Showing 114001 words to 117000 words out of 159134 words
Chapter 39 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
din ba d......
Katse ta kaka tayi ta hanyar kara tambayar shi a karo na biyu" Wai ni Surajo na tambaye ka ina Habiba baka Bani amsa ba har yanzun"
Kallon Ammi yayi wacce ta mai magana da ido,
Juyawa yayi kan Kaka"ki yi haƙuri Kaka,tana Asibiti yanzun haka"
"Me ya same ta,Allah yasa ba hannun bane ya matsa mata?
Furzar da iska yayi cikin yanayi na dan damuwa yace" Ba hannun bane,domin yanzun haka aiki za'a mata zuwa anjima "
Dafe kirji tayi tana salati "wani irin ciyo ne haka ya same ta da za'a mata aiki"
"Jiya ne da aka fito koto,a yanda nake samun labari daga bakin durebanta wai taga wasu sun fito daga cikin koton sun shiga mota,to shine tace ya bi bayan su da ita,suna zuwa ta bar shi a waje ita kuma ta shiga cikin gidan,to bansan waye ta gani ta bi ba, ko kuma me ta ji a can,kawai dai sai gani yayi ta fito da gudu wasu na binta,ashe garin gudu sun samu nasaran buga mata ƙarfe a kai,"cewar Ammi
"Yaya to wasu mutane ne waɗannan? Sannan me tai masu"cewar Khadijah
"Koma dai me tai masu wannan karon sun zaɓi hanya mara bullewa"
"Idan har kasan ba zaka iya kula da ita har haka ba me na bari ta shiga cikin rigimarka? Nurudeen ya fada cikin yanayi na jin haushi,
"Kasan ko su waye ne?gaskiya ko su waye basu kyauta ba"
"Umm na sani" Ya faɗa yana sauke idanun shi akan Shamsuddeen, "Kaka zan fita zai dai zuwa anjima"
"Ka faɗa mana wani Asibiti ne sai mu je mu dubata" Cewar Goggo,
"A'a Goggo ki bari zuwa gobe sai kuje ku dubata saboda yanzun ko kunje ba za ku samu damar ganin ta ba"
"To ba damuwa Allah ya kaimu ya kuma bata lafiya"
Da Amin ya amsa yana fita.
Yana fitowa kai tsaye shiyan Ammi ya nufa,har ya kusa isa yaji daga bayan shi ana kiran kiran sunan shi,
Tsayawa yayi yana jiran karasowar ta,
"Ya aka yi Maijiddarh?
Matsowa tayi ta gefen shi ana ana dukar da kai" Yaya Suraj nayi farin cikin dawowar ka sosai"
"Na gode"
"Yauwa ya jikin Habiba?
" Da sauƙi Alhamdulillah"
Ganin tayi shiru ne kamar wacce bata da abun faɗa yace"ina iya wucewa"
"Eh,amma anjima zan zo Asibiti na dubata"
"Ok ba damuwa sai kin zo" Ya faɗa yana karasa shigewa cikin falon,
Da kallo ta bi shi tana jin tamkar tace ya tsaya,sai dai tasan a yanzun ba tada wannan damar,amma zata jira har zuwa sanda zata samu dama.
Yana shiga shiyan Ammi tsayawa yayi a babban falon su yana tsura ma hoton da sukayi gaba dayan su ido wanda harda Shamsuddeen a ciki,
Ji yayi daga bayan shi an dafa shi,
Juyowa yayi yana ganin ita ce ta rungume ta,
Ita ma rungume shin tayi tana Hamdala ga Allah maɗaukakin sarki,
Hannun shi taja suka shiga har cikin dakin ta sannan ta maida kofa ta rufe,
Zaunawa tayi saman gado yayin da ya zauna a kujeran dake gefen ta,domin baya taba yarda ta zauna mata a saman gado,duk da yasan ba nan suke kwana tare da Abbu ba.
"Shin an samu nasara kuwa?
