Showing 156001 words to 159000 words out of 159134 words

Chapter 53 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

27 Sep 2025

9751

bawan Allah nan ya sake yi ba zaki taba samun ko da mashin shini bane balle a kai ga batun Aure,kuma sai Allah ya jarabceki akan hakkin shi,"busar da iska yayi yana huci"idan har yanzun zuciyar ki na kan Yusuf ne to ki cire,domin wannan karon idan har kika zabe shi to babu mu babu ke har a bada,tunda baki San Alkhairin dake tare da ke ba,wallahi salma ki gode ma Allah,biyo ni ki ga wani abun mamaki"

Tunda ya fara magana take kuka,bin bayan shi tayi har bakin motar shi ta bude ta shiga kamar yanda taga shima yayi,
Har cikin motar Kuka take yi tana ƙara jin tsanar kasancewa da Suraj a rayuwar ta,in dai tun yanzun taraiyarsu zai zamar mata barazana a rayuwa to gaba bata San Me zai faru ba,
Gani tayi sun shiga cikin Asibitin General Hospital Minna,
Yana yin parking suka fito,ita dai tana biye dashi har cikin wani word suka shiga in da kana dosan dakin wani irin karni da wari da za fara ji,duk da tsafta irin na Asibiti,
Tsayawa yayi a bakin kofa ya ciro Nose marks ya mika mata "saka a hancin ki"

Amsa tayi ta saka sannan suka shiga dakin,

Tun da suka saka kafa taji kanta ya sara,ganin mutane kwance tamkar masu ciyon kanjamau sabar rama da kashin jikin su daya fito,wasu ko numfashi kirki basu iya yi,ga wari na masifa dan ko majinyaci daya baya tare dasu,
Abakin wani gado suka tsaya,in da wani tsohon mutum ke kwance yana fitar da numfashi da kyar ko riga babu a jikin shi,wallahi har tsoron kallon fuskar shi take yi yanda fuskar ya rame kana iya ganin duk wani kashi na fuskar,ga ido da yayi zuru_zuru,
Cikin sauri ta riko hannu Abdulmajid tana dan komawa ta gefen shi,

Nuna mata mutum yayi"kinsan waye wannan?

Girgiza kai tayi,

"Kara kallon shi da kyau ki gani"

Tsira mashi ido tayi sai dai sam ta kasa gane shi,

Nan ma kara girgiza kai tayi,

"To wannan da kike gani Yusuf ne,Yusuf dai da kika sani tsohon mijin ki shine,"

Wani irin zaro ido tayi tana kara zuba mai ido,sai yanzun abin ya zo zuciyar ta,tabbas shine,
Muryarta har rawa yake yi wurin fadin "Yaya me ya same shi?

" Abinda ya shuka ne yake girba,Salma shi yasa nace Allah yana son ki,domin ya gama maki duk rahama da zai maki,amma kina ƙoƙarin yi ma kanki mummunan hisabi,
Ki duba irin jinyar da Baba yayi duk da baƙi nan,komai sai an mashi,har zuwa karshen rayuwar shi yayi mutuwa irin ta rashin jin daɗi wannan ma wani ishara ce,ki duba mutuwar Mama da ko haɗuwa Allah bai nufa za ku yi ba duk da irin burin haɗuwar da kuka ci ma juna,ko samu taga fuskar ki ta nime yafiyar ki ba tayi ba,sannan ki duba wannan na gaban ki na yanzun,ko magana baya iya yi,gabaɗaya wurin bahayarshi ya zazzago kashi baya iya tsayawa,fitsari baya iya tsayawa,wurin tsutsotsi ne kawai ke fita suna rarake wurin,shi kuma ke zaki ce a kanshi,
Ke kuma me ya same ki Salma,Ubangiji ba tsoronki yake yi ba da kika tafi yawon duniya da sunan fushi kina ta aikata barna,amma bai hukunta ki ba sai ma ya baki miji na gari wanda zai iya sadaukar da komai domin ke,
Kin san ma kuwa cewar shi ya bada Kodar shi daya aka sai ya maki"

