Showing 87001 words to 90000 words out of 159134 words
Chapter 30 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
ne ya tashi ya fara magana "ya mai shari'a ina rokon Kotu idan har wannan karon Barrister Ummu Salma ba ta kawo kwakkwaran hujja ba ina rokon Kotu data yanke ma Suraj hukunci kisa kamar yanda yama Jesica,wanda hakan zai zama izina ga masu hali irin nashi da kuma shi kanshi,na gode ya mai shari'a" Ya fada yana zama irin na takama alamun zamu ga yanda zaki yi,
Mikewa tayi tsaye ita ma"kamar yanda ɗan uwana Barrister ya faɗa ni kaina ba zan so na bata ma kotu lokaci ba,kuma ina rokon kotu duk wanda yake da hannu a cikin wannan shari'ar kotu ta yi gaggawar kamashi ta mai hukunci,sannan abu na karshe shine ina son gabatar ma kotu da wannan ɗan ƙaramin Video nawa kashin na kuma gabatar da wani shaida "
Ɗayan Alkalin ne yace"Kotu ta baki dama"
Masinja ne ta amsa ya haɗa a babban kayan kallon dake cikin Kotun wanda nan take video Manager da mutanen da ba'a gane ko su waye ba suna magana har irin kudin da aka bashi,da sanda aka shigar da gawar dakin daya sauka,har karshen video,
Kowa jikin shi yayi sanyi da ganin wannan video,
"Ya mai shari'a ina rokon kotu ta Bani dama na gabatar da shaidata na biyu"
"Kotu ta baki dama"
Nan ma gabatar masu da Jusif tayi,in da ta shiga yi mashi tambayoyi yana amsawa har ta kammala,
Barrister ne ya tashi yace"ya mai shari'a in ba damuwa ni ma akwai wasu yan tambayoyin da nake son nama Jusif "
Nan ma kotu ta bashi dama,
Sai dai duk irin tambayoyin da take ma Josif domin ya rudar dashi yaki bashi dama,dan ya kwantar da hankali sosai yana amsa mashi kamar yanda ita ta faɗa mashi hakan na iya faruwa,
"Ko zaka iya faɗa ma koto ta yaya kaga sanda suke magana har kaji ka kuma gani?
" Kamar yamda na faɗa Abinci aka kira kicin akai shi ne aka ce na ɗauka na kai, shi yasa naji abinda suke faɗa "
"Kenan haka na nufin Labe ka yi masu?
" Eh to kana iya saka shi a matsayin haka,domin kan ba zan musa ba idan ka ce Labe ne,dan na Labe na dauki su Video domin na yi amfani dashi na samu kuɗin da zan yi bikin birne kanwata,to sai gashi wanda aka ma abin shi ya taimaka min wanda har yanzun ni da mahaifiyata muna cin taimakon,shi yasa ban yi manager barazana da video ba"
"Amma kasan kotu zata iya hukunta ka akan abinda kayi,sannan ba kaji a ranka kaci amanar yarenka da ƴan uwanka ka zabi wasu"
Dariya yayi kaɗan "Amana fa kace, karka manta na faɗa maka uzurina amma a cikin su ba wanda ya iya taimaka min ko yaji tausayi na har ta dashi manager da nake ma aiki,har vashi na roka su Bani sai a dinga cirewa acikin Albashi na amma suka hana ni,yan uwana sai zagi na suke yi,shi kuma wanda ka kira bare ba tare daya sanni ba ko ya damu kabila ta ko addini na ya taimakamin da kuɗaɗe masu yawa, lta yaya ina da abinda zai taimaka mashi ba zan taimaka ba,ni ban damu da hukuncin da za'a min,in dai har zai fita to zan jure"
Mikewa tayi"ya mai shari'a Barrister yana ƙoƙarin sauka kan layi,domin babu in da aka ba da dama akan a hukunta mutum domin yayi Labe,tunda ba'a kamashi da laifin yima Manager barazana ba,ina rokon kotu ta watsar da wannan kalaman na Barrister ta"
"Barrister ka kiyaye" Alkali ya faɗa,
"Na gode ya mai shari'a" Ya faɗa yana komawa ya zauna,domin cikin ikon Allah duk wani dubara nashi ya kucce,
"Sakamakon hujjoji da muka haɗa daga likitoci wanda ke nuna babu shatin hannun Suraj a jikin gawar,da kuma hujjojin da Lauyar shi ta gabatar,wannan Kotun ta wanke Suraj Abdul basir daka zargin da take mai na kisan kai,ta kuma bada dama da a kamo Manager Hotel domin a fara sabuwar shari'a a kanshi" Nan take mutumin ya buga wannan karamin sandar nashi mai fitar da dan sauti,
Duk in da masoyan Young Ustadz suke a fadin duniya masu kallon abinda ke faruwa ta online godiya suka shiga yima Allah daya fito masu da matashin malamin su lafiya,
Yayin da ta gefe ɗaya kuma hankalin wasu a mugun tashe yake fiye da tunani,dan wannan shi ake kira da rashe ya juya da mujiya ko kuma suce Shari'a saɓanin hankali.