Lumshe ido yayi ya buɗe" Ammi an samu fiye da baya"
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi"kayi haƙuri Suraj na saka ka damuwa da yawa sanadin wannan aiki,sai dai ka sani dole sai ka sadaukar da wani abu kamin ka sami wani abun,
A lokacin dana samu karin bayani akan wannan shirin nasu hankali na ya tashi sosai,na rasa ta wani hanya zan bi domin tseratar da kai,ka yi hakuri shi yasa na juya wasan ta yanda basu yi tsammani ba,sai dai gashi ta sanadin haka the innocent soul is suffering,ina fatan zaka yafe min?
Rike hannun ta yayi"ba kiyi komai ba Ammi,kin yi ne dan ki taimaki rayuwar ɗan ki,and na tabbatar da she will understand you,fata na yanzun Allah ya bata lafiya"
"Amin ya haiyu ya kaiyum "
Ya tsanshi biyu ya saka a cikin idanunshi yai gashi ya ciro wani dan abu kamar leda fari tas wanda ya hade da kwayar ido,baka iya sammanin ya saka abu a ido,buɗe wani karamin contena yayi ya saka wannan ledar idanun guda biyu, wanda nan take asalin kwayawar idanun shi suka baiyana,
Rufewa yayi ya mika ma Ammi"komai yana cikin nan,yanzun abu ɗaya ya rage mana mu kammala haɗa hujja "
"Shima dab muke da cimma shi,sai dai ya maganar iyayenta?
Busar da iska yayi yana shafa fuskar shi" Ada nayi tunanin kiran kiran su,amma dai yanxun ina ganin gara mu bari idan an yi aikin ta samu lafiya"
"Eh hakan yayi,yanzun yaushe zaka koma Asibitin?
" Sai bayan Sallah Magrib"
"Ok Allah ya kai mu"
Da Amin ya amsa yana tashi,
Daganan gidan shi ya nufa inda anan su Bala suka saka sabon kukan murnar ganin Ubangidan nasu.
*Bayan wasu Awanni*
Yana fitowa masallaci ko gida bai koma ba ya wuce Asibiti,
Yana yin parking mota kiran Dr na shigowa wayar shi,
Ɗauka yayi yana karawa a kunne,
Daga ɗayan ɓangaren yace"kana ina sir Suraj?
"Gani a cikin Asibiti"
"To kayi sauri ka same ni a ofishi na"
Ba tare daya ce komai ba ya sauke wayar,yana karasa shiga cikin Asibitin,
Yana isa ofishin ƙwanƙwasa kofar yayi domin mutumin ba Musulmi bane,
Umurnin shiga aka bashi sannan ya shiga,
Nuna mashi wurin zama yayi"zauna"
Zaunawa tayi"ina fatan babu wani matsala?
"A'a da sauƙi dai,dama jini muke nima saboda aikin da za'a shiga da ita,shine nake son na tambaye ka,shin a saka mata jinin siyarwa,ko kuma a family za'a samu wanda zai yi donating blood"
"In dai wannan ne babu damuwa zan yi donating blood dina saboda ni (O-) negative ne"
"Yauwa to yanzun zamu tafi LAB domin a fara ɗiban jinin ka a duba,sai a duba nata jinin ita ma"
Mikewa yayi"to mu je,yanzun saura awa nawa a shiga aikin"
"Saura dai mintuna talatin"
Tare suka jera har Lab din in da anan ka ja jinin shi suka fara gwadawa,shi kuma yana zaune a reception,har suka je dakin da take suka dibo jinin ta,
Yana dai zaune yana danne _danne a wayar shi yaga wanda yazo ya dibi jinin ta ya fito da sauri,kafin wani lokaci kuma sai ga wasu manya daga yan Lab din sun zo sun shiga,
Yana dai zaune yana lokacin_lokaci yana duba agogo,a haka sai gashi har an kwashe kusan mintuna ishirin,
Likitan da zai mata aiki ne ya ga anje an kira tare da wasu likitocin ma,
Hakan ne yasa a jiye wayar a gefe yana tunanin ko lafiya,gashi lokaci na ta kurewa,
Dr Daniyal ne ya fito jiki a sanyaye yazo in da yake,
Shima yana ganin shi ya mike tsaye,
Dafa kafadarshi yayi"mu je Lab akwai abinda nake son nuna maka "
Jinjina kai yayi yana bin bayan shi "da fatan dai lafiya?
