Showing 42001 words to 45000 words out of 159134 words
Chapter 15 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
daya ya kara daga inda yake ya kara matsowa daf da ita "canja wani dai"
"Da gaske kudi nake nima,"
"Baki yi kama da barauniyar kudi ba Biba,sai dai wani abun daban,faɗa min me wannan?
Mamaki ne da tsoro ya kara shigarta dama yasan sunan ta ne,
" Idan da ace kudi zaki ɗauka da tun shigowar ki wancan durowar daki buɗe,ko wancan karon da kika shigo ai baki dauki ko sisi ba,kuma kinga kuɗin,dan haka karki ƙara ce min kuɗi "
Hawayen dake makale acikin ramin idonta ne ya sauko, yau ta kawo kanta ajalinta,
Cikin dakewa tace"kud......
Sai dai duk yanda taso ta karasa kasawa tayi sakamakom wani irin shaka da ya kai ma makogoron ta,
Idanun ta nan take suka yo waje,yayinda da numfashin ta taji yana ƙoƙarin tsayawa,
"Kafin ki tsaya a gaba na ki tabbatar da kwarin ƙwarin gwiwar ki" Ya karasa faɗa yana tunkuɗe ta,sai da ta bugu da jikin kushin,
Tari take yi sosai tana shafa wuyan ta,
Hanyar kofa ya nuna mata"ya zamo karo na karshe "
Cikin tsananin rudewa ta mike ko takan zanin jikinta da ya kwance ba tayi ba sai ma rike shi da tayi a hannu ta fita da gudu,
Tsaye suke ita da Dady da Ibrahim wandanda suke taka mata tana ɗan motsa kafa,dan shi Abbu yana Masallaci shi kewa'azi,
Kallon juna suka yi cikin tsananin mamaki,domin kuwa a idanun su ta fito daga cikin dakin da gudu da kuma zani riƙe a hannunta,tazo ta giftasu,tabbas wannan kamshin turaren mutum ɗaya ne,duk gidan shi kaɗai ne me irin wannan kamshin,
Riƙe mai hannu tayi"me nake shirin gani?
Duk shiru suka yi kafin Ibrahim yayi saurin faɗin "idan da ace ni ne na faɗa da cewa za ku yi sharri nake mashi,to yanzun dai gashi kun gani da idanun ku,har balle Kaka da anyi magana ki ce Surajo babu ruwan shi,to yanzun dai kinga misali,wama yasan me yake aikatawa a garuruwan da yake cewa yana zuwa wa'azi"
Dafe kanta tayi tana kiran sunan Allah,
Dady ne ya dakatar dashi"to ya isa haka,sauran kuma naji wannan maganar a bakin wani,Kaka ki kwantar da hankalin ki insha Allah zan bincika lamarin naga meke faruwa "
"Amadu" Ta kira sunan Dady,
"Na'am Mama"
"Wata yarinya ce wannan?
Da sauri yace" Ai Biba ce"
Hararanshi Dady yayi,
Maimata sunan take"Habiba"
"Ita ce,amma Mama ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zan bincike komai,muje mu karasa mutsa ƙafar"
Girgiza kai tayi"A'a mayar dani gida"
Dole mayar da ita shiyan ta sukayi,domin kamar hankalin ta a tashe yake.
__BIBA.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*28*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Tana shiga daki kullewa tayi da key ta fada kan gado tana sauke numfashi,tare da shafa wuyan ta,
Goran ruwan dake gefe ta buɗe ta kafa kai sai da ta shanye sannan ta ajiye,
Shafa wuyanta tayi tana faɗin "mugu"tare da ciro emvelop ɗin dake ajjihun rigar ta,ita sam shakan da ya mata bata damu ba in dai har zata samu nasaran ɗauko abin harinta,
Buɗewa tayi ta shiga warware takardar,
Tsurama takardar idanu tayi,*Hadarin dake sararin samaniya yayi baƙi kirin,kuma daf yake da saukar da bakin ruwa mai mugun dafi,da fatan za'a shirya ma ƙwaryar taran shi*.
