Showing 141001 words to 144000 words out of 159134 words
Chapter 48 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
ya zo ya dauke ta,
Jin ta a ruwan zafi ne yasa ta buɗe ido tana fashewa kuka,tasan ko bata yage ba to taji rauni,dan sai rintse ido take yi,
Jawota jikin shi yayi ya rungunme "kina so na kara ne,idan baki gamsu ba ni a shirye nake"
"Kawai ka kashe ni ka huta kawai"
Sumbatar wuyanta yayi yana kyara mata suma gefe,"idan na kasheki waye zai dauki nauyi na?
"Daga yau babu ni babu kai,karka kara nuna ka sanni,mugu mai fuska biyu"
Wannan karon kam ya kasa rike dariyar sa sai da yayi,wanda haushin haka yasa ta fasa kuka tana kokarin kwace jikinta a nashi,sai dai yaki sake ta,"ki saka a ranki yanzun zamu fara,domin babu daga ƙafa,bana son ciyon mara yaci gaba da kamamin ke Bebin,"ya faɗa yana sunsunan gefen wuyanta,domin wannan ƙanshin nata ba karamin kara tayar mai da hankali yake ba,
Da kyar ya bar ta tayi wanka sannan suka yi wankan tsarki,ya riga ta fitowa saboda yana son ya kyara in da zasu kwanta,
Wurin takawa har da hawayen bakin ciki take yi jin yanda ƙafarta ya rike yake mata zafi,tun da take biye_biyen ta bata taba haɗuwa da mutum dan duniya ba irin Suraj,yau taga sital har da wanda bata taba sani ba,juyata take ta yanda yaga dama,ita da take ikirarin yi masa Fyaɗe sai gashi cikin sauƙi ya juya da ita,gashi tafiya ma nima yake ya gagare,wallahi in dai haka ne babu shi babu ita,zuwa gobe ma komawa Nigeria zatayi domin dama ba son shi take yi ba,aiki ya kawo ta kuma komai ya zo karshe,komawa gida zata yi tana buƙatar ganin iyayen ta da yan'uwa ta,tana son taga Mama dan haka ba zata zauna dashi ba.........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*85*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Tana fitowa daga banɗaki sanye ta iske shi da jallabiya yana zaune a bakin gado,
Ganin ta yasa ya mike cikin takunnan nashi na nasuwa ya tsaya a gabanta,sai da ya gama kare mata kallo tun daga sama har kasa kamar mai minan wani abu ajikin,dan wannan kallo na shi har ya fara bata tsoro,
Turo baki tayi cikin jin haushi "to me kuma kake kallo na"
Daga gira daya yayi "me yasa ba zan kalli abu na ba"
"Babu wani abun ka anan,ni ka matsamin,wallahi da nasan kai lalatacce ne ai da ba zan taba amincewa na aure ka ba"
Dariya maganarta ta bashi,yanzun fisabilillahi tsakanin ita dashi waye lalatacce,"yanzun dan na taimaka maki shine kike fadin haka?na tabbatar da idan da ban taimaka maki ba ƙila da fyaɗe zaki min"
Zaro ido tayi tana matsawa kamar taga abin tsoro,cikin in in na ta shiga faɗin "ni me me yasa to zan maka fyaɗe,kaɗai ji tsoron Allah Suraj"
Bude baki yayi yana mata kallon zargi tare da nuna ta"kardai ki ce abinda ki kayi niyar yi min kenan?
Da sauri ta juya tana ƙoƙarin barin dakin"ni kalle ka kato da kai ta yaya zan maka hakan"
Bin bayanta ya shiga yi "faɗa min gaskiya dai" Ganin kofar a kulle ne yasa kawai ta haye saman gado tana lulluɓe kanta da bargo "ka ƙyale ni"
Dariya ya shiga yi"to tashi wallahi zan tsaya ba zan maki gardama ba har ki gama"
"Live me alone"
Yaye bargon yayi yana dagota gaba ɗaya ya zaunar,"kina da Alwallah?
