Showing 105001 words to 108000 words out of 159134 words
Chapter 36 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
kallon wasu,sai dai idan ka shiga cikin dakin zaka ɗauka wani duniya ne ka shiga,domin babu abinda babu,katon Falo da dakuna biyu wurin wanki da shanya,barandar shan iska,da kuma wurin girki,har da dan wani wuri da akayi domin hutawa,gaskiya dakin ya haɗu,komai akwai shi a cikin, ɗaki daya ta dauka sannan ta nuna mai nashi,"ga ɗakin nan,kayi wanka ka huta zan mana ordan abinci,zuwa gobe Monday zamu fara shiga School,domin mu karasa abinda za mu yi sai mu fara ɗaukar karatu"
"To Allah ya kai mu" Ya faɗa,
Juyawa tayi ta koma nata dakin data zaba,sai da tayi ordan abinci kafin ta shiga wanka,dan ɗakin akwai na'uran saka ɗumi adaki,
Bayan wasu mintuna ne karrawar kofar ya shiga ƙara,ita ta fito ta buɗe ta amsa abincin ta bashi kuɗin shi sannan kulle kofar,a saman Dinner Table, ta koma daki domin ta shirya,
Riga da ƙaramin wando ta saka iya cinya,a lokacin idan ka kalle ta ba zaka so ko da kyafta ido kayi ba,saboda yanda rayi matukar kyau yanda kasan wata Bebi,
Kwankwasa mashi kofa tayi haɗe da yin sallamah ta shiga ba tare da ta jira ya amsa ba,
A lokacin ya kammalawa saka gajeren wondo irin na maza wanda yake saukowa zuwa guiwa na shan iska,yana rike da Sinlet fari yana ƙoƙarin sakawa ta shigo,
Da sauri ya manna rigar a kirjin shi ya rufewa tare da kauda kai,"ki je ina saka kaya idan na gama zan fito"
Turo baki tayi tana ƙara matsowa inda yake"ai kai Mijina ne yanzun babu abinda zaka ɓoye min"
Amsar karamar rigar dake hannun shi tayi tana warwarewa,taimaka mashi tayi ya saka rigunan duka,"ni ba zan ɓoye maka komai na jiki na ba domin yanzun da daba daya bane"
Bai bata amsa ba sai ma cewa da yayi "mu je"
Tare suka fito suna zaune,ita ta saka masu a plate daya ta kuma hana shi saka hannu sai ma diba da take yi tana bashi a baki,tun yana ɗan kau kauda kai har dai ya zage yana karba,sannan shima yana saka mata a baki tana ci,
Sai dai abunda ya fara bata mamaki koda yake ta mai izini saboda ƙila lokacin shine na farko daya fara keɓancewa da mace,domin ko alamar burgewa ko jan hankali bata gani tare da shiba akan wannan shigar nata,ko a idanun shi bata gani ba.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*64*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Suna kammala cin abincin ta kwashe kayan ta kai kicin wanda zata saka ashara kuma ta saka,
Ko da ta fito baya falon dan haka dakin shi ta leka,yana kwance kan gado daga dukkan alamu waya yake yi,dan haka ita ma fitowa tayi ta koma nata dakin ta kira wayar Mama domin shaida masu sun sauka lafiya,
Bayan ta gama kiraye-kirayen wayarta ne ta kwanta daga nan barci ne mai matukar daɗi ya ɗauke ta,wanda ba ita ta tashi ba sai daf da magriba,cikin sauri ta ƙara yin wanka da ruwan zafi dan jikinta ya sake sannan ta jero sallolin da ake binta,a haka ta zauna har lokacin sallah Isha'i yati sannan tayi,
Jin karar TV tun Dazu ne yasa ta fito falon,
Yana zaune yana kallon Boll a wani tashar,
Zama tayi kusa dashi tana daura kanta a samar kafadarshi,"partner yunwa nake ji"
Zame kanta yayi daga jikin shi yana dan matsawa kaɗan "ki yi mana ordan abinci dan nima yunwa nake ji"
Ƙara matso shi tayi tana riƙe hannun shi,"shine baka tayar da ni ba?