Da sauri ta gado jikakkun idanunta ta daura a kanshi,

"Kwarai kuwa,domin a lokacin an duba namu a ciki babu wanda ya maki,kuma idan har aka bata lokaci to kina iya rasa ranki saboda coyon dake kanki,shi ya yace zai baki nashi ba tare da tunanin komai ba,kuma ya bada,
Kin ma san irin rashin lafiya da yayi a lokacin,domin kuwa wannan da kike gani a kwance so yayi ya kashe shi ta hanyar dukan shi a ciki,
Kiyi tunanin irin raɗaɗi da azabar daya fuskanta,A ranar da za'ayi aikin a ranar Kakar shi da tayi shekara goma sha ɗaya a kwance a ranar ta tashi,ranar da suka dauki tsayin shekaru suna addu'a da fatan zuwan ta,amma haka ya hakura ya kwanta aka yanka jikin shi aka cire wani bangare nashi mai muhimmanci aka saka maki,ba tare da sanin shin zai kara buɗe ido ko bazai iya ba,ko kuma shima tafiyar ke nan,ya watsar da komai nashi da burin shi ya zaɓe ki,
What sannan har kike fadin baya son ki dan kawai bai faɗa maki cewar yana son ki ba,
Wallah kin ban kunya!kin bani kunya Salma! Amma fa babu komai rayuwa ce kuma duniya ce ta isa kowa riga da zani,amma ki tuna da wannan misalin dake gaban ki,yanzun zabi ya rage naki"har ya juya ya juyo ganin yanda take sharbar kuka"muje na kaiki gida"

Bin bayanshi tayi,har cikin mota yana jin yanda take rusa kuka sai dai ko alamar dakatar da ita bai yi ba,gara tayi ko zai taimaka wurin dawo da ita haoyacin ta,

A ƙofar gida ya ajiye tana fita yaja motar shi ya bar kofar gidan.

Babu kowa a tsakar gidan dan haka dakinsu ta shiga ta zauna ta lungun gado tana cigaba da kuka,
Ganin Yusuf a yau a haka kuma ya matukar tayar mata da hankali,Yusef dan gayu mutum mai ji da iya wanka da saka kaya,yau sai gashi kwance ko riga babu,duk irin kudin da yake kashe ma fatar jikin shi sai gashi yau fatar ta mutu ta yakushe ko gane shi ba'a yi,
To yanzun ina duniyar daya nime,ina arzikin da ya tara,ina kuma lafiyar da yake takama da shi,duk basu amfana masa komai ba,gashi kwance tamkar gawa,zai tayi yabar komai,

Suraj zuciyar ta ya ambaci sunan,tabbas Allah ya bata shine domin ya kara gwada imanin ta,sai gashi duhun kai yana nima ya kai ta ga aikata aikin da na sani,
Idan har zata tuna irin zaman ta da tayi da Yusuf da kuma kwana daya kawai da tayi da Suraj sai yanzun take ganin Allah ne ya amsa addu'ar ta ta bata miji wanda zai iya da ita har ma ya fita saboda ya tsayar da ita a wuri da,amma makantar zuci ya shafi ido,
Tabbas ta cancanci da a kira ta da bulu mara godiyar Allah,
Ya kamata tun yanzun ta koma hankalinta ta nuna godiyar ta ga Allah kafin ita ma lokaci ya kure mata ta tafi tana nadamar rayuwar ta.

Sai lokacin sallah ta fito tayi Alwallah tayi sallah,
Ganin har lokacin bata zo ta dauki abinci bane yasa Kaka ta tashi ta shigo dakin,
A zaune take har lokacin saman darduma,
Zama tayi a bakin gado tana fuskantar ta tunda ba komai take yi dan ba carbi take ja ba,
Duk da Abdulmajid ya kira ya faɗa mata yanda suka yi amma tana buƙatar jin ta bakin ta,
"Me ya same ki?

" Yau zanbi Suraj gobe zamu koma tare dashi"

Wani irin murmushi ta saki mai sanyi"Alhamdulillah,Allah mun gode maka,na yi farin ciki sosai da wannan hukuncin da kika yanke,ina kuma fata zaki karɓi mijinki hannu biyu ki yi masa biyayya domin samun Aljannar ki,ta hakan ne kawai zaki iya nuna ma Allah godiyar ki ta hanyar yin bauta a gare shi,domin aure ma yana daga cikin bautar Ubangiji,"

Kara share hawayen ta tayi"na gode Kaka da hakurin da kike tayi da ni"

Saukowa tayi ta rungume ta"ke din dole ta ce dole ne nayi haƙuri dake,ina maki fatan samun farin ciki a rayuwar ki Ummu Salma"

Ita ma rungume Kaka tayi"na gode Kaka"

