Showing 129001 words to 132000 words out of 159134 words
Chapter 44 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
*Bayan Kwana biyar*
Tun daga wannan lokacin bata ƙara saka shi a ido ba har yar yau da aka sallame ta,
Suna cikin motar da zai maida su gida sai gani tayi sun doshi hanyar gida kaka
Da sauri ta juyowa"Yaya ina ce Airport zamu wuce daga Asibiti?
"Me zamu yi a Airport?Abdulmalik ya mai da mata da tambayar,
" Gida mana,ina ɗauka Minna zamu koma a yau"
Wannan karon Abdulrahman ne ya bata amsa"mijinki ya buƙaci da a maida ke wurin mahaifiyar sa kafin ya dawo"
"To ku kuma fa?
" Mu yanzun haka jirgim mu na kasa zuwa ƙarfe hudu zamu wuce"
Aikuwa kamin ya gama rufe baki ta fashe da kuka tana kankame hannun shi"ni dai wallahi ban yarda ba,babu in da zaku je ku barni,kafar ku ƙafa na,babu in da zan zauna ni gida zan je,"
Shafa kanta yayi shima yana jin babu daɗi a ranshi,dan maganar gaskiya yaso su wuce da ita,sai dai ba zai iya rokon Suraj wannan alfarmar ba,ya lura yana da dalilin yin haka,sannan ko wannan Alfarmar daya masu na sake kasancewa da ƙanwarsu ai ya masu,
"Ki ƙwantar da hankalin ki,ai ba cewa akayi ba zaki je gidan ba,cewa yayi ki jira shi idan ya dawo sai ku taho tare"
Girgiza kai ta shiga yi tana cigaba kuka"ni dai a'a,yaushe ma nasan sanda zai dawo, Yaya dan Allah ku tafi dani,ina son in ga Mama da su Baba dan Allah "
Yanda take kuka kuma duk sai ta tashi hankalin su,nan suka shiga lallashi amma sam ta nuna bata san da wannan yaren ba,
Koda motar tayi parkin a harabar gidan fita kawai tayi wuce shiyan Ammi ta bar su nan tsaye sake da baki suna kallon ta,
Ko da ta shiga falon Amira ce kawai zaune dan ita ko lura da ita bata yi ba ta shige dakinta na da tana kullo kofar har da saka key tana ci gaba da kuka,
Ya Abdulrahman "baka ganin ya kamata muma Suraj magana yayi haƙuri ya bari mu tafi da Salma?
" Me yasa?
"Wallahi ta bala'in bani tausayi,na tabbatar da tana jin kewar su Mama ne sosai kuma ta saka ran da ganin su"
Ajiyar zuciya ya saukar"ba zamu bari son kanmu yayi tasiri a zuciyar mu ba,na tabbatar tunda ya faɗi haka yana da dalili,kuma tunda har ya iya kawomu gare ta na tabbatar da zai kai ta gare mu ita ma,dan haka mu ƙara haƙuri"
Ganin wasu yan mata na ƙoƙarin geftawa ne yasa ya dan daga murya kaɗan yana faɗin "Assalamu Alaikum"
Juyowa suka yi suna amsawa,
"Muje su mana jagora cikin gidan"
Kallon samarin dake doso su suka yi "Bilki kamar yannin Biba"
"Ta yaya kikasan ko sune?
" Saboda ban manta fuskar na tsakiyar ba"
Kallon shi da kyau Khadija tayi tana dan mun tsinin ta"ya haɗu "
Juya ido tayi tana "ke ba haka nake nufi ba"
Suna karasowa,gaida su suka yi kafin tace "wa kuke nima?
