Showing 60001 words to 63000 words out of 159134 words
Chapter 21 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
jira su gaishe ta dan haka tayi burus dasu,
Kallon juna suka yi suna jinjina lamarin,
Tashi Zainab ta yi ta ajiye mata wani ɗan ƙaramin takarda "address din wurin da za'a walima ne na matan manyan malamai,kina daya daga cikin manyan baƙi,ƙarfe Goma za'a fara,dan haka sai ki same su a can," Tana gama faɗa suka wuce ba tare da sunce mata komai ba,
Kallon Agogon bango tayi wanda ya nuna mata ƙarfe goma saura mintuna goma sha-biyar,
Karamin tsaki taja tana mikewa tare da ɗaukar takardar,
Har zata haura sama sai kuma idonta ya sauka a kan wani ƙofa wanda tunda tazo gidan bata taba shiga ba,
Juyawa tayi kawai ta doshi dakin cike da tunanin me a ciki.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*38*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Turo ƙofar dakin tayi wanda yake da duhu,da hasken wayar ta tayi amfani ta kunna wutar dakin,
Shiru tayi kawai tana kallon ko ina yanda duk aka rufe kayan dakin da fararen kyalle,
Kalle_kalle take yi cike da tunanin ta buɗe ne ta duba ko zata samu wani abu ko kuma ta fita,dan da alama dakin ya tara kura sosai na alamun an daɗe ba'a yi amfani dashi ba,
Da kushin ta fara,buɗewa tana yi tana tari saboda kura,ganin zai takura mata ne yasa ta zame ɗan kwalinta ta daure hancinta dashi,
Duk wani abunda aka rufe sai da ta buɗe,
Dafe kwankwaso tayi tana kallon dakin kafin idon ta ya sauka a kan wani babban Enlargement mai ɗauke da hoton Ahali,
A hankali take takawa har ta isa wurin da hoton yake,sai dai saboda tsananin kura ba'a ganin fuskokin wasu,hakan yasa ta saka hannu ta share,
Akan wata tsohuwar mata mai kama da Baturiya idanun ta ya fara sauka,tana zaune yayin da wasu Maza su biyu suna zagaye da ita,sai kuma wanda take da tabbacin Suraj ne,dayar matar dake gefe kuma kamar Ammi kamar ba ita ba,tana dai ɗan kokonto,sai kuma ta kasan matar in da nan ma wani mutum ne shima kamar Bature ya rike hannun ta yana dariya,
Shiru tayi tana nazarin hoton,to su waye waɗannan,tana buƙatar sanin su,sannan ina suke yanzun,
Ɗaukar hoton tayi ta juya baya ko zata ga number gidan hoton kamar yanda sukan saka wani lokaci har ma da sunan gidan hoton,
Sai dai duk yanda ta duba bata ga komai ba,hakan yasa ta mai da ta ajiye,
Daukar na kusa da shi tayi,baki ta saka tana hure kuran,
Tari ta hau yi saboda shaka da tayi,
Ajiyewa tayi ta jawo farin kyallen da saka rufe hotunan dashi ta goge,sai dai wannan hoton Suraj dinne da wannan mutumin dake tsugunne gaban Kaka,sai dai kamar ba'a Nigeria aka dauki hoton ba,
Haka dai ta dinga cin karo da hotuna na mutanen da take kwadayin sanin su waye su,sai dai tasan a yanzun babu mai bata amsa,dan wanda take da yakini shi zai bata amsa tasan ko ƙwaya taci bata isa ta doshi in da yake ba da wannan zancen,
Duba Agogon wayar ta tayi,da sauri ta zari ido ganin ƙarfe goma sha ɗaya harda mintuna ishirin,
Maida kayan tayi ta rufe cikin sauri ta bar dakin ta koma daki ta shiga wanka,
Tayi ƙoƙarin koma dai menene sai ta nimo amsar su waye waɗannan na jikin hoton,
Tana fitowa mai kawai ta shafa sai janbaki pink data ɗan mussika kaɗan sai giran ta data gyara,
Doguwar rigar Jallabiya maron kolo ta saka sai hula shima marun kafin ta naɗe karamin ɗan kwalin ta yafa a kanta,