Auty Hulaira ce ta shigo nan ta tared dasu a haka,
Zolayar su ta shiga yi,kafin daga baya su sakata a tsakiya suna mata nasiha,dan ita Aunty Hulaira shekara biyu kenan da ta dawo gida dan mijin ta rasuwa yayi kuma Allah bai taba basu haihuwa ba,yanzun nan ne ma ta tsayar da wani sai dai shi saurayi ne kuma haka ya nace sai ita,kuma ƴan uwan shi sun yi na'am da ita,

Tare ta zubo masu Gurasa a plate da Balango sai kayan ganye suka shiga ci suna janta da hira dan kawai su ɗebe mata kewa,dan a wannan stage din da take ciki ba a buƙatar wani abu da zai dame rayuwar ta,

Su suka haɗa mata kayan ta wuri ɗaya a cikin babban akwati,sannan Kaka ta kira mata yannin ta,har da Abdulmajid ta nime tafiyarsu akan bata masu rai da tayi tun lokacin auren ta na farko da Yusuf har i zuwa yau,ta kuma kara da masu godiya akan dawo da ita hanya da suke ƙoƙarin yi a ko yaushe,
Sun yi farin ciki sosai sun kuma yi mata fatan Alkhairi,
"To sauran ku Allah yasa ina da rabon ganin auren ku" Cewar kaka,

"Insha Allah zaki gani har ma ki goya tattaɓa kunne"duk dariya suka saka jin amsar da Abdulmalik ya bata,

" Yauwa ni fa na samu mata,dama jira nake komai ya daidaita ayi magana "

Duk kallon sa suka yi,
"Shi yasa nake son ka yaya Abdulmajid nasanka ba kada sanya,a ina take?cewar Salma,

" Ai Balki ce ta Kano yar gidan Gaggon yara "

Baki ta buɗe "da yaushe kuka haɗu,yanzun idan ka kaure yarinyar nan kana nufin dole nace mata Aunty"

"Sosai ma kuwa,ai tun lokacin jinyar ki muka dunki"

"Kuma tana son ka?

" Sosai ma kuwa,ban cin haka ai har da mamarta muna waya tana yawan tambayar ki,ta kuma shaida min in har da gaske nake yi na kwantar da hankali na ta bani "

Duk dariyar farin ciki suke yi,

"To kai fa Abdulrahman?

" Yarinyar limamin unguwar mu ce,Nusaiba "

Duk hamdala suka saka,

Abdulmalik ne kafin ma a juyo kanshi yace "ni fa kar ma a tambaye ni domin har yanzun ina kan bincikawa ne"

Dariya ya basu"Allah ya tayaka zaɓar na gari"

"Yaunzun Abunda za'ayi zan kira kanne na maza zasu zo a gudanar da bincike sannan a shiga gida ayi magana"

Da haka suka tsayar da maganar sannan aka dauko wani hirar,anan suka ci abinci dare bayan sallar Magrib sannan suka wuce bayan sun sallame ta.

Sai da ta idar da sallah Magrib sannan ta kira number shi,wanda bugu biyu ya ɗauka da sallamah,

Amsawa tayi "idan ka idar da Sallah Isha'i ka zo "

"Ina fatan lafiya?

" Lafiya glau kai dai kazo"

"To shi kenan sai na zo"

"Um hmm" Ta faɗa ta na sauke wayar.

Tun ƙarfe takwas take jiran kiran shi har sai takwas da rabi ya kira dan sai da ya idar da jan carbi,
Shi yasa yana kira ta dauka cikin jin haushi tace"Me ne"

Murmushi ya saki domin ya haminci haushi ta ji,to ya zai yi da ita dole sai haƙuri ya san ba laifin ta bane wannan yawan fushin da jin haushi,

"Yi haƙuri gimbiya gani a ƙofar gida"

"Na riga na kwanta sai gobe"

"Dan Allah kiyi haƙuri ki taimake ni,yau ba zan iya bacci ba idan ban gan ki ba"

Dan shiru tayi tana sauraren yanda yake magiya kafin tace "gani nan zuwa"

Sai da ta dauki lokaci dan kanta tana tsaye kofar gida yana kira kafin taga sun fito ita da Aunty Hulaira dake janye da katon Akwati,da sauri ya karasa ya amsa"Aunty ina zaku"

"Akwatin matar ka ce,yau dai Allah yayi wai binka zata yi"