Nan take Sojojin suka shiga kwance mashi Ankwa,suna mai ba shi haƙuri,yayin da yana fitowa yan jarida suka lulluɓe shi suna mashi tambayoyi,
Ita kuma ta ɗayan ƙofar ta fito dan ba zata iya da wannan cin koson da akayi mai ba idan sun koma Hotel ya huta sa karasa magana,
Tana fitowa lokacin taga su kuma sun shiga wani bakin mota katuwa,kamar kuma faɗa suke yi ranshi a ɓace,
Tana kallo har matukin motar yaja motar wanda bata sanshi ba,wani tunani ne yazo ranta,to me ke faruwa ai kamata yayi ace taga tsananin farin ciki a fuskar su ba tashin hankali ba da faɗa kamar zasu yi danbe abinda bata taba gani ba,to ko kuma sace su za'a yi,
Kai koma menene gara ta bi bayan su,
Dan haka cikin sauri ta karasa wurin motar Allah yasa Direba na wurin yana jiranta sai gashi ta iso,nuna mashi motar dake kokarin barin harabar Kotun tayi"Yi sauri kabi wannan motar"
"To Hajiya"
Nan kuwa ya tayar da motar ya shiga binsu a baya,duk da suna ƙoƙarin ɓace mai amma haka yake ƙoƙarin,
Sai da sukayi tafiyar mintuna Arba'in kafin kuma suga sun shiga harabar wani babban gida,
Dan haka sauka tayi tace mashi ya jirata tana zuwa,
Ita din a wannan harkar ba bakuwa bace,dan haka tana isa tura kofar tayi zata shiga madu gadi suka hanata,
"Wa kike nima"
"Joj ne yace nazo na same su yanzun"
"Bari to na kira shi na sanar dashi zuwan ki"
"A'a ba sai ka kira shi ba ni bari na kira shi nace masa ka hana ni shiga amma ka tabbatar da zaran ya fito ka rasa aikin ka"
Buɗe mata yayi domin daga gani a tsaye take,dama ga Biba da diri kamar ita ta tsara kanta,"a fito lafiya "
Ko kula shi bata yi ba ta shige,
Sai dai tana ganin ta kure ma ganin su ta shiga sanɗa a cikin falon tana son ta duba dakin da aka ajiye su,
To me haɗin su da Joj kuma Baban Jusica,
Wani ƙofa ta dafa tana shirin buɗewa kenan ta ji an buga tebur har sai da ta firgita,kafin ta ji magana ya biyo baya"wannan wani irin shashanci ne,mun yarda da kai akan zakayi wannan shari'ar yanda ya dace,zaka saka shima a kashe shi ashe ma kai a fagen aikin naku ba kowa bane babu abinda ka iya,tunda gashi yar karamar yarinya ta raina maku hankali,"
Dukawa taga Joj din yayi "ka yi hakuri Shugaba zamu samo wani hanyar da zamu gama dashi,"
"Hanyar uwar ka hanyar banza,kasan tun tsayin shekara nawa muke jiran wannan ranar sai gashi cikin awa daya kasa komai ya ruguje"
Wanda ya juta baya ne ya juyo "yanzun me kake son mu aika,dole sai mun sake wani shirin kenan akan sa"
Daga inda take tsaye tana kwashewa a waya saura kaɗan wayar ya zame a hannun ta,domin ganin na farkon da aka kira da shugaba bai tsayar da bugun zuciyar ta ba kamar wannan,dan numfashin ta ma sai da ya tsaya na wucen gadi,
"Tunda har kotu ta wanke shi na tabbatar yau zamu koma gida,dan haka za'a shirya gagarimin hatsari wanda dole zai rasa ranshi a ciki,domin ba muna da wani zaɓi a yanzun ko option"
Daga bayanta ta ji ance "me kike yi anan"
A zabure ta juya tana ɓoye wayar a cikin siket dinta ta baya,
Suma duk fitowa sukayi daga dakin suna mata kallon me kike yi anan,
In ina ta fara"dama naga kun shiga mota ne da wasu mutane shine na biyoku dan na ɗauka sace ku aka yi"
"Biba shin kinji wani abu ne?