"Hmmm"
"Sauko ga kayan ki na dauko maki ki saka sai mu yi sallah"
"Ni ba zan iya tsayuwa ba kafa na ciyo yake min"
"Don't be a lazy girl"
Cikin shagwabar da bata san tana yi ba har da murza kafa ta shiga faɗin "to ba kai bane ka ji min ciyo,ni ko tashi ba zan iya yi ba"
Shafa fuskar ta yake yi murmushi ya kasa daukewa a fuskar shi"to bari na duba,kin ga da an kara yi sai ki saba lokaci ɗaya"
Da sauri ta sauko kan gado,ba tare da tace masa komai ba ta saka kayan da ya ajiye mata da hijabin,
Sallah ya jasu raka'a biyu,sannan ya jero masu addu'o'i sosai,bata yi mamaki ba kasancewar ta san waye shi,
Koda suka shafa cewa yayi ta hau gado ta kwanta,dama jira take yi dan haka hijabi kawai ta cire ta haye gado,tun tana kallon shi yanda yake jero nafila har bacci ya kwashe ta.
Da Asuba ma kafin tayi sallah sai da ta kuma shiga ruwan zafi,sannan ta dauro Alwallah tayi sallah,tana idarwa kuma tayi kan gado ta lunkume domin ko kadan bacci bai ishe ta ba,
Baccin ta bai yi wani nisa ba,ta fara jin wani baƙon yanayi na ziyartar ta,ta ko'ina jikin ta karɓar sako yake yi,tun tana ɗaukar abin kamar a mafarki har lamarin yasa ta buɗe ido,
Jin kanshi a kirji ta yasa da sauri tayi ƙoƙarin ja baya,sai dai kara rungume ta yayi yana ci gaba da abinda yake yi,
Gabaɗayan su numfashi kawai suke saukewa,so take ta kwace jikinta ta hanashi sai dai ta kasa domin jikin ta ya riga yayi na'am da abinda ke faruwa,
Da kyar ta iya dago kanshi,suna fuskantar juna,cikin kasewar murya tace"pls... Ya isa haka... Bacci nake ji"
Haɗe goshin su yayi wuri ɗaya ya shiga sunbartar ta a hankali yana yi yana kallon idon ta,so yake ya tabbatar yanda yake a tsume ya tsuma ta,
Ganin da kanta ta amsa ragamar ne yasa yace"can you do it?
Kankame shi tayi ba tare da ta bashi amsa ba,dama kuma abinda yake jira kenan,
Bayan shudewar wasu mintuna,baka jin komai sai gunjin kukan ta,
Shi kuma yana tsugunne a gabanta rike da hannun ta yayin da take daure da ƙaramin towel kanta ma daure da daya,daga dukkan alamu wanka ta fito,
"Kin ga a hankali fa na yi,kuma ke kika bani dama,sai da na tambaye ki can you do it kika bani go a heard,har da bude min ƙafa... "
Cikin kuka ta kai mashi duka a kirji "mugu,ai dama da gangan kayi,sai da ka bari na fita haiyacina sannan zaka tambaye ni?sannan ko na ce a'a faɗi min tsakanin ka da Allah kyale ni zaka yi? Ta faɗa tana tsare shi da jikakkun idanun shi,
Dan shafa kai yayi" Eh to kila,"
"Eh to kila,wato ba kada tabbaci,gashi yanzun ka jawo min zama gurguwa,ni dai ba zan iya zama da kai ba"
Tashi yayi ya zauna kusa da ita"is ok ba zan kara ba,sai dai a duk lokacin da zan ganni tare dake ni kadai,kasa riƙe kai na nake yi"
Juyowa tayi ta kalle shi"to me yasa a baya baka min haka?sannan me yasa sai yanzun?ni dai nasan ba haka kake ba,ko dai kasha wani abun ne"
Mikewa tsaye yayi yana kara mikar da ita "idan da Ace na sha wani abun da ko tashi na tabbatar da bazaki iya yi ba,ko dai kina so in kwada ne?
