Showing 39001 words to 42000 words out of 159134 words

Chapter 14 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

27 Sep 2025

9767

the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*26*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Kaka ce tace Nafisa ta tsaya ta yi jinyar ta a Asibiti,ranar data cika kwana biyu kuma sai ga A'i ta zo a matsayin yar uwarta,ta karɓi jinyar har aka sallame ta,

Tana zaune kan gado A'i na haɗa kayan su a jakka ta kalle ta"kina buƙatar hutu dan haka na ɗaukar maki izini wurin Uwar ɗakin ki,idan kin ƙara jin sauƙi sai ki koma"

"Babu in da zanje ki mai dani can kawai,domin sai na ƙarasa aikin dana fara"

Ajiye kofin dake hannun ta tayi ta dago tana kallon ta"a haka ne zaki koma wannan gidan,Gara dai ki bari ki ƙara kwari in ba hakaba karasaki zasu yi"

Kauda kai tayi"ko da zan dauki hutu sai na tabbatar na rama abinda akai min"

"To wallahi in dai zaki bi shawara ta gara ki bar batun ramuwar nan,domin banga amfanin ta ba,wannan da kike gane tunda har ya iya tsallake tarkon ki ba tare da ko kwarzane ba ki tabbatar yana iya saukar da duk wani hatsari da jiji da kai irin na ƳAR TSANAR ZINARI"

"Zamu gani" Ta faɗa cikin kwarin gwiwa,

"Ki kalli yanda ya saka acikin kwana uku kika kusa rasa rayuwar ki,kin kuwa ga ma yanda kika koma,gaba ɗaya duk cikar fuskarki ya tsiyaye sai dogon hanci da idanu,to wallahi ki yi a hankali kar a fito mana da gawar ki"

Saukowa tayi daga kan gadon Asibitin "idan kin kammala haɗa kayan ki same ni a waje" Ta faɗa tana barin ɗakin,

Shiru tayi kawai ta bita da kallo,tausayin yarinyar take yi,domin ta tabbatar da bata san irin girman hatsarin da take saka rayuwar ta aciki ba,
Domin ba ita bace mace ta farko da VIP ya bama wannan aikin ba,ita ce ta shida,
Gaba ɗayan su sunyi aiki ne a sashi mabanbanta a cikin gidan,sai dai wahalhalun dake tattare da zama acikin gidan ke koransu,wasu basu ma samu damar koda magana bane da shi uban gaiyar,Ustaz,balle su samu damar nufar shiyan mazan gidan,acikin su ma akwai waɗanda ko ganin shi basu taba yi ba agidn, a haka kuma ko waccen su da kalar wahalar da zaisa su bar gidan,sai dai da sun fito da kwana biyu ake niman su a rasu sai bayan wani lokaci aga gawarsu,ba dan komai ba sai dan kawai sun san sirrin abinda ake hari,
To amma ita nata lamarin da ban ne tunda gashi har ta samu nasaran sanin wani abu,
Ta san ko da tayi nasara VIP ba zai taba barin ta ba,
Ajiyar zuciya ta sauke sannan da ɗauki jakkan ta fito,
Dole haka ta maida ita gidan ba dan tayi ni ya ba,
Ammi ce tace taje daki ta huta ta bata hutun kwana huɗu ta kara hutawa,
Sosai tai mata godiya sannan ta koma ɗaki,tana tunanin ta hanyar da zata dauki fansa dan ita bawai zata ƙyale shi bane,

Washegari tunda ta tashi,take cikin wani irin yanayi na rashin farin ciki da walwala,zuciyar ta gaba ɗaya zafi yake mata,har balle idan ta tuna yau wace rana ce a gare ta,
Ranar ko shiyan kaka bata shiga ba,sai wuraren bayan sallar La'asar sannan ta fito,ta bayan ɗakunan su nan ta je ta samu wuri ta zauna,

Fito da kwalin sigarin dake jikin ta tayi ta kunna daya,kafin wani lokaci har ta gama dashi ta kuma kunna wani,a haka sai da tasha kara biyar ba tare da taji komai na daga damuwarta ya rage ba,sabaninda da ƙara daya kawai take sha,

