Showing 84001 words to 87000 words out of 159134 words
Chapter 29 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
ta hanyar tacewa"wani irin magana ne haka kike faɗi Amira?koma menene Biba tayi yanzun ba lokacin maida magana da maida tunani baya ba ne tunda har tana iya bakin kokarin ta wurin ganin Yayan ki ya dawo,Lauyoyi nawa ƙwararru aka samu kuma aka roka dan kawai su tsaya masa amma suka kasa,sai ita da take mace ta sadaukar da komai nata domin ta taimaka masa shine har kike da bakin fadin haka?bana son ki zamo mai son zuciya,idan har ba zaki yaba mata ba ki bita da addu'a kar na kuma jin bakin ki a wannan maganar gara ki yi shiru "
Dukar da kai tayi"ki yi hakuri Ammi zan kiyaye"
"Kwana biyu ma ba'a samun number ita Biba dan na kira naji yanda take amma ban same taba na tambaye su Abbu sunce badi san masaukin data koma ba suma kwana biyu kenan rabonsu da ita" Cewar Nurudeen.
"Ka kara kira yanzun ko za'a dace" Cewar Kaka,
"Bari na kira " Ammi ta faɗa tana ɗaukar wayar ta,
Cikin sa'a kuwa sai gashi ringin biyu aka ɗauka dan Video call ne,
"Ammi ina wuni?
Bata ma iya amsa mata ba sai kallon ta da take cikin yanayin tashin hankali" Me ya same ki Biba haka a goshi?
Dan murmushi tayi ganin yanda duk hankalin ta ya tashi "ba komai Ammi kawai dai na ɗan samu Accident ne ƙarami"
"Wannan ai ba karamin bane,kalli yanda dun fuskar ki yasha Plaster"
Shafa goshin ta tayi "babu komai ai naji sauki"
Kaka ce ta karɓe wayar"ke bani in ganta,"
Sake mata wayar Ammi tayi,ta san dole akwai wani abu a kasa,zata kira ta suyi magana amma ba anan ba,dole tana buƙatar kaɗaicewa,ba zata so wani abu ya samu yarinyar ba saboda ita ma din tamkar amana take a wurin ta,
"Ke Habiba me ya faru dake haka?
Sai da tayi dariya" Kaka hatsarin mota na samu amma da sauƙi "
"Garin ya haka ta faru,hala dai kin bari ana ta sharara gudu dake ne?
" A'a kaka kawai dai tsautsayi ne Allah ya kawo,kuma ma abin da sauƙi tunda targade kawai na samu a hannu sai wannan kujewar na fuska,shima zai warke cikin kwana biyu "
"To shi kenan Allah dai ya kiyaye ki ya kuma kare ki dan Allah ki dinga kula"
"To Kaka na godewa sai anjima"
"Yauwa Allah maku Albarka"
Da Amin ta amsa tana kashe wayar.
Mikama Ammi wayar ta tayi"yarinya abin tausayi "
"Kaka ina da magana "
Duk juyowa sukayi kanta, sai dai ita bata damu da suba domin abinda ta ƙudurta sai tayi,
"Maijiddarh ta samu mijin aure"
"Me kike nufi Hajiya Saude?
" Goggon yara abinda kika ji shi nake nufi domin ba zan bar yata tayi ta zama har ta tsofe min a gida ba bayan ta isa aure,tunda Allah ya riga ya nuna mana halin wancan"
"Amma ai kamata yayi ki bari koma menene sai ayi bayan fitowar Sujar"
"Allah ya kiyaye waye yasan sanda zai fito haka kawai,wallahi ba zan jira ba tunda har na samu ta amince tana son shi"
"Kaka ya kamata ki yi mata magana ke ko zata saurare ki" Cewar Goggon yara,
"Me kuwa zan ce mata tunda ta riga ta yanke hukunci,kinsan idan zuciya ta bushe Addu'a ce kawai zata iya sanyaya shi har ta mai dashi mai taushi"
"To yanzun ma da kike maganar Auren waye zai Daura mata aure bayan Ubannin ta basu nan"
"Ai Mustapha na nan shima Ubanta ne dan haka yana da damar da zai Daura mata aure"
Kaka ce ta katse su dan su Ammi ko baki basu saka masu ba balle ta fassara su wani iri,ita da Goggon yara ne kawai take yi,
"Waye mijin da zata aura?
