Showing 117001 words to 120000 words out of 159134 words
Chapter 40 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
taɓa ɓoyewa,
A lokacin girgiza kai kawai yayi ya wuce ba tare da ya ce mashi komai ba,
Da hannu yayi nuni"wannan ba Suraj bane?
Kafin su bashi amsa ne sai ga Dady ya iso in da suke"waye ya ajiye wannan motar a nan?ko anyi baƙo ne?
Girgiza kai Nurudeen yayi cikin disashewar murya yace"Suraj ne"
Shima sai da ya kara kallon motar na saƙonni kafin ya juya ya doshi cikin gida.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*71*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Cikin natsuwa yake tafiya tamkar wanda baida wani damuwa a zuciyar,ya doshi shiyan Kaka,
Da Sallamah ya shiga, tana ganin shi ta shiga washe baki tana dariya wanda hakan ya saka shi murmusawa,
Da sauri Khadija ta tashi daga inda take zaune kasancewar yawancin lokuta yafi zama a nan wurin,
"Yaya ga wuri"
Bai amsa mata ba sai ma zaunawa da yayi kusa da Kaka,
"Tsohuwa barka da safiya"
"Da fatan ka tashi lafiya,?
Bai bata amsa ba sai ma cewa da yayi" Me zan samu na ci?
Kallon Mejiddarh tayi data yi zaune ta tsira mashi ido kamar taga sabon hallita,
Dauke idonta tayi a kan ta tace"ke Balki dauko ma Surajo Kunun tsamiya yana nan cikin fulas a kicin"
Da sauri ta mike ta nufi kicin din domin dauko masa,
Khadija ce ta mike tabi bayanta "bari na taimaka mata wurin dauko kulan kosai da kofi"
Ba wanda ya bata amsa har ta shige ita ma,
Karo suka ci da sauri ta karasa shiga tana jawota baya"ke kinga abinda na gani?
Hararanta tayi"ke dai Khadijah anyi Uwar gulma,yanzun har kin ga wani abu"
Dariya ta saka,sai kuma ta toshe bakinta da sauri tana zaro ido"ba ki lura da kallon da Aunty maijiddarh take masa ba?
"Wani irin kallo kenan?
Duka takai mata a kafaɗa" Irin kallon dan Allah ka kula ni "
Juya ido tayi"ina lura da komai,shima kuma yau naga kamar yan miskilancin sun motsa baki ga yanda ko amsa gaisuwar mu bai yi ba?
Kafin ta bata amsa ne suka ji muryar Kaka na fadin"wai Kunun yaki daukuwa ne?
A tare suka amsa da faɗin "gani nan zuwa"
Rike mata hannu tayi tana kashe mata ido"sai dai fa ya haɗu Balki babu karya,yau na daban ne"
Fisge hannun ta tayi tana yin gaba tare da fadin "ba kida hankali tunda so kike ya sheke mu"
Ajiye mai fulas din tayi a gaban shi sannan ta tsugunna ta tsiyaya mashi,
Ba tare da ya ce mata komai ba ya ɗauka ya fara sha a hankali,
Shigowar su Ibrahim da Nurudeen ne yasa ya dan daga kai ya masu kallo daya sannan ya dauke kai yana cigaba da kurban kunan shi,
Wanda hakan da yayi ba karamin tsayama daya daga cikin su a rai yayi ba,
"Ya jikin Habiba Surajo?an samu an mata aikin kuwa?
Jujjuya kofin dake hannun shi yake yi wanda ya kusa kammalawa" Ba ayi ba "
Cikin nuna damuwa tace"me yasa,ko an fasa aikin ne?
