Showing 69001 words to 72000 words out of 159134 words
Chapter 24 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
yi "wai kije shiyan Kaka ana nimanki a can" Tana gama faɗa ta jawo kofar ta kulle,
Kallon agogo tayi,har ƙarfe tara na safe tayi,ashe dai ta ɓata lokaci a online,
Mikewa tayi ta saka Hijabin ta ƙaramin sannan ta fita,
Tunda tayi sallamah ta ɗaga labulen gabanta ke faduwa,domin mutanin gidan suna cikin falon har ta da Ammi,
Samun wuri tayi ta zauna gefen Ammi bayan ta gaida su,har da kaka,
"Mustapha kira Abbu Sufyan muji ya ake ciki" Cewar kaka,
Amsawa yayi ya saka wayar a amsa kuwa,
Sai da yayi kira biyu sannan ya ɗauka,
Sai ga muryam Abbu ya baiyana,amsa sallamah yayi,kafin su gama gaida juna,"ga Mama"ya faɗa yana mika ma Kaka,
Tana amsa yana ƙoƙarin gaida ita ta dakatar dashi"ina Surajo?ya yake?yana cin abinci kuwa?
"Mama,wallahi tun ƙarfe bakwai da muka samu muka iso har yanzun sun hana mu ganin shi,sai yawo da hankali suke mana,sai turamu ofisoshi suke yi,
Yanzun haka wai sai mun ɗauki lauya sannan zamu iya ganin shi,to munma ce su samar mana lauya amma sai cewa suka yi su badu da wani lauya a ƙasa,sai dai mu samu da kanmu,to yanzun dai abinda muke cike kenan,dan akwai wani abokin mu da muka yi karatu tare,to danshi Lauya ne,yanzun haka yaron yana hanya zai iso sai musan yanda za'ayi"
Share hawayen ta tayi"Allah sarki yaron kirki,Allah ya bashi karfin zuciyar cin wannan jarabawar,Allah yasa komai yazo maku da sauƙi "
"Mama ki dai na kuka,kin san dai abinda likita yace,dan haka addu'ar ku kawai muke buƙata"
Jan majina tana"Allah ya maku Albarka"
"Amin yauwa ina ga gashi ya iso bari muyi magana duk yanda ake ciki zaku ji"ya fada yana sauke wayar,
" Wani gaskiya Allah zai nuna bancin wanda ya nuna mana yanzun,ina ce ko sati ɗaya ba'a cika ba da aka gama rigima akan Auren shi,wanda shima Allah ne ya tona mai Asiri kika gani da idanun ki,da yake Maijiddarh ba tada rabon shan wahala da ganin bakin ciki sai gashi an fasa an daura da Farkan shi,to yanzun ya aikata halin shi a in da Allah ya tona mai Asiri,sannan ku faɗi haka,wama yasan da haka yake yi duk yawon Wa'azin da yake yi,gaskiya Allah na gode maka daka nuna min komai a baiyane Asirin da ake ɓoyewa ya tonu,d..........
Saukar Marin da taji a fuskarta ne yasa ta dafe kumatunta tare da dago idanunta dan san ganin wani isasshe ne mai zarra da zai mata haka,
Kowa na falon tsit sukayi suna mashi kallon mamaki,domin abune da ba'a taba yi ba acikin gidan,balle har a gaban kaka kuma bata ce komai ba,
Cikin tsanin mamaki ta kira sunan shi"Mustapha ni ka mara?
"Kwarai kuwa an Mare ki,ko zaki rama ne?
" To me na maka zaka Mare ni,kan na faɗi gaskiya,idan har ni kun iya rufe baki na zaku iya rufe na mutanen dake waje suna magana ne,ko kuwa zaku dinga binsu da duka ne?