Tana ƙoƙarin kunna na shida ne sai ga kira ya shigo karamin wayar ta,dagawa tayi ta kara a kunne ganin me kira,
Sunan ta aka kira"Babi "

"Ummm" Ta amsa mata,
"Ina fata kina lafiya?
" Ummm"
"Ar you ok"
Share wayen daya zubo mata tayi da bayan hannun ta"yes I am fine"

Dan shiru ne ya ratsa tsakani kafin kuma tace"karki yi kuka,dan Allah kar kiyi shaye-shaye,don't forget were you ar,karki manta me ya kawo ki,nasan yanda kike ji yanzun saboda yau ne,amma karki bari tuna hakan ya raunata zuciyar ki,karki sha Sigret da yawa"

Dan jan majina tayi kaɗan "is really painfull,ji nake kamar zuciya ta zata buga,na kasa manta komai,na kasa anytime i remember is really destroy me,bana son ina tunawa amma it keep coming to my mind and ring is to my head,"

"Na sani,yanzun me kike yi?
" Just setting"
"Me a hannun ki?
Kallon Sigret din tayi"Segret "

"To ki maida shi cikin kwali sannan ki kashe wanda kike sha ki rike sai ki zubar in da ba za'a gani ba"

Kamar yanda faɗa mata haka tayi sai dai kwalin na ajiye a gefen ta,"Ummi ta"ta kira sunan ta,

"Na'am Biba"
"Da zaran na kammala wannan aikin nawa,ba zan kuma yin wani aiki ba,zamu bar kasar nan mu je wani wuri in da babu wanda zai ƙara takura mana,in da ba zamu haɗu da wadanda suka san mu ba balle suyi threatened din mu"

"To Biba idan kina son haka ya kasance sai kin watsar da komai kin maida hankali kin cika aikin ki"

Share hawayen idonta ta kuma yi"zan yi haka,cikin satin nan duk hanyar da zanbi zan bi domin na kammala"

"Yauwa Biba,shi yasa nake son ki,saboda nasan zaki iya"

"Thank you for supporting me all the time,and encouraging me,you are my only Family in this world"

Daga nata ɓangaren ma share hawaye take yi,ta san halin Biba sarai,ta san matsalarta,kamar yanda ita ma ta san nata,Biba ta dauke ta ta maida ita danginta alokacin da take tsaka da niman taimako,ta bata muhalli,ta maye mata gurbin duk wani abinda ta rasa,
Sun maida junan su Ahalin juna,shi yasa ta riga tasan wannan wani irin rana ne a wurin Biba"ke ce farin ciki na,kuma gata na,dan haka ki yi sauri ki kammala ina jiran ki"

Jinjina kai tayi"sai munyi waya"tana gama faɗar haka ta sauke wayar.

Maida kanta tayi ta jinjinar da jikin iccen,idanun ta a lumshe,

Wani irin ni'imtaccen kamshe ne yake shiga hancinta,wanda ta tabbatar da a jikin mutum ɗaya kadai take jin wannan kamshen,
Tuna wanene yasa da sauri ta buɗe idanun ta,wanda cikin rashin sa'a sai a cikin nashi,

Yana tsaye a gefen ta ya zuba mata ido kamar mai nazarin ta,
Da sauri ta ɗauke kai dan ba zata iya jure kallon cikin waɗannan idanun shi ba,
Hannu tasa da sauri tana goge ragowar hawayen dake kwance saman fuskarta,
Tuna kwalin Segret din dake gefen tane yasa da sauri ta zabura tana daura hannun ta saman kwalin,
Ƙara dago ido tayi dan ganin ko yaga kwalin wanda bata fatan haka,
Sai dai har yanzun idanun shi na kanta ne bai dauke ba,
Kara kauda kai tayi a karo na biyu ta dauke kwalin Segret din cikin dubara ta tura a hijabin jikin ta,
Mikewa tayi ba tare data ce mai komai ba tana ƙoƙarin barin wurin,
Cikin muryar nan nashi mai ratsa kashi da barko taji yace"wannan ya zamo karo na karshe da zan kuma ganin inuwar ki a tanan ɓangaren "yana gama fadar haka ya juya yayi tafiyar shi cike da mamakin ta,shi fa ya fara zargin Something is not right about this girl,ya dawo daga masallaci ya shiga bayi domin yin wanka,amma gabaɗaya kasawa yayi saboda bayin shi dake warin hayaƙin Segret,domin windon a buɗe yake,
Yana lekawa shine ya hango ta.