Ajiye kofin yayi"ba'a fasa ba za ayi amma ba yanzun ba,"
Ganin tana shirin ƙara jeho mashi wani tambayar ne yasa yace"akwai wasu gwaje_gwajen da ya kamata su kara yi mata,da zaran sun kammala za ayi"
Ibrahim ne yace "Bro gaskiya motar nan daka shigo da ita ta cije ni"
Kallon rashin fahimta yake mashi,
Dariya yayi kaɗan "ina nufin motar ya haɗu,kasan nawa naji kudinta kuwa,ai ban dauka an samu wanda ya shigo da ita Nigeria ba saboda wata biyu kenan da ya fito kuma a Saudiya aka yi Lunching din ta"
Ganin bai da niyar gama jawabin shine yasa ya mike yana faɗin "Kaka zan fita sai zuwa anjima"
"To Allah ya tsare Surajo"
"In zo ka rage min hanya"ya tambaya dan kawai ya shiga motar ya kafa tarihi a cewar shi,
Bai bashi amsa ba har sai da ya kusa barin falon sannan yace" Ba yau ba"
Dariya su Khadijah suka saka ganin yanda ya ɓata fuska,harara ya dalla masu"bakuda hankali baku san irin motar da nake magana ba ne?
"Ni kan wani irin mota ne haka da har zaka yi marmarin hawa bayan duk irin motocin dake cikin gidan nan"
Karamin tsaki yaja "bari dai na nuna maku abinda nake magana akai," Nan ya ciro waya ya bude data cikin yan mintuna yayi downloading hoton motar sannan ya mika ma Maijidda"kalli mota ki gani tamkar wani jirgin ruwa"
Amsa ta yi tana dubawa yayin da take yin kasa da hoton domin duba kudin mitar,
Ai babu shiri ta buɗe ido cikin tsananin mamaki,
"Kaka kin ga kudin motar nan kuwa? Yanzun irin motar nan Yaya Suraj ya ke dashi?
" Ita ma ya hau yau,idan har bai wuce ba kina fita kofar gida zaki ganta fake "
Fisge wayar Balki taki"ku bamu mu kashe kwarkwatan ido"
Shigowar Hajiya Saude ne ya katse su wacce ke tambayar "cin mu sun ne ake yi?
Balki ce ta mika mata wayar" Momy kalli motar da yaya Suraj yake da,kalli kuɗin motar,
Idan har yana da kudin siyan wannan motar to wani irin kuɗi kenan yake dashi "
Amsar wayar tayi tana dubawa"yanzun Suraj ne yake da irin wannan motar?
"Sosai ma kuwa"
Hararan shi tayi tana mika mai wayar"karyan banza,yaushe yayi wannan Arziƙin,waye Ubanshi?me kuma ya mutu ya bar mai da har zai mallaki irin wannan motar,sai dai in yana haɗawa da wata hanyar ne na ƙarƙashin ƙasa wanda bamu sani ba"
Ta karasa faɗa tana zama a daya daga cikin kugerun falon.
Dariyar da Kaka tayi ne tana girgiza kai ya maido hankalin su kanta,
Kallon ta tayi tana jinjina kalamanta "kika ce waye uban Surajo Saude?sannan kika ce Ina yaga kudin siyan wannan motar?to bari na sanar dake wani ɗan ƙaramin abu da baki sani ba game da Ahalin sa,Kakan shi,a wancan lokacin hamshakin mai kuɗi ne wanda idan ma baizo na daya ba a masu kudin kasar MARDESH to zai zo na biyu,domin Allah ya Azurta wannan Ahalin da dukiya na ban mamaki,sai dai kuma su jarabawar su shine Allah bai yi su da samun Ya'ya ba,yawancin su ba su da haihuwa wanda suke matukar so,kafin a samu haihuwar uban Surajo ba karamin wahala suka shaba wurin rokon Allah,kakan shi ya mutu ya barma kakar shi mace dukiya wanda dana auren dangi suka yi ba mai nuna ma wani arziki,ita kuma dan da take dashi ya mutu ya bar mata jika ƙwaya daya tal,wanda shine magajin duk wani abunda suka mallaka a duniya,
Dan ma Allah ya tsare shi Surajo ba mai nuna komai bane ai da baku isa ku haɗa mazauni da ku ba,ko a yanzun iya Business nashi da Allah ya hore mashi kun san abunda ya mallaka a kasashen duniya,"ƙaramin tsaki taja tana mikewa "kawai dai kuna ganin mutane ne kuna wulakanta su ba tare da kunsan iya baiwar da Allah ya masu ba,sannan har kuke mamaki dan kun gan shi ya hau wannan motar da kudinta a wurin ko cikin chokali bai kai ba" Ta karasa faɗa tana shigewa dakin ta,ta bar su nan zaune cikin mutuwar jiki.