"Naga kin ji daɗin barci ne shi yasa,"
"To bari na baka number su koda wani lokaci idan kana bukatar abinci sai ka nime su"
Hannun shi ya cire cikin nata yana mika mata wayar shi dake gefen shi,
Amsa tayi ta saka mai sannan tayi seving,
Lura da tayi kamar baya son tana taɓa shi ne yasa ta kyale shi,koda suka kammala cin abinci daki ya koma,duk yanda taso tajashi da hira,
Ita ma bata jima tana kallon ba ta kashe kayan kallon ta koma daki,
Ta dauka idan ta shiga daki zai biyo ta su kwana tare kamar yanda taga sauran sababbin ma'aurata ke yi,sai dai shi ko kofar ɗakinta bata jin ya taɓa,gashi kuma maganin da taje ta dinga banka ma cikinta wanda ta siya a ɓoye ya fara mata aiki,dan da kyar ma ta iya barci,
Washegari da safe tana idar da sallah dakin shi ta shiga,yana kwance saman gado yayi dai daya yana sharar baccin shi hankali kwance,ji take kamar ta fada kamshi ta rungume shi,
Ajiyar zuciya kawai take saukewa,
Jan bargon tayi tana kiran sunan shi a hankali,
Da kyar ta samu ya tashi"tashi ka shirya kasan yau zamu shiga makaranta"
Shi sam yama manta da wanin karatu,dan nashi bangaren kasuwanci zai karanta,amma duk makaranta daya ne sai dai kowa da Department din shi,
Tashi zaune yayi yana yamutse fuska "ki je ki shirya ganinan fitowa"
Fita tayi dakin tana jinjina nauyin barci irin nashi,
Wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga na jallabiya baki sai karamin mayafi data naɗe kanta da shi,
Fitowa tayi riƙe da karamin jakka a hannun ta,dayan hannun kuma makullaine,
Cira wasu daga cikin shi tayi ta mika mashi"ga makullin dakin ka,wannan kuma na gida ne sai ka riƙe ɗaya,nima na riƙe data saura kuma zamu ajiye saboda tsaro,ko mantuwa "
"Ok" Kawai ya fada,
"Idan mun fita sai mu tsaya ka ci abinci"
Dagowa yayi ya kalle ta"ke fa "
Wannan ne karo na farko tun zuwan su jiya daya mata tambayar dake nuna alamun an damu da mutum,
Dan haka murmushi tayi"ni sai zuwa ƙarfe goma zan karya "
"Ok to nima ba wai ina karya da wuri bane,ki bari idan zaki cin abinci sai ki kira ni"
Jinjina kai tayi,
Koda suka isa katafaren makarantar tare da mutumin ba Baba ya hada su shi ya taimaka masu sukayi komai,sannan aka tura dan sako ya kai kowannensu Department din shi har kuma ajinsu,sannan aka nuna masu dakin karatu na ɗaliban,
Babu abun da yafi mata daɗi sai ganin cewar ƴan ajinsu basu da yawa basu wuce su goma sha ɗaya ba,
Kujeran ta a kusa da na wata yarinya me suna Suba yake,ita ƴar ƙasar Rasha ne,balarabiya,
Mika mata hannu tayi suka gaisa take fada mata sunan ta,da kuma garin su,ganin yanda tayi shiga kamar wata yar uwar su balarabiya,ta kuma yi mamakin jin cewar ita ƴar Nijeriya ce,
Koda suka kammala darasi ƙarfe sha biyu na rana,kallon agogon hannun ta tayi"lokaci ya tafi,ni zan wuce sai mun haɗu gobe"
Daga mata hannu tayi,"karki manta gobe ƙarfe biyu na rana muke da darasi"
"Insha Allah" Ta faɗa tana cigaba da tafiya tare da ciro wayarta a cikin jakka,number shi ta shiga kira,sai dai sai da yayi kara kusan sau uku sannan aka ɗauka,"kana ina ne"shine tambayar data fara mashi,
Dan shiru yayi kafin taku ta ji yace"ina wani wuri "
"Acikin makaranta? Ta kuma tambayar shi,
" A'a na bi wani aboki na ne zan karba abu a wurin shi,amma ba jimawa zan yi ba yanzun zan dawo,kin koma gida ne?
