Showing 45001 words to 48000 words out of 159134 words
Chapter 16 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
matar auren ka,ba tare dana duba laifin dana ganka kana aikatawa ba,amma shine ba zaka iya riƙe kanka har nan da kwana uku ba sai ka nuna asalin halin naka"
Tofa gabaɗaya maganar kaka ya ɗaure ma kowa kai a wannan wurin face wadanda dama suka san da shirin,
Abbu ne yace"me kike nufi da kasa riƙe kai Mama,da kuma wani hali na shi?
Cikin kuka ta nunashi da hannun ta"gashi nan ku tambaye shi me yake aikatawa a ɓoye da yar mutane"
Duk maida kallon su kanshi suka yi,suna jiran jin karin baya ni,sai dai kanshi a kasa yake domin ji yake kamar kanshi na juyawa,yau me ke shirin faruwa dashi,
Ammi da tuni ta fara hawaye tace "Suraj kai muke saurare ka faɗa mana Komai"
"Ai ba zai iya faɗa ba amma ku duba abinda ya ke aikatawa kenan" Ta fada tana watso wasu hotunan a tsakiyar falon,
Gabaɗaya hankalin duk wanda ke cikin falon tashi yayi,domin kuwa tabbas shi ne ba wani ba,nan take kaji salati ya shiga tashi ta ko ina,
Tunda ya daga kai ka kalli hotunan saudaya ya maida kai ya dukar,tabbas yanzun kam yasan meke shirin faruwa dashi,
Kukan Ammi ne ya karaɗe falon sosai yayin da cikin gunjin kuka ta nufi shi,rike hannun shi tayi ta duka a gaban shi "Suraj!dan Allah ka ce min ba kai bane wannan,kaci musu,ka ce ba kai bane" Ta fada cikin matsanancin kuka da tashin hankali,
Dady ne yace "dama ita tsintacciyar mage bata mage,Allah mun gode maka daka nuna mana wannan sirrin nashi kafin haɗa zuri'a dashi,dan haka na janye baka aure yata,ba zan iya haɗa zuri'a da kai ba"
Ammi ce ta riƙe hannun Abbu wanda yake zaune yama kasa cewa komai "dan Allah Sufyan kama ɗan Uwan ka bayani,wannan ba halin ɗan mu bane,wannan ba halin Suraj bane"
Sai dai ga mamakin ta sai zame hannun shi yayi daga cikin nata"ɗan ki dai,domin kowa yasan cewa Suraj ba ɗa na bane,ƴaƴa na biyu ne daga Shamsuddeen sai Amira,wanda ina da tabbacin Shamsuddeen ba zai taba aikata hakan ba saboda ya haɗa jini da ni,banga laifin wadanda suke cewa basu karɓar dan wani a matsayin nasu ba,saboda karya bata ma nasu tarbiya,ƙila dai ta ɓangaren ubanshi ya dauko irin wannan halin"
"Ai matsalar Auren mace mai ɗa kenan,yanzun ga irin ta nan,ka jawo shi a jiki tamkar naka,amma ji abin kunyar da yazo yake aikatawa,mun gode ma Allah da abun ya tsaya a kan masu aiki bai kai ga ya'yan mu mata ba" Cewar Goggo,
Kukan Ammi ne ke kara ƙaruwa"Kufa malamai ne,masana Addini,me yasa kuke faɗin haka,me yasa ba za a ji ta bakin shi ba"
"Ammi sai dai kawai in baki son ki yarda da abinda ke gabanki na zahiri,amma ni kai na na sha ganin shi ba sau daya ba,ba sau biyu ba"
"Amma me yasa baka taɓa sanar da ni ba Shamsuddeen,me yasa?
