Showing 150001 words to 153000 words out of 159134 words
Chapter 51 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
Goggon yara sai da aka saka mata ruwa saboda hawan jinjin ta ya tashi,jin Yayan ta ne ya kashe mijinta"
Dan zabura tayi "ya mutu ne?
Dafa kafadar ta tayi" Bayan sun kamashi da shekara uku shine ciyo ya kama shi wanda yayi sanadin rayuwar sa"
Duk da bata sanshi ba,taso ace ko da sau daya ne ta gan shi,
"Karki damu,nasan me kike tunani,Goggon yara macece mai sauƙin kai,sai dai tana da faɗa,baka sanin sauƙin ta sai ka zauna tare da ita,yanzun haka ta san komai game dake,sannan ashirye take data karɓe ki a mayin ya,a cewarta ke baki aikata mata komai ba,kuma ba laifin ki bane da kika zo duniya a haka,itama tayi kuka sosai tace kuma in nima mata gafarar ki,duk abinda tayi maki ki yafe mata"
Girgiza kai tayi"ni dama ban rike ta ba Ammi,kuma bata min komai ba,na gode da karbata da tayi,ina mata jaje da fatan Alkhairi "
"Hakan da kika yi shine dai-dai Salma,domin Allah yana son masu hakuri,
Shi kuma Abbu yanzun haka yana gidan yari,domin washegarin dawowar ki suka turo shi nan tare da kwararrun hujjoji,yanzun haka an yanke mashi hukuncin rama gidan yari har karshen rayuwar shi tare da aiki mai tsanani,Salma gabaɗaya ya bata rayukan ahalin nan,idan kin je gidan yanda kika san babu mutane saboda rashin kwanciyar hankali da farin ciki"
Katseta tayi"Ammi kin je ne?
"Naje na duba Kaka,na tabbatar mata da ta kwantar da hankalin ta ni ban rike ta ba a rai na,kawai wanda yayi laifi ne ake hukuntawa,domin abinda yayi ba irin wanda za'a iya yafe mashi bane,ya aure ni bayan raba ni da mijina da yayi,yasan komai sannan ya tsaya yana cuta ta,yana da mata amma bai taba fada min ba,abubuwa marasa dadi Salma,ina matukar son mijina amma haka sukayi amma da kishi na suka raba mu,suka kuma kashe min su,ta yaya zan iya yafe ma mutum irin wannan,tsayin shekarun dana zauna dashi na zauna ne cikin kunci,rashin tabbas da dana sani tun farko,to amma ya zan yi,dole in jira har zuwa lokaci,lokacin daya dace"busar da iska tayi"na gode ma Allah da komai ya zo karshe,dazu da muka yi waya da Goggon yara tace zuwa gobe za'a sallami Kaka,mu kuma zuwa gobe idan anyi sadakar uku zan koma London saboda Mama"
Ji tayi jikinta yayi sanyi idanun ta sun taru da hawaye "Ammi amma dai zaki dawo ko?
Riko hannun ta tayi" Acan zan zauna saboda Ummi,ita ma tana buƙata ta,sai dai tunda kuna nan zan dunga zuwa lokaci-lokaci in duba ku,sannan ga waya zamu dinga yi kullun karki damu"ta faɗa tana rungume ta.
Ranar bata ƙara saka shi a ido ba har ta kwanta kwanta bacci,
Cikin magagin bacci ne ta ji wayarta na kara,sai dai saboda gajiya da kuma rashin son yin magana a waya da daddare yasa kawai ta kashe wayar ba tare data duba mai kira ba.