"Koma me zamu yi dasu babu ruwan ki,amma ke kuma muna da yanda zamu yi dake,ban taɓa sanin rashin mutuncin ki ya kai har haka ba Saudat sai yau,ace a gaban Uwata,a gaban Mahaifiyar Yaro kike fadin haka dan ba kiɗa imani da hankali" Ya karasa faɗa a tsawace cikin bacin rai,
"Haba Abba me yasa zaka Mari Momy bayan kowa nan yasan maganarta gaskiya ne,ya aikata,idan da ace be aikata ba da hakan be faru ba,ga abu a zahiri babu sharri a ciki amma ku baku son ku gani" Mi kewa yayi ya riƙe hannu Hajiya Saude data dafe kumatu "Momy tashi muje"mi kewa yayi tabi bayan ɗanta suka fita,yayin da itama Aunty Hajjo tabi bayan su ta fita,
Girgiza kai Kaka keyi kawai,
Da sauri ya karaso inda take" dan Allah Mama kiyi haƙuri,Nasan abinda ta faɗa bai kamata ba,in sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba"
"Me yasa zaka Mari uwa a gaban ya'yanta,so kake yayanka su tsana ka?wannan ba abu mai kyau bane ta aikata,sai ka bari idan kun keɓe ja mata duk abinda kaga dama amma banda duka banda Mari,domin wannan baya daya daga cikin halin kwarai,na tabbatar da idan ma da kyale ta ka yi da tana gama faɗa wucewa zata yi"
"Mama kiyi haƙuri zan dinga kiyayewa,"
"Dan Allah ku bari a gama da wanga jarabawar da ya same mu"
Komawa yayi ta zauna,
Hajiya Rahama ce ita ma ta mike "to kowa dai ya dibo da zafi bakin shi,dan haka nayi gaba" Tashi yayi ita ma ta yi wucewar ta,
Kallon Kaka ta yi,cikin kwana daya gabadaya ta zabge ta yi rama,
"Kiyi haƙuri Ammi sannan ki rage damuwa a zuciyar ki,karki bari wani ciyo ya kamaki,addu'a ita ce mafita"
Dan murmushi yake ta saki,domin ita ba mahaukaciya ɓace"In sha Allah kaka "
Nurudeen ne yace"yanzun haka na bada aikin saukar Kur'anai makarantun goma,har zuwa sanda lamarin zai yi sanyi"
"Na gode Nurudeen Allah ya maka Albarka"cewar kaka,
" Karki damu kaka,ai Suraj ai ɗan uwa na ne "
Karan Wayar Abba ne ya dakatar dasu"yauwa gashi ma sun kuma kira Allah yasa an dace sun samu shiga "
Duk da Amin suka amsa,
Gyara zama tayi,domin Allah ya gani ita kanta ta matsu ta ji halin da ake ciki.....
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*43*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Ɗaukar kiran yayi ya saka a amsa kuwa kamar dazu,
Bayan amsa sallamah ne yace"Ya ake ciki Sufyan ?
"Gabaɗaya wannan lamarin ya wuce da tunanin mu,domin yaron ya iso shine yake faɗa mana ai in dai a nan garin ne ba za mu taɓa samun lauyan da zai ɗauki case ɗin nan ba,domin gabaɗaya goyon bayan mutumin nan suke yi,idan kuma har wani loya musulmi yace zai karɓa ƙoƙarin koranshi suke yi daga aiki,yanzun haka shima a saboda kawai yace zai amsa wannan Case din an yi Seizing License din shi na Loya,
Yanzun gashi har karfe goma amma wallahi mutanen nan yanda kasan basu san da mu ba"
Inna'lillahi wa'inna ilaihi rajiun,shine kawai abinda suke ta maimaitawa,
"Insha Allah zamu dai ci gaba da jarabawa ko za'a dace,ku kwantar da hankalin ku,sai dai zuwa anjima duk yanda ake ciki zaku jimu"
"To shikenan"daganan sallamah suka kuma yi,
Nasiha sosai Kaka da Abba suka ma Ammi ciki harda ita sannan aka sallame su akan duk yanda ake ciki anjima za su ji,
Suna fitowa tana biye da Ammi a baya,har sun kusa isa falo tace" Ammi ina son zanje can gidan na kwaso kaya"