"A'a yanzun muka gama lecture,dama na kira ne na tambayeka ko kun kammala sannan kaci abinci?
" Eh karki damu na ci abinci,ki tsaya ki siya kici sai ki wuce gida,"
"Ok sai ka dawo"
Kit ta ji an kashe wayar ba tare da ya bata amsa ba,gyaɗa kai tayi tana mamaki da yaushe yayi aboki daga fara zuwa makaranta yau har kuma zai bi shi gida,koda yake su maza ne sunada saurin sabo da juna,
Da wannan tunanin tabar makaranta ta tsaya a wurin cin abinci ta ci sannan ta wuce gida.
Wanka tayi ta sauya kaya sannan ta shiga gyaran gidan nasu,har ɗakin shi sai da ta kyara tayi moping sannan ta fito da kayan daya cire ta saka a abin wanke kaya ta shanya,
Ko kafin ta kammala ƙarfe uku tayi,dama ta riga tayi sallah dan haka wanka tayi,
Jin motsi a falo ne yasa ta fito daure da tawul,
Kallon shi take yi yana daura wani leda daya shigo dashi a saman tebur,
"Ka dawo" Ta faɗa tana karasa fitowa,
Kallo daya ya mata ya ɗauke kai "eh na dawo,ga fruits na siyo,naga kina so"
Murmushi tayi"Thank you"ta faɗa tana ƙoƙarin karasawa inda yake,sai dai kafin ta karaso har ya doshi dakin shi,
Tura baki tayi tana jin wani iri a zuciyar ta,shi wai me yasa baya nuna ɗoki a kanta,baya nuna yana ra'ayin ta kamar sauran amare,sai ma gudunta da taga yanayi,
Jin wayarta na ƙara ne yasa da sauri ta koma daki tana ɗaukar wayar,
Ganin sunan Mama a rubuce ne yasa ta ɗauka da sallamah,
Amsawa tayi cikin sakin fuska"Amarya ya kike"
"Mama" Ta kira sunan ta a shagwabe,"ko dai na cemin amarya "
"Me yasa zan daina ce maki amarya,tukun na ma ya naji kamar ranki a ɓace yake?
" Ba komai kawai dai yanzun na dawo makaranta na gaji ne,kin San kuma bana shiri da yunwa,wallahi har na fara jin kewar gida "
Dariya Mama ta saka"in banda abinki ba sai ku yi odar ba,ina shi mijin naki?
"Ya shiga wanka dan tare muka dawo,yauwa gashi ya fito,bye Mama i Love you" Kit ta kashe wayar tana zama bakin gado,tama rasa wani irin tunani ya kamata tayi,
Tashi tayi ta saka kaya ta fito ta shiga kicin,dan yau ita zata masu girkin dare tunda suna da komai a kicin,
A haka suke wannan zaman har yau da suka cika kwanaki huɗu da zuwa garin,babu wani abu ɗaya canja a tsakan zaman takewar su,baya wani nuna damuwar shi a kanta ko abinda ya shafeta,idan ya dawo yana kunshe a daki yana kallo a wayar shi,ita bata masan Uwar me yake kallo ba,amma da zaran ya ganta ta shigo da sauri yake kife wayar,idan kuwa ka gansu tare to abinci suke ci,
Ta gefe ɗaya kuma gashi maganin da ta sha sai nukurkusar ta yake yi,da kyar take iya samun barci da daddare,
Kamar dai kyau tsabar nauyin da maranta keyi mata tasa ta zauna tana sharan hawaye,dumin duk wani hanya da zata bi domin karkato da hankalin shi kanta tayi amma abun baiyi aiki ba,idan yaga ma kamar zata matsa mashi sai ya shige ɗaki ya kulle ƙofa,
Karan da wayarta ke yi ne yasa ta share hawaye tana jawo wayar,ganin sunan Mama ne yasa ta sai saita natsuwar ta tana ƙara wayar a kunne,
"Barka da Dare Mama"
"Barka dai Salma ya kike"
Ji tayi wani hawayen ya sauko mata saboda jin yanda maran ke ƙara tsungulinta "ina lafiya Mama"
Dan shiru tayi na wani lokaci kafin ta ce "ina mijin naki?