" Da sauri ta girgiza kai,a'a ni ba abinda naji dan yanzun na shigo"
Murmushin yayi"Ke Yar tsana ce mai matukar wayau,wacce dama kuma Dama nake jira wanda zan samu na batar da wannan yar tsanar,sai gashi cikin sauki ta kawo kanta har in da nake,"
Bata fuska yayi cikin rashin imani yace"Ku kamamin ita"
Ai kuwa cikin sauri ƙattan sukayi kanta,tafi kusa da ƙofa dan haka fita tayi da gudu yayin da suke binta a baya,ɗayan dauke yake da katon ƙarfi a hannun shi wanda duk cikin su ya fi su gudu,
Cikin sa'a kuwa ganin ba zai iya kamata ba ya daga wannan katon ƙarfen ya buga mata shi sai akan keyar ta,
Duk da ta ji wani abu tsuuu daga kanta hakan bai sa ta tsaya ba daga fita gef din da tayi wanda dama ƙafarta daya na ƙoƙarin karasa fita ne ya samu nasarar buga mata,
Kafin ta kai bakin motar ne ta ji jikin ta ya fara saki kamar ana kokarin janta baya,
Tana shiga ya fisge motar a tsiyace ganin yanda aka biyota ya bar layin dasu,
Sai da sukayi tafiya mai dan nisa kafin yaji
Kiran sunan shi da take yi"Hashi"da kyar ya iya ji domin da kyar maganar ta fito,
"Na'am Hajiya"
"Tsaya ka duba min me ke zuba a kaina"
"Faka motar yayi gefe ya juyo,
Wani irin ihu yayi yana matsawa gefe ganin irin yanda gaba ɗaya ta jike da jini,
" Hajiya kina zubar da jini sosai "
"Ka kai ni wurin Suraj" Ta faɗa da kyar,
"A'a bari mu je Asibiti"
"Ka kai ni wurin shi,akwai abinda zan faɗa mashi,dan Allah"
Gabaɗaya hankalin shi ya tashi,domin ba karamin jini take zubarwa ba,yanzun ina zai ga Suraj,
Yauwa tabbas yana Hotel din da iyayen shi suke,sai dai tafiya ne mai dan tazara ba lallai ta iya jurewa ko takai ba,amma ba yanda ya iya,
Haka ya shiga mota shi bai masan kuka yake yi, dan bin hanya yake lungu da sako saboda gujewa cikowar abin hawa ta yanda zai iya isa da wuri,yanayi yana kallon yanda take sauke numfashi a hankali ta madubi
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*54*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Gudu yake zubawa sosai kamar zai tashi sama,
Cikin hukunci Allah lokaci kankani ya isa Hotel ɗin,yana yin parkin, motar su Dady na tsayawa ita ma,
Da sauri ya karasa wurin da Suraj din ke tsaye yana jiran Dady ya jawo hannun shi domin ya kasa magana sai kuka da take yi,
Shi kuma bin shi yayi dan ya lora da motar da yake mai nuni,
Da sauri ya buɗe bayan motar inda take kwance "Duba ka gani ban San yanda zan yi ba"
Cikin sauri ya kara leka motar da kyau damin tabbatarwa,
Salati ya fara yana kiran sunan Ubangiji duk wanda yazo bakin shi,
A hankali ya ciro ta yana rungume da ita,ganin yanda jinin ke ƙara fita ne yasa cikin tashin hankali ya shiga kiran sunan Dady,
