Showing 15001 words to 18000 words out of 159134 words
Chapter 6 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
ana sallamah ne yasa yace mata"je ki dauko ma Ammi Hijabi"shi kuma ya tashi ya fita,
Bai wani jima ba ya shigo tare da mutumin,wanda anan ya duba kafar ya kuma tabbatar masa da cewa ta samu targade a babban ɗan yatsa,sai tsagewar kashi ta gefen ƙafar,
Sai da ya koma gida yazo da abubuwan da yake bukata kafin ya fara mata ɗaurin kafa wanda ba karamin azaba ta ji ba,
Allah dai ya taimaka an samu nasaran kyarawa,sai dai ba daman Kata kafar sosai,
A ɗan kwana biyun da tayi wannan ciyon ƙafar aiki kamar zai kashe Amira,wacce ga zuwa makaranta ga kuma islamiya,
Hakan ne yasa Kaka da kanta ta bada shawara akan dole a dauki ƴar aiki domin ba ta yanda za'a yi Amira ta iya waɗannan aiyuka ita kaɗai,
Duk da Ammi bata soba ba yanda ta iya tunda lalura ne ya kamata wanda dole tana buƙatar mataimakiya,
Matar da take kawo masu masu aiki Kaka ta kira ta sanar da ita suna buƙatar me aiki,kamar dai ko wani lokaci mace mai tsafta suke so,
Ce mata tayi zuwa yamma za'a kawo ta.
_____misalin karfe biyar,zaune take a saman tabarmar da aka shimfida mata,ta turo bakin nan nata gaba,wanda kallo daya zaka mata ka fahimce irin bacin rai dake tare da ita,
Matan nan ce naga ta zo ta zauna kusa da ita tana miko mata wata waya Nokia wanda tasha lobali ko marfi ba ta dashi,
"Biba karba mana"
Kin karɓar wayar tayi tana mai da hannun ta baya kamar wata karamar yarinya,
Duk yanda taso ta ɓoye dariyar ta dan karta ƙara tunzura kasawa tayi sai da ta saka dariya,ganin yanda tayi yanda kasan yarinya ƴar shekara shida,ga kayan data saka riga da zani wasu masu kalan tsofaffin,zanin leɓe daya yafi ɗaya kasan ya matse wanda da ƙyar ma in zata iya tafiya dashi,rigar gashi nan babu fasali dan ya mata yawa ajiki,
Fuskarta dai yayi wani fari tas dashi mai ban sha'awa,gashi sumul babu wani ɗigon baki ko kurji,idanun ta sun kara haske domin ko kwalli babu,sai ƴan madai_daitan labbanta jawur dasu ta turo su gaba,
Idan har kai mai lura ne kallo daya zaka ma hallittar jikin Biba kasan jikinta ba kalan wanda ya saba aikin wahala bane.
"Kinga Biba haƙuri zaki yi ki karɓi wannan wayar haka,na saka maki sim a ciki,akwai kuma number ta a ciki,idan kina buƙatar wani abun sai ki sanar dani,kuma ta wannan layin VIP zai neme ki"
Amsa tayi ba tare data ce mata komai ba ta mike tana daukar jakkan dake gabanta zata goshi ƙofa,
"A'a tsaya kinga sai kin saka hijabi" Ta faɗa tana dauko hajabin dake ajiye a gabanta,tabi bayan ta,
Sai da suka shiga Adaidaita sannan ta karɓi hijabin ta saka.
"Kinga karki damu,ba wani daɗewa zaki yi a gidan ba,da zaran kin dauko masa abinda yake buƙata shikenan aikin ki a gidan ya kare,ko da kuwa a yau ne,kuma akwai littafin girki a cikin jakkan ki na saka maki,wanda zai taimaka maki"
Ita dai bata ce mata komai ba domin bacin randa take ciki ma ya ishe ta,
Jin mai Adaidaita ya saya ne yasa ta dago kanta tana kare ma wani tafkeken kofar Get din da suke tsaye,wanda akwai babban masallaci a kofar Get ɗin,
Fitowa suka yi daga cikin Adaidaita suka doshi kofar gidan tare da jakkan ta a hannun yayin da take jin bugun zuciyar ta na sauyawa a ko wani taku da tayi......
