Showing 57001 words to 60000 words out of 159134 words

Chapter 20 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

27 Sep 2025

9763

again?nunata yayi da yatsa " Habiba,for God sake stop being like a real wife,I now you are just Acting,pretending,please a don't want any trouble, keep pretending like one,but stop coming into my way,I don't like you at all,I think you have to know even living with you is like hell to me,Dan haka kici gaba da aikin dake gabanki amma ki fita harka na,sannan ki tattara ki barmin daki kafin ranki ya ɓaci "
Har ya juya zai bar dakin ya kara juyowa "na baki minti biyar" Ya faɗa yana karasa fita,

Duk da maganganun shi sun soso mata zuciya nisa ba kusaba,hakan yasa ta lumshe idanun ta na wani lokaci kafin ta buɗe tana ƙoƙarin shanye duk wani ɓacin ranta,
Zaciyarta take lallashi,tabbas da ba dan akan aikinta take ba da Suraj bai isa ya faɗa mata irin waɗannan maganganun ba,sai dai zata dinga tuna Ummita wanda hakan ne zai kasance mata ƙwarin guiwa,zata iya jurewa ko dan ita,tayi haƙuri da duk wani abunda zai mata har zuwa sanda zata samu nasara ta fita rayuwar sa,zata dauki ƴar uwarta su koma kasar waje kamar yadda suka tsara,to amma me take da yace tana pretending ne akan komai,ɗan shiru tayi tana nazari,ko da yake yasan basu son juna shi yasa ya faɗi haka,to kuma yace aiki,wani aiki yake nufi,wani zuciya ne ya bata amsa to ko dai yasan aikin da take yi ne,da sauri ta girgiza kai,ina ba zai sani ba,ta yaya ma zai sani,kawai dai yana nufin,shiru tayi to yana nufin me?ajiyar zuciya ta sauke koma dai me yake nufi bashi yake nufin yasan komai ba,
Ɗan murmushi ta saki wanda ita kaɗai tasan ciyon da take ji a zuciyar ta dole ta maida shi murmushi,
A kwatunanan ta fito dasu ta ajiye a ƙofar dakin ta sannan ta sauko kasa,
A falo ta same shi yana waya,
Zama tayi tana jira ya kammala sai dai yana ganin ta zauna ya mike yana ƙoƙarin barin wurin ba tare daya katse wayar da yake yi ba,

Ganin abunda yayi ne yasa ta tashi tabi bayan shi har zuwa falon gidan na biyu,sai dai jinta a bayan shi yasa ya katse wayar ba tare daya kammala ba ya juyo yana kallon ta"Lafiya? Ya tambaya,

Sam ita bata son wannan tsaretan da ido da yake yi,sai kace mai ƙoƙarin daukar wani abu a fuskar ta,bai san irin kwarjinin da yake mata ba,dauriya kawai take yi tana nuna masa gagaranta,
Tsuke baki tayi tana juya idanunta a hankali tace"bana son irin wannan kallon"

Babu zato taji yace"idan baki da ƙwarin gwiwa jurewa ki daina baiyana"

Da sauri ta kuma juyowa,
har yanzun kuma idanun shi tsaye suke a kanta,sai dai duk yanda taso fassara yanayin fuskar sa ta kasa,"idan da banida shi da ban shigo rayuwar ka ba"

Giranshi daya ya daga"duk juriya irin na mage ba hakan ke nufin zata kai labari ba"

"Duk iya farauta irin na Zaki hakan ba yana nufin wata rana zai nime taimako wurin mage ba,sai dai kuma ina mai bashi shawara da yabi takunshi a hankali domin shima gab yake da fadawa hannun mugayen mafarauta,wa ya sani ko mage ce kawai wacce zata iya taimakon shi a wannan lokacin" Ta faɗa tana ƙoƙarin daura nata idanun akan nashi,sai dai tsabar mugunta Inji ta irin nashi sai dauke kanshi yayi a kanta yana canja zance ba tare da ya faɗi komai ba kamar yadda taso,sai cewa yayi"me kike buƙata "

Haushi ya bata,amma ita ma sai ta share,ko ba komai a juye zuwa rafi wata rana Tulu zai fashe"ina buƙatar ATM card din ka,zan fita siyayya akwai abinda nake buƙata "