Washegari ne da karfe goma na safe aka gudanar da Addu'ar sadakar uku na Baba wanda aka haɗa da na bakwai din Mama,
Bayan kammala Addu'ar sai da suka kammala sallamar baki sannan ya kira ta awaya dan yana son zai wuce ne,ganin ba'a ɗauka bane ya kira layin Ammi,bugu biyu ta dauka da sallamah,
Amsawa yayi yana faɗin "Ammi dan Allah in akwai wani kusa dake ki kice a faɗa ma Salma ta kira ni a waya"
"Babu kowa kusa dani,sai dai in ni zanje na faɗa mata"
Dan murmushi yayi"wane ni na aiki Abin alfahari na "
Itama murmushi tayi"na maka uzuri,yauwa ƴar albarka kaga gata ma ta shigo"
Yana jin sanda ta mika mata wayar tana faɗa mata ga mijin ki zai yi magana dake,
Amsar wayar tayi tana barin dakin,sannan ta saka a kunni,
"Hello"
"Ki same ni a dakin Abdurrahman"
Kallon wayar tayi ganin ga katse,karamin tsaki taja tana komawa ta kai ma Ammi wayar ta,
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*91*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Kamar yanda ya faɗa a dakin Ya Abdul-rahman ta same shi,sanye yake da ƙananan kaya a jikin shi,ta lura ya ɗan yi rama,hannun shi na rike da waya kamar ko wani lokaci,
Zama tayi kusa da shi "barka da safiya"
"Kin tashi lafiya"
"Lafiya qlau"
Ajiye wayar yayi yana fuskantar ta"yau zamu wuce "
"Umm haka naji Ammi ta ce"
"Yaushe zaki dawo"
Dan shiru tayi tana dauke idanun ta a kanshi,"na riga na faɗa maka bazan koma ba,dan Allah ka sauwake min"
Ba tare da ya kuma ce mata komai ba ya tashi ya fita,
Da kallo ta bi shi,ita ba taga wani dalili da zai saka yaki rabuwa da ita ba,tunda ba wai sun shaku bane,koma dai ne zai yi sai dai yayi amma fa ba zata taba komawa rayuwar shi ba,
Itama tashi tayi ta fita,
Ranar ma sai a bakin Aunty Hulaira taji cewar ya wuce,
Dan ita Ammi sai da akayi sallah Azahar sannan ta wuce,saboda zata kwana a Abuja gobe tabi jirgi zuwa London.
Kwana biyu da yin sadaka baƙi na nisa dana kusa duk suka gidajen su,gida ya rage daga ita sai Aunty Hulaira sai kuma mazan,
Kaka ce tace bata yarda Aunty Hulaira ta barta ta zauna a gidan ita kaɗai ba sai dai su dawo Bosso,dan in tana can ita kadai hankalin ta ba zai taɓa kwanciya ba,
Suma su Abdulmalik sun yi na'am da hakan,
Ita kuma sam ba ta so haka ba,tafi buƙatar zama ita ja dai akan zama da Kaka,dan ita Allah ya mata surutu ne,to amma ya ta iya dole ta tattara suka kwasa zuwa Bosso,
Yau tsayin kwana biyar kenan da komawarta gidan kaka,wanda yake dai-dai da sati ɗaya rabon da suyi waya dashi,ranar sadakar uku,
Jin yanda Kaka ke kwalla kiran sunan ta ne yasa dole ta tashi ta fito tana turo baki,
A bakin kofa ta tsaya ba tare da ta iso inda suke zaune saman tabarma ba"gani"
"Ai na ganki,wai ke meke damun ki ne,ace ayi mutum baya sakewa da mutane kullun shi kenan ƙunshe a ɗaki kamar Daudauwa,maza zo ki zauna ki sha iska,irin haka ba shi ke sakawa kafa mutum ya nukushe ba?
Dariya Aunty Hulaira ta saka" Haba Mama sai kace wata tumatur ko Kankana"
"Yo me marabin su da ita"
"Kin ga Salma,zo ki zauna kisha iska qyale Mama"
Takowa tayi ta zauna saman tabarmar "ni wallahi na gaji da zama haka"
"Au duniya ta zo karshe,wato dai faɗa mana kike kin gaji damu gidan mijin ki zaki koma"
Zaro ido tayi"ni da Kaka ba haka nace ba,Aunty Hulaira ni fa kishi ga tsakani ni da Kaka,dan na lura tunda nazo gidan nan ba ta da aiki sai ja na da faɗa "
Hannu ta saka ta rufe baki,dan wannan fadan nasu yafi karfin ta,
"Uwata an kai maki karata banji duka ba"
"Umm,ina zuwa bari naje nasha ruwa"ta fada tana barin wurin,dan wannan faɗar na Kaka da Salma in sun fara sai su saka ka rasa abin faɗa,
Ganin ta wuce ne yasa ita ma tashi ta bar ta zaune duk da tana jin irin kiran da take mata,
Tana shiga daki taji wayarta na ƙara,ko kafin ta karasa ta dauka wayar ya katse wani kiran ya ƙara shigowa,dauka tayi na nazarin number,saboda number na kasar waje ne,
Tasan kila Ammi ce,dan haka ta dauka da Sallamah,
Jin shiru ne yasa ta kuma maimaita sallamar,tana kara tattara natsuwarta,domin haka kawai taji jikinta na bata ba Ammi bace,sunan shi da zuciyarta ta kama ne yasa tace"idan har kasan ba kada ƙwarin gwiwa magana me na kira?