"Me ya same ta,maza saka ta a mota muje asibiti"
Shida ita ne a baya kanta na saman cinyarshi ya tattare da rigar shi da ya cire saboda jinin ya tsaya,
Shafa fuskanta yake yi yayin da hawaye ke fita daga idanun shi yana sauka saman fuskarta,
A hankali ta buɗe idanun ta,wadanda take ji sun ji matukar yi mata nauyi har bata iya ganin shi da kyau,
Ƙoƙari take tayi magana amma ji take makoshinta kamar a kwai a binda yazo ya tsaya a wurin,
Ganin idanun ta sun dan buɗe ne yasa ya shiga kiran sunan ta wanda take jin shi can da nisa,
Bakinta ta buɗe tana kokarin yin magana sai ta kasa fusta komai,
Ya fahince so take tayi magana,
Girgiza mata mata kai yake"please don't live me Beb!stay with me!I have so many things to tell you please we need you,"ya karasa faɗa yana haɗa goshin shi da nata,yayin da hawayen shi ke sauka saman fuskarta,
A hankali yaji saukar hannun ta saman hannun shi dake rungume da ita,
Cikin sauri ya kamo hannun ya sumbata yana ci gaba da sha fuskarta,da zaran ya ga zata lumshe ido,da sauri yake dan jijjigata yana kiran kiran sunan ta tare da faɗin "pls don't close you eyes"yan kara matse hannun ta a cikin nashi,
Zai iya cewa a wannan lokacin ya manta rabon daya shiga tashin hankali irin na wannan ranar,
Duk da yasan ko yaushe komai na iya faruwa dashi ko wani nashi,kai ko lokacin da yaga gawa a matsayin wacce ya kashe bai shiga firgici da tashin hankali ba irin na yanzun,wanda ba komai bane ya jawo haka face ganin ta da yayi lifeless wance a jikin shi,
Allah ya gani tsoro yake ji,yana matukar jin tsoron rasata a karo na biyu,
Ire-iren sambatun da yake tayi kenan har suka isa asibiti,cikin gaggawa likitoci suka karbe ta emergency,yayin da su kuma suke tsaye sun kasa zama,
Gani suke yanda likitocin ke shige da fice a dakin har na tsayin awa daya,kafin wani babban a cikin su ya kira su Ofishin shi,
Nuna masu kujerar zama yayi amma cikin su ba wanda ya iya zama,
"Doctor ya jikin nata? Ya tambaya muryar shi na rawa,
" To yanzun dai ba za mu iya cewa komai ba,domin dai mun yi nasaran tsayar da jikin dake zuba,sannan mun gudanar da bincike wanda ya tabbatar ma na da cewar ta samu tsagewar kashin kai,
Dole tana buƙatar aiki na gaggawa idan ba haka ba tana iya rasa rayuwar ta,"
"Doctor idan har babu wani matsa a fara aikin kawai"
"Ba aikin bane matsala akwai wasu matsaloli da za'a iya samu"
"Kamar me"
"Aiki ne mai makutar hatsari wanda a ko wani lokaci ana iya rasa patient,na biyu idan an samu nasara aikin yana da Complications misali,tana iya rasa ganin ta,ko kuma ta rasa jinta,shi yasa a Nigeria ba ko wani asibiti ake yi wannan aikin ba,amma ke kace?