"Me yasa sai nawa,in baki da kuɗi ki bar fitar mana" Ya juya zai tafi,

Gaban shi tasha tana wani marairaice fuska"Allah sarki kai da malami ne,mai tsoron Allah,kuma kasan haƙƙoƙin miji akan matar shi,ko da ta ƙarya ce,balle namu an shafa fatifa,k.. "

Mika mata ATM card din yayi daya ciro a cikin walet"Mage mai kwanciyar ɗaukar rai"

Da sauri ta amsa"wata rana Magen ce zata taimake ka"

"8487" Ya faɗa yana barin wurin,

Jujjuyawa take a hannun ta"Ohho dai ba dai ka bani ba,ka ji a jikin ka"ta fada tana fita falon gabaɗaya,

Tsayawa tayi tana kallon motocin dake fake a wurin ajiye mota,
Direban gidan ne ya taso da sauri yazo inda take"Hajiya fita zaki yi ne?

"Eh ina makullin wannan motar? Ta nuna wani sabuwar mota Maron kolo dake cikin leda alamu ma ba'a taba amfani dashi ba,

" Yana wurin Ubangida domin ba'a taba amfani dashi ba"

Gaskiya motar ya tafi da imanin ta,taji kewar tuƙi,ji take kamar ta buɗe ta shiga taja,sai dai bata son nuna zalamar ta a fili,dan haka tace"ɗauko ma kulli muje shopping "

Da sauri yace"An gama Hajiya "

Shi ya buɗe mata ta shiga sannan ya ja suka tafi,
Babban wurin siyayya na garin Kano ya kai ta,
Farko layin data fara shiga shine na kayan shafa,Glow gold ta dauka man da take shafawa,wanda kudin sa Naira dubu saba'in ne,sai kuma Sabulan wanka na ruwa da turare wanka kala-kala,man baki, da jan baki,sai kuma turaruka inda anan ne tayi ainahin ɓarna da kuɗi,
Bangaren kayan sakawa ma ta kwasa ba kaɗan ba,dogayen riguwa jallabiyoyi,dana kanti,ƙananan kaya wanduna da riguwa sai after dress,pant da bran,takalma,Agogo,sarka na wuya da kunne,man wanke kai dana kamshi,a takaice duk wani abunda ta san tana buƙata ko kuma zata buƙata sai da ta siya,dan bayan but din motar sai da aka cika shi da kaya,

Har zata fita sai kuma ta tambaye ko akwai inda ake sai da waya a ciki,nan ma nuna mata akayi,lafiyayyen Iphone ta dauka amma na dubu dari da gamsin ta dauka,a cewar ta gaba ta canja wani,sai kuma tayi ɓangaren gyaran jiki,in da anan aka kara kyara mata suma aka wanke kafa da hannu,sannan aka mata ƙunshi a kumbuna na hannu da ƙafa duka ja,dan bata son barin kumbunan ta fari,
Ba ita ta fito wurin ba sai kusan biyar na yamma,a gajiye suka dawo gida,
Cikin sauri ya buɗe mata ta fito yana ta faman washe baki,dan shikan yau ta burge shi,tunda sau biyu tana aiko mai da abinci bayan haka harda turmin zani biyu masu kyau ta siya ta bashi tace ya kai ma matarshi ko Maman shi,gaskiya ba ta da rowa,
A bakin ƙofar falo suka jibga kayan shi kuma Bala yana kwasa yana ajiyewa a ƙofar ɗakinta na sama,
Ita kuma tana shigar dasu daki,
Sai da ta kammala sannan ta jera komai in da ya dace zuwan lokacin har an tada sallah Magrib,dan haka ƙara kyara dakin tayi ta share ta goge sannan ta shiga wanka,
Tana fitowa tayi sallah sannan ta fito dan mai da mashi da ATM card din shi,
Sai dai tana tura kofar dakin ta shiga taga gabaɗaya yanda kasan ba dakin ba,domin babu abinda ba'a canja ba na dakin tun daga kan gado har komai na banɗaki data leka,sai ƙamshi dakin ke zubawa kamar na sabuwar Amarya,
Tabe taki tayi"kudi na faɗa maka ƙarya "kwalbar turaren data siyo mashi dan karami mai matukar kyau da kamshi ta ajiye mashi nan saman madubi ta fita,
Cike da tunanin ya kamata ta fara gudanar da aikinta zuwa gobe da safe idan ya fita,dan yau kam ta gaji...