*Last free page*
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*12*
*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*
Mai gadi ne ya buɗe masu Get suka shiga bayan sun faɗa mashi wurin Kaka zasu,duk da dama ya santa,
Tunda suka shiga gidan take kallon ko ina cikin taka tsantsan,yayin da matar wacce taji yaran gidan na kiranta da A'i take nuna mata da ido waɗannan shiyoyin guda huɗu,"wannan dake kallon Arewa anan zaki yi aiki,sauran kuma duk na Ya'yan Kakar ce,sai na karshe wanda ɗiyarta ke ciki da nata yaran,idan mun shiga wurin tsohuwar dan Allah ki yi mata ladibi sannan waɗannan idanun naki da suke a tsaye ki dinga rusunar dasu"ta faɗa tana turo kofar wani shiya,"kinga kuma ta can baya ne dakin samarin gidan yake"
Sallamah tayi a ɗan madaidaicin tsakar gidan wanda yake a share tas,
Jin ba'a amsaba yasa suka karasa har kofar shiga cikin falon Kaka,
Nan ma wata sallamah tayi,wanda suka ji an amsa masu ta bayan su,
Duk juyowa suka yi suna kallon ta,ƴar budurwa ce wacce bata wuce sha tare,kusan tsaran Biba ce,dauke da ninkakkun kayan da aka wanke,alamun ta kwaso ne daga shanya,duk da kayan jikinta ba laifi amma daga dukkan alamu yar aiki ce,
Murmushi ta sakar masu"barkar ku da zuwa,wa kuke nima"
"Wurin Kaka muka zo tana ciki?
" Eh ku shigo"ta faɗa tana shiga gaba,har cikin falon kafin ta nuna masu wurin zama,ta shiga kicin da dauko masu gorunan ruwa tare da kofi,domin yin haka dokar Kaka ne,in dai baƙo zai shigo wurinta,
Wani daki tashiga bata jima ba sai gashi ta fito"ku jira tana zuwa"
"To mungode ƴan mata"
Basu wani jima ba saiga wata kyakkyawar tsohuwa ta fito daga cikin daki,ƙafarta tasha lalli na Hausa,tayi kyau abinta,
Da murmushi ta karaso inda suke,
Da sauri taga A'I ta tsugunna kasa tana gaishe ta,wanda ita ma ganin hakan ne yasa ta tsugunna,
Zama tayi a kushin din dake fuskantar nasu tana dan dariya,"a'a maza ku tashi ku zauna,A'I kinsan bana son irin wannan gaisuwar"
Komawa suka yi suka zauna kan kushin,
"Ga ta na kawo kaka,da fatan tayi maki"
Kallon ta take tun daga sama har kasa tana jinjina kai,"ya sunan ki yan mata"ta tambaya
Kanta a duke yake domin matar ta mata kwarjini sosai,"Habiba,amma ana kira na da Biba"
"Masha Allah suna mai daɗi,Habiba,shakaranki nawa"
"Ishirin nake"
Maida kallon ta tayi kan A'I wacce ke addu'a a zuciyar ta akan Allah yasa ta amsheta"wannan din tayi A'I,da fatan ba zamu samu matsala da ita ba"
"Insha Allah Kaka domin ita ba tada matsala ga tsafta,na tabbatar sai kin yaba"
"Allah yasa,yanzun dai za'a dinga biyanta ta hannun ta ne ko kuwa ke za'a ba"
"A'a Kaka kawai ku dinga bata a hannun ta,shi zai fi,"
Yarinyar dazu ce ta fito zata wuce,kaka ta ce "Nafisa kawo masu abinci"
"A'a Kaka a barshi domin sauri nake ina son in shaga kasuwa ne kafin a tashi,"
"To ba matsala,zubo ma Habiba ita," Kuɗi ta ciro wanda zai iya kaiwa dubu goma taba A'I "gashi kiyi kudin komawa "
Amsa tayi tana washe baki"nagode sosai kaka Allah ya biya,ya ƙara lafiya "
Cikin sanyin murya tace"kaka nima na koshi"
"Ki saki jikin ki sosai damu Habiba,na tabbatar ba zaki yi dana sani ba"
Dukar dakai kawai tayi domin haka kawai ta ji matar ta kwanta mata.