Murmushin shakiyanci tayi" Yauwa Kaka tambayar daya kamata tun farko sumin kenan amma sun tsaya suna Challenging di na"
"Ki faɗa min abinda na tambaye ki"
"Sunan shi Yusuf,shi din shahararren ɗan kasuwa ne,yawancin kasuwancin shi a kasar waje yake yi"
"Iyayen shi fa?
" Mutanin Niger state ne"
"Menene Nasabar shi dana iyayen shi?
" Wai ni kaka duk wannan tambayoyin na menene "
"Idan ba kida duka amsar waɗannan tambayoyin to ki nimosu kafin ki zo min da batun aure domin ko ke kafin ki shigo cikin zuri'a ta sai da na tabbatar Nasan ko su waye iyayen ki da kakanin ki,dan haka bana son wata magana tashi ki fitar min a falo"
Cikin jin haushi ta tashi ta bar falon yayin da ta bar kowa da saƙar zuci.
____________*LEGOS*
Suna kammala waya da su Ammi hawa kan gado kayi ta kwanta dan tana buƙatar hutu,
Ranar yini tayi tana barci sallah da cin abinci kadai ke tayar da ita,dan ita kanta ta san idan har bata huta ba tana iya rasa hankalin ta,
*Washegari da safe*
Karfe takwas yayi mata ne a Gidan yarin domin daganan so take ta koma Hotel ɗin nan akwai binciken da zata yi a karo na karshe,
Kamar ko wani lokaci yauma haka ne yana zaune yana jiran shigowarta,
Sai da ta mai sallamah sannan ta zauna, jan kujera tayi ta zauna sannan ta buɗe jakka ta ciro takardar ta tura mashi a gaban shi "gashi ka saka hannu"
Ja yayi gaban shi ya saka hannu"idan har na fita me kike buƙata?
Shiru tayi tana kallon shi na wani lokaci,wato ma tambayar da zai mata kenan,nan take wani tunani ya zo mata,ai kuwa zata yi maganin shi,kare ma fuskar shi kallon take yi kafin ta tsayar da idanun ta akan lips din shi"kome nake bukata zaka Bani?
"In dai bai tsaba ma shari'a ba"
Murmushi ta sake tana ture jakkan ta gefe ta mike tsaye,
A hankali take takowa har ta iso in da yake zaune,
Jan kujeran da yake zaune tayi baya sannan ta zauna a saman cinyar shi ba tare da fargaban komai ba a zahiri,
Kyara zamanta tayi da kyau a saman cinyan shi,"Kace kome nake buƙata ?
Ƙoƙarin kauda kai yake yi tasa ɗan yatsan hannun ta tadawo da fuskar shi ta yanda suke fuskanta juna,
Tun daga saman goshinshi ta shiga zagayewa da ɗan yatsar hannun ta har ta gangaro izuwa cikakken giran shi,idanun shi masu matukar jan hankali,
Lumshe ido yayi yana jin yanda take yawo da yatsanta saman fuskar shi,
Gangarowa ta kuma yi saman lip dinshi inda nan ma sai da ta ɓata sakanni tana zagayeshi kafin yaji saukar nata bakin saman nashi,
Kara lumshe nashi idanun yayi,
Bata damu da yanayin da zai shiga ba ko yake ciki,ita dai abinda tayi niyar yi mai shi take kokarin aikatawa,
Dan haka kama Lip dinshi na sama tayi ta shiga tsotsa a hankali tana mai kokarin kamo harshen shi,
Bai hana ta ba sai ma dama da ya bata,
Sai da ta gamsu dan kanta sannan ta sake masa baki wanda saura kaɗan ta ciye masa shi,
Haɗe goshin su wuri ɗaya tayi ta yanda suke iya shakar numfashin juna,
Dago kai tayi ta tsura ma fuskar shi ido na wasu sakanni,duk da idanun shi a lumshe suke baka isa ka fassara a wani irin yanayi yake ciki ba,
Ta dai san duk wannan Kiss din data mai ko sau daya bai yi respond ba,bai kuma hana ta ba,
Kamar wacce aka tsikara haka ta mike ta dauki jakkan ta ba tare data ƙara kallon inda yake ba ta bar wurin.......
