Showing 144001 words to 147000 words out of 159134 words
Chapter 49 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
A yau da karfe hudu na Asuba Allah ya karɓa abin shi"
Wani irin shiru ne ya ratsa falon,jira suke suga tayi kuka ko ta saka salati,sai dai ko daya ba ta yi ba sai ma dukar da kai da tayi,
"Baba fa?
" Yana Asibiti a kwance,tunda ya samu labarin rasuwarta"
Mikewa tayi tsaye"mu je ka kai ni wurin shi"
"Ki bari ki huta ko ruwa fa baki sha ba"
Wani irin kallo ta jefa mashi,ba tare da tace komai ba tayi gaba yana biye da ita a baya,
Tana fitowa gaisuwa mutane suka shiga yi mata,sai dai babu wanda ta amsa sai shi dake bayan ta ne yake karbawa,
A wurin parking ne ta iske su Bala zaune suna cin abinci,ganin ta yasa duk suka mike,da hannu tai masa alama a kan yazo,cikin sauri kuwa ya ajiye plate dun dake hannun shi ya iso in da take,
Kallon Agogon hannun ta tayi"ƙarfe biyu yanzun,zamu iya komawa Abuja ku kwana gobe sai ku koma Kano,idan kuma har zaku iya tafiya Kano a yau kuna iya wucewa na gode"
Dukar da kai yayi dan sai yake ganin ta kara masa kwarjini har balle da babu wani digon fara'a a fuskar ta,
"Ubangida na yace mu tsaya dake,duk in da zaki muna iya kai ki,sannan akwai gidan saukar bakin sa a nan garin a can zamu sauka"
"Bana bukatar ku,ku faɗa masa ni nace ku wuce damun ba komawa zan yi ba" Tana gama fadar haka ta buɗe motar da Abdulmajid ke ciki,ba tare da ta kara kallon in da suke ba,
Tunda taga sun doshi hanya har sun wuce Tunga ta san I.B.B Hospital zasu nufa kenan,hakan na nufin jikin shi yayi tsani kenan,
Mai da kanta tayi jikin windo tana hadiyar wani abu mai ɗaci da tauri da ya tsaya mata a makoshi.
Har suka isa Asibitin babu wanda yayi magana a cikin su,
Shi ya buɗe mata kofa ta fito sannan suka shiga ciki,a wani daki na musamman aka kwantar dashi shi kaɗai,
Buɗe ƙofar yayi suka shi,sai dai kasa karasawa tayi in da take hango mutum kwance sanye da Oxygen,
Janyo hannun ta yayi har bakin gadon,
"Roƙon Allah yake yi a koda yaushe a kan kar ta ɗauki rayuwar shi ba tare da ya ganki ba,gashi yau Allah yayi kin dawo"
Ita kanta ba zata iya shaida me take ji ba a zuciyar ta,lallai duniya ba bakin komai take ba,yanzun Baba da ta sani tsayayyen mutum mai nagarta da lafiya shine ya zama haka,shine kwance a nan kamar wani tsumma,shine haka ya koma kamar mai ciyon kanjamau,har tana iya ganin kashin awazan shi,
Lallai Ubangiji ba'a mashi isgili,yanzun ina lafiyar da yake takama da ita,ina kuɗin da yake takama da shi,ina ɗaukakar da yake ganin yana dashi,yau gashi kwance duk abinda yake takama dashi ba su isa su mai maganin komai ba.
Numfashin ta har wani rawa taji yanayi,
Ganin kamar jiri yana ɗibar ta ne yasa ya dauko kujera ya ajiye mata tare da zaunar da ita gaban gado yana ɗaukar hannun Baba dake ajiye ya damka a cikin hannun ta,
"Ki yi masa magana zai jiki"ya faɗa yana barin dakin tare da bar mata dakin,
Ta kwashi mintunan da ita kanta bata san adadin lokacin da ta bata ba a zaune, tana riƙe da hannun shi,jin yana motsawa ne yasa ta daura idanun ta a kanshi,a hankali har ya gama buɗe idanun shi,
" Baba!