Sallamah A'I taimasu ta wuce,
Daukar waya tayi ta shiga wurin kira,bugu daya aka ɗauka,amsa sallamah tayi"ki turo min Amira "
Sai kuma tace "to" Tana sauke wayar.
"Iyayenki ƴan wasu gari ne Habiba"
"Daura a Katsina" Ta bata amsa domin haka aka tsara mata,
"Aikuwa nasan katsina sosai,a wata unguwa"
Kafin ta bata amsa ne taji anyi sallamah a bakin ƙofa,
Amsawa suka yi,kaka na bada umarni ta shigo,
Tana zuwa zama tayi kusa da kaka tana rike hannun ta tana jujjuyawa "Wow kaka hannun nan naki yamin kyau,kamar muyi canje"
"Ko dai zamu yi canjen ne,ai ku yaran yanzun kyuya ke hanaku kwalliya"
"Ni dai banda ni,idan na samu lokaci zan zo kimin da kanki"
"Sake min hannu karki karya ni,ga sabuwar mataimakiya nasa an kawo wacce zata dinga taimaka ma Ammi,kafin taji sauki,idan har ta mata kuma tana iya riƙe ta,idan kuma taga bata butarta zuwa lokacin ni zata dawo shiyana da aiki"
Juyowa tayi inda Biba ke zaune tana kallon su,"Wow kaka ina kika samo ƴar aiki mai kyau haka? Tasowa tayi ta dawo kusa da Biba tana shafa fuskarta"Wow,gaskiya kina da kyau,kamar ba yar ƙauye ba"
"Ke ni bani son zuba,tashi ki kaita ta gaida Ammi ki kuma nunnuna mata wuraren daya kamata ta sani"
Tashi tayi tana rike hannun Biba,wacce ta dauki jakkanta da hannu daya,"muje"
Tare suka fito da Amiran wacce take ta zuba mata surutu akan kyanta,ita dai sai dai tayi murmushi,
Babban falo ne suka shiga wanda ba laifi komai an zuba shi daidai hankali,cewa tayi"ki ajiye jakkanki anan kafin muji me Ammi zata ce"
Ajiye jakkan tayi a gefen kushin suka nufe wani ƙofa,nan ma cewa tayi"tsaya na sanar da ita shigowar mu"
Nan ma tsayawa tayi,ita kuma ta shiga ciki,
Bata jima ba ta fito fuskarta dauke da murmushi"muje tace ki shigo"
Bin bayanta tayi,har cikin wani madaidaicin falo in da anan suka tarad da wata mata kyakkyawan zaune a kan kushin tasha kwalliya sai kamshi take zubawa,
Samun kanta tayi da zama a ƙasa tana gaishe ta"ina wuni"
Kallon yarinyar take yi cikin kulawa"lafiya ya kike"
"Lafiya"
"Ya sunan ki"
"Habiba,amma ana kira na da Biba"
"Daga wani gari kike"
"Katsina a Daura"
"Yayi kyau,da fatan dai ba kiɗa matsala,domin bana son kazanta ko kadan,ta ko wani bangare ya kasance kina da tsafta,idan har kin kiyaye zamu zauna lafiya"
"Insha Allah Hajiya"
"Nuna mata ɗakinta Amira,sai ki nuna mata kicin ta daura girkin dare,Sinasir da miyan ganye zata yi,sai ki bata shinkafar da nasa kika jika dazu"
"TO Ammi"
"Idan kin kammala nuna mata ki zo ki tafi islamiya kafin yayanki ya shigo"
Nan ma amsa mata tayi,
Tunda taji ance tayi Sinasir taji wani zufa na karyo mata,ita da batama taba jin sunan abinci haka ba,bata ma sanshi ba,shine za'a ce taje tayi,
Duk wani surutu da Amira ke yi ba fahimtar ta take ba,har ta nuna mata ɗakinta wanda karamin gado ne kawai a dakin sai sif da kuma bayi a ciki,
"Yauwa ki ajiye jakkanki kizo in nuna maki kicin dan zan tafi ne,idan kin kammala sai ki zo ki kyara dakin.