Bai bashi amsa ba har suka shiga ciki,sai dai ba ta inda aka diba jinin shi ba ne,wannan wani madaidaitan falo ne,mai dauke da kujeru sai kuma likitocin dake zaune a wurin su uku ko wanne fuskar shi dauke da damuwa,
Nuna mashi wurin zama sukayi ya zauna,
Sannan daya daga cikin su ya fara magana kamar haka"Malam Suraj Abdulbasir,matarka ita ce Ummu Salma Abdullah "
"Haka ne"
Ajiyar zuciya likitan ya sauke"muna son mu sanar da kai cewar cuta ba mutuwa bane,sannan duk wani cutar da Allah ya saukar dashi sai da ya saukar da magani,sai dai wani lokaci kafin mu fahimce maganin ne sai ya dauke mu shekaru masu yawa,"
Katseshi yayi"ka fada min meke faruwa kai tsaye "
Daukar Rimot din wani karamin TV yayi dake jikin bango ya danna,sai gashi wasu irin abu na yawa a cikin TV,kamar dai a saka mai a cikin ruwa yanda yanda yaje rabewa yana hadewa,
Nuni ya mashi da TV"wannan shine gwajin jinin Matar ka da muka yi,wanda ya tabbatar mana da tana dauke da *LEUKEMIA* *CANCER OF THE BLOOD* wanda ya nuna a cikin jinin ta sakamakon kwajin da muka je yi tsakanin jinin ka da nata.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*70*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Gabaɗaya karamin falon shiru ya ɗauka na sakanni yanda kasan babu mutane a cikin shi,
Sai da suka ƙara maimaita mai maganar ganin kamar baida niyar cewa komai,
"Rayuwa da mutuwa duka na Allah ne,nasan cewar tun daga lokacin da aka hallicci ɗan Adam Allah ya riga ya dibar masa iya numfashin da zai shaka a rayuwar sa,
Bai isa ya kara ƙofa da ja daya bane" Dago idanun shi yayi wanda suka sauya daga farin da suke zuwa wani yanayi da baka isa ka fassara halin da zuciyar shi ke ciki ba,yanayi ne da duk wani bawa mai tawakkali da karfin imani kan tsince kansa a ciki a duk lokacin da wata masifa ko jarabawa ta same shi.
"Hakan na nufin lokacin rasa ta yayi?
" A'a ba haka lamarin yake ba Sir Suraj,wasu mutane sun dauka da zaran ance mutum na dauke da ciyon Cancer shi kenan lokacin mutuwar shi yayi,abun kuma ba haka yake ba,yanzun an samu cigaba a duniya fiye da yanda mutum ke tunani,kullum sababbin lamari ƙara fitowa suke yi,ka ga kamar na Matar ka,ya zama matsalarta biyu ne,wanda nake ganin idan har muka shawo kan matsalar zata samu lafiya ta koma dai-dai kanar da"
Ganin bai ce komai ba ne yasa yaci gaba da bayani kamar haka,yana matsar da hoton dake jikin TV zuwa wani,
"Wannan hoton Kidney ta ne,wanda ya nuna mana saboda rashin functioning yanda ya kamata ya janyo wannan Leukemia ɗin,
Ɗan Adam yana iya amfani da Kidney daya kuma ya rayu,to sai dai ita dama a sakamakon binciken da muka yi ya nuna an taba mata aikin Kidney har an cire daya,da daya take amfani,wanda shima yanzun ya samu matsala ta sanadiyar shan kwayoyin da take yi ko wani lokaci,sannan da shan taba,ma'ana Sigari,duk da illar sigarin ba sosai bane dan bai kai kwayar da take ci yawa ba"
Hannun yasa yana shafa gaban goshinshi da yaji yana mashi ciyo lokacin daya,ba tare daya dago ba yace"me abin yi yanzun?
"To da farko dai dole muna buƙatar wanda zai iya Donating blood cell,sai ayi abinda ake kira da *STEM CELL TRANSPLANT* kafin nan kuma ita kuma za'a mata *Chemotherapy* is to kill the blood forming cell,
Idan har an kammala an samu nasara,sannan ne zamu mata asalin Surgery na kai da kuma Kidney Transplant"
"Yaushe ne za'a fara gudanar da aikin?