Cikin sauri ta girgiza kai,
Jan hannun ta yayi suka fara takawa,taku biyu ta tsaya tana yarfe hannu " Ba zan iya ba"
"Zaki iya,mu koma ban daki na kara taimaka miki,kiyi iya kokarin ki wurin ganin kin ɗaure,saboda yau zaki tafi Nigeria,idan kuma har Ammi ta lura ba zata bari ki tafi yau ba"
Ai bata san sanda ta tsaya da kyau ba,wani irin gwarin gwiwa mai haɗe da farin ciki ne ya lulluɓe ta,ko ba komai yau zata rabu da azabar nan nashi,kwana daya kawai da suka yi tare ya fitine rayuwar ta,ya hanata barci,ita duk abinda zai shiga tsakanin ta da bacci bata kaunar shi,
Rashin ganin fara'a a fuskar shi bai dame ta ba,tunda dai har zata wuce shi ya sani,cikin zumu di tace"karfe nawa jirgin zai tashi?
"Takwas"
Kwalalo ido tayi ganin bakwai da kwata,cikin sauri ta juya ta koma ban dakin,zaman minti biyar tayi a ruwan zafi dan tana buƙatar shi,Allah ya gani ita ta san raɗaɗin da take ji,
Ko da ta fito baya ɗakin,dan haka dakin ta shiga,sai dai turus ta tsaya ganin akwati a tsakiyar dakin alamun an shirya kaya,
Jin motsi bayanta ne yasa ta juyo tana bin shi da kallo,hannun shi riƙe yake da wani madaidaicin tray mai dauke da kofin shayi sai plate din abinci,
Ajiyewa yayi sannan ya kalle ta "zo ki karya kar yayi sanyi,na riga na haɗa maki kaya tun dazu"
A hankali ta tako har in da yake ta zauna a gefe tana ƙoƙarin daukar chokali,
Amsa yayi a hannu ta ya diba yakai mata baki,ganin taki karɓa ta tsaya tana Kollon shi ne yasa yace"upen your mouth"
A hankali ta buɗe bakin ta ya saka mata,a haka har ta kusa kammalawa,ta kasa rike tambayar dake ranta "Do you Love me?
Shima dagowa yayi ya mata kallon sakan uku kai tsaye ya bata amsa da" No"
Dan zaro ido tayi"to Why i you feeding me?
"Do you want me to Love you? Shi ma ya jefa mata nashi tambayar,
Ɗan hararanshi tayi tana kama hannun tare da tura chokalin a bakin ta, sai da ta hadiye sannan ta bashi amsa" No need,saboda ni ma ba son ka nake yi ba,ka ga zamu rabu cikin sauki "
"Waye yace maki zamu rabu?
Cikin mamaki take kallon shi" Saboda ba mu son juna"
Mikewa yayi dauke da tray "hakan bai da amfani,ki shirya ki same ni a kasa" Ya kasara faɗa yana barin ɗakin,
Dan shiru tayi na wasu mintuna"to me yake nufi"karamin tsaki taja shi ya sani.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala shiryawa cikin doguwar riga na jallabiya sai karamin Baby hijab data Daura saman rigar sanyin ta,fuskarta yayi wani irin Fresh dashi har wani daukar ido take yi,babu digon kwalliya a fuskarta ko kwalli yau bata shafa ba sai man baki,
Ganin baya falon ne yasa ta fara shiga dakin Grandma,anan ta tarad dasu zaune har da Ammi,
Cikin girmamawa ta gaida su,
Amsawa suka yi cikin kulawa Grandma tace"zaki tafi kenan?
"Eh Grandma"
"To adai ta haƙuri da rayuwa,duk wani abinda zaki je ki tarad ina fata ki karbe sa da hannu bibbiyu,dama kuma haka Ubangiji ya kadarto,ba laifinki bane suma kuma ba laifin su bane,inda taje muma muna nan tafe idan lokacin mu yayi"
Ji tayi gabanta yayi wani irin faduwa wanda nan take taji duk wani zumudi da farin ciki da take ji ya yaye a lokaci daya,cikin sanyin murya ta ce"Grandma waye ya rasu?