___________Niger State.

Kusan mintuna biyar kenan yana tsaye a kanta amma bata San ma da zuwan nashi ba,
Dukawa yayi a hankali ya saka hannun ya amsa Album din dake hannun ta,wanda take kallo tana shafa hotunan ciki,

Dago kai tayi ta kalle shi,
Hannu yasa ya shiga share mata hawayen dake bin Fuskarta,"har tsayin wani lokaci zaki ɗauka kina zubar da hawaye Mama?

Dagowa tayi ta kalle shi da rinannun idanun ta"har zuwa sanda zata dawo cikin rayuwar mu,ko da ta dawo har sai na nime yafiyarta ta kuma yafe min sannan zan iya samun salama "

"Mama yau tsayin shekara biyar kenan,rabon da muga farin ciki acikin idanun ki,gashi sanadin yawan kukan da Kike yi idanun ki na son ya samu matsala,dan Allah Mama koda sau daya ne,ko da na rana daya ne muna son muga farin ciki a fuskokin ku,muna son muga dariya a faskarku"

"Abdulmajid" Ta kira sunan shi,
Rike hannun ta yayi"na'am Mama"

"Tun daga ranar da ƙanwarku ta saka kafa tabar wannan gidan ta tafi da duk wani farin ciki namu,kai ma ka sani,ko da nace zan ɓoye bakin ciki na nayi dariya a fili,to is feck,abu ne da bazan iya ba," Share hawayen ta tayi"yaune ranar zagayowar haihuwar ƙanwarku,yaune kuma naran da tayi aure,"idan da ace tana nan kamar shekarun baya,da tunda Asuba zata fara bi ɗakunan ku tana tayar daku akan sai kun bata gift na karin shakara,haka za ku korata waje ku saka sakata a ƙofar ku,amma duk da haka sai ta hanaku barci da buga ƙofa,har sai ta saka kun fito ba tare da dakun shirya ba,koda tayi aure ma haka sai dai tai ta damun ku da waya tunda Asuba,idan kuma kuka kashe wayoyin ku sai ta kirani tana korafi,"

Dariya yayi kaɗan shima yana share nashi hawayen,"wani lokaci idan na tuna soyayyar dake tsakanin mu Mama,sai naga kome yayi zafi bai kamata Salma tayi irin wannan nisan ba"

"Na tabbatar kuma saboda kun danne zuciyar ku ne shi yasa baku tafi kun barni ba,sai dai ku yi haƙuri domin wannan shine tawa Kaddaran," Ta karasa faɗa tana fashewa da kuka,

Rungume ta yayi ajikin shi yaya lallashinta sam baya son hawayen ta ya karu,dan haka ɗauko Album din da ya ajiye a gefe yayi ya buɗe "Mama kin ga nan hoton salma ne lokacin tana shekara biyu,a lokacin ta fara iya magana,kin tuna ba tada aiki sai na cizo,ko hannunka ka kuskure yayi hanyar bakin ta saita kai maka cizo,in kuma kaki yarda ta dinga kuka kenan tana binka"

Nan take ta shiga shafa hotun murmushi mai tattare da hawaye yana bin fuskarta,
Ko a cikin ya'yan ka Ubangiji kan jarabceka da son daya daga cikin su,wanda zaka ji duk kafi son shi,to su nasu gabaɗaya soyayyar akanta ne,domin ita kadai ce mace acikin su hudu.