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*37*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Tana shiga daki ta turo kofa ta zauna kan gado,
Jakkan data fita dashi dazu ta buɗe,wanda kwalayen Sigari ne guda biyu a ciki,ciro kwali daya tayi ta cire wanda zata sha guda daya sai wani magani data balla guda daya ta raba biyu ta wurga a bakin ta tana tsosa ba tare data damu da dacin shi ba,
Sai da ta tabbatar ya narke sannan ta kora da ruwa ta kunna Sigret tana mashi kyakyawar zuka,
Tana kammalawa ta tashi ta cire hijabin dake jikin ta da zani ta maida kayan bacci wanda yake ɗan ƙaramin pant ida duwawu sai karamin singileti mai tsansi iya haƙarƙari,gabaɗaya tundaga shafaffen cikin ta har zuwa kasan maran ta a buɗe yake,yayin da Cibiyar ta dake sanye da ɗan kamin makale na zinari wanda zaka yi mamakin ta ina aka bula aka saka shi,dan har wani daukar ido yake yi,
Dama gashi suman kanta yasha gyara dan haka ta baje shi a tsakar bayanta yana lilo,
Shafe jikinta da turarukan kamshi tayi kamar yanda ta saba in dai har zata kwanta,
Jin kanta ya fara nauyi ne yasa ta tashi daga gaban madubi ta haye saman gado taja bargo sannan ta rage hasken wutar dakin sosai,
Lumshe ido tayi ta buɗe tana kallon Silin,abubuwa ne da dama suke dawo mata acikin kwakwalwa,ƙara lumshe ido tayi sai ga hawaye ya sauko ta gefen ramin idanun ta,
A hankali bakin ta ya furta "Ma" Ba tare da ta karasa ba ta haɗiye sauran a ranta,tana jin wani abu mai matukar girma da ɗaci yana tsaya mata a makoshi,
Tasan ita yarinya ce mai matukar Kawazucin iyayenta,har balle Mama,ko ina bata yar da ta je ba tare da ita,sai makaranta daya zama dole,to amma gashi cikin lokaci kankani komai ya sauya,tana rayuwa ba tare dasu ba,tana rayuwa ba tare da tasan halin da suke ciki ba,tana rayuwa ba tare da jin muryar su ko ganin su ba,shin suna raye ko sun mutu,
Tunanin hakan ne yasa ta fashe da kuka daga kwancen da take,kuka take sosai kamar wacce aka daka,
Rayuwar ta bai da wani amfani,ta shiga duniya ne kawai saboda bakin ciki,tana son taci gaba da gujewa wannan bakin cikin har zuwa ƙarshe,to sai dai ina ne ƙarshen?ta ina zata bi ta kai wannan ƙarshen?ko yaushe a ciki gudu take amma har yanzun bibiyar ta yake yi,duk da ta canja gari,ta canja suna,amma har yau ba abinda ya sauya,
Sai dai koda kafin ta kai wannan ƙarshen zata rasa ranta a hanya,ba zata taba juyawa baya ba ga inda ta boro,ba zata taba juyawa ba ɓalle ta ga nisan da tayi,ko da hakan na nufin zata iya fadowa daga saman tsaunin data hau,ba zata taba waiwayarsu ba har abada,

Ta dauki lokaci mai tsayi tana kuka kafin daga nan Sarkin iya sata ya dauke ta,wato Barci wanda tayi shi ba dan daɗi ba,

Jin yanda jikinta ke ciyo ne ya sakata tashi zaune ba tare data buɗe ido ba,dan ƙwayar data ci tuni ya gama jukuwa,
Saukowa tayu daga kan gado ta dawo kasa ta kwanta,nan ma ba daɗi taji ba sai ma mulmula data gama yi ta kara tashi, kai tsaye fita tayi ta nufi ƙofar ɗakin shi wanda yake kallon nata,
Turawa tayi ta shiga ba tare data damu da duhun da ɗakin ke dashi ba,
Da lalube ta faɗa kan gado tana jawo bargon data ji a shimfede ta shige,
Cikin ƙanƙanin lokaci barci mai matukar daɗi yayi awon gaba da ita,dama kuma gashi yanayin garin yau akwai sanyi,