"Kisa Direba ya kaiki,sannan ki zauna a can dan zaman ki a nan baida wani amfani,ƙila zaman ki a can zai iya taimaka maki"tana karasa faɗa tana shigewa falon,
Me kuma take nufi da zaman ta anan bai da wani amfani,
Dan shiru tayi,to kuma gaskiya ta faɗa fa,duk da ta san abin zai yi kamar bai dame ta bane idan ta koma,amma komawar shi yafi,dan haka ba tare data shiga ciki ba ta juya ta nufi wurin ajiye motoci dan ta san anan zata samu mai kaita gida,
Tana zuwa kuwa daya daga cikin direbobin gidan ne ya kai ta har gida sannan ya dawo,
Bala ne da sauran ma'aikatan gidan suka shiga jajanta mata,tana amsawa ta shige falo,
Yau dinnan ba zata zauna ba duk wani daki na gidan nan sai ta tabbatar data bincika shi,
Anan falo ta ajiye Hijabin ta,kai tsaye dakin shi ta shiga ta fara dubawa lungu da saƙo,har ta gado,da dorowar kayan shi sai da ta matsar a tunanin ko zata samu wani ɓoyayyen daki ko ma'adana,sai dai ko fallan takarda bata samu ba a ɗakin,
Ba lallai bane ta iya maida dakin yanda yake sai dai kawai tayi iya yin ta tabar saura in ya dawo ya kyara abin shi,ƙila ma lokacin ta daɗe da barin gidan,
Ɗayan dakin dake gefen na kasa taje buɗewa,sai dai kamar daga ta ciki aka kulle dan taki buduwa,
Ta kwada yin amfani da dan karamin ƙarfe dan kwada ko zai bude amma sai da ya dauke ta kusan awa daya kafin ta iya buɗewa dan ma taki hakura,a cewar ta sai taga me a ciki,
Lafiyayyen daki ne,sai dai shima kamar wancan an rufe komai na dakin da farin kyalle wanda hakan ke nuna an jima sosai ba'a yi amfani da dakin ba,
Gabaɗaya ta yaye kyallayen tana kare ma ɗakin kallo,daga dukkan alamu dakin mace ce,
Durowar kayan ta bude nan ma kayane amma kuma na tsofaffi ne,sai dai kayan yawanci dogayen riguna ne,harda su sarƙoƙi masu matukar tsada,mai da su tayi inda ta dauki su,tana kokarin rufe wurin ne wani karamin fefa ta fado daga ƙasan akwatin sarƙoƙin,
Ɗauka tayi ta buɗe ta warware,
*Wudil,sabon layi,house no 120,Ilyasu Shehu*
Abinda ke rubuce kenan a cikin ɗan ƙaramin takardar kenan,
Ba tare da tunanin komai ba ta ɗauke takardar,ta bar ɗakin,
*Bayan Kwana biyu*
Abubuwa marasa daɗi ne kekan faruwa game da wannan lamarin,domin maganar so yake yafi karfin tunanin su,duk inda suke tunani za su samu lauya abin ya faskara,domin ko da sun samu da zaran ya amsa da kanshi zai dawo yace ya fasa abin yafi karfin shi,
Su kuma su Abbu har yanzun an hana su ganinshi,sun rasa yanda zasu yi,domin mutumin ba karamin mugun mutumi bene,duk kuma wanda ya amsa aiki kashedi ake masa da rayuwar sa ko data ahalin shi,dole ya ajiye aikin,
Sun ce kuma a cikin kwana na biyar zasu kai shi kotu a yanke mai hukunci tunda sun kasa samun Loya,
Su kansu kungiyar malamai sun so a dawo da case din Arewa,sai dai sam uban yarinyar yaki yarda dan haka addu'a kawai suke mashi,
Duk waɗannan labaran tana samu ne daga bakin Kaka idan kullun taje gaishe ta,
A wana na biyun ne kuma suka samu baki daga South African,Kanin Kaka ne tare da yaran shi uku,Babban dan shi,wanda yake wani gabjeje a kalla zai yi shekara Arba'in da biyar,sai mai bi mashi,sai kuma ƙanwar su mai ishirin da shida,
Shi kuma uban ya dan fara manyanta amma yanda kasan yaro haka yake,domin a tsuke yake cikin Kananan kaya,irin mutanin nan ne waɗanda daka gansu kasan budurwar zuciya ce dasu,
Ta gama shiri kenan tana ƙoƙarin fita sai ga Bala ya shigo da sauri har suna shirin cin karo,"kai lafiya?