Abdulmajid dake tsakiya ne ta bata amsa" Ko zaku mana jagora zuwa wurin kaka"
"Eh babu matsala mu je"
Suna baya ƴan matan na gaba har shiyan Kaka,
Tsayawa suka yi a ƙofa har sai da suka shiga suka nimar masu izini wurin kaka,
"Wai ku shigo" Cewar Khadijah data fito,
Ita kaɗai ce a ɗakin sai su Balki da ke ciki tare da Nafisa,suma suna cikin gaisawa da Kakan suka fito suka wuce daga dukkan alamu wani wurin zasu,
"Ya masu jikin?ta tambaya,
" Duk sunji sauki Kaka,dan ita Salma ma ina ga tana shiyan Ammi"
"Hakan yayi Allah ya ƙara masu lafiya"Abincin dake gabansu wanda Nafisa ta kawo ta nuna masu" Kuci Abinci "
"To Kaka mun gode" Sun san halin tsofaffi basu son su baka abu kaki ci,dan haka suka buɗe kulolin wanda lafiyayyen dambun shinkafa ne a ciki yaji kayan haɗi,
Dama shi Abdulmajid yana matukar son dambu,dan haka ko suka ci kaɗan shi ya karasa sauran sannan ta kora da ruwa,
Dariya kaka ke masa ganin yanda ya keta santin dambun,har da tambayarsa ko a karo masa,
Yace ta ko shi,
Sun dan jima a gidan kaɗan sai da suka bata labarin duk abinda ya faru,sai dai kuma ba komai suka faɗa mata ba saboda wannan sirrin Ahalinsu ne,wanda suke fatan ya kasance a binne har abada,
Sai dai basu ɓoye mata batun auren Yusuf da ita Salman ba,
Da zasu tafi ta rako su har bakin falo,duk da sun so tayi zamanta saboda ƙafar ta,
Sawa tayi Nafisa ta kai su shiyan Ammi,
Nan ma sai da akai masu iso sannan suka shiga,ita sai lokacin ma ta san cewar Salma na gidan,
Basu wani jima a shiyan ba suka tashi zasu tafi,bayan Ammi ta masu Alkawarin zuwa har gida idan Suraj ya kammala abinda yake yi zasu taho tare da Biba,
"Bari na kira naku ita kuyi sallamah"
"A'a Ammi ki bar ta domin wani rigimar zata saka"
"To shikenan" Ita ma ta rakasu bayan Alkhairin data masu sosai ga kuma na Kaka da suka samu shima,gaskiya hankalin su ya kwanta sosai da mutanen.
Bayan tafiyar su ne Ammi ta nufi kofar dakin ta,ƙwanƙwasawa ta shiga yi a hankali tana kiran sunan ta,
Jin muryar Ammi ne yasa dole ta taso tazo ta buɗe ƙofar tana kauda kanta gefe,dan bata son Ammi taga waɗannan kumburarrun idanun,
Murmushi tayi tana karasa shiga tare da zama a gefen gado,nuna mata kusa da ita tayi"zo ki zauna"
A hankali take takowa kanta a kasa dan Allah ya gani tana girmama matar kuma kunyar ta take ji,
A maimakon zama saman gadon in da ta nuna mata sai zaunawa tayi a kasa kusa da ƙafafunta,cikin sanyin murya tace"Ammi ina wuni"
"Lafiya qlau Salma ya jikin naki"
"Da sauƙi" Ta faɗa tana share hawayen da yaki tsayawa,
"Har yanzun kukan ne?
Ita dai shiru tayi bata bata amsa ba,
Hannun ta tari ko cikin nata,cikin kwantar da murya irin na wanda ake rarrashi ta shiga yi mata nasiha mai ratsa jiki,akan Kaddara da kuma yarda da ita" Kaddara wata aba ce da Ubangiji ke Daura ma bawa domin ya gwada karfin imanin shi,Salma duk wani bawa mai imani da zaki gani a ɗoron duniya tabbas yana fuskantar tashi ƙaddarar,wani za'a jarabce shine ta hanyar Ya'yan shi,wasu ta Matan shi,wasu kuma ta yan uwa ko ya'yan yan'uwa ko kuma miji,
Duka dame zamu kira shi?kaddara wanda muke fatan mu cinye ta hanya mai kyau,
Ke Allah ya jarabce kine ta hanyoyi uku,na faro mijin ki,na biyu mahaifinki,na uku kuma mahaifiyar ki,amma sai gashi a lokacin daya kin manta da Allah da ya jarabce ki yana sane dake ba kuma ya manta dake bane,kin zabi hanyar saba mashi,a maimakon komawa gare shi,kin manta cewar duk in da kika je kika dawo dole wurin shi zaki koma in da yake jiran ki a madaka domin amsa tambayoyi,kin yi zina,me zaki ce masa akan haka Salma,idan da ace a wancan ranar kin mutu ba tare da kin tuba ba me zaki ce masa Salma?