Kara fita sukayi ta kaita har babban kicin dinsu ta kuma nuna mata in da kayan abinci suke da komai da komai har da Firig din da suke ajiye nama daban na saka abinsha da ban,
Anan ta barta tsaye ta wuce,
Komawa ɗaki tayi ta ɗauki waya ta kira number A'I,wacce sai da taimata kira uku kafin ta ɗauka so disgusting,jin tana tambayar waye ne,dan ba makaranta tayi ba,cikin jin haushi tace "Biba ce"
"Ohh ya aka yi?
" Sun ce nayi Sinasir,ni kuma ban san yanda ake ba"
Cikin daga murya tace"ni bana jinki ki daga murya kin san wayar ki sai a hankali "
Kara maimaita mata abinda ta ce tayi,
"Oh,shinkafar da aka baki jikakke zaki wanke sosai sai ki zuba a Blender ki duba acikin firig in akwai nono mai kyau sai ki zuba kaɗan a cikin shinkafar sai ki niƙa,idan ya yi sai ki juye a kwano ki rufe shi dakyau sai ki ajiye a wuri mai dumi,ko kuma ki rufe da Flannel zuwa mintuna talatin,daga nan sai ki hau suya"nan ta sanar da ita yanda zata soya,miya kuma tace ta duba a cikin jakkanta zata ga littafin girki idan ta duba akwai wanda kalolin miya ne kadai aciki.
Da taimakon A'i dana takardan nan ta samu tayi Sinasir da miya,kuma ya fita sosai saboda bata cika wuta ba kamar yanda A'I ta faɗa mata.
Koda ta kammala har an fara shiga sallah Magrib,dan haka dakinta ta shiga tayi wanka sannan ta canja kaya tayi sallah,tana idarwa ta koma kicin ta wanke kayan da ta bata ta kuma goge duk inda ta bata,
Samun kanta tayi da son dafa shayi irin wanda ta ɗauki lokaci mai tsayi a rayuwarta bata dafa irin shiba,wato shayin da mahaifinta ke matukar so,kullun ita ke dafa mashi a wannan lokacin.
Dauko tukunya tayi ta dauraye ta goge,sannan ta daura a gas,sai da ya bushe sannan ta zuba ruwa madaidaici a kai,kayan marmari ta dauko ta yanka shi kanana_kanana sai dai banda kankana da gwanda,ta zuba a ciki,sannan ta kawo kayan kamshi ta zuba,hade da wasu ganyayyakin shayi masu kanshi data gani a store,ta rage wuta sosai dan haka a hankali yake dahuwa,
Kulolin abincin data zuba na mutanen gidan ta dauka ta kai in da suke cin abinci,sauran kuma guda biyu ta bar shi a anan ɗan bata san ko na waye ba ne.
Sai da aka idar da sallar Isha'i kafin ta juyo shayin ta tace ta zuba a fulas kananu guda biyu,
Shayin kawai ta diba ta shige dakin ta,
Ammin ce ta fito rike da wani ƙarfe irin wanda masu ciyo a kafa suke amfani dashi,
Kicin ta fara shiga ta dudduba domin tabbatar da tsaftar ta,babu komai na datti domin komai a kyare yake saf,
Dawowa falo tayi nan ma ta buɗe kulolin abincin ta duba,ba laifi tayi ƙoƙari,ganin fulas ne yasa ta buɗe wanda wani irin kanshi mai matukar daɗi ya ɗaki hancin ta,kofi ta jawo ta zuba kaɗan,kalan shayin ruwan zuma ne farar saƙa,kaiwa bakinta tayi ta kurbi kaɗan tana lumshe ido,domin kamshin fruit ne ya haɗu da kayan ƙanshi sai ya bada wani kamshin na musamman,gashi kuma da zaƙi dai dai mitsali, in kana bukatar suger kana iya karawa,
Jinjina kai tayi tana sakin murmushi,
Tana kwance tana jujjuya karamin wayar nan a hannun ta,sai ji tayi ana kwankwasa mata kofa ta ji an yi,tashi tayi ta fara buɗe ƙofar,Amira ce ta gani tsaye,"Ammi na kira"komawa tayi ta dauki karamin hijabin ta iya guiwa ta fito falo,
Tire Amira ta miko mata wanda yake ɗauke da kuloli sai fulas daya a kai"wannan ki kaima Kaka,ni zan kai ma Yaya nashi"