Daga cikin wayar tana jin yanda ya sauke ajiyar zuciya,kafin ya amsa mata sallamar,
Dama kuma yanzun kaka ta gama bata haushi,cikin yanayi na masifa_masifa kamar wacce dama jira take ya kira ta sauke mashi tace"dama ai kai ɗan kyaluwa ne,kana jina ina ta sallamah amma ka kasa amsawa,kawai dan a saka bakin mutum ciyo,"
Jin tayi shiru ne yasa ya kyara zaman shi a ƙasan ya yake zaune saman lafiyayyen darduma,"na baki hakuri ne? Ya tambaya,
Waiyo Allah aikuwa ji tayi kamar ya ƙoda mata mari "ban sani ba,ta yaya za kayi laifi sannan har ka tsaya tambayar ko ka bada hakuri ne,ban sani ba,sannan kar ka ƙara kira na" Kit ta kashe wayar,
A nashi bangaren rike wayar yayi a hannu yana tunanin to lafiya,irin wannan masifa haka me ya same ta,ko dai shi ne ya bata mata rai,
Dafe goshin shi yayi yana murzawa,ko tambayar da yake so ya mata bata bashi dama ba,
Number Abdulmalik ya kira,bugu daya kuwa ya ɗauka,cikin girmamawa suka gaisa,
Dan Allah ko zaka turo min Address din Kaka,da Account number na Salma"
"Ok babu damuwa Bani minti biyar"
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gashi ya turo mashi,
Godiya ya mashi,sannan ya kashe ya kira number Bala.
Ana ta bangaren tana gama wayar Aunty Hulaira ce ta shigo "taso muje ki raka ni Baipass"
"Ina ne kuma Baipass?
" Ohh Allah na gode maka,yarinya kamar ba garin Minna aka haife ki ba"
"Kinsan Baba baya bari muna zuwa ko'ina shi yasa"
"Haka ne,sai dai Baipass din bai da nisa sosai da nan,da ta wurin Al_Amin bread zamu je,"
"Wurin wa?
" Zamu kaiwa Hajiya Kaya ne,sannan Amina ma ta dawo daga Dubai jiya,kila kiga abinda ya maki a can "
Mikewa tayi tana ƙoƙarin cire rigar jikin ta domin ta canja,
Ganin haka ne yasa ta fita ta bar mata dakin dan ta san halinta yanzun ba kunya ne da ita ba tsaf sai ta kwabe kaya a gabanta babu kunya,
Suna fitowa kaka ta kalle da ɗan ƙaramin gyalenta raka ni ganta,ai kuwa tace bata fita dashi,in dai har ba zata saka hijabi ba sai dai ta fasa fitar,
Allah sarki har da hawayen ta kuwa,amma ya zata yi da kaka tunda tana son fita dale ta saka babban hijabi iya guiwa,kalar navy blue,ba karamin kyau ya mata ba,
Adaidaita suka samu a bakin Bosso Clinic suka shiga,
Kallon hanya kawai take yi tana jin daɗi yanda take shakar iska,
Hankalin ta ne yayi nisa wurin kallon wani babban makarantar Sakondiri mai hade da wuraren wasanni manya,filin kwallon ma yanda aka kawatashi kadai abin sha'awa ne,
Nuna ma Aunty Hulaira tayi"nan ina ne?
"Ahmadu Bahago secondary School"
"Amma gaskiya Babba ne"
"Sosai ma kuwa"
Juyowa tayi"yaushe zamu je kasuwa?
"Me zaki yi a kasuwa?