Kallon Maijidda tayi yayin da suka haɗa idanu,sai dai ba wanda yace komai yayin da jira kawai suke su keɓe dole akwai magana,dole ne ma,
Hajiya Saude ce ta fara tashi ta bar dakin.
_____________yana fita daga shiyan Kaka kai tsaye shiyan Ammin shi ya shiga,tana zaune a falo tare da Amira dake ta faman ja mata ƙafa,
Amsa Sallamar shi tayi fuskarta dauke da fara'a na farin cikin ganin ɗan nata,
Zama yayi saman shimfidaddiyar darduma dake zagaye da kalon a maimakon zama kan kushin yana karbar ƙafarta da Amira ke matsawa,
Ita ma ganin haka yasa ta sakar mashi tana gaida shi ta bar falon falon ta nufe shiyan Goggo,
"Barka da safiya Ammi"
"Da fatan ka tashi lafiya?
" Alhamdulillah"
Shiru ne ya ratsa falon na ɗan wani lokaci kafin ta katse shirun ta hanyar faɗin "ya jikin nata?
" Alhamdulillah "
Ajiyar zuciya ta sauke wanda ke nuna damuwar da take ciki"yanzun dole sai mun jira?
"Umm"
Girgiza kai tayi"sun iso?
"Eh tun dazu,suna masauki "
"Kaje ka kai su,zuwa anjima zamu haɗu"
Cigaba yayi da mammatsa mata kafa"insha Allah "
Sai da ya kammala sannan ya mata sallamah ya fita domin zuwa Hotel din da ya saka suka sauka.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*72*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Yana fakawa a harabar Hotal din ya fito daga cikin motar,sai dai bai shiga ba dan sam baya ra'ayin shigar,
Daukar wayar shi yayi ya shiga wurin kira,kafin naji ya amsa Sallamah,sai kuma yace"gani a harabar "sai kuma ya sauke wayar yana sauke ajiyar zuciya tare da jingina a jikin motar,
Ganin duk wanda yazo wucewa sai ya kalle shi wasu harda juyowa ne yasa ya saka facing cap din dake hannun shi ya saukar dashi da kyau ta yanda ba zaka iya ganin idanun shi ba,
Tunda suka fito suke waige_waige ko zasu hango shi,
Sai dai rashin sanin kamannin shi yasa dole sai da Abdulmajid ya ƙara kira yana jira yaga ta in da zai hango shi,
Inda yake tsaye yana iya hanzo zaratan samari masu jini a jiki wadanda ke dan jujjuyawa alamun nimar wani,hannu ya daga masu daga in da yake "ka juya damar ka gani nan ina daga maku hannu"
Da sauri ya juya,ai kuwa yana hango shi yace"mu je gashi can"
Tun daga nisa suke kare mai kallo tun daga kan takalmin kafarshi har zuwa bakin hular dake kanshi wanda bai basu damar ganin fuskar shi ba,face farin fatar hannun shi dake baiyane saboda rigar hannun ta ba mai tsayi bane wanda hakan zai tabbatar ma da mai kallonshi shi din fari ne tas,sai kuma zaro_zaron yatsun hannun shi dake dauke da zobe guda daya,
Suna isowa inda yake hannu ya mika masu tare da kara masu Sallamah cikakkiya,
Amsawa suka yi suma sannan suka yi musabaha,
Bude masu kofar baya yayi "Bismillah"
Sai da suka kalli juna kafin dai su shiga kamar yanda yayi masu nuni,
Juya sitiyari yayi ya bar cikin Hotel din dasu,
Tunda suka dauki hanya babu wanda yace ma ɗan uwansa komai,kowa da abinda yake rayawa a zuciyar shi,
Ganin an dube masu wani katon Get ne yasa suka ɗaga kai suna kallon zanen rubutun dake rubuce wanda aka rubuta da manyan harafi,*Jiddarh Hospital*
Asibitin makekene na gasken gaske,domin Asibitin hawa biyar ne bayan kuma wasu manyan ɓangarori dake gefe,gashi ta ko ina ka juya yaji ado da furanni koraye masu saka nishaɗi da sanyaya zuciya,