Lumshe ido yayi yana buɗewa,
"Baba! Ta ƙara kiran sunan shi a hankali,
Jiyowa yayi ya tsira mats idanu,dan kara matse hannun nashi tayi" Salma ce"
Ta cikin oxygen din ya maimaita abinda ya faɗa,kokari yake yi ya cire oxygen din sai dai ya kasa,
Taimaka mashi tayi ya cire,ta daga gadon kaɗan,
Ƙara rike hannun ta yayi,"kin dawo ne?
Jinjina mashi kai tayi"ka yafe min Baba"ta faɗa tana dukar da kai,
Da kyar yake iya magana,kai da gani kasan yana jin jiki,"na gode ma Allah da ya nuna min dawowar ki,tabbas na cutar da rayuwar mahaifiyarku da naku,gashi ta tafi ta barni,ki yafe min"
Girgiza mai kai tayi "Baba na yafe maku kai da Mama har cikin zuciya ta,ina roƙon Allah ya bar mana kai ko zamu samu sanyi"
Hawaye ne ke yawo a idon shi "ko haka Allah ya dauki raina na gode Salma,ina maki fatan nasara da farin ciki a rayuwar ki"
"A'a zaka rayu damu"
"Ina mijin ki,Abdulrahman ya fada min kin yi aure,nayi farin ciki"
"Baba zan mai da maka oxygen numfashin ka yana katsewa"
Girgiza kai yayi"ki bari nayi magana dake"
"A'a idan ka huta zuwa anjima zamu yi magana,na maka Alkawari"
Ba dan ya so ba ta mai da mashi,
Ranar sai dare suka bar Asibitin,
Acikin mota ne ya kalle ta"me yasa ba ki yi kuka ba"
Ajiyar zuciya ta sauke tana jinginar da kanta jikin Glass"na kasa"
"Ya kamata ki yi domin gudun abin da zai iya haifar maki"
"Ji nake zuciyata ta zama kamar dutse,kamar Baba wani jini dake yawo a ciki,wata kila ni ma lokaci na yana dab ne"
Bai bata amsa ba sai ma girgiza kai da yayi,dole tana buƙatar kuka ko ta yaya ne,shi shaida ne akan yanda suka Shaku da Mama,sannan ace yau bata duniya amma ko hawaye bata zubar ba,Allah kaɗai yasan irin ƙonewar da take yi a ciki,
Yanayin parking a cikin gidan,ta fito ta shige ciki,tunda bata ga motocin su Bala ba ta san sun wuce kenan,
Dakin Mama ta buɗe ta shiga,
Aunty Hulairaw ce ta biyo bayan ta"Ki yi wanka bari na kawo maki abinci "
Girgiza kai tayi"bana buƙata,hutu nake so"
"Amma kin san bai kamata ki zauna da yunwa ba ko?
Cikin tsananin damuwa ta juyo gare ta" Dan Allah!ina son in huta,ki ajiye zan ɗauka anjima "
Fita tayi kawai tana jawo mata ƙofa,gaskiya akwai matsala,ita kan ba zata bari haka kawai ka kashe kanta ba,gara ta faɗama Abdulrahman ya kira mijinta ya faɗa mashi........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*87*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Tana shirin kiran shi kenan sai gata ta fito"Aunty Hulaira,zan sha Tea "
Ajiye wayar tayi"yauwa to bari na haɗa maki"cikin yan mintina ta haɗa mata shayi mai ƙauri,ta kuna zaunar da ita anan falo kasancer sauran yan uwa na ɗayan falon,
Sai da ta tabbatar ta sha sannan ta shiga yi mata nasiha,
Washegari ma bata zauna a gida ba tana Asibiti wurin Baba,wanda ba karamin daɗi hakan ya masa ba,domin ko ba komai ganin ta ya rage kaso casa'in na damuwar shi,
Ranar ma sai dare Abdulmalik ya komar da ita gida,su kansu hankalin su yafi kwanciya akan ta zauna a nan din suna ganin hankalin ta ba zai kwanta ba,
A ranar ƙarfe uku na dare suka samu kiran gaggawa daga Asibiti,
Inna'illahi wa'inna'ilaihi rajiun,kafin su isa Allah ya amshi abin shi,a wannan ranar na Laraba sha huɗu ga watan shida shekara ta dubu biyu da ishirin da uku,
Mutuwar data kara girgiza su da kara masu imani,
Basu faɗa mata ba sai da aka dawo da gawar ƙarfe takwas na safe,
Abdulrahman ne ya jawo Aunty Hulaira gefe"kin faɗa mata kuwa?