Agogo ta makala a hannun ta sai karamin jakka,wani katon gilashi ta saka wanda ya kusa mamaye mata rabin fuska,
Masha Allah,sai dai maƙiyi,ko shi sai dai ya kushe dan bakin ciki,domin ta fito a YAR TSANAR ZINARI,tsabar kyau,duk in da ta juya kamshi kawai ke tashi,
Kayan ya bala'in mata kyau ne dan Jallabiyar tasha duwatsu wanda ko su abin jan hankali ne,
Ta inda ake ajiye makullan mota a durowan falo ta tsaya,kallon keys din tayi,hannu tasa ta dauki wani mai kalan ja ajikin shi dan zuciyar ta ya bata kila na jan motar nan ne,
Tana fitowa wurin parkin ta danna makulli sai gashi motar tayi kara,
Murmushin ta saki sannan ta doshi motar wanda yake kalan kayanta ta shige,tana sauke ajiyar zuciya,tare da shafa sitiyarin motar,
Jin ana kwankwasa Glass din motar ne yasa ta saukar dashi ƙasa,
Cikin tsoro direba yace"Hajiya fita zaki yi"
"Eh"
"Fito sai na kai ki"
"A'a ka barshi zan je da kaina"
Ganin kamar ya shiga tunani ne yasa kafin ma ya ankara sai gani yayi ta kunna motar ta doshi Get wanda tana zuwa ya buɗe mata ta fita da mugun gudu,
Mamaki yake dama ta iya mota ne ko yaya,
A'i ta kira akan taimata kwatancen Address din da aka bata,
Da taimakon ta dana sign bord,ta isa katafaren dakin taron wanda daga gani ba na wasa bane yanda wurin ke ɗibar mutane,gabaɗaya duk mata ne a dakin domin taron nasu ne,wasu sun zo ne dan jin irin wa'azin matan manyan malamai zasu yi,yayin da dayawa a cikin su sun zo ne domin ganin wata mai sa'a ce ta samu nasarar aure tauraron su,
Ita sam bata masan cewa akwai motoci biyu dake biye da ita a baya ba sai da tayi parking tana ƙoƙarin fitowa taji an buɗe mata mota,
Kallon mutumin tayi mai sanye da bakin kaya "Malam kai kuma waye? Ta tambaye shi tana karasa fitowa,
" Mu masu tsaran lafiyar ki ne,yallabai ya turo mu domin baki kariya "
Cikin mamaki tace"wani yallabai,"dan har zuciyar ya fara karkata wani wuri,
"Yallabai Suraj"
"Suraj" Ta maimaita sunan mamakin ta na ƙaruwa,to me ya same shi zai hada ta da masu tsaro,anya kuwa shine?ta yaya akayi kuma yasan ta fito,
"Da yaushe kuke bina"ta kuma jeho ma mutamin tambaya,
" Ranki ya daɗe tunda kika fito gida"
Ɗaya daga cikin sune shima sanye da baƙaƙen kaya ya iso inda suke"ranki ya daɗe an sanar da isowar ki yanzun ke kaɗai ake jira"
To fa sabon salo,ko me yake nufi da duk wannan abun ohho,
Cikin takun kasaita ta nufi Hall din tamkar wata Sarauniya,dama ya lafiyar kura yake balle an samu nama,in dai batu ne na iya tafiya tamkar Hawainiya to salo_salo ta iya,
Tunda ta doshi Hall din yayi shiru yanda kasan ana jira aga waye zai shigo haka idanun su ke tsaye a kan kofa,
Basu kadai ba har da yan gidan su dake zaune a wurin su Aunty Hajjo da Aunty Atuwa,Maijiddarh,da sauran yaran gida mata,
Dariya Aunty Atuwa ke yi kasa_kasa tunda taji an sanar da isowar ta,
Maijiddarh ce ta zungureta "wai Aunty dariyar me kike gaka tun dazu "
"Jira nake naga ta shigo,Allah yasa dai ba katon rigar nan data saba sakawa tasa ba,ai kuwa data kunyatar da Suraj"
"Ai shi ya nima,maganin shi kenan,kina tunanin ko hawa stage ƙaramin aiki ne,kalle fa mutanin dake nan an fi dari da hamsin,ko idon wani ya isa tsorata ka,balle ita ƴar ƙauye"
"Ke dai bari muga yanda zata kaya"Aunty Atuwa ta faɗa da murmushi a fuska ta,