Ta ɗayan gefen kuma babban wurin ajiye motoci ne in da anan yayi parking sannan suka fito,
Yana gaba suna biye dashi a baya har suka doshi wani babban wuri da suka ga an rubuta Restaurant,
Suna shiga ya saka hannu ya zame hullan dake kanshi ba tare daya juyo ba ya nufe wurin wani mutum dake tsaye a babban teburi wanda daga dukkan alamu daga nan ake ajiye odar,
Su dai basu san meya faɗa ma mutumin ba,sun dai ga cikin girmamawa da rawar jiki yake amsa mashi kamin ya fito yaje ya buɗe masu wani kofa dake cikin babban wurin cin abincin,
Sai lokacin ya juyo inda suke tsaye"Bismillah " Kalmar da ya kara fitowa bakin shi kenan,yayin da su kuma kowa da abinda yake rayawa a ran shi game da wannan fuskar,
Bin bayan shi sukayi har cikin wani karamin falo wanda ya ji kujeru manya da kayan kallo,daga dukkan alamu daki na musamman ne,
Zazzaunawa suka yi suna kara nazarin dakin,cikin lokaci kankani aka cika masu gaba da kayan motsa baki,sai dai ba wanda ya taɓa komai domin ba shi bane a gaban su kamar yanda shi ma ya sani,
Murmushi ya saki mai sanyi wanda sai lokacin suke ƙara ganin asalin baiwar kyau da Allah ya mashi,
"Ni Suna na Suraj kamar yanda na faɗa ma Abdulmaj a waya,sannan ni Miji ne ga ƙanwar ku Ummu Salma,shima kamar yanda na faɗa masa" Dan shiru yayi na sakanni kafin cikin sanyi muryar nan nashi mai fita a natse yaci gaba da faɗin "Nasan duk abinda ya faru da ita a baya,har dalilin barin ta gida,sai dai kuma a lokacin da zuciyar ta yayi sanyi take jin zata iya karɓar ƙaddarar ta,a lokacin shi kuma Ubangiji yayi nashi ikon ta haɗu da hatsari wanda ba na ce ba,idan ta farka zata faɗa mana me ya faru a wancan ranar,sai dai har yanzun bata farka ba tana hali ne na doguwar suma,
Na so a ce ba zan sanar daku ba har sai ta samu sauƙi,sai dai na kasa domin kome yana hannun Allah ne ba hannu na ba,shi yasa na yanke shawar gaiyatarku nan domin ku ga kanwar ku"ya karasa fada yana dago kai domin sanin a wani hali suke ciki.
Hawaye ke sauka daga cikin idanun su babu kakkautawa,yayin da Abdulmajid ya sauko daga saman kushin ɗin da yake ya karaso in da yake,tsugunnawa yayi akan gwuiwowin shi ya rike hannun Suraj"Bawan Allah duk da ban sanka ba,ban San a ina ka haɗu da kanwar mu ba!sai dai muna matukar yi maka godiya da kasancewarka mijinta!muna matukar maka godiya da karɓar ta da kayi bayan sanin kome dangane da ita!muna kuma gode kama daka tuna damu a matsayin ƴan uwan ta a wannan lokacin!wallahi tun jiya daka faɗa mana ba mu kara samun rintsawa ba da natsuwa!dan Allah ka kaimu mu ga ƙanwar mu"
Mikewa yayi yana mikar dashi"kai tamkar yaya kake a gare ni,dan Allah ka tashi, tunda har ka ga na kira ka ai dole ne na kaiku in da take "
Share hawayen fuskar su suka yi suna ƙara yi mashi godiya,
Tare suka fito suka nufi asalin cikin Asibitin,
Abin mamaki duk inda suka bi a cikin Asibitin cikin girmamawa zaka ga manyan likitoci na gaida shi a haka har suka isa hawa na biyar in da anan take kwance,
Wasu Nurs ne da suka zo giftawa suna biye da wata Doctor a baya suka ga ta gaida shi cikin girmamawa amma hannu kawai ya daga mata ya wuce,dan ya gaji da ansa gaisuwa tun daga hawa na daya,
Duk da kallo suka bishi,yayin da daya daga cikin su tace "Ma wannan sabon likita ne?