Dafe kanta tayi"na kasa,ina tunanin irin halin da zata shiga,har yanzun taki kuka akan na Mama,ka duba ka gani acikin kwana biyun nan yanda ta koma,gabaɗaya tayi rama yanka kasan wacce ke ciyo,bata cin abinci,haka kuma bata bacci,yanzun idan na faɗa mata abinda ya faru bansan me zai same ta ba"
"Dole ne zamu faɗa mata ko ba komai dole tayi sallamah da shi,bari naje na same ta"
Ɗakin ya shiga da sallamah,a zaune ya same ta a bakin gado bata dago ba sai dai ta amsa,
Ya dan jima tsaye a kanta sai dai ya rasa ta yanda zai fada mata,
"Salma" Ya kira sunan ta,
"Na'am" Ta amsa masa,ya kira ta ya kai sau uku tana amsa mashi sai dai ya kasa fadar komai,
Dago shanyayyun idanun ta tayi wandan suka zurma acikin kwanakin da basu gaza biyu zuwa uku ba,tunda yau din ne sadaka ukun Mama,
"Yau mun karasa zama marayu gabaki daya ko yaya?
Sai da ya dan zabura,kafin kuma ya sukar da kai,
Mai da kanta tayi kasa" Na rika na sani tun lokacin da kuka bar gida ƙarfe uku na dare cikin tashin hankali,na sani! Sai dai ka sani ni ba zan zamo maku damuwa ba,ni musulma ce na san hakan ƙaddara tace wanda ban isa in guje mata ba"
Rungume ta yayi yana fashewa da kuka,domin shi kam bai da karfin zuciya,
Sai da yayi kuka sosai tana jin shi amma ita ta kasa yin kukan,
Aunty Hulaira ce ta shigo ta daga ta"mu je ku sallame shi saboda lokacin yayi da za'a mika shi dakin shi na gaskiya "
Ganin kamar tana layi ne yasa ta riƙe mata hannu,a haka har suka shiga dakin shi da anan aka wantar da gawar wanda fuska kawai ya rage a ɗaure,
Duk zama sukaya suka zagaye shi,
Addu'a kowa ya shiga yi mashi da fatan samun da cewa,Abdulmalik da Abdulrahman ne hawaye ke zarya a idanun su,yayin data mai da idanun ta kan Abdulmajid da idanun shi suka yi ja suka kumbura alamun shima yaci kukan,sai ita da take yi wani irin nauyi a zuciyar ta,yayin da idanun ta suka shige ciki sannan suka yi ja yanda kasan wacce yaji ya shigar ma ido haka take jin suna mata raɗaɗi,
Kallon dakin take yi yayin da rayuwar su ke sake dawo mata acikin ƙwaƙwalwar ta,da yanda suka mu'amala dashi a cikin wannan dakin,yau kuma shine yake bankwana da wannan dakin,a hankali ta fara ji fitar numfashin ta na nimar gagaran ta,dakin kuma na juya ma a lokacin daya,
Ta dai ji an rungumi ta ana salati,daga nan bata ƙara sanin abinda ya faru bayan nan ba.