" Eh aikin ba shine matsalar ba,matsalar shine wanda nasu cell din zai dace da juna wanda zai iya bata kyauta ko kuma dai a siya,sai kuma batun Kidney,duka ba abu bane mai sauƙin samu nan kusa,dan haka dai zamu cigaba da daurata a cikin Coma har sanda za'a mata aikin in an samu"
Mikewa tsaye yayi"na gode "ba tare daya jira cewarsu su ba ya fito daga ɗakin,
Har yayi taku uku yaji an kira sunan shi,
Ji yayi kamar ba zai tsaya ba,sai kuma ya juyo,da sauri Dr din ya karaso in da yake" Wucewa zaka yi"
"Umm" Ya bashi amsa yana kauda kai,
"Mu je ka ganta"
"No"ya faɗa kamar mai ciyon baki,
Cikin mamaki yace " No fa kace,I thought you care so much,kuma zaka so ganin ta"
"Zan iya tafiya,domin inada abun yi"
Kasa ba shi amsa yayi,sai ma rakashi da ido da yayi har ya bulle ma ganin shi,
Shifa a nashi tunanin yanda yaga ya nuna damuwa sosai a Legas a ranar farko da aka kawota,hankalin shi a tashe,sai yake tunanin zai iyayin komai domin ita,yanzun ma yana tunanin wannan maganar da suka faɗa mashi sai sun rike shi,amma sai gashi yana nuna kamar abin bai dame shi ba,shifa bai gane ba,
Ganin kanshi na ƙoƙarin kullewa ne yasa ya gyaɗa kai yana wucewa.
Yana fitowa daga cikin Asibitin kai tsaye wurin parking mota ya nufa inda ya ajiya Motar shi,ji yake zuciyar shi na mashi wani irin zafi da raɗaɗi,a maimakon daya shiga ya tayar da motar ya wuce,sai kunna AC da yayi ya rufe Glass ya haɗa kai da Sitiyarin motar,
Ya dauki lokaci mai tsayi a zaune a cikin motar da ana tunanin samun mafita wanda aƙalla yayi awa daya zaune kafin ya yanke shawarar da zuciyar shi yafi tsayawa a kai kafin ya tada mota yabar Harabar Asibitin,
Kai tsaye gidan shi dake Sultan Road ya nufa,
Yana shiga daki zama yayi a baƙin gado yayin da hannun shi ke riƙe da waya ya tsura ma wata number ido kamar mai shirin tantance wani abu,
Ajiyar zuciya ya sauke a karo na ba adadi kafin ya danna number cike da fata iri-iri,
Sai da wayar yayi Ringim sau biyu sannan aka ɗauka da Sallamah,
Amsawa yayi cikin muryar nan nashi mai matuƙar sanyi,"Ina magana ne da *Abdulmajid* ?
"Eh dashi ne,pls waye ke magana?
Shiru ne ya ratsa wayar na ɗan wani lokaci wanda har sai da ya ƙara maimaita tambayar kafin ya buɗe baki kamar wanda aka tilasta yace" Kana magana ne da Suraj Abdul basir "
Tun daga nan ban kuma sanin me yake faɗi ba saboda yanda yake magana a hankali,
Sun dauki lokaci mai dan tsayi yana magana kafin naji yace"Sai kun iso "ya sauke wayar ya koma ya kwanta yana lumshe ido,wanda Allah ne kaɗai yasan me ke gudana a ran shi.
Ranar a gidan ya kwana,yayin da yanda yaga rana haka yaga dare,sai dai banbancin shine bai bata lokacin shi a banza ba,domin Alwallah ya dauro yana mika kukan shi da godiyar shi a wurin Allah mai yin yanda ya so.