Kiran sallah dake shigowa kunnen shine ya tilasta shi ƙoƙarin buɗe ido wanda yake jin yayi masa nauyi,
Ɗan shiru yayi yana saurare kamar mai nazarin wani abu,
Tabbas yana shakan wani irin kamshi wanda ya san ba daga jikin shi yake fitowa ba,sannan yana jinshi kamar a jikin mutum,
Hannu ya miƙa ya kunna wutar dakin gabaɗaya,sannan a hankali ya shiga yaye bargon dake jikin shi,
Wani irin zabura da yayi ya faɗo daga saman gado hakan yasa itama ta firgita ta mike tsaye cike da tsoro tana kalle_kallen ko abun gudu ne ita ma ta gudu,

Kallo daya ya mata ya kalli kanshi ai dasauri ya runtse idanun shi yana fadin"Bismillah,A'uzu billah,ya haiyu ya Kaiyum"
Da sauri ta duro daga saman gadon cike da tsoro ta dawo ta bayan shi ta rike mai hannu,cikin muryar Tsoro tace"Suraj mu gudu,ni tsoro nake ji hala maciji ka gani,dan Allah ka fitar dani "dan ita a rayuwar ta ba abun da take tsoro irin maciji,

Ba tare da ya kalli in da take ba yace" Fitar min a daki"

Gabaɗaya ma rungume shi tayi ta baya tana kwantar da kanta a bayan shi wanda bai saka riga ba,"A'a babu inda zan je,sai dai in goya ni zaka yi,tsoro maciji nake yi"

Duk wani addu'a da ya zo bakin shi faɗi yake a zuciya,ba tare daya dire wani ba yake daukar wanu,rokon Allah kawai yake daya mai tsari da ita da kuma sharrin ta,

Da kyar ya iya danne zuciyar shi"ki hau kan gado bari saka kaya sai na fitar dake "

Bata ci masa musu ba ta hau kan gadon ta tsaya tana kallon shi har ya saka doguwar Jallabiya ba tare da ya juyo ba ya nuna mata hanyar waje "zoki fita"

Makale kafaɗa tayi"Umm Umm"

Ranshi ne ya bala'i ɓaci dan haka juyowa yayi yana fuskantar ta dan dai kawai taga bacin rashin,sai dai duk yanda yaso ya jure kallon ta kasawa yayi,saboda yanda gabaɗaya ta turo baki ta narke yanda kasan wata Baby,gashi kuma duk wani motsawa da zata yi sai sharasharan rigarta na sama ya daga wanda hakan ke kara bayyana cikakken Kugun ta,da kuma ramin Cibiyar da ɗan makalen ke ɗaukar hankalin shi,
So yake yaga me a wurin,dan bai taba tsammanin ana saka abu a wurin ba,dan bai kasance mai kallon tsiraicin mace ba,
Da hannu ya nuna cibiyar nata"me kika saka anan"

Kallon inda yake nunawa tayi,ɗaga rigar sama tayi tana kallon shi"me?

Ɗauke kai yayi yana jin kanshi na sarawa,kafin ya tako inda take,ba zato taji ya jawota ya daura saman kafaɗa,a bakin ƙofa ya dire ta "ki cire wannan abun na Cibiyar ki" Garam ya maida kofar ya kulle,
Ƙwanƙwasawa ta fara tana kiran yazo ya buɗe mata,sai dai bai da alama zai buɗe,
Cikin jin haushi ta buga ƙofar ta da ƙofar,sai kuma ta dafe ƙafar tana faɗin"uch"falo ta koma kan kushi ta yi kwanciyar ta,har ya fito ya tafi masallaci ya dawo tana kwance,
Ruwan sanyi ya dauko a firig ya buɗe,
Ji tayi yanda ruwan sanyin ke ratsa ta yasa ta tashi a firgice tana niman wurin gudu,sai dai rike mata hannu yayi da hannun shi daya,duk yanda taso ta kwace kasawa tayi,haka kuma duk yanda taso ta rungume shi yaki bata dama,
Hakan yasa kawai ta sadakar ta tsugunna a gabanshi ta dukar da kai har sai da ya karar da gogar ruwa masu azaban sanyi a kanta,
Ji take kamar ta sheke saboda sam bata shiri da sanyi shi yasa ma ko abu mai sanyi bata cika sha ba,
Gashi ba kayan ƙwarai ne a jikin ta ba,ga sanyin AC dake ƙara butso sanyin,ta jike sharkaf yayin da
sumanta ya rufe mata fuska,
Dagota tsaye yayi da hannun shi dake cikin nata,
Murmushi ya saki wanda har tana iya jin sautin shi a kunnen ta,
Ta kasa buɗe ido saboda ruwan dake diga daga cikin kanta,ga kuma suma daya rufe mata rabin fuska,