Juyawa tayi ta kalli in da yake zaune,girgiza mata kai yayi,
"Ohh babu kowa kawai dai magana nake yi,kin ga tashi kuje karki makara"
"Insha Allah nan da kwanaki uku munanan tafe"
"To Ammi" Ta fada tana mikewa,
Koda suka fito yana biye da ita,yayin da kayanta an riga da an saka a bayan mota ko,
Tunda ta shiga gidan gaba ta zauna bata ƙara faɗin komai ba,tayi wani irin shiru babu abinda take saurara face bugun zuciyar ta,
Kallon ta yayi ganin ko sit belet bata saka ba,dan haka dan rankafowa yayi ya saka mata,
Har suka isa Airport bata ce masa ba sai dai binsa da take yi duk in da yayi,har ya kammala mata duk wani abinda yayi saura,
Jan hannun ta yayi suka zauna a daya daga cikin kujerun dake wurin,
Kafin yace wani abu ta riga shi "fada min waye ya mutu" Ta faɗa tana tsareshi da idanun ta,"Nasan kai tsaye haka kawai ba zaka ce na shirya na tafi gida ba koda kuwa baka sona "
Hannayen ta duka biyu ya haɗa ya riƙe cikin nashi yana murzawa a hankali yayin da yake kallon idanun nata,sai dai ya kasa furta mata komai,
Hawaye ne suka shiga saukowa daga ramin idanun ta,"Abdulrahman ne?
A hankali ya girgiza mata kai,
"Abdulmalik?
Nan ma girgiza mata kai yayi,
" Abdulmajid ne?
Nan ma girgiza kai ya kuma yi,
So take ta furta suna na gaba amma ta kasa,tsoro take ji,tsoro take ji akan abinda kunnuwanta tasu jiye mata,
Jawota kirjin shi yayi ya rungume ta gaba ɗaya,
Kuka ta fashe dashi sosai tana kara kankame shi tare da kara cusa kanta a kirjin shi,"na fasa zuwa,ba zan je ba"
Dago ta yayi yana share mata hawayen fuskarta wanda suka kasa tsayawa da hannun shi,"look at me"
Girgiza kai tayi tana kara dukar da kai,
Dago fuskar ta yayi"kalle ni Bebin"
Dago rinannun idanun ta tayi ta zuba masa,
"I Trust you,no matter what comes I no you will overcome it,na maki Alkawarin nan da kwana uku zan zo,do you want me to come?ya faɗa da alamun tambaya,
A hankali ta jinjina kai,
Mai da ita kirjin shi yayi ya rungume yana shafa bayanta" That is my Girl "
Dagota yayi ya bata light kiss a goshi kafin ya mike rike da hannun ta jin ana faɗar lokacin shiga jirgin su yayi,har iyakar in da zai iya rakata yaje sai da yaga ta shige kafin ya juya ya koma,cike da jimamin halin da zata sake shiga idan ta isa gida,
Wannan hukunci ne na Ubangiji wanda babu wanda ya isa yayi hakan bayan shi.........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*87*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Jirgin su a Abuja ya sauka,tana fitowa daga Airport ganin motoci tayi jere kusan guda uku,tayi mamakin ganin Bala sosai,
Akwatin hannun ta ya ansa cikin girmamawa yace"barka da isowa Uwar ɗaki na"
Murmushi ne ya kucce mata,domin ko ba komai ta ji daɗin ganin wanda ta sani,"Bala kana lafiya?
"Lafiya qlau nake"ya faɗa yana buɗe mata motar tsakiya,
Sai da ta daidaita zaman ta sannan ta juyo" Me kazo yi anan?
"Tarbar ki muka zo yi"
Dan waro ido tayi"tun daga Kano?