Wato ido yayi yana kallon ta,dauke kai tayi kamar bata ganshi ba,

"Kai da kata na ka bita a hankali domin kasan ba ita kadai ba,ina maku fatan Alkhairi da fatan sauka lafiya,"

Ji yayi kamar ya rungume Aunty Hulaira tsabar murna"na gode sosai Aunty,Allah ya biya ku"

Da Amin ta amsa tana shegewa gida tare da daga masu hannu,

Murmushi ya saki yana buɗe mata gidan gaba,
Shiga tayi ya mai da kofar ya kulle,
Har suka bar unguwar bata ce mashi komai ba,sai da suka hau babban titi sannan ya dan juyo "kina bukatar wani abu ne?

" Fruits"

"Ok"

A ta bakin titi ya tsaya ya tsiya masu sannan suka kara kama hanyar gidan shi dake unguwar Bosso Lokos,
Dama kuma ta san gidan,
Yana parking a harabar gidan ya buɗe ya fito sannan ya buɗe in da take,kamar wata karamar yarinya haka ya dauke ta ba tare daya dire ta ba har cikin daki saman gado ya zaunar da ita,

Fita ya kuma yi ya shigo da akwatin kayanta ledar kuma ya kai kicin,yayyanka fruit din yayi ta yanda zata ji daɗin sha sannan ya dauko,

Tsayawa yayi rike da tire a hannu yana kallon yanda ta jinginar da kanta jikin gado idanun ta a lumshe alamun barci na son ɗaukarta,

Murmushi ya samu kanshi da saki,domin aduk sanda ya tuna gudan jinin shi na tare da ita sai ya ji wani irin farin ciki mara misaltuwa tare da ƙaunarta na ratsa zuciyar shi,
Ajiye tire din yayi a hankali sannan ya taka zuwa in da take,
Zube guiwowin shi yayi a kasa ya tura hannun shi cikin rigarta yana shafa marar ta,

Ɗan zabura tayi tana sauke ajiyar zuciya tare da kyara zama,
"Sorry na tsorata ki"

Bata ce mai komai ba sai kokarin cire hannun shi tayi daga cikin ta,

Tashi yayi ya hau kan gadon gaba ɗaya ya jawota kan gadon yana kwantar da ita tare da karasa cire mata karamin kyalen dake kanta,
Rigarta ya tattara ya mai da shi saman kirjinta tana saka hannun shi a tsakanin siket dinta ya jawo shi kasa,

Tsira ma shaffen cikin ta idanun yayi,yana kure in da yaga ya ɗanyi tudu kaɗan idanu na kusan mintuna goma kafin a hankali ya kai hannun shi sai tin wurin yana dan shafa wurin,sai kuma ya duka ya sakar mata Kiss a wurin,yana kankame ta hanyar zagaye hannun shi gabaɗaya ta bayanda kanshi kuma saman cikin ta"Allah ya Albarkaci rayuwar ki,ya faranta maki kamar yanda kika faranta min,ya yafe maki kura-kuran ki har abada ya saka Aljanna ce makomar ki"

Hannu tasa ta shiga shafa lallausar suman kanshi"ya kuma barni tare da kai har karshe rayuwata "

Da sauri ya sake ta yana dagowa "da gaske kike kina son Allah ya barmu tare?

Jinjina mashi kai tayi tana rungume shi tare da saka kuka" Dan Allah ka yafe min akan duk abinda na maka,nasan na faɗa maka maganganu marasa daɗi wadanda Allah zai iya tuhuma ta,na maka alkawarin ba zan sake ba dan Allah ka yafe min"

Shafa bayan ta ya shiga yi"shiii ya isa haka,ni dama ban taba rike ki a raina ba,na san kuma idan nayi haƙuri komai mai wucewa ne zaki fahimta,dan haka tun tuni yake yafe maki"

"Ni dai kace ka yafe min"

"Na yafe maki duk abinda kika min da kuma wanda zaki min nan gaba,Allah ya yafe mana baki daya"

Ƙara rungume shi tayi"na gode Zauji "

"Kin tabbatar ni din Zaujin ki ne?