*Jiddarh ce* 🦚
*Yanzun aka fara*
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*52*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Tana fita daga wurin mota ta shiga ta zauna a gidan baya"muje "
"To Hajiya" Ya fada yana tayarda motar,
Ya riga ya san inda zasu je dan ta riga ta sanar dashi tun kafin su fito dan haka kai tsaye Hotel din suka nufa wanda yake da tazara sosai da in da suka baro,karin abin takaici shine yawan Goslow da hanyar,
A tafiyar da zaka yi mintuna talatin sai ka bata kusan awanni biyu zuwa uku,
Abinda ya bata haushi ya kuma ɓata mata rai shine bayan irin wannan dogon tafiyar da suka sha sai gashi masu gadin bakin Get din shiga wurin sun hana su shiga,
Ba irin rokon da bata masu ba har ta I.D card dinta ta nuna masu amma suka ki yarda wai umurni ne na Ogan su,
Ta kira Number wancan Inyamurin shi kuma bata shiga wanda daga dukkan alamu blocking din ta yayi,
Ko kusa da bakin Get din sun hana su tsayawa,dole dan nisa da Hotel din suka samu wuri suka yi parkin mota,
Fitowa tayi daga cikin motar ta jingina da jikin motar ta dafe kai,
Tunani take ta ina zata fara,komai ƙoƙari yake ya kwace mata,gashi gobe ne za'a koma kotu sai dai har yanzun komai baya iya samu ba,
Ta tabbatar ko yaya ne idan har bata samu wani abun da zata kai ba suna iya yanke mashi hukuncin da suka ga dama wanda bata fatan haka,
Ji yayi daga gefen ta ance "Hi"
Dagowa tayi ta kalli mutumin shima zubin Yarbawa gare shi,
Mai da mai da "Hi" Din shi tayi kafin tace"me kake buƙata "dan a yanda ya tsaya mata daga dukkan alamu akwai magana a bakin shi,
Kalle_kallen gefen shi yake" Zamu iya shiga motar ki muyi magana,domin ba na son a gammu tare ni ma'aikacin wannan Hotel din ne "ya faɗa yana nuna mata I.D din shi,
Cikin sauri ta buɗe mashi gidan baya" Shiga "
Sannan ta zagaya ta shiga"ya kamata mu ɗanyi nisa da nan kaɗan "
Jin abinda tace ne yasa Direban dake jiran umurninta ya tayar da motar ya bar layin dasu.