" Yana daki "
"Me ya same ki?
Kara share hawayen ta tayi" Babu komai "
"I expect more than this,dan haka faɗamin,zan iya taimaka maki da shawara,karki boyemin komai"
Bata masan santa ta fashe da kuka ba,kun san yanda lamarin yake,tsakanin uwa da ɗa sai Allah,
Dan haka sai da ta bari taci kuka ta dan kanta har zuciyar ta yayi sanyi kafin tace"fadamin yanzun meke faruwa"
"Mama ki yi haƙuri,ana sauran kwana uku aure na naji maganar da kuka yi keda Aunty Hulaira akan kayan Mata,ki yi haƙuri bansan me kika gani ba,ban kuma san dalilin ki ba na kin bani nasha,amma shine na ɗauka ko dan baki son aure na da Yusuf ne shi yasa kika hanani,shine na haɗu da wata mata a online yar Sokoto na siya kayan mata a wurin ta,a washegari aka kawo min saboda na zuba mata kuɗi,
Yanzun kuma gashi tunda muka zo babu abinda ya shiga tsakanin mu,Mama marana ciyo yake min kamar ya fashe"ta karasa faɗa tana saka sabon kuka.
Ajiyar zuciya ta sauke "kina jina Salma"
"Ummm"
"Ina son ki natsu ki saurari abinda zan faɗa maki,a duk lokacin da kika ji kina bukatar mijinki karki saka kunya a lamarin,domin shi mijinki ne duk abinda kika mai ba abin kunya bane,ki je ki same shi ki faɗa mashi you need him,kina bukatarshi,karki ji kunya,ina nufin ko wani lokaci,domin irin su in kina zaune dasu ba zaki taɓa burge su ba,"
"Mama kenan ba zan taɓa birge Yusuf ba kome zan mai,ina ƙoƙari kullun in share gida in yi girki sannan in wanke masa kaya,amma kuma duk da haka ba zan taba burge shi ba?
Bata son ta bata tsoro ko ta sare mata guiwa,amma maganar gaskiya shine abinda ta faɗa,ba zata taɓa burge shiba,"Sweet heart kina jina?
"Umm".
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*65*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
"Daga yau karki kuma yin komai domin ki birge shi,ban yarda ki dinga yin wanki ba,ba laifi idan kin yi aikin gida kin gyara masa daki,amma banda wanki,
Yanzun yana ina ne?
" Yana dakin shi"
"Tashi ki je ki same shi a dakin ki faɗa mashi kina bukatar shi"
"Mama ta yaya a matsayina na mace zan fara kai kaina wurin mijina,shin kina ganin hakan ba zai zamar min abun magana ba?
" In dai a wurin sune hakan ba komai bane,ki yarda dani hakan ne kawai mafita a gare ki,ba wai ina nufin daga yau shikenan ki rabu dashi ba dan kin samu abinda kike so,ki yi tunanin ai zai biyo ki,ba zai taba binki ba,tashi kawai ki tafi,da safe ki kirani "dif ta kashe wayar ba tare da ta jira ta ji me zata ce ba.