Amsa tayi domin ta gane shiyan,
Kasan cewar gidan akwai haske wuta ta ko'ina yasa bata damu da duhun da garin yayi ba,
Sai da takai ƙofar falon sannan tayi sallamah,amsawa aka yi,
Dan haka jin an amsa ne yasa ta shigo kai tsaye,
Maza ta gani zaune wadanda zata iya kira da manyan samari,biyu suna daddana waya yayin da daya kuma suke surutu da Kaka sai dariya suke,
Kallo daya taimasu ta kauda kai tana gaida su,sai dai ba wanda ya amsa mata,wanda ba karamin haushi hakan ya bata ba,wai yau ita Biba take magana har ayi kaman ba a san da ita ba,
Karasawa tayi wurin kaka cikin girmamawa tace"kaka ina zan ajiye maki abinci "
"Ƴar Albarka ajiye anan,jiki kicin gashi can ki dauko min kofi,"
"To" Ta faɗa tana mikewa tabi hanyar da kaka ta nuna mata,
Tana sako kai cikin kicin din shi kuma yana fitowa hannun shi riƙe da kofi mai dauke da ruwan zafi a ciki,
Cikin rashin sani suka ci karo wanda kofin ruwan zafin ya faɗi ƙasa yayin da ruwan ya zubar mata a hannu,shi kuma ya zubar mai a ƙafa,
Wani irin zafi taji ya sauko tun daga cikin ƙwaƙwalwar ta har yatsun hannun ta,dan haka kafin ma ya ankara dawa yaci karo har ta buɗe baki ta shiga kwara ihu tana yarfe hannu tare da fitowa falo da gudu rike da hunnun tana ihu.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*13*
*Wannan Littafina mai suna a sama na kuɗi ne,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*
Jin ihu ne yasa duk suka maida hankalin su ta ƙofar kicin ɗin,
Ganin yanda ta fito a gigice ne yasa Kaka mikewa tana salati tare da kiran sunan"Biba,Biba"amma ina gaba ɗaya ma hankalin ta baya wurin su domin ni man hanya fita kawai take daga Falon domin ta samu ruwan sanyi ta zuba a hannun,dan ko kaɗan bata shiri da ruwan zafi,
Nafisa ca data fito ɗaki da sauri kaka tace"Nafisa riƙo ta muji me ya faru"
Da sauri ta riƙe mata hannu "sannan Biba,zo ki zauna a nan" Ta faɗa tana zaunar da ita in da Kaka ta nuna mata,
Yarfe hannu kawai take tana hawaye"waiyo hannu na,ki bani ruwa"
Kaka ce tace"miko ruwa "
Da sauri ta bude firig ta dauko goran ruwan sanyi ta buɗe sannan ta mika mata,
Tana ƙoƙarin zubawa ne Kaka ta riƙe goran ruwan"karki zuba ruwan sanyi,muga wurin"ta faɗa tana jujjuya hannun wanda tuni wurin yayi ja,
"Nafisa ɗauko kwano a banɗaki"
Jin takun tafiya a hankali ne yasa suka maida idon su kanshi,shima a hankali yake ɗan dingisa ƙafa in da ruwan zafin ya zubar mai,
Maida kallon ta kan Biba tayi "wai me ya faru ne?
Cikin muryar kuka ta nuna shi da ɗayan hannun " Wannan ne ya kona ne da ruwan zafi,"
Ƙara kallon shi suka yi,shi kuma sai ɓata fuska da yayi ya nime wuri ya zauna,
Ajiyar zuciya kaka ta sauke"Nurudeen zo dan Allah ka duba mata wannan hannun gashi har yayi ja"
Bai ci musu ba,domin kuwa tunda ta fito kicin din idon shi ke kanta har zamanta ƙare mata kallo yake tun daga kan ɗan yatsar ƙafarta har zuwa fuskarta wanda ɗan kukan da tayi yayi ja,
Tasowa yayi ya zauna a gefenta,"kawo hannun mu gani "
Ba tare da tunanin komai ba ta daura tafin hannun ta saman nashi,
Kallon yatsun hannun nata yake wanda suke zaro_zaro,gasu farare tas,ɗan shafa tafin hannun yayi yayin da yaji wani laushi da tsantsi a hannun nata,kai ko fatan ta abin kallo ne,"Sorry "ya faɗa a hankali,