Hannun ta ya riƙe duka biyu ya daura a saman ƙafar shi,
Suman daya rufe mata fuska yasa hannu yana maida mata dashi gefe,
Kallon lip din ta yayi yanda yayi jawor yana dan motsawa saboda rawar sanyi da take yi,
"Buɗe idanun ki"

Kin buɗewa tayi,saboda yanda ranta ke tafasa,

Ba zato taji hannun shi a saman boturan maɓallan rigar ta shara_shara na saman,

Duk da haka bata buɗe ido ba, sai ma ƙara rintsesu da tayi,

Duk Boturan uku ya cire,ya zame hannu rigar zuwa cinyar hannun ta,wanda hakan ya bayyana manyan kirjinta dake cikin ƙaramin rigar,
Hannu yasa ya shafi saman kirjin ta sannan ya gangaro ruwa Cibiyar ta inda nan ne yafi ko'ina tsole mashi ido,
Shafa wurin yake yana zagaye ƴan yatsun shi,

Jin yana ƙoƙarin gangarawa kasan maranta ne yasa ta buɗe rinannun idanun ta a kanshi,
Dama kuma duk abinda yake idanun shi na kan fuskarta yana karantar ko wani hawa da saukar numfashin ta,ganin ta buɗe ido ne yasa ya kuma sakin murmushi,
"Wannan jikin naki ba komai bane a wuri na face madaddalan datti,in da wasu kazai mai suka gama zub da ƙazantar su a ciki suka tafi,ki sani in dai kece ko da zaki yi yawo tsirara ba zaki taba jan koda digo bane daga cikin hankalin,
Domin ni mai tsafta ne,bana hulɗa sai da mutane masu tsafta,
Ki kama kanki,karna kuma ganin wannan kazamin jikin naki a inda nake," Ya karasa faɗa yana shafar ƙugun ta,"ke abin tausayi ce,har yanzun baki San komai ba acikin duhu ki ke "juyawa yayi ya barta a wurin yayi shigewar shi ɗaki,

Ta jima tsaye a wurin har saida ta ji ƙafarta na niman gagara ɗaukar ta sannan ta taka a hankali ta shige daki tana turo ƙofa,
Tun daga lokacin ban kuma jin duriyarta ba.

*Bayan Kwana Biyu*

Tun bayan faruwar lamarin ta fita harkan shi,bata ƙara barin sun haɗu ba,a duk lokacin data tuna kalaman shi akanta sai ta zubar da hawaye,shi bai san komai ba dangane da ita,me yasa zai ce jikinta matattaran ditti ne,,eh tasan abunda ya faɗa gaskiya ne jikin ta akwai dauda,amma abin ne da ciyo,domin idan da ace tana da damar da zata bar wannan aikin da tuni ta bar shi,da bai kara ganin ta ba har a bada,kuma ko yanzun hakan ne ta ƙudurta a ranta,da zaran aikinta ya kammala zata yi wucewar ta,
Shi yasa ma yanzun ta yanke hukuncin fita harkar shi ta ci gaba da lalube cikin duhu ko zata dace,
Jin ana ƙwanƙwasa kofar dakin ta ne yasa ta rufe karamin takardar da take rubutu a ciki,ta jefa cikin durowa sannan ta zura karamin hijabi ta fito,

Bala ne a tsaye bakin ƙofa "Hajiya kin yi baki a ƙasa"

"Su waye?

" Kannen megida ne"

Daki ta koma dan canjo hijabi sannan ta fito,

Khadija ce da Zainab,

Ba tare data ce masu komai ba ta zauna a ɗaya daga cikin kushin tana daura kafa daya kan ɗaya,
Kamar yanda suke jira ta gaishe su ita ma haka take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login