*Washegari*
A hanka ta fara buɗe idanun ta,dakin take ganin yana mata dishi_dishi,kanta na dan sarawa kaɗan,
Hannu takai tana ƙoƙarin dafa kan,sai jin saukar lallausar hannu taji saman goshin ta sannan a hankali ana mata massage,hakan yasa ta mai da idanun ta ta kulle,an dauki mintuna ana mata kafin taji an saya sannan an daga gadon da take sama kaɗan,hakan yasa ta kara dube idanun ta,jin tayi an zauna kusa da ita sannan an riƙe hannun ta,
Kokari take da idanun ta wurin son tantance wanda ke zaune kusa da ita,
Cikin shakakkiyar muryarta da baya fita sosai ta kira sunan shi domin son tabbatar da ko shi din ne "Suraj"
Sumbatar hannun ta dake cikin nashi yayi"Bebin "
"Zan sha ruwa"
Goran ruwa dake ajiye ya ɗauka tare da kofi wanda ke ajiye a cikin Basket din da aka saka kulolin abinci,tsiyaya mata ruwan yayi ya da gata baki daya ya jinginar a jikin shi,ma'ana rabin jikin ta yana saman nashi,
Ƙafa mata kofin ruwan yayi,kirɓa biyu ya bari tayi ya cire kofin ya ajiye,
"Zan kara ruwan"
Girgiza mata kai yayi"zai saki ciyon ciki,ki bari an jima sai ki sha"
Komar da kanta tayi ta jinginar a kafadarsa idanun ta lumshe,kamar minti biyu tayi wani irin zabura wanda da badan ya riƙe ta ba cikin zafin nama, da babu abinda zai hana ta faɗowa har ma taji ciyo,
"Baba" Sunan da ya fito bakin ta kenan,tana ƙoƙarin sauka daka jikin shi,
Duk yanda yaso ta nutsu kin natsuwa tayi sai kokawar sauka take yi,gashi jini har ya fara biyo Cannula dake hannun ta da aka saka mata drip,
Hakan yasa ya daka mata tsawa wanda sai da dakin ya ɗauka,ai kuma nan take ta natsu jin yanda jikin ta ya amsa wani riƙo da ya maka,
Cikin fushi yace"so kike ki kashe kanki?idan wani abu ya same ki fa?ance baki cin abinci,baki bacci,sannan baki yi kuka,me kike son ki zama?
Ita ma cikin muryar kuka tana kwace hannun ta daga nashi"ya same mana,ina rukan ka dani "
"Naji ina zaki je?
" Babu ruwan ka da in da zanje "
Kin bari ta sauka yayi"idan har ba zaki faɗamin in da zaki ba, ni kuma ba zan bari ki tashi ba"
Duk yanda taso kwace kanta kasawa tayi domin da hannu daya kawai ya rike mata hannu,"kalle ni"
Dago jajayen idanun ta tayi ta saka cikin nashi,
"Maman ki ta mutu kwanaki hudu da suka wuce,jiya kuma Baban ki shima ya mutu,dukkan su ba zasu dawo ba,kin zama marainiya,wacce ba tada uwa ba tada uba" Ganin yanda ta nasu tana kallon shi ne yasa ya sake mata hannu yana furzar da ajiyar zuciya,"sun tafi in da ba zasu taba dawowa ba,sun tafi in da babu wani abunda zaki iya yi domin su dawo,haka Allah yaga dama,bai kadarta zaki haɗu da ita ba,ba zaki iya yin komai akan haka ba,zuciyar ki zafi kawai zata ci gaba daya,idanun ki kuma zasu ci gaba da yin ja,wanda hakan ke nuna rashin karɓar ƙaddarar ki,kinki ki karɓi ƙaddara,so kike ki nuna ma Ubangiji ke mai taurin kai ce, ko kuma ke mai taurin zuciya ce,b.....
Gani yayi hawaye sharrr ya sauko daga cikin idanun ta,
Ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauke "wannan shi ake nufi da taushi,idan har zuciyar ka ta kuntata,har ka samu ka saka tayi laushi,to zaka samu sassauci,har ka iya ɗaukar ƙaddara,s....
Duka ta kai nasa a kirji tana fashewa da kuka" Waye ya faɗa maka ban karɓi kaddara ba?kai ba kasa halin da zuciyar mutum ke shiga ba idan ya rasa wanda yake muradin gani,kai baka san wannan kuncin ba"ta kara fada tana kara karfin kukan ta,
Zame hannun ta daga saman kirjin shi yayi ya jawo fito ya daura mata saman cinya sannan ya tashi ya bar dakin,dama wannan shine burin shi,
Ta yi kuka iya yanda take jin hawayen sun tsaya,ta zubar sadu ko zata samu sa ida a zuciya,
Koda ya fita bai yi nisa da dakin ba,asali ma jin gina yayi a ƙofar dakin yana sauraran yanda take kuka mai tsuma zuciya,
A nata ɓangare kara matse filon dake cinyarta tayi,ji take komai na dawo mata sabo har ta da mutuwar Mama,shi kenan ta rasa su har a bada kamar yanda yace.