Lallai Allah yana son ki da rahama da har ya nufe ki da tashi ba tare da kin samu wani nakaso ba,wannan na nuna wata dama ce da Ubangiji ya kara baki domin ganin kin share wannan kuskuren da kika aikata,shin me zaki yi game da haka?
Ina mai baki shawara da ki yi gaggawar watsar da komai ki fuskanci rayuwarki,ki kuma ga Allah ki nime yafiyar shi,domin shi gwanine a fagen yafiya,ki dage da yin istigfari ina ganin hakan zai fi idan har kika karɓi kaddara ki da hannu biyu"
Tunda Ammi ta fara magana take kuka tana kuma auna kuraruran ta da lafukanta,
Rungume Ammin tayi tana ci gaba da kuka"tabbas na aikata laifi mai tarin yawa wanda na aikata cikin sani ba cikin rashin sani ba,domin rufewar ido dana zuciya,ina ganin tamkar babu wani wanda yake cikin kuncin rayuwa sama dani,shin kina ganin idan na nime yafiyar Allah zai yafe min?
"Me zai hana,ai shi Allah mai yin gafara ne,dan haka zai gafarta maki,ke dai kawai ki tsarkake zuciyar ki,ki kuma tabbatar ba zaki ƙara komama zunu banki ba"
"Nayi Alkawari Ammi,in sha Allah daga yau na cire komai a raina,sai dai kuma VIP,ba lallai bane ya barni,sannan Suraj....
Yatsa ta saka mata a baki," Karki damu da wannan domin Suraj zai ji da komai"
"Ta yaya aka yi kuka san da batun VIP Ammi,naga shima Suraj yawancin abubuwa baya mamaki a kansu,sannan dama kin san da aikin da ya kawo ni gidan nan tun farko me yasa kika amshe ni?sannan ya akayi kika sani?
Murmushi mai ciyo a saki,wanda iyakar shi fatan bakin ta,
" Abu ne da aka fara shekaru goma sha ɗaya data wuce,har i zuwa yau,kin ga mu ba abin mamaki bane a gare mu,har balle kamar yanda suke tunanin sun san ko wani motsi na mu,to muma kusan haka ne,duk da ba duka ba,
Tun kafin zuwan ki wannan gidan nasan da batun turo ki,a lokacin da suke niman har yar shigo dake cikin gidan a lokaci na basu hanya ta hanyar zubar da man gyada na zame har samu targade a kafa,ta hakan ne suka samu damar shigo dake,
Sun saka kina masu aiki cikin duhu ba tare da sun san ta gefe ɗaya muna muna amfani dake ba,nasan ba zaki manta wanda ya kiraki yake shaida maki ki yi maza ki bar Legas ki koma Abuja domin rayuwar Ummita na a cikin hatsari,tabbas shima yaron mijin ki ne,wanda yake bibiyar dum wani motsi nasu har ma da naki,
Sannan shi karan kanshi wanda yake saka ki aiki da sunan VIP,da kuma mutanen dake zagaye dashi dukansu yanzun a tafin hannun mu suke,Domin yanzun Kaka ta farka,dama ita ce cikon shaidar mu,kuma ta tashi,"
Tunda Ammi ta fara magana ta kafe ta da ido,cikin tsananin mamaki,wato a cikin wannan wasan dai ita ce katin wasan da kowa ke bugawa yanda yaga dama ba tare da sanin ta ba,"da yaushe ta tashi"
"Ranar da za'a maki aiki,yanzun haka mijin ki na can"
Lumshe ido tayi ta buɗe "baki bani amsar yanda akayi kija sanni ba,har kome dan gane dani,ina son sanin komai"
"Zaki sani sai dai ba yanzun ba,amma na maki Alƙawarin zan warware maki komai a gaban mahaifiyar ki,a lokacin da muka haɗu,sannan nan da kwana Takwas da za'a shiga ƙoto domin Kaka ta shigar da kara a yanzun haka,amma a London za'a yi shari'ar domin a can komai ya faro"
"Amma an kama su ne?