Yana parka motar a wani ɗan hanya ya fita a motar ya bar masu wuri,
"Ma,Suna na Josif, ni ma'aikaci ne a wannan Hotel ɗin,tun wannan ranar da kika fara zuwa wurin Manager mu na ganki,naso na maki magana amma ban samu dama ba kuma ina jin tsoron a ganni dake dan amma gargaɗi sosai akan ki,sai dai kuma yau ma na ga an hana ki shiga shi yasa nace bari nayi amfani da wannan damar domin ba zan taba manta taimakon da wanda kike karewa yayi min ba,a lokacin da kowa ya juya min baya na rasa yanda zan yi,shine ya taimake ni ba tare daya duba yare na ko Addini na ba wanda gashi har ta sanadin haka na buɗe ma Mama na shago ta na sayar da kaya a ƙofar gida tana samun kuɗin abinci ba tare data jira ni ba ko taci bashi,"
Ita dai sauraren shi take yi tana kuma mamakin wani taimako ne ya mai haka,
"Ranar da abin ya faru ina kicin ina aiki sai gashi Manager ya kira akai mai abinci shida baƙi a Ofishin shi,
Ko da na shiga kai abincin suna ta cikin dakin hutawar shi dake cikin Ofishin,har zan juya naji daya daga cikin su yana daɗin Tunda mun samu ya fita daga dakin ya kamata ka saka a hanzarta a shigar da Gawar yarinyar dakin shi ta yanda komai zai yi dai daidai,
Jin wannan maganar ne yasa da sauri na ciro wayata na shiga wurin kwasar Video da daukar murya na labe ina ta kwasar su har suka kammala tsara shirin su,
Jin za'a fito ne yasa da sauri na fita,
Sai dai ban koma wurin aiki na ba na labe a ta bayan kofar baya da naji ta nan za'a shigo da gawar,
Sai da na tabbatar na kwashe komai sannan na wuce,sai dai a lokacin ban cewa ɗakin shi aka saka gawar ba,kuma ni ma dalilin da yasa na ɗauka saboda ina son idan na koma gida na kira Manager na masa barazana da wannan Video na samu kudin bikin binne kanwata data mutu,
Ana cikin haka sai ga kiran Mom din mu tana faɗi min irin munanan kalaman mutane ƙauyen mu a kanmu,wanda sai da nayi kuka,
A wannan lokacin ne Allah ya haɗa mu da shi yaji kukan da nake yi shine ya tambaye ni akan meke damuna,dana faɗa mashi nan take ya amsa account din na ya turamin dubu dari da hamsin,
Shi yasa da na ga abinda ya faru dashi ban tura ma Manager Video ba na ajiye domin na san zai taimake shi wurin fitowa"ya faɗa yana mika mata Memory,
Tsabar farin ciki ji tayi kamar ta rungume mutumin sai godiya take tayi mai kafin ya fita yayi wucewar shi,
Direban ne ya shigo motar"ina zamu Hajiya?
"Gida" Ta bashi amsa fuskarta dauke da murmushi.
Ranar haka tayi ni cikin tsananin farin ciki domin ta san Allah ne ya kawo mata sauƙi har in da take,jira kawai take gode tayi a shiga kotu.
____________*Washegari*
Ƙarfe tara na safe tayi mata ne a cikin kotu dan ma tun ƙarfe bakwai suka fito,to amma saboda yanayi na cikowar abin hawa shi yasa basu iso da wuri ba,
Ko da ta isa a haraban babban Kotun ta samu su Pa da Abbu sai Dady,
Cikin girmamawa ta gaishe su,suka amsa,
Dady ne yace"ƴa ta da fatan an samu wani abun,dan gaba ɗaya hankalin mu a tashe yake yau bamusan yanda shari'ar zata kasance ba"
Dan fuskar damuwa ita ma ta nuna"Dady sai dai ku taya mu da addu'a kawai,sai dai abinda Allah tayi"
"Haka ne Addu'a kuwa munanan muna taya ku dashi kullun" Cewar Abbu,
Hango shi zaune tayi a saman wani ɓENCI hannun shi tsarkafe da Ankwa sai masu tsaron shi dake tsaye suna hira suma dan wurin cike yake da jami'an tsaro,
"La gama Suraj din can"
"Ai ba zasu barki ki karasa in da yake ba,dan mun yi kokarin haka ko gaisawa muyi dashi amma sun hana" Cewar Pa,
"Bari naje na gwada ai ni lauyar shi ce"
Bata jira amsar suba ta nufe in da suke,
Suna kallon yanda take Challenging da Masu tsaron shi daga karshe suka ga ta karasa in da yake zaune yana kallon su ta zauna fuskarta dauke da murmushi,
"Barka da Safiya Malam Suraj"
Kim amsa mata yayi,
Bata fuska tayi cikin shagwaba tace"ba zaka amsa ba?