_______Kano

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*27*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

______________Kano.
Ganin ta gaji da zaman tunani ne yasa ta fito falo domin taya Amira yin girki,sai dai koda ta shiga kicin din kin yarda tayi ta bari tayi aiki, wai ta bari ta ƙara jin sauƙi,
"To ki bari na taya ki koda ƙyara ganye ne" Ta faɗa tana jawo kujeran kicin din ta zauna,

"So kike Ammi taimin faɗa?
" To ai tana ɗaki "
"Yauwa abunda za'ayi kawai shine ki shiga dakin Abu ki taya ni kyarawa kinga kafin ta sauko kin kammala"

Cikin sauri tace "na amince" Dan ji ta yi kamar ta kama kumatum Amira ta sumbace ta,

Nuna mata ɗan key din tayi"gashi nan ki ɗauka sai dai ki yi sauri"

Daukar makullin tayi,tana barin kincin din da sauri,cikin tsananin zakuwa da kuma Addu'ar Allah yasa ta dace,

Tunda ta shiga falon ta dafe Kwankwaso tana ƙare ma ko'ina kallo,ta ina zata fara,daga kan durowoyi ta fara bincike har karkashin kujeru,sai dai duk bata ga komai ba,tana yi tana share dakin tare da gogewa sama sama dan kar a fahimta,
Hannu tasa tana ƙoƙarin murda hannun kofar data gani,ta ji daddadar kamshin nan na tashi,
Bata juyoba taci gaba da murdawa ko Allah zai sa ya buɗe,
Daga bayanta ta ji ance"me kike yi"

Tsabar tsoratan da tayi batasan sanda ta yar da tsintsiyar dake hannun ta ba ta makale jikin bango tana dafe kinji,
Kallon shi take cikin jin haushi wai me yasa shi baya sallama ne,kawai sai dai kaji kamshin shi,

Ƙara jeho mata wani tambayar yayi"what ar you looking for?

Ba tare data bashi amsa ba ta raɓa ta gefen shi tana kokarin wucewa,hannun yasa ya kama gefen hijabinta kaɗan "fadamin me kike nima"

Kallon shi tayi ta kuma kalli hannun da ya riƙe ta dashi yanda kasan wanda ya rike kashi"gyaran daki nake yi "
Sake hijabin yayi,babu abinda daya kona mata rai irin yanda ya dauki abin goge hannu ya goge hannun shi gaba da baya ya wurga a wurin saka shara,wato yanda kasan wanda ya taba kashi,
"Nan ba wurin zuwan ki bane kina iya tafiya"ya faɗa yana nufar wurin kofar,tana kallo nan ma sai da ya ƙara gogewa sannan ya saka makulli,
Juyawa tayi ta fita daga falon gabaɗaya dan babu abinda ta samu,sai dai yau dinnan sai ta shiga dakin shi,domin ta ji abakin Amira cewa zasu yi wa'azi yau bayan Isha'i a masallacin kofar gida,dan haka yau kam damarta ce.

Daki ta koma lokacin ana daf da kiran sallah Magrib,wanka tayi ta saka doguwar riga na bacci iya cinya mai karamin wando a ciki,sai ta daura zani a sama,da hijabi,tana jira ayi sallar Isha'i sannan ta tafi,
Sai da ta tabbatar an idar da sallar Isha'i sannan ta fito,
Tana fitowa suka hadu da Nafisa a falo,rungume ta tayi"Biba ya jikin naki"

"Da sauƙi Nafisa"
"Kiyi haƙuri ban samu na koma na duba ki ba,ni ma Baba nane bai da lafiya shine na tafi duba sa"
"Ya jikin nashi?
" Yaji sauki dama wai Maciji ne ya sare shi a gona,amma Allah ta taimaka gidan mu suna bada maganin,sai zazzabi da yayi"

Kankame hannun ta tayi tana jin tsigar gikinta na tashi"waiyo Allah na tsani maciji,kinga ya jikin nashi"
"Yaji sauki sosai ko da na dawo,yauwa muje an aiko ni na kira ki ne"

"Waye?
" Goggo yara"
Sam bata son shiga tsabgar matar nan dan haka tace"me zan mata kuma?

"Kin ga ba ke kaɗai bace,ina ga zata sakamu aiki ne"

Turo baki tayi"duk ma'aikatan gidan nan,sai ni da Bani da lafiya?

Jan hannun ta tayi"dan Allah mu tafi kinga dare nayi"

Ba dan taso ba tabi bayan ta har shiyan Goggo,in da suka same ta a falo tana kallo,

"Yauwa Nafisa ku shiga dakin na ku duba min har kasan gado ni gabaɗaya ma na rasa meke motsi ne a cikin dakin,Allah dai yasa ba bera bane"

Dakin suka shiga suka fara dubawa,
Motsi taji ai kuwa ihu ta saka tana daka tsalle sai saman gado
Dariya Nafisa ta saka"kardar ke ma tsoron beran kike yi?