" Ummm to wannan dai yana hannun mijin ki,sai yanda ya tsara,amma a nasu bangaren basu san yasan komai ba"
"Ammi please waye VIP" Ta tambaya tana tsare ta da ido,
Girgiza mata kai tayi"bana ce ba,amma mu jira har zuwa lokacin da za'a shiga kotu,da idanun ki zaki ga ko ma waye,dan idan na faɗa maki ba lallai ki iya yarda ba"
Tana shirin ƙara jeho mata wani tambayar ta Daura mata yatsa a baki"shiiii no more question,sannan da zaran kome ya kare zamu mai da ke gida,sai dai ina son in zaki koma ki koma cikin mutunci da kyawun gani,dan haka zuwa anjima zamu fara kyaran jikin ki"tana gama fadar haka ta tashi ta fita tana kara jawo mata ƙofa,
Gabaɗaya zuciyarta bata mata daɗi,wato a wannan wasan ita ce a tsakiya,kuma a duhu,amfani dukan su biyu suka yi da ita wurin cin ma burin su harda Suraj,wato tun farko yasan komai,gashi sanadin wannan wasan nasu Ummita ta rasa rayuwar ta har abada,ita ma kuma Allah ne yayi da sauran shan ruwan ta a duniya,da yanzun kuma ba wannan labarin ake yi ba,ita ce babbar mai asara a cikin su,domin ta baro gidan su da komai nata,ta kuma zabe hanyar da take ganin zai fi mata sauki bata san rami take tura kanta ba,
Amma babu komai ko yanzun ta koyi darasi a kan wannan aikin,dan haka zata bi shawarar Ammi ta koma ga Allah da niman tuba,sannan da an gama wannan shari'ar zata koma gida taci gaba da rayuwar ta cikin yannin ta da iyayenta,zata manta da komai ta fara gina sabuwar rayuwar ta,
Da wannan tunanin ta tsayar da zuciyar ta wuri ɗaya.......
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*80*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Da Sallamah ta shigo dakin hannun ta rike da tiren kuloli,ajiyewa tayi a gefe ba tare data ce mata komai ba,ita ma din dai tana zaune ne a in da Ammi ta barta tun dazu,
Ganin har tana shirin fita bata dago ta kalle ta ba yasa ta ɗan dakata"ya jikin naki?
Kara kauda kai tayi tana kwantar dashi saman gado "da sauki"
"Allah ƙara lafiya" Ta faɗa tana fita,ita a da bata son Biba ko kadan tunda ta aure yayan ta,kuma ba tada ilimi,sai gashi cikin lokaci ƙanƙani ta shayar dasu mamaki,ashe da gaskiyar hausawa da suke cewa duk yanda kake ganin mutum karka taba raina shi saboda baka San irin baiwar da Allah ya mai ba.
Bata maci abincin ba sai da tayi barci ta tashi,sannan ta watsa ruwa,ganin lokacin sallah la'asar yayi ne yasa ta dauro Alwallah tayi sallah,ko da ta idar zaman yin istigfari tayi,har kusan ƙarfe biyar da wani abu,sannan ta shafa addu'a ta tashi,dan sau biyu Ammi na aikowa a leko ko ta gama,sai da ta ci abinci sannan ta fita,ganin bata falo ne yasa ta nufe dakin ta,
Sallamah ta yi,daga ciki aka amsa tare da tambayar"Biba ce"
"Eh ni ce"
"Shigo"
Shigowa tayi,nuna mata kan kushin tayi "zauna"
Zaunawa tayu tana kare ma dakin kallo wanda yake a kyare tsaf a ko wani lokaci,ga kamshe mai ni'ima da ke tashi,domin Ammi macece mai matukar tsafta da son kamshi,
Wani dan karamin jakka ta dauko ta zauna kusa da ita tana fito da kayan dake cikin jakkan,
Wasu madaidaitan robobi ne masu kyau a ajiye a gabanta,
Nuna mata su ta shiga yi data bayan daya,
Wannan sabulun wanka ne,dashi zaki rinka yin wanka,wannan kuma man shafawa ne,sai wannan shi kuma zaki dinga cire kwaya daya kina sha ɗaya da safe daya da yamma,wannan kuma ki maida shi ruwan shanki,ba shida wani illa ko side effect,sai wannan turaren da shi kuma na tsugunnawa ne sai na jiki,a duk lokacin da zaki yi amfani dashi za'a kawo maki kaskon,dan Allah ki dage ki yi yanda nace,wanda baki gane ba zaki ga komai a rubuce "ta faɗa tana maida su cikin jakkan tare da mika mata,