"Ki fara yin sallamah tukun na"
"Ohh na manta tare da Ustazu nake,Assalamu alaika"
Amsawa yayi yana kauda kai daga kallon ta,
"You look Happy"
Dariya ta yi wanda ke ƙara baiyana farin cikin ta"sosai ma domin yau zaka fito"
"Kina da tabbaci a kan haka kenan?
" Hundred and ten percent "
Ganin bai ce komai ba ne yasa tace"to ka juyo mana,ni na fison idan ina magana ana kallo na"
Har yanzun din ma kin kallon nata yayi,
Ji yayi ta shiga jan hannun shi "ni dai ka juyo,ni dai sai ka kalle ni"
Ganin tana shirin ja mai magana ne yasa ya juyo yana daura idanun shi a kanta,
Murmushi ta saki"yauwa ko kaifa,to mu koma maganar mu na jiya tunda ina saka ran komai ya kare anan"
Ganin kamar bai gane me take nufi bane yasa tace"jiya baka tambaye ni me nake bukatar ba"
Dantse Lip dinshi yayi da hokora,wanda ganin abinda yayi ne yasa ta shiga kwasan dariya tana nunashi,shi kuma sai bata fuska yake yi,sai da tayi mai isar ta sannan ta dafa shi"kaga relax,i am not ganna kiss you"
Har yanzun bai cire haƙoran ba"da gaske nake yi,kaga bari ma na fada maka abinda nake so"
Juyowa yayi yana sake Lip dinshi a hankali ya mai da hankalin shi kanta,
Wannan karon a kwai natsuwa a tare da ita wanda hakan ke nuna muhimmancin abinda take son faɗa,
*Idan har naci nasara yau ɗin nan zaka rubuta min takardar saki* ?Ta faɗa tana dagowa suna kallon juya cikin idanu..
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*53*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Kamar ba zai ce komai ba dan har ta fara cire rai ga amsar shi,
Sai ta ji yace"me yasa kika zaɓi wannan?
Ajiyar zuciya mai ɗan ƙarfi ta sake yayin da nan take wani irin damuwa mai tattare da kunci ya lulluɓe kyakkyawar fuskarta mai dauke da dariya "Ada ina son nayi wani irin tafiya ne da babu waiwaye a cikin ta,sai dai kuma duk nisan da nayi sai gashi na tsince kai na a baya,ina nufin a mafarin tafiyar wanda hakan ke nuna dole sai dai na sake sabuwar farawa,
Ban damu ba ada,amma kuma yanzun na rasa kwarin gwiwa tun mutuwar Ummita,
Na tabbatar a kwai abinda ke jana baya,shi yasa na yanke hukun komawa baya na fuskaci rayuwata dana baro,wacce nake jin tsoro,"dago kai tayi ta kalle shi "a hanya muka haɗu da kai ina kan wannan tafiyar,shi yasa nake son na rabu da kai a wannan hanyar,bana son na tafi da nauyin ka ba tare daka sauke min shi ba,zan koma gida,zan koma wurin iyayena"
Dukar da kai tayi tana share hawayen daya ɗigo daga idanun ta"ka yi hakuri komai na wancan auren Karya ne"
Ya buɗe baki da shirin yin magana kenan sai ga sako daga masinjan kotu wai su shigo lokacin shari'ar su yayi,
Mai da abinda ke zuciyar shi yayi har zuwa sanda zasu fito,
Ita ma mikewa tayi"idan mun fito ma karasa magana,dan bazan koma Kano tare da ku ba"
Bai bata amsa ba suka fara yin gaba da sojojin kafin ta bi su a baya,
Wannan karon ma kamar wancan lokacin ne dan sai da akayi gaisuwa da kuma gabatarwa,
Lauyan wanda suka shigar da kara