" Saboda koda na faɗa maki ba yarda zaki yi ba Ammi,kamar dai yanzun ma da ga shaida a gabanki amma baki son ki gasgata "
"Ai ku ne baku sani ba,amma ni ba abinda ban sani ba,ko yawon tafiye-tafiye da yake yi na karyan yana zuwa wa'azi ai tare yake zuwa da ƴan matan shi,wasu kuma a can yake samu suna hutawar su" Cewar Ibrahim,
"Haɗa jini da Bayahude mutum hatsari ne,komai daren daɗewa sai ya nuna maka halin su na Akuyanci,ni banga laifinshi ba tunda Kakar shi bayahudiya ce wa yasan abinda ta aikata lokacin yarinta,kuma shi dama ƙazanta ai jini yake bi"Hajiya Rahama ta faɗa,
Jin maganganun su yake har tsakiyar kanshi,suna mai amsa kuwa,ko wace kallama daya da zasu faɗa ji yake yana shiga cikin jikin shi ya bula zuciyar shi ya shige,zafi yake ji,raɗaɗi yake ji sosai,ji yake kamar yace su tsaya ya huta,su tsaya ya sauke numfashi daya tsayamai a kirji kafin su cigaba,sai dai ya kasa koda ɗaga kai ya kalle su,domin mutanen da yayi rayuwa dasu,ya yarda dasu,yake zaune dasu tamkar ahalin shi sune suke fadar munanan kalamar akanshi,harda wanda yake kira da dan uwa kuma yaya,Shamsuddeen,da kuma wanda ya ɗauka a matsayin Kani,Ibrahim,
Yana sauraran yanda Ammin shi ke kuka,duk kuma saboda shi.
Maijiddarh wacce tunda taji batun fasa aurenta take kuka ta matso wurin kaka,cikin kuka tace"Kaka kema kinsan ina son shi,ba zan iya rayuwa ba idan bashi,dan Allah kar ki bari a fasa wannan auren ina son shi a haka"
Jawota Aunty Atika keyi"kina da hankali kuwa,ba ki ganin abinda ke gaban ki,"ta faɗa tana nuna mata hotunan da har yanzun suke watse a tsakar falon"a haka zaki aure shi,mutum irin shi sam bai dace da zuri'ar wannan gidan ba,kuma koda kin aure shi ba fasa halin shi zai yi ba,dan haka ki dawo hankali ki"
Aunty Hajjo ce tana mikewa ta kai mata Lafiyayyen mari a fuskar ta.........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*30*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Aunty Hajjo ce tana mikewa ta kai mata lafiyayyen mari a fuskarta,
Duk mai da kallo kansu suka yi,sai dai shi uban gaiyar ko inda suke bai kalla ba,sai ma lumshe idanun shi da yayi gabaɗaya,
Nuna ta tayi da ɗan yatsa"ai wannan ita ce babbar munafukar,kuma mai laifin,ta yaya ta aikata abu irin haka sannan ta zauna ba tare da tace komai ba"
Dafe kumatunta tayi da taji yana mata raɗaɗi dan wallahi har gara marin da ya mata dazu akan wannan na Aunty Hajjo dan katon hannu gare ta,
Tattara hotunan tayi ta watso mata shi a jikinta,"tunda shi dan gidan Yahudawa yaki mana bayani ke sai ki mana bayani akan waɗannan "
Hajiya Saude ce tace"kika sani ko tursasa ta yayi?
Daukar hotunan take cikin tsananin mamaki wanda ya kasa boyuwa,kallon wanda ke hannun ta yi"wannan lokacin da muka je Asibiti ne"
Da sauri Ibrahim yace"ba dai zubar da ciki ba"
Duk da halin da take ciki hakan bai hana ta hararanshi ba"tir,tir Allah ya kiyaye duk iskanci na ban taba zubar da ciki ba"
Salati yawancin mutanen falon suka saka yayin da Kaka da Ammi suke ci gaba da kuka,
"Kenan dama kun daɗe kuna iskanci?wannan karon Shamsuddeen ne ya mata tambayar,
Dago kai tayi ta kalle shi,sannan ta maida kallon ta kanshi,idanun shi a lumshe suke,sai dai fuskar nan nashi yayi ja,
Wannan ne karo na farko da taji ya bala'in bata tausayi,domin duk maganar da suke faɗi da aibantashin da suke yi bai ce masu komai ba,bai kuma ƙarya tasu ba,Ashe shi ba Asalin jikan kaka bane,kuma ba ɗan Abbu bane,to me yasa zasu mai irin wannan fahimtar lokaci ɗaya haka,
"Ke muke saurare" Ya kara faɗa,
"Ban taɓa Iskanci da shi ba,asalima babu wani abu ɗaya taba shiga tsakani na dashi sai yau,wannan hoton da kuke gani lokacin da suka raka ni Asibiti ne shida Amira duba Mama ta da bata da lafiya"
"To ya akayi ya rungume ki a hoton"
Shiru tayi kamar mai nazari,tabbas ma nazarin take yi,domin a ranar da abin ya faru taci kwaya bata cikin hankalin ta"ba zan iya tunawa ba"
"Magana ta tabbata kenan,a kwai dai abinda ya kaimu" Nuna ɗayan hoton yayi "wannan ma kamar na yau ne?