"Muhimmancin ki a wurin shugaba ya kawo hakan"
Tabe taki tayi tana mai da kanta ta jinginar,
Ganin haka yasa shima ta saki murmushi yana shiga dayar motar tare da bada umarni tafiya,
Tafiyar awa daya da rabi ne ya shigo dasu garin Minna,kallon ko'ina take yi kamar yau ta taɓa shigowa garin,hannu ta saka ta dafe kirjinta jin yanda bugun zuciyar ta ke tsananta bugawa,addu'a kawai take yi akan Allah yasa yanda ta tafi ta bar kowa lafiya a cikin gidan Allah yasa ta same su lafiya,
Jin tsayuwar mota ga ƙarar buɗe Get ne ya dawo da ita cikin hayyacinta,da sauri ta ƙara buɗe idon ta ganin in da suke,wato a harabar gidan su,mamaki take yi dama sun san gidan ne,sai dai mamakin ya tsaya ne a lokacin da taga mutane ta ko'ina a cikin gidan,sannan duk wanda zaka gani baya cikin daɗin rai,
Kamar yanda yawancin hankalin mutane dake zazzaune saman tabarmi ya dawo kan waɗannan jerin motocin haka ita ma hankalin ta yake kansu,sai da ta kasa fito,kuma bata da shirin fitowa,
Abdulrahman ne ya fito daga cikin gidan da sauri sai Aunty Hulaira dake biye dashi,kallo daya zaka masu ka shaida rashin natsuwa a tare dasu,
Ganin isowar su ne yasa Bala bude ƙofar motar da take ciki,
Lekawa Aunty Hulaira tayi tana kiran sunan ta,"Ummu Salma!
Ita din ma kallon kanwar mahaifiyar ta tayi,ganin yanda take ƙoƙarin son ɓoye hawayen da ya kasa tsayawa a idonta ne yasa ta kasa ce mata komai sai binta da kallo da take yi,
Hannun ta ruko ta na fitowa da ita,
"Ina Mama?shine tambayar da ya fito daga bakin ta,
Kallon juna sukayi,sai dai babu wanda ya bata amsa,sai ma jan hannun ta da tayi suka doshi cikin gidan,
Duk in da tabi da kallo kawai mutane ke bin ta,duk da basu san Me ya faru ba amma sun san cewar ta daɗe bata gida,a tunanin su kila tana zaune ne a kasar waje,
Kale_kale ta hau yi a falon,ganin babu wacce take nima ne yasa ta nufi dakin Mama,sai dai har bayi ta leka babu kowa,dakin Baba ma ta shiga,shima baya ciki,duk wannan nimar da take masu babu wanda da dakatar da ita kamar yanda babu wanda yace mata komai,
Cikin tashin hankali ta fito falo in da duk suke tsaye cirko cirko ta riko hannun Abdulmajid "Yaya!ina Baba da Mama?
Cikin sauri Aunty Hulaira ta rungume ta tana saka kuka" Kiyi haƙuri Salma,wanda ya fimu son ta ya karɓi abin shi,"
Ji tayi kamar mata fahince me take nufi ba,dan haka zane jikin ta daga na ta tayi"Aunty ni fa ban gane in da maganar ki ta dosa ba"
Tana ƙoƙarin yin magana Abdulrahman ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu,sannan ya kama hannun Salma"biyo ni "
Bin bayan shi tayi har suka zauna a daya daga cikin kujerun dakin,
"Mama takasance cikin jiran ki na tsayin waɗannan shekarun da suka wuce,kulun cikin kuka take rike da hoton ki tana begen sake kasancewa dake domin ta nime tafiyar ki,sai dai Allah bai yi fuskokin ku zasu sake haɗuwa ba har izuwa numfashin ta na karshe,har i zuwa lokacin kuma sunan ki ka dai take kira,
Tayi data sanin abubuwan data aikata a baya,tayi data sanin biyewa son zuciya,
Muna roƙon ki a matsayin ki na ƴar uwar mu da ki yafe ma mahaifiyar mu kawo ki wannan duniyar da tayi bata hanyar da Ubangiji ya shardanta mata ba,mu mun jima da yafe masu"
Ta kasa kuka ta kasa zubar da hawaye,jin idanun ta take suna mata raɗaɗi kamar ana zuba mata barkono,
"Ina Mama?shine tambayar data ƙara gefa masu yayin da take daura idanun ta a kanshi,
Ji yayi gaban shi ya ɗan faɗi,ganin yanda idanu ta sukayi ja yanda kasan wanda jini ke ƙoƙarin kwantawa a ciki,tsoro yake yi kar ta zo ta cutar da kanta,
"