Leken kasa take yi"duba ta nan naji motsin abu"

Dariya ta kuma sakawa tana nuna ta"kinga leda ne na taka shine kika ji motsi "

Saukowa tayi tana sauke ajiyar zuciya,a haka suka cigaba da dubawa,ganin har takwas da rabi basu gama kwaliman da ta saka suka fara ba yasa ta yanke shawarar fita dan ƙarfe tara ake gama wa'azin,
Kallon Nafisa tayi"bari nage nayi fitsari na dawo"
"To dan Allah ki yi sauri"
Koda ta fita Goggon bata falo Hadiza ce kawai,dan haka bata ce mata komai ba ta fita,
Tsayawa tayi ta duba ko akwai mai kallon ta,ganin ba kowa ata wurin yasa da sauri ta nufe shiyan mazan gidan,

Tsayawa tayi a ƙofar dakin shi tana kallon ƙofar,
Hannu ta saka cikin Aljihun rigar barcinta ta ciro wani ƙaramin kati,
Tana mannashi jikin ƙofar cikin sakon goma sai gashi ƙofar ya buɗe,
Cikin sauri ta shiga ta maida kofar ta kulle,
Kallon dakin take yi yanda yake a kyare tsaf dashi,ga kuma mayataccen ƙanshin nan nashi dake tashi,
Hango wasu takardu tayi a saman table,da sauri ta karasa wurin ta shigo buɗewa tana bincikawa,sai dai takardun duk na wani business da yake gudanarwa a Dubai,sai kuma kimanin kudin da zai kai Biliyan biyu a kudin Najeriya,
Zaro ido tayi tana mamakin wani irin kasuwanci ne haka,
Mai da takardun tayi ta mike tana jawo wani durowa dake wurin,nan ma takardune,tana buɗe wa wani karamin emvelop ya faɗo kasa wanda yake a like,da sauri ta dauka ta saka acikin Aljihunta,dan tunda ta ganshi a like ta san koma menene a ciki me muhimmanci ne,
Daukar sauran takardun tayi tana ƙoƙarin kara buɗe su taji motsi daga bayan ta,wanda hakan yasa ta juya da sauri,
Hmmm mutuwar tsaye tayi yayin da takardun hannunta suka zame suka faɗi ƙasa,
Bugun zuciyar ƙaruwa yake a ko wani sakan,yayin da take jin yanda jinin ta ke hauhawa,idanun ta na ƙoƙarin rufewa sakamakon jirin dake ƙoƙarin ɗaukar ta,

Tsaye yake sanye da farin Singlet fari tas a jikin shi,sai dogon wando baki na jins da kuma towel dake rike a hannun shi wanda hakan zai tabbatar maka daga banɗaki yake,saboda ruwan dake jike a fuskar shi,
A hankali yake ta kowa yana doso inda take,yayin da take tsaye kamar wacce aka dasa a wurin,sai dai duk taku daya da zaiyi haɗe yake da bugun zuciyar ta,yayin da kamshin shi ke kara mamaye hancin ta,yake kara sanar da ita kusancin su,
Yana isowa bai ce mata komai ba ya duka ya kwashe takardun dake zube a bagan ta ya maida su cikin durowar ya kulle,sannan ya dago idanun shi ya zuba acikin nata "kina son na kyale ki?
Da sauri ta jinjina kai alamun eh,
" Idan na tambaye ki kibani amsa kai tsaye,idan kika min karya kuma zan sani"

Kokarin cire idanun ta acikin nashi take yi,sai dai sam yaki bata dama,sai ma kara tsare ta dasu da yayi,wanda ita hakan da yaye shike kara tsorata ta,kallon idanun nashi,jikinta har ya fara daukar ɗumi,

"Me kike nima?

Idanun ta ne suka ciko da kalla domin yaki bata damar saukar dasu,sai dai ba zata taɓa faɗa masa me tazo nima ba,saboda ka'idar aikin sune a haka,
Ji tayi ya ƙara maimaitawa" Me kike nima?

"Kuɗi" Ta faɗa cikin rawar murya,

Taku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login