" Me kake nufin da me kace?ba zan taba yarda ai mata aikin da zata rasa idanun ta ko rasa jinta ba,balle akai ga mutuwa,ba zan iya ba"
"To yanzun me kake son ayi,dole ne cikin biyu ayi da"
"Kawai zan fitar da ita kasan waje,na tabbatar su din zasu iya"
"Kaga ka kwantar da hankalin ka domin duk abinda kasar waje zasu mata muma nan muna da kayan aiki muna da kuma ƙwararrun likitoci,kuma duk inda kaje bayanin daya domin Surgery na ƙwaƙwalwa aiki ne mai hatsari balle irin nata da kashin ya tsage"
Hawaye ya fara yayin da zuciyar shi ke cike da kunci,yana tuna maganar su na karshe da ita a dazu da take faɗa mashi zata koma gida wurin iyayenta,ta yaya zai iya bari haka ya faru da ita har ta rasa ranta,
Rungume shi Dady yayi"ya isa haka addu'a zaka mata ba wai ka kama kuka ba kamar karamin yaro "
Shima rungume Dady yayi"bana son na rasa ta "
"I know,sai dai ba muna da wani option"
"Yaushe za'a aikin?
" Nan da awa ishirin da tara,daga nan zuwa gobe da yamma kenen,domin akwai wasu gwaje-gwaje da za'a mata"
Jinjina kai yayi"dan Allah ka yi min ƙoƙarin kar ta rasa komai nata,ka yi min Alkawari "
"Na maka Alkawarin zan yi iya kokari na,kai ma sai ka dage da addu'a"
Hannun shi Dady ya yawo suka fito"tunda har tana karkashin kulawar likitoci kuma ba zasu bari a ganta ba,ya kamata kaje gida ka yi wanka ka huta"
"A'a ba zan iya tafiya ba Dady"
"Ba nason musu tashi muje"
Suna fitowa suka hadu da Hashim da sauri ya karasa in da yake"me ya faru dazu,wa ya aikata mata haka?
"Ban sani ba nima,amma abu ɗaya na sani shine daga Kotu dazu ina tsaye sai gashi tazo ta same ni wai na bi wancan bakin motar,shine na bi su har wani unguwa tace nayi parking a gefe zata shiga ta fito,
Daganan dai Nasan ta shiga amma bansan me ya faru ba sai ganin ta nayi ta fito da gudu wasu maza na binta tana shiga mota ni kuma naja,shine tace na kawota wurin ka akwai maganar da zata fada maka,iya abinda na sani kenan "
Lumshe rinannun idanun shi yayi ba tare da yace komai ba ya juya ya buɗe mota yashiga,in da Dady ke jiran shi,wallahi wallahi duk mai hannu a cikin wannan lamarin koshi waye ba zai taba barin su ba,domin idan har ta sanadiyar shi wani abu ya same ta ba zai yafe ma kanshi ba,
Dafe zuciyar shi yayi dake mai zafi,idan har ya tuna rabuwar su da kuma abinda ta mai a jiya sai yaji hankalin shi ya ƙara tashi,
Har Dady ya tayar da mota yace masa yana zuwa,kiran Hashim yayi "Ina jakkan ta,a wani Hotel take zaune?
" Ba Hotel take zaune ba a gidan Oga na take zaune"
Cikin mamakin daya kasa boyuwa yace"gidan oganka kuma"fuskar shi na nuna wani yanayi,
"Eh amma shi yana Abuja ita kaɗai ce a nan," Nan ya faɗa mashi sunan unguwar da number gidan,sai jakkan ta daya miko mashi,
Jan motar Dady yayi suka bar Asibitin zuciyar shi cike da tunanin me take son ta faɗa mashi.
Suna shiga Hotel din Dady ya amsar mashi makullin daki kusa da nasu ya bashi,
Wanka yayi ya sauya kayan jikin shi,
Sannan ya kunna wayar shi da suka mai da mashi,
Number Ammi ya duba ya danna ma kira,
Ai kuwa makar dama jira take yi ta dauka da sallamah,
Sunan shi ta kira domin son tabbatar da ko da gaske din shine"Suraj "
Ji yayi idanun shi sun cika da hawaye"Na'am Ammi"
"Alhamdulillah,Allah na gode maka Alhamdulillah, yau zaku dawo ko?
" Umm um "ya faɗa yana share hawayen shi,
Dan shiru tayi kafin tace" Me ya faru,na yana ji kamar kana kuka,why are you Crying?
"Ammi tsoro nake ji"
"Nasan duk abinda ya girgiza wannan zuciyar har ya samu nasarar tsorata shi ba ƙarami ba ne,faɗa min me ya faru ?
"