Ta karanta wannan wasikar yafi sau ishirin amma ta kasa fahimtar koda kalma daya me yake nufi,tayi tunani iya tunani amma ta kasa fahimtar komai,
Nannaɗe takardar tayi ta maida sannan ta buɗe jakka kayanta ta saka aciki,
Komawa tayi kan gado ta kwanta tana lumshe,shakar numfashi tayi tana busarwa,yayin da take jin yanda gabaɗaya jikinta ke tashin kamshim turaren shi,duk da yana da kyau na jan hankali amma sam baya burge ta,saboda bai da tausayi a nata fahimtar,sai dai kuma duk yanda zai yi da ita sai dai yayi,domin kuwa sai ta koma,tana buƙatar komawa,dole ne ta cika aikinta a cikin kwanakin nan ta je ta sami Ummita,
Mikewa tayi sam ta cire wannan rigar na jikinta,ta sauya wani sannan ta kwanta.
Washegari misalin ƙarfe tara na safe sai ga shi kaka ta aiko a kira ta,
Koda taje a zaune ta same ta a falo tana tsinkar Zogale,
Zama tayi kusa da ita "Kaka me za ki yi da zogale?
Cikin sakin fuska kamar ko yaushe tace" Yau dambu nake jin ci"
"Wow kaka ai kuwa ina son danbu,har balle idan aka saka gyaɗa,a lokacin ina gida Mama tana saka wa ana min"
Murmushi ta sake "me sunan Maman naki"
"Fatima,sunan ta Fatima" Ta faɗa muryar ta dauke da murmurewa,
"Kin ji kewar ta sosai kenan? Ta tambaya,
" Tamkar rayuwa,wata rana ji nake kamar na buɗe idanu na ganni a gabanta"
"Idan har kinji kewar su har haka me zai haka ki dauki hutun sati ɗaya sai kije ki gansu"
"Har abada bazan taba zuwa ba"
Cikin mamaki ta dago tana kallon ta"me kike nufi "
Cikin sauri ta daidaita natsuwarta domin ada ta manta dawa take magana har take shirin sakin layi,da sauri tace"ohh ina nufin ban daɗe da nage gida ba,kinga ko sati ba'a yi ba,bai kamata na koma ba yanzun"
Jinjina kai tayi"amma a katsina a wace unguwar kike?
Shiru tayi domin tama manta sunan unguwar da A'i ta faɗa mata,dan bata taba zuwa garin ba,juya idanu ta fara tana kokarin tuna sunan wurin,
Wayar kaka ne da yayi kara ya dakatar dasu,
Ganin ta dauki wayar ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tana dafe kirji,
Bata wani jima ba ta sauke wayar ta juyo "ina jinki"
"Emm,Umm,yauwa kaka dan Allah ki taimaka ki koya min dambu" Ta faɗa a kokarin ta na kawar da maganar,sai dai ta manta wanda ya rigaka kwana ya rigaka tashi,
Murmushi kawai Kaka tayi"kina da number A'i?
"Eh ina da shi"
Mika mata wayar ta tayi "ga shi ki saka min sai ki adana min shi a yawa"
Amsa tayi ta saka mata,daga nan suka cigaba da hira hankali kwance,sai zuwa goma da rabi ta koma shiyan su.
Bai samu ya shigo gaida kaka da safe ba,sai bayan Sallar Azahar wanda bama a gida yayi shi ba,
Suna gaisawa tace"dama ina son magana da kai "
Kyara zaman shi yayi saman darduman ta,
"Sai dai kafin nan kiramin Amadu a waya idan yana gida bai fita ba yazo"
Ya gane wa take nufi,dan haka kiran wayar dady yayi,ai kuwa ya shaida masa ga shi nan zuwa,
Bayan wasu yan mintuna sai ga shi ya iso,zaunawa yayi shima yana ƙara gaida kaka dukda basu daɗe da rabuwa ba,
Kallon Dady tayi"ina son ka zama shaidar komai shi yasa na saka a kira ka"
Jinjina kai yayi"in sha Allah ina tare da ke Kaka"
Kiran sunan shi tayi"Surajo "
Amsawa yayi da "Na'am"
"Shin ka tashi aure ne? Ko ince kana buƙatar aure ne?