" Kawai dai ina son zuwa ne,kuma ma ai ba a rasa abun siya a kasuwa"
"Sai dai zuwa ran Lahadi lokacin babu cikowar mutane sai mu je"
"Allah ya kaimu"
Har ta ƙofar gidan aka sauke su,wurin gidan Aimajirai,wadanda gasunan suna ta karatu,
Kallon yaran take cike da burgewa,domin fes suke babu wani alamun datti a jikinsu yanda kasan ba Almajirai ba,suna riƙe da Allunan su,
Murmushi kawai take siki,
"Lafiyar ki kuwa kike murmushi ke kaɗai?
Muma mata yaran tayi" Sun burge ni ne,yauwa Aunty mu je na basu sadaka duk da ban fito da kuɗi ba"
Ai kuwa bin bayanta tayi,sai da suka gaisa da Malamin sannan ta ciro yan dubu dubu dake pos dinta wanda zasu kai goma koma sufi ta mika mashi,"Malam gashi aima yara sadaka"
Dodiya ya shiga yi mata tare da saka mata Albarka,
"Malam iyaye na sun rasu dan Allah ka saka su a cikin Addu'ar ku koda ta yau ce kaɗai"
"Insha Allah za'a saka su yarinya,Allah ya barbarkaci rayuwar ku" Da Amin suka amsa,
Tafiya kaɗan suka isa gidan saboda abinda hawa baya iya hawa ta wurin,
Sosai Hajiya ta ji daɗi dan har zungumeta sai da tayi,
Amina ita tayi masu girki,yarinyar nada matukar kirki da son mutane ga hiri yanda kasan ta daɗe da sanin Salma,dama ita Hulaira yar gida ce,saboda Hajiya tana matsayin yarinyar Kaka ce,
Ranar sai dare suka dawo dan a can suka yi sallah Isha'i,,
Ba kamin daɗin wannan fitar ta ji ba,ko ba komai ta siya kaya sosai a wurin Amina,dogayen riguna na yayi,da jakukkuna,sai wani sarka da Agogo,kayan sun mata kyau sosai,haka ma ita ta zaɓar ma Aunty Hulaira,ta kuma biya kudin nan take ta hanyar trasfer.
Suna shiga gida daki ta shige ta cire kaya,kasancewar a kwai bayi a dakin Aunty Hulaira shiyasa ta shiga ciki ta jona ruwan zafi tayi wanka,
Tana cikin saka kaya Aunty ta shigo"zaki ƙara abinci?
Girgiza kai tayi"na koshi sosai "
"To Kaka na kira"
"Um hmm"sai da ta kammala shiryawa sannan ta shiga dakin Kaka,
Zaune take tana tana saukaren labaran da ake yi a gidan rediyon prestige,
Zama tayi kusa da ita" Gani tsohuwa"
"Uwa ki ma tsohuwa ce tunda ajiye irin ki"
"Amma ai bata kai ki tsufa ba,kinga fada min abinda zaki faɗa min dan ni barci nake ji"
"Ai sai ki shake mako shi ki fito da maganar"
Tabe baki tayi ta na hayewa kan gado ta kwanta,"idan na fara bacci kuma karki ta dani "
"Dazu Ɗan Albarka ya aiko mana da kayan abinci da abun sha kala-kala,suna nan a kicin wallahi har babu wurin sakawa dole wasu a dakin baki aka jibga,ko shinfa kadai buhu goma,wannan ai sai ya shakara muna ci, bancin jarkokin manja dana man gyada, in...
Katse ta tayi"Oh dama dan ki faɗa min haka kika hana ni kwanciya,ni kinga sai da safe"
"Oh ba zaki tambaya waye ya kawo kayan ba,to Mijin ki ne sai ki masa godiya idan ya kira"
"Ai ba ni na saka shi ya kawo ba,idan dan Allah yayi baya bukatar godiya"
Duka ta zuba mata a cinya,"wallahi ki fita ido na in rufe "
Ihu tayi tana durowa daga kan gadon"na fasa kwana anan ɗin "
"Dama ban gaiyace ki ba"
Wurga mata wani karamin jakka tayi"kashi nan wai a baki"
Dauka tayi ta fita ba tare data ce mata komai ba tana gunguni,
Zama tayi kan gado ta buɗe dan karamin jakkan,ATM card ne sai karamin wasiƙa,da kayi rubutu wanda bai wuce layi biyu zuwa uku ba,
*idan kina buƙatar wani abu ki yi anfani da wannan katin*
Tsaki taja tana wurga jakkan cikin jakkan ratayawar ta,kome ya mai da ita Oh ho,ya zo ya same ta.
