabbatarwa,
Shi kuma da wannan damar yayi amfani yabar Asibitin yana hamdala dan ko takan Amira bai bi ba.
*Bayan Sati ɗaya*
Tunda ta dawo gida bata ƙara saka shi a ido ba har yau,haka kuma ta kasa tuna me ya faru a wannan ranar,ita dai kawai tasan ƙwayar da ya kamata ace ta raba guda daya kashi uku ta sha,shine ta shenye guda ɗaya,
Sai dai tana iya tuna ta shiga mota zasu Asibiti,amma daga nan bata iya tuno komai,sai farkawa da tayi ta ganta kwance a Gadon asibitin bayan awa biyar.
Tsakanin ta da kaka kuwa a kwai shakuwa sosai,dan yanzun duk yamma ita ke mata dannan ƙafa,yayin da suke shan hiran su sosai,
Yau ma kamar ko yaushe ne a wurin ta,sun saka Kaka a tsakiya ita da Nafisa sai dariya suke mata tana basu labarin lokacin da zata yi aure irin lallin amare da aka mata,Lallin gida aka saka mata tun daga tafin kafa har zuwa guiwar kafa,shine wai idan zasu yi aure irin shi zata ma kowanne su,
Sallamar da akayi ne tare da shogowa shi ya katse su,
Cikin jin haushi da ɗan tsawatsawa matar tace "wannan wani irin rashin hankali ne da tarbiyya zaku buɗe baki haka kunata dariya kamar wasu batattu,"
Kallon Bibi tayi dake kwance samar dadduma "come on,Dalla sauka,dama ku ƴan aikin nan baku iya samun wuri ba,ni bansan me yasa kike haka ba Mama,ai wannan raini ne,ace inda ɗan gida ke zama nan nasu aiki ke zama,kai ku saurare ni,daga yau bana son na ƙara ganin ku a a zaune irin haka,indai ba wani aiki ba,"
"Kin dai sana'a bana son irin wannan halin Rahama,da masu kuɗi da talaka ai duk na Allah ne,dan haka bana son kina banbacewa ba, "
Daga bakin ƙofa taji ance"wlh Mama Gara ta banbance,dan masu aikin yanzun idan ka yi sake sai su ce sune masu gidan kai kuma kai ne ƴan aiki,"
Nuna Biba tayi"ƴar uwa Kinga waccen yarinyar,duk gidannan babu mara kunya irin ta,kiri_kiri na saka ta abu ace bata yi"
Cikin Mamaki ta maimaita kalmar "bata yi"
"Kwarai kuwa"
Kaka ce ta kuma katse su"ni fa bana son haka,abinda ya wace kuma me na maimaita shi,bana son haka,ku kuma ku tashi ku tafi"
Da sauri Nafisa taja hannun ta suka bar falon zuwa cikin ɗakinta,
"Wai waye wannan matar?
Mikewa tayi saman gado " Wash Allah,wannan da kike gani ita ce Babban Suraka ta wannan gidan,matar Abba Al-Mustapha,Ajiya Rahama,
Kin ganta nan halin su daya da Goggon yara,idan ta saka ma mai aiki ido to ko bata so da kanta zata gudu ta bar gidan ba dan ta so ba,
Matar ba ta da sauƙi ko kaɗan,yanzun bari kiga,ba dai ta ɗauki fuskarki ba,to kin shiga uku domin ta dinga aikawa a kiraki kenan,"
Katseta tayi"in dai har zan shiga uku ta sanadin ta to fa sai dai mushiga uku ni da ita,dan in ban huta ba ita ma ba zata huta ba"
"To ni dai na faɗa maki gara kiyi a hankali"
Dafa Kafadar ta tayi tana mikewa "kowa dai ya bi a hankali domin har yanzun Biba nake"
Da yamma ta kammala girkin dare kenen sai ga kira daga Momy Rahama wai tana buƙatar Biba,
Dama wanka take shirin shiga sai ga Amira ta zo ta fada mata,
Tare da me aikin da aka aika ta zo ta bi,har cikin babban falon su inda me aikin tace ki jira a nan,
Kare ma falon kallo take yi tana tabe baki,ba laifi an zuba karya,
Ganin ta gaji ne yasa ta ni me guri kan kushin ta zauna tare da daura kafa daya kan ɗaya tana kallon TV dake kunne ana hasko Namomin daji,
Salatin data ji daga bayan tane ya ta juya,
Karasowa gabanta Hajiya Rahama tayi tana tafa hannu "yanzun ashe da gaske ne abinda Goggon yara ta fada a kan ki"
Mikewa tayi tsaye tana ɗan kyara rigar ta,
Ibrahim ne ya shigo yana tambayar "Mom lafiya?
" Ni da fitsararriyar yarinyar nan ne"
Kallon ta yayi "Biba me ya faru"
"Ba wannan ba,maza ɗauko abin goge kushin ki koge min inda kika zauna,A'a daka ta,bana son da injin,dauki Soso ki saka ruwa ki goge,yanzun kafin magriba"
"Mom ta yaya zata iya goge kushin da hannu,pls mana ba zama kawai tayi ba"
Jan hannun shi tayi"bana son ka saka baki akan wannan maganar mu je "ta faɗa tana jan hannun shi suka bar wurin.
Ajiyar zuciya ta sauke tana fitowa daga cikin falon domin ganin in da zata samu soso da Bokiti,
Ta bayan shiyan ta samu yan aikin shiyan su uku duk sun yi tsurotsuru," Kai ina zan samu Soso da bokiti "
"Bari a dauko maki" Dayae ta faɗa,
Haɗa mata ruwan da