" Eh tabbas na yau ne,sai dai ba laifin sa bane,ni ce da kaina na sumbace shi ba tare da son ranshi ba"
Duka Aunty Atika takai mata"sannu manafuka uwar Karuwai,wato kare shi zaki yi,ta yaya zaki sumbace shi ba da son ranshi ba,kalli fa harda rike mata ƙwanƙwaso"
Janye ta Hajiya Rahama tayi"rufamin Asiri kar ki haɗa kashi da ita,domin irin su ba'a faɗa dasu sai su shafa maka zufan su na tsiya "
"Abu ɗaya kawai nasan zan masa na karshe a matsayina na wanda yake amsa sunan mahaifin shi,shine aura masa wannan yarinyar a yau ta yanda zai zama ishara a gare shi"cewar Abu Sufyan
Tunda aka fara maganar nan wannan ne karo na farko daya buɗe baki yayi magana" Kayi haƙuri Abbu amma ban yarda da wannan auren ba"
Salati Goggo ta saka"kai kaji min ɗan duniya,bayan ka gama ɓata masu yarinya shine zaka ce ba zaka aure ta ba,ai kuwa baka isa ba"
"Ai dama irin su haka suke,anci moriyar ganga za'a yada koren ta"
A zabure ita ma tace"wallahi ban amince ba,ni ba zan aure shi ba,"
Buge mata baki Aunty Atika tayi"munafuka yi mana shiru"
Kallon Ammi Kaka tayi"idanun ɗan ki ya buɗe sosai yanzun,har tsoron yi masa magana nake yi,dan haka ina ga ƙila ke ki nada sauran daraja a idanun shi ki masa magana ko zai amince"
Kafin tace komai sai ji suka yi yace "na amince"
Ihu ta saka "wallahi ban amince ba,ni dai ba na son shi tafiya ta ma zan yi yanzun" Ta faɗa tana ƙoƙarin mikewa,
Aunty Hajjo ta jawota kiiiii ta cillata dakin kaka ta kulle ƙofa "tunda har kwadayin ku yaja maku to sai dai ku karasa da juna"
"So nake a ɗaura auren daganan zuwa sallar Magariba,zuwa lokacin Iyayen yarinyar sun iso an masu bayani nasan idan sun ji komai ba zasu ki yarda ba"
Ba tare da yace masu komai ba ya mike ya bar falon,kamar yanda suma basu ce mai komai ba sai bakaken maganganu da wasu a ciki ke jifan shi dasu,
Yana fitowa bai koma dakin shi ba da kyar ya samu yakai kanshi wurin Parking ya buɗe mota ya shiga,
Ganin hakan ne yasa daya daga cikin direbobin gidan yazo ya shiga yana tambayar shi ina zai kai shi,
Da kyar ya iya furta kalmar "gida"
Ya gane inda yake nufi dan haka jan motar yayi suka bar gidan,
Yayin da yake jin numfashin shi kamar zai bar gangan jikin shi.
Kuka ta fashe dashi tana zama anan bakin kofa,to me ke shirin faruwa kuma a rayuwar ta a karo na biyu,Aure! Aure fa!dama abinda VIP ke nufi kenan da yace ta je tayi kissing din shi kuma ta bar kofa a buɗe,
To waye ya shigo ya ɗauke su hoto,dama ya shirya ma hakan kenan,amma ai baya cikin tsarin aikin su,baya cikin yarjejeniyar su,
Cikin sauri ta lalubo number shi a wayar ta tashiga kiran shi,sai da ta kira sau takwas ba tare da kakkautawa ba kafin a ɗauka,
Kuka ta fashe dashi"me haka! Me haka! Wannan fa baya cikin yarjejeniyar mu,kokarin aura min shi ake yi,gaskiya a canja wani hanyar "
Daga ɗayan bangaren yace"kina da wata hanyar ne daya fi wannan,?