Kallon mamaki ya shiga yi mata" Kamar ya? Ya tambaya cikin rashin fahimtar in da ya dosa,
"Tambayar dana maka shi nake nufi"
"Kai muke saurara ka bamu amsa kawai" Cewar Dady,
Numfashi yaja ya sauke yana ƙoƙarin daidaita kanta"A'a kaka,bana bukatar aure"
"Me yasa" Ta kuma tambayar sa,
"Saboda ban shirya ma hakan ba"
"Ko da baka shirya ma hakan ba me zai hana ka fara ajiye daya a kusa da kai,na tabbatar da yanzun kana bukatar haka"
"Ta yaya nake buƙatar hakan?sam aure baya gabana yanzun"
"Na fahimta,amma me zai hana ka yarda cikin satin nan a aura maka yar uwar ka Maijiddarh"cewar kaka,
Wannan karon baki buɗe yake kallon su," What? Why? Sai kuma yayi shiru tuna waye Dady a wurin shi da kuma wurin Maijiddarh,domin mahaifinta ne,duk cin fuskar shi ba zai iya yi a gaban shi,amma me dalilin kaka na dauko wannan zancen,
"Me ka ga" Dady ya kuma tambaya,
Shiru yayi gaba ɗaya ma ya rasa me zai ce,
"Kai muke saurare"
"Ayi abinda ya kamata" Ya faɗa kasan makoshi,
"Ina iya tafiya?
Cikin sakin fuska gaba ɗaya suka amsa mai da "eh"tunda sun samu amsar da suke so,
Ganin ya fita ne yasa Kaka sakin murmushi" Alhamdulillah tunda ya amince,yanzun abinda nake so sai a fara gudanar da shirye-shiryen tunda yau Lahadi nan da kwana biyar sai a ɗaura auren kowa ya huta"
Zuciyar shi wasai domin yasan matarsa yau sai tayi rawar daɗi "to amma Kaka wani hanzari ba gudu ba,yaya za'ayi da batun ita wannan yarinyar,kinga bai kamata ma kwata_kwata su dinga ganin juna ba"
Dan shiru tayi kamar mai nazari kafin tace"babu damuwa akan haka,domin nan da kwana biyu zan sallame ta,tunda ita Ammi din ma taji sauƙi"
"To shikenan bari naje dan a fara shirye-shiryen da wuri"
"To Allah ya maka Albarka"
Da Amin ya amsa cikin tsananin farin ciki.
Yana fita shiyansu kai tsaye ya nufa,anan yake sanar da iyalan shi kyakkyawar labari wanda sai da Maijiddarh tayi kukan farin ciki,
Kafin kace me tuni gida ya hargitse da murna,
Ammi ita ma Kaka ke nasar da ita hukunci data yanke,duk da abin bai mata daɗi ba ko kaɗan kuma ya kona ranta haka ta hakura ta ke sakin murmushi ba tare data nuna damuwarta ba,amma a ranta ta san duk inda yake yanzun baya cikin walwala,
Aunty Atika Maijiddarh ta kira tan sanar da ita abinda ke faruwa,cikin wayar ta shiga zuba ihun farin ciki,tana taya yar uwarta murna,
"Ki ce tun yau na fara kiran ki da Hajiya Maijiddarh"
Dariya tayi"kai Aunty Atika "
"Dama ina da ƙawa yar Sudan bari na kira ta na maki bukin gyaran jiki"
"Ai kuwa da kin taimake ni"
"Ke dai ki jira gamu nan zuwa"
Daga haka ta sauke wayar tana kuma niman number kawayen ta domin sanar dasu,
Itama a bakin Amira ta ji batun Bikin,duk da taji abun a ranta wani iri,amma sai kara ɗaukar ƙuduri tayi akan kafin bikin ta samu abin harinta ta bar gidan,can su kara ta abin su,
Tun daga lokacin da aka sanar da wannan bikin basu kara samun hutu ba domin yanda ake ta faman gyaran gida ana sake sabon fenti shiya_shiya,
Kuma tundaga lokacin daya shake mata wuya basu kara haɗuwa har yau da ya rage saura ƙwanaki uku bikin shi,
Kira ne na gaggawa ya shigo wayar ta daga VIP,sai dai bansa me yake faɗa mata ba amma abu ɗaya kawai naji tace shi ne "me kake nufi da yau Kaka zata sallame ni a aiki" da ganan kuma sai naji tace"yanzun? Sai kuma ta ajiye wayar,