Amira ce kamar zata fashe da kuka ta rike hannu Zainab "ni dai zan fita,ba zan iya jure wannan abun ba"
"Ai gara ki tsaya dai muga yanda za'a kare"
"Kofa karatu bata yi ba,idan ta hau nan me zata ce,ta ina zata fara"
Kofar da malamai ke shigowa da aka buɗe ne ya kuma jan hankalin mutane,
Cikin natsuwa ta karasa gaban sauran malaman dake kujeru na musamman ta shiga mika masu hannu tana masu sallamah,yayin da matar dake tsaye da mic take sanar da cewa ga Mata muka Amarya ga Ustaz Suraj,wanda mutane suka fi sani da Young Ustaz,
Wannan shi ake kira da kallo ya koma sama,domin ko waɗanda suka santa da kyar suka shaida ta,
Zama tayi a kujerar da aka nuna mata,
Sannan aka cigaba da wa'azin,
Kamar wasa taji an kira sunan ta akan ana buƙatar tayi ma mutane nasiha aka wani abun,suka bata zaɓi,
Murmushi kawai ta saki wanda ya ƙara tafiya da zuciyar mutane,
Tashi tayi cikin takun nan nata na isa ta amsa mic din,
Sallmah ta fara ma mutane kafin ta fara jawabi akan muhimmancin suturta jiki ga mace musulma,yayin da take kawo aya da hadisai tana haɗawa dasu,ta fassara,ta gefe ɗaya kuma takan sako turanci wanda jifa_jifa take yin shi,
Hall din yanda kasan mala'ikan mutuwa ya gifta tsabar shiru,ba kajin komai sai hawa da saukar numfashin mutane,
Muryanta kadai daya karaɗe wurin abun sauraro ne,har balle kuma idan tana jawo aya da hadisai yanda kasan ba daga bakinta yake fitowa ba,
Maganganun ta sun ratsa zuciyar mutane,sun motsa ruhinsu,sun kuma girgiza wasun su,yayin da wasu kuma suka yi mutuwar zaune,
Tana kammalawa nan Hall ya cika da kabbara ta ko'ina,yayinda da malamai ke jinjina sa'a irin na Suraj da wayau irin nashi,wato sai da ya zaɓa ya darje ga kyau ga kuma ilimi,
Cewa tayi idan da me tambaya yana iya yi domin tana da uzuri zata wuce,
Amma ta bada dama tambaya uku kawai zata amsa sauran kuma sauran malamai zasu amsa masu,
Mutane uku da suka fara ɗaga hannu aka ba dama,
Ta farkon tana cikin masoyan Suraj,dan haka tambayar data fara yi shine akan abunda ke cikin zuciyar ta "Malama Habiba tambaya ta na farko anan shine su waye iyayen ki?ta yaya kika samu nasarar sace zuciyar mutum kamar Young Ustaz Suraj?ko zaki bamu shawara akan muna zamu iya cikin nasara akan wadanda muke so?
Wannan shine tambaya ta" Tana gama faɗa ta zauna,
Shiru Hall din ya kuma ɗauka kowa ya tsura mata ido yana jiran jin me zata faɗa,
Duk da tambaya na farko ya daki zuciyar ta har ya so saka ta girgiza,hakan yasa tayi saurin ƙara kame kanta,sannan ta saki murmushi "well yammata da ace tambata kika yi akan wace ni zan baki amsa,amma duk da haka zan faɗa maki,iyayena sune Suraj,abokai na sune Suraj,ƴan uwa na sune Suraj,dangi na sune Suraj,because Suraj is my husband,he is my Father,My mother,my Aunty,my every thing,that is who I am" Ta karasa faɗa cike da kwarin gwiwa,
Kafin kace me Hall ya kara rikicewa da Kabbara harma da ihu da shewa,domin ba karamin burge mutane tayi ba da wannan amsar nata,yayinda wasu da yawa ke ɗaukarta Video,kafin kace me har wannan kalaman nata sun fara zagaye akan social media,
Ganin yanda Hall din ya rikice ne yasa kawai tai ma malaman sallah ta fita abunta ita kanta farin ciki ne ya kamata,ba dan komai ba sai dan ganin ta kubuta daga wannan tambayar,ta kuma ba da amsar daya dauke hankalin mutane.
__________ya fito daga Asibiti kenan dubo Grandma ya shiga mota zai koma gida sai ga kiran Ammi daga Nigeria,dan tun ranar da suka yi faɗa ya jikata da ruwan sanyi ya bar garin da yamma zuwa Germany duba Grandma da jikinta ya kara tashi,
Daukar wayar yayi ya ƙara a kunne yana amsa sallamar ta,
Daga ɗayan bangaren tace"Suraj kaga abunda yake faruwa kuwa"
"Meke faruwa Ammi" Ya tambaya,
Yana iya juyo sautin murmushin ta "hau online yanzun zaka gani"
Dayar wayar shi ya dauko ya kunna data,sai ga saƙonni suna ta shigowa,
Buɗe wanda ta turo mashi yayi,
Tun daga farkon fara wa'azin ta har zuwa tambayar da aka mata da amsar da ta bayar ya kalla,
"Son ina tunanin wannan karon mun dace"
"Ba hakan ke nufin zamu sake jiki ba"
"Haka ne,amma na yaba da kwazon ta,nasan kuma zata iya"
"Ina fatan haka,sai dai juriyar ne kamar zai mata wahala"
"Ni ma na fahimci haka,amma dai muci gaba da saka ido mu gani"
"In sha Allah Ammi"
"Ka haɗu da shi kuwa?
" Sai daya tunda nazo"
"Kayi taka tsantsan Allah ya tsare ka,yaushe saka dawo"
"Nan da kwana biyu in sha Allah,in na kara ganin yanda jikin nata ya kasance"
"Shikenan Allah ya bata lafiya"
Da Amin ya amsa yana sauke wayar,
Shiru yayi yana dan nazarin kalaman nata,kara kunna Video din yayi yana kallo,
tsayar dashi yayi dai_dai inda take faɗin he is my every thing,
Dan guntun murmushi ya saki wanda idan bawai idanun ka na kan fuskar shi bane ba zaka taba Fahimtar yayi shi ba,kafin bakin shi kuma ya furta"this girl ba"sai kuma ya kauda kai yana maida kallon shi akan manyan gine-ginen da suke ta wucewa,can kuma ya kara furta"Stubborn"yana lumshe ido cike da tunanin abunda ya faru dazu,
Wato lokacin yana Asibiti aka kira aka sanar dashi batun zuwanta taro da aka gaiyaceta,wanda ya sanar dashi ya so ya hanata zuwa amma yace karya ce komai ya bar komai a hannun shi,duk da ya san manufar gaiyatar ta da akayi wanda ita bata sani ba,
Shi ya saka securityn shi suka mata jagora har kuma yanzun da take hanyar komawa gida yana jin komai,
Buɗe mashi kofar da baturen direba yayi ne ya tabbatar mashi da sun iso,
Hakan yasa ya buɗe idanun shi yana saukewa a makeken gidan wanda kallon shi kadai da tsaruwarshi ya isa ya kara ma mai rai imani,
Yayinda shi kuma a nashi bangaren kallon gidan da rayuwa a cikin ta yana tuna mashi da Asalin waye shi ada da kuma yanzun..