Shiru tayi"amma kai ai ba zaka rasa ba"
"Haka ne,shi yasa na zabar maki da wannan,domin shine hanya mafi sauki da zai kaiki ga kammala wannan aikin cikin kankanin lokaci"
"To auren fa?
" Biba me yasa kike abu kamar ba wayayyiya ba,auren ai na baki ne tunda baki son shi,da zaran kin kammala aiki da kaina zansa ya sake ki"
"Ni dai ba na son wannan hanyar,domin ka sani a rayuwata babu abunda na tsana sama da Aure,ta sanadin aure komai daya faru dani ya faru,ta sanadin wannan kalmar na gano abinda bai dace nasan dashi ba har abada,idan sai da aure zan cika wannan aikin to na ajiye,na janye"
Wani irin shegen dariya ya fashe dashi,irin wanda da ka jishi kasan irin na rashin imani ne"dama nasan irin haka na iya faruwa,shi yasa na shirya ma wannan ranar Biba,ina ga har yanzun ba kisan da wanda kike aiki ba,ai tunda kika fara aiki dole ne saikin ƙarasa,ko kina so ko baki so,bari na tuna maki,ina kika bar ƴar uwar ki Ummita,"ya fada yana ƙara sakin wani dariyar,
Gabanta ne ya faɗi "me kake nufi,ina Ummita?
" Karki damu,tana hannu na cikin ƙoshin lafiya a yanzun,amma ban dai san daga nan zuwa nan gaba ba idan kika cimin musu,kina iya rasa ta,domin a wurina hakan ba komai bane,dan haka rayuwar ƴar Uwar ki yana hannun ki,idan kin ga dama ki yi wasa dashi idan kuma kinga dama ki cece ta tahanyar kammala aikin dana saka ki"
Idan ranta yayi baki to ya baci"idan har wani abu ya samu Ummita ba zan taba barin ka,sai na binciko ko kai waye naga bayan ka "
"A'i zata zo yanzun domin mun riga mun shirya wadanda zasu tsaya a matsayin iyayen ki,idan kinga dama ki nuna abinda zai sa a zarge ki,Gara ki kwantar da hankalin ki kiyi komai cikin natsuwa domin nasan babu abinda zaki iya" Yana gama faɗar haka ya kashe wayar,
Ihu tayi na bakin ciki tana haɗa wayar da bango,nan take kuwa ya tsarwatse,
Dukawa tayi a wurin ta shiga rusa kuka ko zata ji sanyi a zuciyar ta,wannan wani irin ƙaddara ce haka,idan har ta rasa Ummita bata san Me kuma ya rage tayi ba a rayuwata ta,ina zata samu mafita,wani irin tunani ya kamata tayi,
Kuka take sosai na rashin sanin mafita.
A falo kuwa Kaka ce ta bada number A'i aka kira ta Goggo tai mata bayanin komai,ita ko harda kuka,tace masu yanzun zata sanar na mahaifinta,kuma komai yazo da sauƙi tunda yayan mahaifin Biba aman Kano yake anan kuma yake sa'ar shi,
Daganan ne taro ya watse inda mazan suka nufe masallaci dan lokacin sallah Azahar yayi,
Mata kuma kowacce ta koma shiyan su.
Ko da A'i ta iso gidan Ana daf da kiran sallah la'asar dan ta bata lokaci ne wurin koya ma wadanda suka yi haya yanda zasu yi idan sun zo nan ɗin,
Cikin mutumci suka gaisa da Kaka kafin ta nuna Mata dakin Nafisa da Biba ta koma,
Ko da ta shiga a kwance ta same ta idanunta a buɗe tana kallon ƙofa,
Ganin shigowar A'i ne yasa ta tashi da sauri tazo ta rungume ta tana fashewa da kuka "A'i dan Allah ki taimake ni! Ki taimaki rayuwa ta,ya ɗauki Ummita,idan wani abu ya same ta ba zan iya yafe ma kaina ba!