" Kai rayuwata ta ce"

Sunbatar goshin ta yayi yana sauko da ita,tare suka sha fruit din sannan ya mai da kayan kicin,

Ranar tare suka yi kwanan farin ciki,babu wani da ya shiga tsakanin su sai dai kyakkyawar runguma daya mata har gari ya waye,

Haka washegari ko tsinke bai bari ta dauka shi yake mata komai har ta wanka shi ya mata ya shirya ta,
A ranar ta ga wani abu wai shi tarairaya,ko kwakkwarar motsi tayi sai ya tambaya mai take so,
Jirgin yamma suka bi zuwa Abuja daga nan suka tafi London,

Da yaba Ammi takardar Sikainin din ta gani har da kukan farin ciki ita da Grandma,
Kwanan ta biyu tare dasu ya zo ya dauke ta ya maida gidan shi dake nan bayan dogon gargaɗi da bayani daga Ammi akan ya rinka binta a hankali,

Rayuwar ta koma tamkar na wata Sarauniya,domin ta ko wani bangare ba karamin kula take samu ba,har balle da cikin ta ya kai wata biyar lokacin ya fito sosai kana ganin shi,

Sau biyu ta zo Nigeria a lokacin bikin yanninta sai kuma lokacin da Amira ta kammala makaranta,a nan Kano a dakin Goggon yara ta sauka,
Dawowar su da sati biyu aka rataye Pa,Allah sarki rayuwa shi kuma a inda nashi babin ya kare kenan,

Bayan wata huɗu sai gashi Allah ya sauke ta lafiya in da haifi ɗan ta namiji mai matukar kama da mahaifinshi,tun a Asibiti yama danshi Huɗuba da Abdulbasit wanda zasu rika kira da (Abid) kasancewar sunan mahaifinsa,
Grandma da Ammi har da Kukan murna,wannan dama shine burin su,
Tunda aka haifi yaro sun dauki son duniya sun daura mashi,har balle Ammi ko ƙara bata yi sai tace ai yayan ta ne,

Yan Nigeria ma sun zo Suna ciki har da Maijiddarh,Allah sarki ita ma da nata cikin,sai fatan sauka lafiya,
Sai da sukayi sati ɗaya sannan suka dawo da goma sha tara na Arziki,domin sunje gidan Arziki sun ga inda aka gaji Arziki a bar Arziki,

Sai da tayi Arba'in bayan haɗi da tsumi na musamman da Ammi tai mata sannan ta bashi matar shi suka koma gidan su,cike da sharadin kullun za'a kawo mata Yayanta ta ganshi,
Ganin yanda Suraj din ke yi masu zarya a gida kamar zai sace ƴar mutane,

Randa ta koma kuwa data shiga hannun shi sai da tayi har sai da idanun ta suka kumbura,saboda ya nuna mata tsakanin ta dashi babu sassauci,domin kwanakin daya ɗauka yana haƙuri sai da fanshe shi,
Sai da komai ya lafa sannan ya rungume ta yana aikin lallashi,
"Ke rayuwata ce Bebin,ba zan iya rayuwa ba babu ke,ina mai rokonki da kiyi haƙuri da ni da kuma halina,ban taba jin haka game da wata mace ba face ke,shi yasa bana iya riƙe kai na a duk lokacin da nake tare dake"

Shafa fuskar shi take yi tana jin wani shaukin shi na kara taso mata"kai din jarumi ne a cikin jarumai,a duk lokacin da naso nuna jarumta ta a gabanka sai naji ni ba kowa ɓace face YAR TSANAR KA wacce zaka juya kayi yanda ranka yake so da ita,ina matukar Alfahari da kai"

Mumushi ya saki wanda ya bayyana fararen jerarrun haƙoran shi,yana ƙara matso da ita jikin shi"soyayyarki kullum takan narka tunani na acikin shaukin iske goben rayuwata a tare dake, tamkar jini ina da bukatar a ko da yaushe ki kasance a cikin jiki na,
Sabanin haka kuma,hakika zan azabtu sau lokacin da yawa,
Haka kuma da soyayya nauyi ce ga jiki,tabbas dana roƙi Allah ya hukunta jiki na ya zamo mafi nagarta iya dauka domin kada na bada rauni yayin tafiyar da soyayyar ki,
Kece ƙaddara mafi daraja wacce farashin ki baya taɓa faduwa a rayuwata,kullum hauhawa kike sama tamkar shekaru na Bebin,ina matukar son k....

Haɗe bakin su tayi wuri ɗaya domin ƙwaƙwalwar ta ba zata iya jurewa sauraron waɗannan tausasan kalaman dake fitowa bakin shi ba,masu saka ta jin shaukin soyayyar shi dake kokarin fasa kinjin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login