Komawa tayi ta kwanta kusa da Aunty Hulaira tana ja masu bargo..
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*92*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
*Bayan watanni biyu*
Zaune yake a bakin ruwa yayin da ƙafafun shi ke cikin ruwan yana dan motsa su lokaci-lokaci,
Yana kallon yanda iska ke kada ruwa,yayin da iskan ke ratsa duk wani sassa na jikin shi,wanda hakan ke kara saukar mashi da kasala,
Duk da yaji sanda ya zauna kusa dashi hakan bai sa ya juyo ya kalle shi ba,duk da kuwa sunan shi daya kira,
"Suraj"sanin yana jinshi amsawar ne kawai bai yi niya ba yasa yaci gaba da faɗin" Shin kana kallon kan ka a madubi kuwa?wai ko so kake yi damuwa da shauki su kayar da kai?duk da nasan dama kai ba mai jiki ba ne,amma duk da haka ka rame ka rage walwala,kafi son zama kai kaɗai fiye da zama cikin mutane,wai me damuwar ka,a tunani na ni da kai mun zama daya,ina iya faɗa maka damuwa ta,kai ma kuma ka faɗa min naka,amma wannan lokacin kana nuna min ni ba kowa bane a gareka,haka ne?
Lumshe ido yayi yana fesar da iska mai zafi daga bakin shi,yasan maganar Faisal gaskiya ne,bashi da wanda zai tunkara da wannan damuwar,Ammi ma kyale shi tayi,taki cewa komai,
Juyowa yayi suna fuskantar juna"Salma ce"
Shiru yayi yana nazarin wacece ma Salma,sai can ƙwaƙwalwar shi ta kamomai hoton ta"Oh matarka?
Ganin bai bashi amsa bane yasa da sauri ya kuma cewa"me ya same ta,ina fatan ba wani abu ba ne "
Kauda kai tayi kamar mai jin nauyin abinda zai dafa "taki dawowa,a duk lokacin da zan mata maganar dawowa da faɗa muke rabuwa,ta koyi wasu dabi'u wanda ba nata ba ta Daura ma ranta,Yawan faɗa,da saurin fushi,komai ka yi a wurin ta kaifi ne," Shafa goshin shi yayi"na rasa yanda zan yi da ita,"
"To Ammi fa?
" Taki saka baki,wai sai dai in yi duk yanda zan yi"
Dafa kafadarshi yayi "ban taba tunanin akwai macen da zata saka ka tagumi ba haka"
"Ban taba tunanin zan haɗu da mace irin ta ba "
Wannan karon kam sai da ya dara,"Be a Man"
"Idan na kira a waya da tana ɗauka ko masifa ne tayi,amma yanzun kusan sati ɗaya taki ɗaukar waya na"
"To ka kira yannin ta mana"
Girgiza kai yayi"a'a,hakan kuskure ne"
Kyara zama yayi"ni kan Suraj ka taba furta ma yarinyar na cewar kana son ta?
"Kamar ya in ce Ina son ta?
" Kamar dai haka ko kuna waya,ko kuna zaune tun can baya har yanzun ka taba furta mata I Love you?
Lumshe ido yayi ya buɗe"faɗin haka bai da amfani "
Zaro ido yayi"me yasa,ko dai baka son ta ne?
Shiru yayi kamar mai nazarin abin faɗa yayin da ya tsira mashi ido kamar a fuskar shi zai ciro amsa,
Ganin shirun yana niman yin yawa ne yasa ya kara maimaita mai tambayar,
"Ummm,fadin ina son ki ko ina son ka ba wani abu bane mai amfani,zama wuri ɗaya da yin rayuwa tare shi zai tabbatar da abinda ke zuciyar ka harma da irin muhimmanci da matsayi da abokin rayuwar naka ke dashi a gareka,"
"Banki ta abinda ka faɗa ba,sai dai ka sani yawancin mata sun fi son ko da yaushe kana faɗa masu cewar kana son su,kuma suna da matukar muhimmanci a rayuwar ka,ta yu ita matarka tana