Hannu ta saka mata a baki alamun tayi shiru,zaunar da ita bakin gado tayi,sannan ta maida kofa ta kulle, wayarta ta buɗe ta cire batir sannan ta zauna" Ya saka tiraka a waya ta duk abunda muka faɗa yana iya ji"
Share mata hawaye tayi"nasan haka zai fara,kuma abinda yafi haka ma yana iya faruwa idan shi ne,"
"Me kike nufi A'i"
"Shi mutum ne mai matukar hatsari,yanada wayau sosai da basira"
"Ta yaya zan iya taimakon ƴar uwa ta,ki taimaka min"
"Ki yi hakuri Biba,ban San ta wace hanya zan taimaka maki ba,amma kuma bari na faɗa maki abunda baki sani ba,kila nan gaba hakan na iya taimakon ki"
Rike mata hannu tayi"ki faɗamin koma menene"
"Bake kadai ce kika fara aiki a wannan gidan ba,kafin ke a kwai mutum shida,acikin su babu wacce tayi nisan da kika yi suke barin aiki,sai dai da sun fito da kwana biyu ake niman su a rasa,sai bayan wasu ƴan ƙwanaki ake tsintar gawar su a wuri mabanbanta"
Zaro ido tayi cike da tsoro"me hakan ke nufi?
"Kashe su yake yi saboda suntsan komai,kuma kema ina mai tabbatar maki idan har baki kammala wannan aikin ba zai iya kashe ki,haka kuma idan har kika kammala masa aikin shima ba barin ki zai yi ba"
A tsorace tace"to me ya kamata nayi,idan na kammala a kashe ni idan ban kammala ba akashe ni,to me zan yi kenan na tsira,ba na son na mutu a hannun wani?
"Hanya daya ce kawai zaki iya bi domin ceton kanki dana ƴar Uwar ki"
"Dan Allah ki taimaka ki faɗa min A'i"
Ajiyar zuciya ta sauke "saboda ina ƙaunar ki tun ganin farko shi yasa na yanke shawarar taimaka maki,sai dai ban sani ba ko abinda zan faɗa haka ne,? Sauke numfashi ta kuma yi" Ki yarda ki aure Suraj,domin shi kadai ne wanda zai iya taimaka maki,shi kadai ne wanda yasan Asalin waye suke takun saƙa dashi,domin ni kai na bansan waye VIP ba,amma ina da tabbaci a kan shi ya sani,
Ko ta halin yaya kar ki taba dauko abinda ake buƙata,domin da zaran kin miƙa naki ya ƙare,haka kuma kar ki taɓa kin daukowa,kar ki bari ko ta halin yaya VIP ya zargi wani abu,ki ci gaba da nuna kina kan aiki,
Sannan akwai wani gagarumin matsala da zai taso ma Suraj,wanda ba lallai bane ya rayu,abu ɗaya kawai nake son na sanar dake,shine ko ta halin yaya kisan yanda zaki taimaka masa ya rayu,domin fa idan kika bari suka samu nasarar kashe shi to lallai zasu samu damar cimma manufarsu sannan kema su gama dake ko kina so ko baki so,
Dan haka daga yanzun sai ki fara tunanin ta hanyar da zaki tseratar da rayuwa uku"
Tunda uwata ta haihota duniya bata taba shiga tashin hankali da ruɗani ba irin wannan "A'i wani irin matsala ne wannan da zai taso"
"Gaskiya ba na ce ba,domin bansan me suke shiryawa ba,amma nasan koma dai menene to ba ƙarami bane,zai iya kaiwa matakin da za'a rasa rayuwa"
Ganin yanda ta shiga damuwa ne yasa ta dafa kafadar ta"ki kwantar da hankalin ki,na tabbatar idan har kika natsu,kika kuma bi komai daki_daki zaki iya cin nasara "
"A'a matakin cin nasara ta sufili 0 Zero ne,ba ni da kwarin gwiwa da jarumta"
"Idan kika tuna mahimmanci rayuwar ki data ƴar Uwar ki su zasu kasance maki kwarin gwiwa"
Ajiyar zuciya ta sauke,amma Allah ya gani gabaɗaya ƙwaƙwalwar ta ya toshe,ta yaya zata iya fuskantar wannan Ustazun ma,ta san yanzun haka duk inda yake ji yake kanar yaga bayanta,
"Ni zan wuce amma zuwa anjima zan dawo kafin a ɗaura auren"
Jinjina kai kawai tayi,dan ba zata iya ce mata komai ba,tana kallo har ta fita ta jawo mata ƙofar.....
*yanzun aka fara*
*Jiddarh 🦚ce*
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi