Showing 6001 words to 9000 words out of 159134 words

Chapter 3 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

27 Sep 2025

9734

ake ma magana taja"ke dai bari yar'uwa,ai ni bakin cikina yanda muka kaso kudi tun daga Sokoto har Abuja saboda mutumin nan,sai gashi naga hadaddun ƴanmata waɗanda suka fimu,wasu fa daga Adamawa,wasu Bauci,ke har daga Zamfara,kinga wadancan yan matan guda uku na wancan layin na kusa da karshe,to wallahi tun daga Ghana suka zo,kuma yawanci abinda ya kawomu daya ne,wato ko Allah zai sa kina da rabon sa'a a rayuwar ki YOUNG USTAZ ya yaba ko soyayya kuyi,inma Allah yayi ki da kashin arziki ya ce yana so zai aureki ai daga ke har dangin ki ku da talauci har tattaɓa kunnen ku,sai dai kuma yawan yammatan dake nan wallahi yau har tsoro suke ban duk in da ka juya,wasuma da kansu suke kawo yayan su"

Wanda ake ba labarin ne tace"ke yar uwa kinje wa'azin da yayi a Kaduna kuwa,watancan daya wuce?

"A'a ban samu zuwa ba"

"Hmmm,ai kuwa ana cikin wa'azi sai ga wata mata ta tashi wai ta ba Young Ustaz sadakan ƴar ta"

Zaro ido tayi har tana rike mata hannu "Allah yasa bai karba ba"

Dariya tayi"ai wallahi daya karɓa,ni kaina da kaina zan kira Babana yazo ya bada sadaka ta,
Sai dai Allah ya so shi,sai godiya ya mata yace tayi haƙuri ba zai iya karɓa ba saboda wani dalili,"

Ajiyar zuciya ta sauke har da dafe kirji "kai Allah na gode maka"

Ji suka yi wani Malami ya fara sanar da Shigowar karamin kuma Babban malamin su wato,Ustaz SORAJ ABDUL BASIR,

Aikuwa nan take ɗakin taron ya ɗauke da kabbara wanda yake tashi ta ko wani lungu da sako na cikin ɗakin,

Wasu manyan mutane na gani su biyu sun sha bakin kot na maza,fuskar su a turbune,kamar yanda ko wanne su kunnen shi ke manne da abun jin magana,
Su biyu a gaba biyu a baya yayin da suka saka wani matashi a tsakiya wanda nake kyautata zaton shine Ustaz din,

Dakyar dai na samu nasaran lekawa dan na gano mana wannan mutumin da yan mata da samari ke buri akan shi,shin yama kamannin shi suke ne,

Tun daga ƙasa na fara kallo inda ido na suka sauka akan wani haɗaɗɗen takalmi na maza,na yayi irin wanda sai a MBC Action nake gani suna tallan shi,masu matsifar kyau da tsada na fata,
ina karawa sama sai na cin karo da wando na farar shadda wanda daga kasan kafa ya Dan matse na samari ya ma farin kafar wani irin kyau
Sai hannun shi wanda yake dauke da agogon Azurfa mai matukar ɗaukar ido,da hannun shi wanda yake sanye da zobe kwara daya tal,
Sai kuma rigar jikin shi wanda ya kasance ya zaune mashi a jiki sosai kuma iya guiwa ya tsaya mashi,sai dan siririn dizai da aka ma rigar har kasa kuma fari tas,wanda ba karamin kyau da zauna mashi kayan yayi ba.

A kanshi na tsayar da kallo na kafin na gangaro fuska,
Wato suman kanshi nada ɗan yawa kaɗan sai dai a murmurde yake irin na Asalin Hausawa,
Sai dai daga ganin murdewar kasan kamar dai an dan murmurdene ba yin kanta bane,an kyara ta sosai har wani daukar ido take saboda baki,sai dai bai daura hula.

Masha Allah baki na ya furta a lokacin da ido na suka sauka a kan nashi,domin kuwa kyau,idan nace kyau ina nufin sosai din nan,to Allah ya bashi,wanda mace bata isa ta tsaya mashi yanga ba in dai akan kyau ne,gashi fari yanda kasan ka taɓa jini ya fito haka yake,ga kwarjinin da haiba da Allah ya mashi,
Ko kallon fuskar shi kaɗai kayi sai kaji wani iri a jikin ka,

Ni a tunani na zanga wani babban malami ne duk da naji ance young amma ban taba tsammanin zan ga malam da irin wannan shigar ba,ban taɓa tunanin yaro irin haka wanda bai wuce shekaru ishirin da biyar ba zai samu irin wannan tarin ilimin daukaka da girmamawa,kuma abin daure kai gaba ɗaya Al'ummar dake wurin babu wanda ya damu da kalan kayan dake jikin shi,sai ma murna da matasa keyi akan sun samu wata sabuwar wanka a wurin Ustaz yau.
Lallai dole ƴan mata su ruɗe, domin yanda kasan wani celebrity haka yake.

Tunda ya shigo yake daga ma mutane hannu fuskar shi cike da sanyayyiyar murmushi,har ya zauna a inda aka tanada domin shi,

Cikakkiyar Sallamah ya fara masu,wanda nan take dakin taron ya fara amsawa daga bakin mutane mabanbanta,

Godiya ya fara ma Allah daya kawo shi wannan garin da kuma irin tarbar da mutanin garin suka mashi,

Daganan kuma ya dauki topic daya wanda zai yi magana akai wato ZINA,

Tun daga lokacin daya fara magana yana jawo aya ya fassara tare da hadisai kaji gabaɗaya wurin ya ɗauki wani irin shiru wanda ko tari baka ji sai jifa jifa,sai kuma sautin daddarar Kira'an da kuma muryar shi mai saka mutum natsuwa,

Cikin harshen Hausa wacce bata fita mashi sosai kamar dai bayajin Hausar sosai,dan wani bi yafi haɗawa da Turanci wanda ba kowane ke gane abinda yake faɗa ba saboda yanda yake furtasu,sai dai duk da haka yana ƙoƙari wurin sassauta turancin shi,
Daga karshe yayi magana kuma akan illolin shan giya,kafin ya fara rufe taro da Addu'a sosai,wanda a kalla sun dauki awa uku suna wa'azin,sannan ya sanar dasu sai sun haɗu kuma a wani garin domin gobe zai koma,
Kafin mutane su yayyabeshi security din shi su buɗa mai hanya har ya shige moto dan su mai dashi babban Hotel din daya sauka,dan akwai mutanen da zai gana da su kafin tafiyar shi gobe da yamma.........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*07*

Tunda ta idar da sallar asuba ta koma ta kwanta ba ita ta tashi ba sai ƙarfe sha ɗaya na safe,wanka ta fara yi sannan ta saka wata doguwar riga na atamfa,rigar bata wani matseta ba kamar yanda bai mata yawa sosai ba,sai dai dinkin ya zauna sosai a jikinta,sai ɗankwali data naɗa wanda kusan rabin sumanta a waje yake,haka kuma mayafin ta baida girma dan madai_daici ne ko nace ɗan ƙarami ne,

Tana fitowa ta dauki makullin motar ta sabuwa wanda ajiya da daddare aka bata kyautar shi,sai kuma ta maida ta ajiye tana jan tsaki,da kafa ta tako har bakin Get inda me gadi yake zaune,tana kara waya a kunne,maganar mintuna biyu tayi ta kashe wayar tana karaso in da yake,

"Barka da safiya ranki ya daɗe"

"Yawa barka,ya aikin naka"ta faɗa tana zama akan bencin dake wurin,

" Alhamdulillah Hajiya"

Bata ce mashi komai ba kuma ta shiga danne_danne da yawarta kusan mintina goma zuwa sha biyu sai ga wani me Adaidata ya zo ya tsaya da sauri ya fito ya shiga gaida ita cikin girmamawa,
Amsawa tayi sannan ta tashi,buɗe karamin jakkan dake hannun ta tayi ta zaro dubu goma ta mika ma tsaho mai mata gadi,
Godiya ya shiga yi mata yana saka mata Albarka,a zuciyar shi kuwa yana mata fatan shiriya,domin kuwa ba karamin kyautata mashi take yi ba,kusan ko wani lokaci in dai tana nan to cikin yi mashi kyauta take,kai Allah dai ya shiryata ta koma gaban iyayenta,

Shiga cikin Adaidaitan tayi,ya ja suka fito bakin babban titi,
Sai lokacin ya ce "Hajiya ina zamu?

" Gidan Aunty Babba"

Yasan in da take nufi dan haka jan Adaidaitan yayi ya dauki hanya wanda tafiyar mintuna ishirin da biyar ne ya kai su har bakin Tangamemen Get din,
Cewa tayi ya tsaya ya jirata a bakin Get,ta fita
Tana isa mai gadin yana ganin ta ya shiga dariya tare da washe hakora ya na gaishe ta,tare da bude mata ƙaramin kofar ta shiga,

Wato gida ne babba mai hawa uku mai dauke da ɗakuna sama da guda hamsin,
Tun daga shiga cikin harabar gidan zaka fara tabbatar ma kanka da wani irin gida ne wannan ,domin kuwa mata ne wanda ke sanye da kaya dai dai son ransu,wasu da riguna iya cinya,wasu sunyi dandali suna zukan shisha pot,yayin da wasu ke buga karta,a ta wani bangare kuma wata haka gani zaune a saman cinyar saurayi ko tsoho a zaune suna sha'anin gaban su,

Duk inda ta gifta baka jin tashin komai face na ihun mata da shewarsu suna kiran sunan ta"sai Yar Tsanar Zinari "wannan sunan kawai suke mai maitawa tare da mata kirari,"zinariya abin bege ga kowa,sai dai duk kudinka baka isa ka mallaka ba sai da rabonka,ko da rabon ka,sai dai ka ara amma baka mallaka ba,domin zinari dashen Allah ce"wannan ce kirarin da wasu ke mata,yayin da take daga masu hannu tana tana murmushi,

Wani ɗaki wanda yake yafi ko wani daki a wurin girma da kuma ƙwalliya a ƙofa shita shiga batare data damu da yin sallamah ba,

Duk juyowa suka yi suka kalle ta kamar yanda ita ma ta kalle su ta watsar tare da zaunawa a kan daya daga cikin kushin din dake wurin kusa da wata mata wacce aƙalla zata kai shekara arba'in da biyar zuwa da uku,amma tasha kwalliya yanda kasan yar shekara talatin ta haɗe cikin wani Les,

Kallon baƙin ta tayi waɗanda suke maza ne ta kuma kalli Biba wacce bata da niyar gaida su,karshe ma sai cingan data ciro a jakkanta ta wurga a baki ta shiga tauna,tare da kada ƙafafu,

"Biba wani irin rashin tarbiyya ce shigowa wuri babu sallamah?

Kallon ta tayi tana tabe baki" Tarbiyata ce a haka"

"Ni fa ba haka nake nufi ba,kin dai san ya kamata ki ni me izini kafin shigo ko?

" Banga wanda zan ni me izini a wurin shi bane,"

"To gaisuwa fa,domin su baƙi na ne kuma masu mahimmanci"

Ɗan murmushi tayi tare da sauke ƙafarta ta daga masu ƴan yatsun ta"hello gentlemen"

Suma sakar mata fuska sukayi suna amsawa,

Dafe kai Aunty Babba tayi tare da basu haƙuri ta sallamesu akan sai sun haɗu gobe,

Suna fita ta jiyo tana dalla mata harara "tun yaushe nake kiran ki a waya amma baki ɗagawa,ni keke ma wulakanci ko Biba,"

"Ni fa damuwa ce bani so,to yanzun gani akan me kika ni ma na?

" Ina kaso na,naji ance kin je aiki kasar waje ina nawa saƙon "

Cikin rashin kunya tace "tunda tare da ke muka je ai dole ki tambaye ni naki kason"

"Kar ki manta ni dai na dauraki akan wannan harkar"

"Kar ki manta ko da na shigo wannan harkar da arzikina na fara ba a tsiyace na faɗo ba"

Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kai,in dai Biba ce ba a cinta a tabarman roba a ƙare lafiya"ok ya isa haka,to yanzun me zan samu?

Komawa tayi ta jingina da kyau a kan kushin ɗin "yanzun kika yi magana Uwar karuwai"

Karamin filon dake gefen ta ta wurgo mata"Biba bana son iskanci "

Ita ma ɗan dariya tayi kaɗan "to ai sunan ki ne"

"Ni dai ki bani kaso na"

"Oh Allah ke dai da wannan kason naki, ki duba na tura maki ta banki"ta faɗa tana mikewa" Dama ba wani abu bane kika addabi mutum da kira,

"A sauka lafiya ni dai tunda na gani"

Ko da ta fito tsakar gidan sai da ta masu barin kudi kafin ta fita taba mai gadi na shi ta shige cikin Adaidaitan ya ja,

Tunda suka hau kan babban titi suka haɗu da wani irin kuna taccen Go Slow,
Sai tsaki take,domin abinda ta fi tsana kenan,

Kamar daga sama ta ji ana kiran "Ummu Sallah,Ummu Salma"

Juyawa tayi yayin da gabanta ya yi wani irin faduwa wanda sai da ta rintse ido tare da dafe kirjinta,
Shikuwa mai kira sai kara kiran sunan yake yana nufo in da take zaune a cikin Adaidaitan,

Ganin ya kusa isowa in da take bayan ya fito daga cikin nashi motar ne yasa da sauri ta fito cikin Adaidaitan har jikinta na rawa tace mashi su haɗu a gida,
Da sauri ta shiga kutsawa ta cikin motoci domin bata fatan ko da a mafarki ta haɗu da wanda zai kira wannan sunan,dan haka wata mota dake gefen ta baƙa mai baƙin gilashi kawai ta buɗe ta shige tare da mai da kofa ta rufe ba tare data damu da motar waye kuma suwaye a ciki ba,
Jingina taye tana dafe kirji tare da kallon mutumin wanda yazo har ta gaban motar da take ciki ya dafe kai yana ƙara kiran sunan "Ummu Salma"yana juye yuye,

Lumshe ido tayi tare da katanto duk wani addu'a da yazo bakinta domin saisaituwar buguwar zuciyar ta,

Jim kamar motsi a gefen ta ne yasa ta buɗe ido tare da kallon inda ta ji motsin,
Mutum ne zaune a gefen ta namijin,ya zuba mata idanun shi masu matukar haske da daukar hankali,kamar yanda furkarshi har wani daukar ido yake,

Ita ma kallon shi tayi tana tabe baki tare da harara shi,a hankali kuma ta furta "Maye"
Tana juyar da kai,

Mamaki ne ya kara kamashi,wai yau shine mace zata shigo ma mota har ta kalli tsabar idanun shi ta kira shi da Maye,karo na farko a rayuwar shi ya samu harara a garin Abuja,aranar da yake shirin barin garin,domin komawa in da ya fito.......
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*08*

Mai da kanshi yayi ya jingina yana lumshe ido,
Yayin da shi kuma Direba yake cigaba da jan motar shi har ya samu suka bar Traffic din,

Dafe kai tayi tana jan dogon tsaki,tare da tunanin dole ta bar garin Abuja koda na wani lokaci ne,
Dafa kujeran da direba ke zaune ta yi "kai tsaya na sauka a nan"

Da sauri ya juyo yana gangarawa gefen titi tare da yin parking,dan ba karamin tsoro da mamaki ganin ta acikin motar da Young Ustaz yake ciki yayi ba,ta yaya ta shiga,ko dama tana ciki ne,
Cikin rawar jiki ya fito yana buɗe ta bangaren da Malamin nasu ke zaune,yayin da sauran motocin dake binsu a baya suma suka tsaya,