Amsa tayi" Na gode sosai Ammi"
"Ki yi ƙoƙari ki shiga ki gaida Kaka"
"To" Ta fada tana tashi,
Daki ta kai kayan ta ajiye sannan ta ɗauki ƙaramin hijabi ta saka sannan ta fita,
A hankali take takawa dan ji take kamar iska zai dauke ta saboda rashin nauyin jiki,
Tana dab da shiga shi yana taji an riƙo mata hannu,
Zabura tayi tana dan matsawa baya kaɗan dan ta dan tsorata,
"Oh Sorry na baki tsoro "
Kallon shi take yi tare da kokarin janye hannun ta,sai dai yaƙi saki, "me haka Nurudeen sake min hannu"
Ajiyar zuciya ya sauke"Thank God baki manta suna na ba"
"Ka sake ni bana son haka,idan wani ya ganmu fa"
"Ai nafi son ma a ganmu kin ga sai a saka wannan hoton mijin naki ya sake ki ni kuma na aure ki"
Daga bayan su suka yi an ce"sakar mata hannu"
Duk juyawa suka yi,ganin wanda yayi maganar ne yasa da sauri ya sakar mata hannu,
Ba tare data ƙara kallon su ba ta saka kai ta shige,
Ita gabaɗaya daga shi Nurudeen din har Shamsuddeen,tun lokacin da shi Shamsuddeen din ya bada shaidar karya a gaban su kaka a kan ita da Suraj ta ji ya fita ranta,ɗan girman da take ganin shi dashi duk ta zube,
Da fara'a Kaka ta tare ta "Habiba ya jikin naki"
Zama tayi kusa da ita"na ji sauki Kaka sai kewar ki da nake yi"
Dariya tayi "ke dai faɗi gaskiya,ko dai kewar mijin ki kike yi"
Nan take ta bata fuska tana shirin yin magana kenan suka haɗa ido Maijiddarh dake zaune,
Nan take ta canja salo zuwa yanayin shagwaba "ban cin ya tafi ya barni da kewar shi,ni fushi nake dashi"
Dariya kaka ta saka"ke da ba kida lafiya ina zai dauke ki yai ta yawo dake"wayar ta dake gefe ne ya shiga ƙara,ɗauka tayi tana miƙa ma ta"dubamin wake kira,dan ban fito da Glass ba,
Ganin sunan me kira kaɗai sai da yasa zuciyar ta girgiza"Suraj ne"
"Yauwa dan Halak ke nan,to ɗauki wayar"
Girgiza kai tayi"A'a ai ke ya kira,ni kin ga ma bari naje amma anjima zan dawo "
Karɓa tayi tana karawa a kunne tana dariya,
Daga can ɓangaren yake tambayar "kaka dariyar me kike yi"
"Ni da matar ka mana,wai fushi take da kai"
Dan murmushi ta saki "me tace na mata?
" Ka kira ta ka tambaye ta"
Dariya yayi "ke dai na baki wannan damar ki lallasar min ita"
"Ja'iri ya jikin Nana A'isha"
"Da sauƙi,gata ku gaisa"ya faɗa yana karama Kakar shi wayar a kunne,
_________kwance take saman gado tana rusar kuka,tunda ta dawo shiyan kaka yanzun kusan mintuna talatin kenan tana abu daya,babu abinda yake kara tada mata hankali shine ganin yanda Biba ta zama jaruma akan idanun kowa,
Jin shigowar Momy bai sa ta tsagaita daga kukan da take yi ba,
Zama tayi a bakin gadon tana dagota "zauna muyi magana"
Kokarin komawa kwance take yi"ni dai ki kyale ni,babu wani maganar da zamu yi da ke"
Wannan karon cikin jin haushi ta ce"idan baki saurare ni ba ta yaya zamu samu mafita? Ƙara dagota zaune tayi,
"Yanzun shi Yusuf ya kuke ciki akan maganar shi?
Jan majina tayi tana sheshsheka"idan na kira wayar shi baya ɗauka,karshe ma sai turomin saƙo yayi cewar ni ba iri ajin shi bace,saboda ya lura ni ban waye ba ban San Me duniya ke ciki ba,"
"Tsinanne,shi har ya isa yace haka akanki,ki kyale shi shi yake da asara"
Kara fashewa tayi