Koda Abdulmajid da Ammi suka zo,cewa yayi tana kuka su barta tayi kawai kar su shiga,su koma gida shi zai dawo da ita,
Abdulmajid ne yace"ya kamata kai ma kaje ka huta,tun jiya da kuka iso kana nan Asibiti tare da ita,gashi har kwana ka yi anan,kai ka koma da Ammi idan ta gama kukan zan dawo da ita"
Girgiza kai yayi"she is my responsibility,hakki na ne kaje kawai "
Ammi ne tace"mu je Abdulmajid,rai iya"
"To Ammi"
Yana kallon suka wuce,sai kyara zaman shi yayi,
A jiya sun iso ƙarfe tara na safe dan sun samu halartar jana'izar shi,saboda jirgi suka biyu,
Anan suka samu ana ƙoƙarin kaita Asibiti,Aunty Hulaira da wasu mata su biyu ne suka kai ta,su sai da suka dawo Makabarta sannan suka tafi dubata a Asibiti,
Su sun koma gida saboda karɓar gaisuwa shi kuma ta tsaya da ita, to bata farkaba tun jiya sai yanzun,duk da an samu ta farfaɗo daga dogon suman data tafi,sai suka kara yi mata allurar bacci saboda ta samu ta huta.
Ta dauki kusan Awa daya tana kuka kafin tayi shiru dan kanta tana sauke ajiyar zuciya,fuskar ta gaba daya ya kumbura yayi ja,abinka da farar mace,
Buɗe ƙofar dakin yayi ya shigo da sallamah,zama yayi bakim gadon in da take zaune sanye da hijabi,
"How ar you filling?
" Better "Ɗan dagowa tayi ta kalle shi kaɗan" Thank you"
Bai bata amsa ba sai na riƙo hannun ta da yayi yana mikar da ita"mu je gida?
Kai ta gyada mashi,
Yana riƙe da hannun ta suka fito bai damu dak in da suka gibta kallon da ake masu ba,shi ya buɗe mata gidan baya ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga,Bala ya ja su,
Idanun ta a lumshe suke shi yasa bata san hanyar da suka bi ba sai jin tsayuwar mota da tayi,
Shi ya ƙara buɗe mata,sai da ta fito take bin harabar gidan d kallon kafin ta juyo in da yake,cikin shakakken muryarta tace"nan ina ne? Tana kara kollon ko ina,
Bai bata amsa ba sai ma ɗaukarta da yayi kamar wata karamar yarinya ya nufi tangamemen gidan da suke fuskanta,ba tare da ya damu da ma'aikatan shi da ke wurin ba.....
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*88*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Ba ta da karfin da zata ce zata ci musu ko ta tsaya jayayya dashi,dan haka kwantar da kanta tayi a saman faffadar kirjin shi,
Kofar wani daki ya buɗe ya shiga,kai tsaye banɗaki ya shigar da ita,
Zaunar da ita yayi a saman wani kujera dake a cikin lafiyayyen bandakin,tsaftacecce kuma,
Buɗe idanun ta tayi tana bin shi da kallo yanda yake haɗa mata ruwan wanka da zuba duk wani abinda yasan zai taimaka mata wurin saukar da gajiya,
Dawowa yayi ya da gata tsaye,
Hijabin dake jikin ta yake kokarin zamewa ta riƙe "me zaka yi?
Zuba mata idanun shi yayi,kafin ya busar da iska yana riƙo hannun ta," Taimaka maki zan yi,ba wani abu ba,ki yarda da ni "
Ta san shi ta kuma san shi ba mutum bane mai cutarwa,yana da tsayawa akan maganar shi,dan haka a hankali ta saki hijabin ta data kanainaye,
Kanta na katsa,tana jin yanda yake zame duk wani sutura dake jikin ta,sai da ya rage daga ita sai