"Hajiya baƙi aka yi"
Karamin tsaki taja "daga ina"
"Kanin kakar Ubangida mu ne,kuma yazo ne tare da nashi ƴaƴan"
Shiru ne ya ratsa falon na wani dan lokaci kafin tace"dama idan sun zo anan suke sauka?
"Eh to sau daya dai na taba ganin yazo nan kuma shi kadai yazo a wancan lokacin,dan a sannan Kakar Ubangida tana nan"
Falon take kare ma kallo,"yanzun ta ina zata sauke su,ita bata cika son tana zama wuri ɗaya da mutanen da bata sani ba gaka,
Ajiyar zuciya ta sauke,"da fita zan yi amma mu je "
Tare suka fito daga cikin falon ta nufi inda suke cikin takun ta nan mai jan hankali wanda ya riga ya bi mata jiki tun da jimawa ba tare ma data San tana yi ba ko a gaban waye,
Su din ma nufarta suke yi sai dai ganin ta kusa karasowa ne yasa suka dakata suna jiran isowar ta,
Tunda ta daura idanun ta a kansu zuciyar ta ke tsinkewa,domin bata yi tunanin ganin su a haka ba,manya zarata dasu har uban,sai dai shi kalar shi kamar ba Bature ba,yafi kama da yan American,sabanin yayar shi data gani a hoto wacce take Baturiya sak,
Tana isowa ta sakar masu da murmushi mai sanyi tana karasa kusa da wanda take da tabbacin shine Baban su "Welcome to Nigeria Grandpa "
Murmushi mutumin shima ya sakar mata yana buɗe mata hannu Alamun zai rungumeta,
Ita ma da yake yar duniya ce sai ta rungumeta suka gaisa,sannan ta juyo wurin mazan suma dai irin gaisuwar da suka yi kenan kafin ta masu jagora zuwa cikin falon tana rike da hannun maccen,
Nuna masu wurin zama tayi tace suyi haƙuri a gyara masu wurin da zasu zauna,
Bala ta aika yayi masu ordering abinci,
Matashiyar budurwar ce tace mata"Daughter in low ni tare dake zan zauna"
"ba damuwa tashi mu je"cikin sakin fuska tana mika mata hannu,
Kama hannun ta tayi suka yi ɗakinta ta nuna mata banɗaki ta kuma cire mata sababbin kayan wanka,
Jakkan kayanta kuma ta saka mata a gefe,
Sai da Bala ya kowa abinci sannan ta fito daga dakin da tasa ana gyara masu,ta sanar dasu an kammala suna iya shiga kowa daki daya,idan sun kammala ga abincin su nan,
Godiya suka mata,
Baban su da taji suna kira da Pa ne yace idan sun huta zuwa anjima zata kaisu wurin Maman Suraj,
Tana fitowa dakin wayar Ammi ta nima dan gara ta faɗa mata da zuwan su akan ta ganta da baƙi babu sanarwa,
Yana ta kara ba'a ɗauka har tayi kira na biyu yana ma shirin tsinkewa taji an ɗauka,
Ƙoƙarin yin sallamah take yi taji ance"wai lafiya kike damun ta da ƙira da rana tsaka"
Sai da tayi dan jim kafin tace"idan Ammi na kusa ki ba ta waya"
"Bana jin zan iya bata,tukunna ma ke wacece da zaki aike ni"
Ranta fa ya fara ɓaci da wannan rashin kunyar na yarinyar"Amira,ko kinki ko kinso ni din matar yayanki ne,idan baki karɓe ni ba wannan damuwar ki ne tunda yayanki ya karɓe ni ya kuma haɗa shimfida dani,uwarki ta karɓe ni,idan kin ga dama ki kaimata wayar idan kin ga dama karki bata,wawuya Stupid"tana jin lokacin da zata sauke wayar ana tambayar keda waye ke waya,ta sauke wayar tana faɗin ai Gara na karasa lalata alakar dake tsakanin mu na san cewa bama shiri gabaɗaya,
A can ɓangaren kuwa,ji tayi ranta ya bala'in baci har balle ce mata wawuya da stupid ɗin data yi,gashi ta sauke wayar balle ta rama ko za ta ji sanyi,
Jin tambayar da Ammi ke mata ne yasa idanun ta cika da Hawaye ta mika mata waya"Habiba ce,wallahi Ammi sai nama yarinyar nan rashin mutunci,cemin da tayi wawuya harda cemin stupid "
"Ta birgeni,dama ta haɗa maki da Doluwa tunda baki gane komai ba"
"Ammi!"