Kallon Agogon bango tayi,wanda ya nuna ƙarfe goma na safiyar ranar Talata,
Riga da Siket ne a jikinta wanda ya zauna mata cas ajiki dan kayan ma har yaso ya dan matse ta,dan Amira ce ta bata,kuma ta dan fi Amira kiba kaɗan,
Bata iya saka ɗankwali ba dama kuma sumanta ta kama shi da ribbon ne,dan haka hijabinta mai dan jirma ta saka ta fita tare da daukar wannan katin na buɗe ƙofa ta nufi shiyan mazan gidan,
Tana zuwa ba tare da shakkun komai ba tayi ammafi da katin wurin buɗe ƙofar ta shiga kanta tsaye,ba tare data damu data kulle kofar ba,
Kallon ta yake rike da goran ruwa a hannun shi,kamar yadda itama take kare ma shi kallo,
Wannan karon babu riga a jikin shi,gaba ɗaya tana kallon farar fatan jikin shi,wanda yake a cike ko ina yake,yayin da alamun ƙarfi ya gama bayyana a jikinshi wanda Kirjinsa babu ɗigon suma ko dis,
Ganin kallon da take masa ne yasa cikin tsananin bacin rai wanda ya nunka wanda yake ciki ya nufota a hargitse,"wai ke wata irin jahila c....
Kafin ya karasa faɗa ta shire hijabin jikinta ta yar haɗe da ribbon wanda yayi sanadin saukowar sumanta har gadon bayanta,
Yana isowa daf da ita kafin ya ƙarasa faɗin abinda ke bakinsa sai ji yayi ta shige jikinshi tare da bashi kyakkyawar runguma tana haɗe bakinsu wuri ɗaya,
Duk yanda yaso ya kwace bakin shi acikin nata ta hana shi ta hayan kin bashi dama,wani irin tsotsa take ma harshen shi,yanda kasan wacce bata San dawa take tare ba.......... 🤭
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*29*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Duk yanda ya so ya kwace bakin shi a cikin nata ta hana shi ta hanyar ƙin bashi dama,
Wani irin tsotsa take ma harshen shi yanda kasan wacce bata san dawa take tare ba,
Cikin zafin nama da jarumta ya dago ta daga jikin shi,wannan ne karo na farko a rayuwar sa da mace ta samu galaba har haka a kansa,kuma wannan ne karo na farko daya taba ɗaga hannu ya Mari wata mace kamar yanda bai jira komai ba ya sauke mata lafiyayyen Mari a saman farar fatan fuskarta,
Hannu yasa ya shiga goge baki tare da jawo tulin Tissue paper ya shiga goge bakinsa dashi,sam hankalin shi baya kanta yana kan yanda zai yi ya taimaka ma kanshi ta hanyar goge najasan data saka mashi,
Daukar hijabinta tayi fuskanta fes cikin farin cikin halin da taga ya shiga"ina fatan yanzun na tabbatar maka da ƙwarin gwiwa ta? Ta faɗa tana daga mashi gira daya,
Juyawa tayi ta shiga takawa a hankali har wani rausaya take yi tsabar farin ciki,sai da takai bakin kofa sannan ta kuma juyowa"Excuses me"
Juyowa yayi da rinannun idanun shi ya sauke a kanta,wanda ita kanta sai da gabanta ya faɗi,amma tsabar tsaurin ido irin na Biba sai sakin murmushi tayi tace"you Smell nice "tana gama fadar haka ta kashe mai ido daya tare da barin ɗakin,wanda Allah ne kaɗai yasan irin juriyar da tayi wurin gudanar da wannan aikin,dan zuciyar ta tsabar zillo ji take kamar zai fito ta baki,dan haka tana fitowa dakin bata jira komai ba ta kwasa a guje sai shiyan su,tana shiga daki ta kulle kofa ta saka Key,
Jingina tayi da jikin ƙofar ta na sauke numfashi ɗan ji take makar biyo ta zai yi,zamewa tayi ta zauna a wurin tana tunanin makomar ta,idan har yau Kaka ta kore ta a gidan ya makomar aikin ta,me kuma makomar rayuwar ta.