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*39*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Wanda ya tuko ta acikin motar data tafi dashi ne kaɗai ya shiga har cikin gidan yayi parking wurin ajiye motoci sannan ya fito ya buɗe mata,dan tayi_tayi su bari ta tuka motar amma suka hana,dole ta shiga baya ta zauna cikin jin haushi har suka iso gida,
Tana fita a motar cikin falon ta shige sannan ta wuce dakin ta,cire kayan jikinta tayi ta shiga banɗaki ta watsa ruwa dan sam bata jimirin zafi,in dai zata shiga rana ko yaya ne sai tayi wanka in ta dawo,
Tana cikin duba kayan da zata saka ne wani tunani ya faɗo mata,
Dan haka cikin hanzari ta kasara shirin cikin doguwar riga mara nauyi sannan ta fito,
Akwatunan da aka kawo mata wanda har yanzun suna nan bakin ƙofarta ta sauko da yaɗa wanda bata masan me a ciki ba,
Da wayar falo tayi kira akan sarkin gida ya turo mata Bala tana son ganin shi,amsa mata yayi da an gama,
Dan haka zama tayi a daya daga cikin kushin din tana bude akwatin wanda hijabaine sai kyalulluka da takalma,
Shigowa yayi ya tsugunna a gefe "ranki ya daɗe gani"
Buɗe marfin akwatin tayi gabaɗaya ta shiga juya kayan ciki tana yamutsa shi ta yanda yake iya gani komai na ciki,
Yamutse fuska tayi"kayannan duk basu min ba"kallon shi tayi"Bala matan ka nawa ne na duba naga ko a wai abinda zai matsu?
Ai kuwa nan take ya shiga washe baki yana ƙara leken kayan,ai shi wallahi in dai ta bashi wannan aure kawai zai kara,"Mata ta daya ce amma ina zaune tare da mahaifiyata,amma dai in na samu dama Hajiya zan ƙara ta biyu"
Hijabai biyu ta ciro ta ajiye a gaban shi,"gashi sai ka basu kowa dai daya "
Da sauri ya jawo su gaban shi ta rungume yana kara washe baki"na gode Uwar daki na,gaskiya Yallabai yayi dacen mace ta gari,ai daga ke babu ƙari "
Murmushi ta saki,tana kara ajiye mai sunkin sabulu a gaban shi,"ai babu komai Bala,ai ya faɗa min ka jima kana aiki a gidan nan"
"Ah sosai ma kuwa,domin na kai shekara goma sha biyu ina Girka ma maigida abinci"
Takalmi ta kuma tura mashi gaban shi "A'a lallai ka daɗe,kace ka zauna da surukarta na"
"A'a ban zauna dasu sai dai lokacin Kakan mai gida tana zuwa lokaci-lokaci ta duba shi"
Juya ido tayi,tana kara mika mashi wani takalmin"yanzun ta daina zuwa kenan ?
Gyara zama yayi"ai in faɗa maki rabona da ita tun wani zuwa da tayi har tati ma maigida girkin irin abincin su na turawa ra zubo mana,tunda nake ban taba cin abinci mai daɗi ba irin wannan "
"Ai sun iya girki sosai, to bata ƙara zuwa bane?
" A'a bayan komarta da kwana biyu wasu mugayen ƴan ta'adda suka shiga gidan suka harbe ta,"
Rike baki tayi "su ko me tsohuwa tai masu?
" Ai in faɗa maki,a yanda naji wai akwai wani abu mai matukar daraja da suka sata a gidan,kuma wannan abun tun zamanin kakanta ita ma ta gaje shi,to shine suka dauke,
Tsayin shekara goma sha ɗaya kenan tana cikin doguwar suma har yau bata farka ba,shi yasa duk bayan wani lokaci maigida yana zuwa ya dubata,ai ina ga ko yanzun ya tafi can ɗin ne ko kuwa? Ya karasa faɗa yana tsare ta da ido,
Cikin sauri tace"Eh haka ne,ai muna waya dashi"dan bata son yayi zargin komai,
Jakkan ratayawa guda biyu ta mika mai"amma me suka sata a gidan?
"Wama ya sani,ni wallahi bansan ko me suka sata ba,amma dai na tabbatar koma menene abu ne mai matukar muhimmanci"
Ɗan shiru tayi kamar me tunani"to amma an kama wadanda suka aikata aikin?
"A'a har yanzun da nake baki labari babu labarin waɗannan mutanen,sai dai kuma wasu na zargin idan Kakan nashi ta tashi zata San wadanda suka aikata mata haka"
To me wannan me muhimmanci da aka sata,su waye kuma suka aikata wannan aiki,
Mai da kallon ta kanshi tayi"yama sunan garin da kakan nashi take"
"Tana can dai ƙasashen turawa,ba kin ce kuna waya ba,hala bai faɗa maki bane?
Dan murmushi ta kakaro" Ya faɗa mun