"Yes na,oya tashi ki barmin daki bana son surutu"
Cikin jin haushi ta tashi ta bar dakin tana turo baki,
Girgiza kai kawai rayi tana ƙara kiran wayar Habiban,
Ɗauka tayi da sallamah tana gaida Ammi,ita ma amsawa tayi,sannan tace"kin kira bana kusa"
"Eh Ammi dama baki aka yi kuma sun ce zuwa anjima na kawo su wurin ki,so karki ganni da baƙi shi yasa na kira ki"
Dan murmushi tayi"na gode Habiba,amma su waye?
"Kanin Kakar Suraj ne da yaran shi,"
"Kanin kakar Suraj?
" Eh"
"Kin tabbata"
"Eh to ni dai yanda Bala ya faɗa min kenan,sannan na taba ganin hoton shi tare da na Kaka"
Shiru ne na ɗan wani lokaci ya ratsa wayar wanda har sai da tayi tunanin ko kiran ya katse ne ta shiga fadin Hello,
Jin ta sauke numfashi ne yasa tace "ok sai kin zo"
"To Ammi"
Sauke wayar tayi tama tunanin yaufa ta so taje Wudil,amma ba komai taje gobe.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*44*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Koda suka kammala cin abinci kwanciya suka yi domin su samu su huta,
Sai zuwa yamma sannan suka shirya,Direba ya jasu har gidan su Ammi,a falon Kaka akai masu masauki,sannan Ammi tazo suka gaisa,cikin mutumtawa,
Kuka Pa ya saka yana yabon Suraj da harshen turanci,ita sam bata ma taɓa tsammanin kaka na jin Turanci ba sai yau,in da take ta bashi haƙuri tana kuma tsanar dashi halin da ake ciki,
Cewa yayi Gobe zasu tafi Legos din suje su samu su Abbu dan asan halin da ake ciki,
Babu zato ta ji Ammi tace"sai ku tafi tare da Habiba dan ko ba komai ya kamata tana kusa"
Cikin sauri ta kalle ta,sai dai kauda kai tayi tana jiran ta ji me kaka zata ce,
Kamar zata musa sai kuma tace "to ba damuwa sai su tafi tare"
Ita wallahi ba haka taso ba,dan haka tashi tayi tace masu tana zuwa ta koma shiyan Ammi tayi zamanta,
Sai da zasu wuce ne Ammi ta saka aka kirata sannan suka tafi,
Direba na sauke su ta amsa makullin mota tana kokarin shiga,budurwar da suke kira da Nadiya ce tace "zaki kuma fita ne?
" Eh"ta bata amsa,
"Zanje " Ta faɗa tana ƙoƙarin zagayawa ta shiga mota,
Da sauri ta tada motar"Sorry ana jira na ne yanzun zan dawo"ta faɗa tana fita daga gidan,tunda abun ya zama haka gara ta tafi duk dare ta dawo,
Da Marp ta yi amfani ta tafi Wudil,
Ranar ba ita ta dawo ba sai ƙarfe kusan sha-biyu na dare,dan ba ƙaramin wahala tasha ba,
A matukar gajiye ta shigo gidan kai tsaye ɗakinta ta buɗe wanda tana tura ƙofar hayaƙi ya fara turnike mata fuska,
Ƙara hasken wutar dakin tayi tana kallon ta cike da mamaki,
Tana zaune a kasa ga kwalin sigari a gabanta ga kullin wiwi irin yanda suke yin shi kamar taba da kuma ƙananan kwalaben giya masu ƙarfi da tsada guda biyu,sai shan abinta take yi cikin kwanciyar hankali,
Ganinta kuma bai saka ta fasa abinda take yi ba,
Ɗan dariya tayi"Sorry Beb na bata maki daki ko?
Shigowa tayi ta faɗa kan gado tana sauke ajiyar zuciya"no is ok"
"Thank you"
Bata ce mata komai ba sai lumshe ido da tayi tana nazarin maganar da suka yi da Dattijon