Gabadaya he is speechless yama rasa me ya kamata yayi,ji yake makar yayi hawaye tsabar bakin ciki,
Yanzun kenan duk tattalin kanshi da yake yi ya tashi a banza kenan?domin ita ce mace ta farko data fara sumbarta shi,tuna ranar daya fara ganin ta tana shan Segret yayi,da kuma kwana uku da suka wuce,ai nan take yaji hanjin cikin shi ya murda,cikin hanzari ya shiga bayi ya fara kwara Amai tamkar zai amayar da hanjin cikin shi.
*Bayan Awa Biyu*
Gabaɗaya ta tashi hankalin Aunty Atika da ta zo gaishe ta,saboda tana shigowa ta isketa zaune tana faman rusa kuka,kuma tayi lallashin har ta gaji taki faɗa mata meke faruwa,
"Dan Allah Kaka ki faɗa min me ke faruwa,wai ko dai rasuwa aka yi?
Fyace majina tayi da tissue paper" Yanzun nan ki kira min yaran nan gaba ɗayan su"
"Wasu yara kenan kaka?
" Ki kira min Mustafa da Abbu Sufyan da Amadu,ke kowama na gidan nan ki kira min shi yanzun nan babba da yaro ina son ganin su"
"Too,Allah dai yasa ba wani abu bane" Daukar wayar ta tayi ta shiga kiran su daya bayan daya,waɗanda ma basu kusa duk cawa suka yi ga sunan zuwa.
Kafin wani lokaci ahalin gidan babba da yaro sun halarta a wannan falon,kowa hankali a tashe ganin yanda tsohuwa ta tashi hankalin ta,gashi kuma sai kuka take yi,
Da yar dai su Goggo da Hajiya Rahama suka samu tayi shiru,
Dagowa tayi ta kalle ko wanne su,sai dai bata ga mutum ɗaya ba,"Ina Sirajo? Ta tambaya tana kallon Nurudeen,
"Na kira shi yace gashi nan zuwa"
Jinjina kai tayi"Salmanu, Zainabu,Hadiza,Khadija, Bilkisu,Amira,ku tashi ku tafi wannan maganar da zan yi ba naku bane,na iyayen ku ne da yanyin ku"
Nanfa suka shiga turo baki dan wallahi ba haka suka so ba,amma ba yanda suka iya dole suka fita,
Kallon Maijiddarh tayi"Je ki kira min Habiba"
Tashi tayi tana ƙoƙarin fita sai gashi ya shigo,sanye yake da farar shadda a jikin shi,yayi matsifar kyau sai kamshi yake zubawa,sai dai ko kaɗan fuskar shi babu fara'a kuma ya ɗan faɗa kaɗan,dan fuskar shi ya nuna ramar da yayi,
Sallamah yayi sannan ya gaida iyayen nashi,ya zauna kusa da Ibrahim,
Tunda Maijiddarh ta sanar da ita kiran Kaka gabanta ke matsanancin faɗuwa,wanda ta san bai rasa nasaba da rasa aikinta da zata yi,
Sai dai ganin irin taron dake falon ne yasa tsoron karuwa,dan haka bayan ta gaida su wadanda zasu amsa suka amsa sannan ta koma gefe ta rakube.
Maida kallon ta kan shi tayi"Sirajo "ta kira sunan shi,domin tunda ya shigo ya zauna kanshi a duke yake,
Dago idanun shi yayi wanda har yanzun suke a birkice" Na'am "ya amsa da muryar shi da bata fita sosai,
" Ya muka yi da kai a game da bikin ka da Maijiddarh?
Shiru yayi yana kallon ta yana son ya fahimci inda maganar ta ya dosa"na ce na Amince"
"Me yasa tun farko da kaji kana ra'ayin mace baka faɗa amaka aure ba?
Wannan karon kam ya rasa ida zaren maganar ya dosa,dan haka shiru yayi bai ce mata komai ba,tunda bai san me take nufi ba,
Kuka ta fashe dashi" Na dauke ka tamkar jika na,harma na fifita ka akan sauran,na nuna maka soyayya har na dauki jika ta ina ƙoƙarin baka a matsayin