Kallo shi tayi sai dai idanunshi a lumshe suke kamar mai yin bacci,amma ta tabbatar ba bacci yake ba,dan tafiyar da suka yi na ƴan mintuna bai ci ace har mutum yayi barci ba,

Bata cikin yana yi mai daɗi,dan haka ce mashi kawai tayi "idan kana ji na ka rage wannan suman na kanka,idan kuma kai kurma ne Allah ya baka lafiya" tana gama fadar haka ta kulle mai kofar mota ta wuce,

"Ko ina ruwana ma da suman shi ohh" ta faɗa tana tsallaka titi dayan barayin tare da tare adaidaita ta shige,

Tambayar shi suka shiga yi ko yana lafiya,
Domin dai sun ga ko da ta fito sai da ta tsaya suka yi magana dashi a nasu fahimtar,amma kuma abin ya basu mamaki domin tunda suke dashi basu taɓa ganin shi da wata mace haka ba balle har su zauna tare,to wacece wannan.
Ganin duk irin tambayoyin da suke mai yaki kula su ne yasa dole suka koma cikin motocin sannan suka tada tare da daukar hanyar Airport in da zasu kai shi.

Suna isa airport din basu wani jima ba jirginsu ya tashi,ƙarfe biyu ta musu ne a cikin Kano,ko da suka sauka motocin gidan su ne suka zo daukar shi,
Suna tsayawa kofar gida ana kiran sallah,dan haka tsayawa sukayi a bakin Get ya sauka dan sun san ka'idar shi,

Ya fara Alwallah kenan yaji an ɗan buge kafadarshi ana dariya "Ustaz Suraj an dawo kenan,yau yamma ta nawa ka haɗu da su,domin so nake ka haɗa ni da guda biyu zafafa ko na rage hanya dasu,kasan ku malamai ba a rabaku da eh yane" Ya karasa faɗa yana dariya.

Duk maganar da yake yi yana jinshi sai dai bai bashi amsa ba har ya idar da Alwallah ya dago,
Kallon shi yayi,shima dai matashi ne wanda a ƙalla zai iya ba Suraj din shekara uku zuwa huɗu,kuma suna da dibar kama sosai da shi,daga gani dai kamar suna da alaƙa sosai da juna,

Bai bashi amsa ba ya juya ya shige cikin masallaci dan in dai Ibrahim ne yasaba da irin wannan halin nashi.

Shima kuma ganin bai kula shi bane yasa ya fara daura Alwallah kafin Abba ya fito,dan yasan yanzun zai iso masallacin,idan kuma yazo bai gan shi ba zai iya samun matsala.

Koda aka idar da sallah kafin ya fita masallaci sai da ya tsaya suka gaggaisa da mutane sannan ya fito,

A ƙofar gida ya haɗu da Abbu a tsaye wanda yana ganin shi ya sake murmushi kamar shima yanda ya samu kanshi dayi,
Karasawa yayi inda yake yana ƙoƙarin tsugunnawa ya gaisheshi,sai dai kafin ma yakai ga yin haka har ya rungume shi,

"Abbu mun same ku lafiya? Ya faɗa shima yana rungume mahaifin na shi.

" Lafiya qlau ɗan albarka,ya fama da jama'a?

"Alhamdulillah Abbu,"

Riƙe hannun shi yayi "mu je Ummin ka na jira"tare suka jero suna tafiya yana ɗan mashi tambayoyi game da tafiyar tashi,wanda haka yake matukar mantar dashi damuwar shi,dama kuma shi ba mai bari karamin abu ya tsaya mai a zuciya bane,dan yanada harkoki da yawa a gabanshi shi yasa ba karamin abu bane zai sa kaga ya riƙe ka ko a fuska ne.

Gidan babban gida ne sosai mai dauke da manyan bangarori guda biyar,
Part din dake tsakiya wato na uku shi suka shiga.
Falone babba wanda ya ji kayan alatu na rayuwa dai-dai gwargwado ba a cika komai irin na nuna isa kona Almubazzaranci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login