Murmushi ta saki tana bin bayan shi da kallo har suka bulle ma ganin ta,
Girgiza masu kai tayi" Umm umm"
"Ba likita bane shine muka ga kin gaishe shi cikin girmamawa"
"Ba likita bane,shi ɗin jarumin Miji ne da duk wata mace zata yi alfaharin kasancewar sa miji a gare ta,shi din jarumin miji ne da sai mace mai sa'a zata taka matsayin amsa sunan matarsa,shi din jarumin miji ne da zai iya yin komai domin matar sa,shi din jarumin miji ne da zai iya sadaukar da ko nawa ne domin iyalansa,shi din shine Young Ustadz karamin su babban su,"
Cikin tsananin mamaki suke kara bin hanyar da kallo kamar zasu kuma ganin shi
"Waiyo Allah gaskiya ashe yafi kyau a fili,kai kaga mutum kamar bugun injin"
Dayar ce tace"to me yake yi a asibiti?
"A jiya aka kawo matar shi ba ta da lafita daga Legas,amma kunsan wani abun mamaki?
Duk girgizar kai suka yi,
" A jiya da daddaren ya siya wannan Asibitin a kan miliyoyin kudi,ya kuma ƙara ma duk wani likita dake aiki a wannan Asibitin Albashi,duk da akwai kayan aikin da za'a ma matar shi aiki sai da ya kara yin odar wasu daga ƙasashen waje sababbi na zamani wadanda a kanta za'a fara aiki dasu,kunsan irin farin cikin da duk wani likita dake Asibitin nan yake ciki saboda shi?maganar gaskiya munji daɗin kawo wannan Zinariyar matar tashi wannan Asibitin,dan haka daga yanzun duk inda kuka gan shi ya zamo abin girmamawa a wurin ku,domin mutane da yawa zasu amfana saboda shi"
Dayar ce ta rungume hannu a kirji cikin shauki take faɗin "waiyo Allah ina ma ace ni ce wannan matar tashi,dana tsula tsiya a duniya"
"Sai kuma Allah yayi ko me sharan gidan shi baki zama ba,com on Jare kuxo mu tafi"
Bin bayanta suka yi suna masu fadar abubuwa da dama a kanshi,yayin da shi kuma ko sanin suna yi bai yi ba.
_____daga bakin kofar suka tsaya suna kallon kanwar tasu dake wance bata da maraba da gawa face ta hanya daya wato numfashi wanda yake fita a hankali,
Hankalin su ya tashi sosai da ganin halin da take ciki,duk yanda suka so su daure ma zuciyarsu kasawa suka yi,sai da suka dinga zubar da hawaye yayin da abubuwa masu yawan gaske ke dawo masu a ransu game da rayuwar su na baya daya shuɗe,lallai dan Adam ba abakin komai yake ba,
Basu jima sosai a wurin ba yace su tafi domin ko da ma sun tsaya babu wani abunda zasu iya yi mata,dan haka dole suka fito suka bar ta ba dan ransu yaso ba,
Yanzun ma a motar shi suke sai dai bai nufe Hotel din da suka sauka da suba sai gidan shi daya kai su,
Abdulrahman ne yace"Kanin mu nan ina ne"
Murmushi yayi jin sunan da ya kira shi dashi"nan gida na ne "
"Ai da ka maida mu Hotel kawai" Cewar Abdulmalik
"Ta yaya zaku zo har in da kanwar ku take ba tare da kun shiga gidan ta ba,duk da