A gaskiya tana buƙatar shi yanzun,idan har bata yi yanda Mama tace ba,to ba lallai bane ta iya kaiwa wayewar gari,
Dan haka tashi tayi ta saka kayan barci marasa nauyi farare sannan ta doshi dakin shi,
Allah yasa yau ƙofar a buɗe take,saboda yasan bata cika shigowa ɗakin da daddare ba,
Yana kwance yau ma kamar ko wani lokaci yana kallon a waya,kanshi na saman filo ya daga wayar sama,
Duk sallamar da tayi bai ji ba domin daga dukkan alamu yayi nisa wurin kallon abinda ke cikin wayar,
Dan girgiza mashi kafa tayi tana kiran sunan shi,
Cikin sauri ya kife wayar yana zabura,
Wannan ne karo na farko da ta fara ganin bacin ranshi, cikin fushi da jin haushi yace"wannan wani irin rashin hankali ne da rashin tarbiyya,wani irin hauka ne zaki shigo min daki babu sallamah,"dafe goshinshi yayi "shi yasa auren yaran masu kuɗi matsala ne," Tsaki ya kuma ja
Karo na farko da tsoron shi ya fara shiga zuciyar ta,bata son ihu,dan nan take hankalin ta ke tashi,
A tsorace ta matsa baya tana kallon shi"na yi sallamah har sau uku baka ji ba"
"Karya kike yi,ni kurma ne da zaki ce kin yi sallamah banji ba,karya kike yi"
Ita yarinya ce sosai a lokacin,domin shekaranta goma sha biyar a lokacin,amma duk da haka tasan ciyon kanta,bata kaunar ace mata karya take yi,sai taga kamar an muzanta ta ne,
Juyawa tayi kawai ta bar dakin tana fashewa da kuka,domin abun ya bata mata rai,
Daki ta shiga ta turo ƙofar ta kashe wuta tana cigaba da kuka,
Dafe kai yana tunanin kar taje kuma ta sanar da mahaifiyarta,dan yasan idan mahaifinta ne ba zasu samu matsala sosai ba,
Kila akwai abinda take so,
Dan haka fitowa yayi ya shiga ɗakinta,ganin wutar dakin a kashe yake yasa ya mika hannu ya kunna wutar,
Karasa yayi in da take kwance kan gado ya rungumota jikin shi"i am Sorry Baby,ki yi hakuri ba zan sake maki ihu ba"
"Ka fita kawai ni bana son ganin ka"
"Ki yi hakuri kinji ai nace ba zan sake ba"
Da wannan damar tayi amfani wurin baiyana masa manufarta ta hanyar haɗe bakin su wurin daya,
To tana iya daurewa ta kira wannan daren da First Night din ta,amma ba wai dan ranta yaso ba,domin kwata_kwata bai wuce minti goma ba yayi releasing a jikin ta,kuma ya sauka ba tare da damuwar ta gamsu ko bata gamsu ba,
Ita a yanda ma take daukar daren sai gashi ba haka yazo mata ba,
Ganin ya saka kayan shi ya fita ne yasa dole ta tashi ta haɗa ruwan dumi ta shiga sannan tayi wanka,
A maimakon ta ji zuciyarta yayi sanyi sai ji tayi wani abu ya tsaya mata a wuya,dan haka dunkulewa tayi a wuri ɗaya ta fara kuka ko zata ji sanyi a ranta.
Washegari koda ta fito har ya riga ta fita,dan haka kyaran gida tayi sannan ta wuce makaranta,
A hankali lokaci ke tafiya yayin da dare ke yi kafin ka sani gari ya waye,
Wanda a haka suka wayi gari suna da shekara daya harda watanni biyar a wannan garin,domin kuwa har sun fara lissafin lokacin komar su gida,
A cikin wannan lokacin ta fuskanci matsaloli masu tarin yawa na rayuwa,
Domin kuwa zata iya rantsewa sau uku kaɗai Yusuf yayi mu'amalar aure da ita,shima kuma kamar bada son ranshi yake haka da ita ba,tayi mashi rokon duniya akan idan yanada matsala ne ya yarda suje suga likita,amma ya ki amincewa,
Wani lokaci sai yayi kwana biyu zuwa uku baya kwana gida,a haka kuma bata isa tayi korafin ba,zai fara faɗa da tayar da jijiyoyin wuya,
Sam bata jin daɗin rayuwarta,wanda da wannan damar ne ƙawarta Suba tayi amfani ta fara koya mata harkar shaye-shaye,tun daga shan Sigari har zuwa tauna Kwaya,in da Allah ya taimaka dai shine basu shan giya,
Kuma har yau idan har ta kira Mama ta fada mata halin da take ciki sai dai ta ce taci gaba da addu'a,
Ranar da suka kammala makarantar su aka