Bashi ya kwanta ba sai bayan ya dawo daga sallar Asuba sannan bacci ya dauke shi,
Jin yanda wayar shi ke ta ƙara ne ya tayar dashi daga nauyayyen baccin da yake yi,
A hankali yake buɗe idanun shi yana lumshewa har sai da ya tabbatar da ganin shi ya dawo dai-dai sannan ya mike zaune,nan ma bai tashi kai tsaye ba saboda yasan illar dake tattare da mutum yana farkawa daga bacci yayi saurin tashi,
Sai da ya ƙara mintuna uku kafin ya mike tsaye ya nufi ban ɗaki,
Wanka yayi cikin sauri ya shirya cikin Kananan kaya da jaket na maza wanda kayan ba karamin fitowa dashi sukayi ba,sai baƙin facing cap daya saka saman lafiyayyen gyararren gashin kanshi,wanda yasha Kalolin mayuka masu matukar kamshi,
Turaren shi mai matukar sanyin kamshi ya fesa sannan ya mai da ya ajiye,
Fuskar nan nashi har wani ƙyalli yake da ɗaukar ido,yayin da kwarjinin shi yake karuwa a duk lokacin da zaka daura idanun ka a kanshi,
Ko kaɗan yau babu fara'a a fuskarshi,domin yau yan halin na kusa,
Agogon Azirfar dake ajiye gaban madubi ya ɗauka ya saka a hannun shi sannan ya fito bayan ya ɗauki makullin daya daga cikin sabbin motocin dake fake a cikin gidan a wani keɓantaccen wurin wanda in dai ba lura kayi ba da wuya ka gane a kwai wannan garejin a gidan,
Wata Musulman mota baka katuwa mai numfashi ya buɗe,wanda sai ƙyalli da daukar ido irin na niman magana yake yi,
Irin motar nan ne da manyan masu kuɗin Larabawa zaka ga suna hawa,saboda su basu son karamin mota,to irin ta ne,
Kunnawa yayi ya tayar sannan ya bar harabar gidan cikin kwarewa,da iya sarrafata,
Tunda ya shigo layin unguwar duk in da ya gefta kallon mitar ake yi,wasu har leke suke yi suga a ina zai tsaya,
Bai shigar da motar cikin gida ba dan yasan ba jimawa zai yi a ciki ba zai fito shi yasa ya faka ta a waje,
Duk suna tsaye a ƙofar gidan wasu a zaune,kasancewar a kwai ɗaurin auren da aka gama gabatarwa yanzun,
Kallon motar kawai suke yi suna jira suga wani hamshaki ne zai fito daga ciki,sai dai tsayin sakanni ba'a buɗe ba,kai babu ma wata alama da zai nuna maka na cikin motar nada niyar fitowa,
Kallon Nurudeen yayi"gaskiya duk me wannan motar ba karamin tarawa yayi ba,wata biyu kenan da akayi Lunching dinta a Saudiyya"
Ɗayan gayen dake tare dasu ne yace"ai Ibrahim ni wallahi ko wanke wannan motar aka bani na kwana daya an gama min ko mai "
Duka ya kai mashi yana dariya,
Shi dai nurudeen bai basu amsa ba,ya dai zuba ma motar ido ne kawai,domin kusan wata shida kenan tunda aka fara tallar motar ya fara tara kuɗi domin siyan ta sai dai ko rabin rabi har yanzun bai hada ba,duk da Dream Car din shi ne sai dai ya fara cire rai,dan yasan sama tayi ma yaro nisa,kai shi bai ma ɗauka a Nigeria an samu wanda ya shigo da ita ba sai yanzun da yake ganin ta a gaban shi,
Lallai ko waye mai wannan motar to ba karamin kusa bane ko dai a gwamnati ko kuma a wani masarautar,shi jira kawai yake yaga waye a cikin ta.
Sai da ya gama amsa wayar da yake yi kafin ya buɗe marfin motar ya sako kafar shi mai ɗauke da takalmi but farare sabon dizai wanda ba sai an faɗa maka ba kasan bana sawar yara bane,
Karasa fitowa yayi ya maida ƙofar motar ya kulle hannun shi riƙe da wayar shi ya doshi hanyar shiga cikin gida yayin da ya cire facing cap ɗin dake saman kanshi.
Duk da kallon Mamaki suka raka shi har ya bulle ma ganin su ba tare dashi yasan ma suna yi ba,
Basu kadai ba duk wani wanda hankalin shi ke kan fakawar wannan motar sai da yayi mamakin ganin wanda ya fito,domin sun san cewa a rayuwarshi shi mutum ne ba mai fariya ba,da wuya kaga ma yana tuka mota da kanshi,in ma zai tuka to sai dai ya shiga na matsakaita kuɗi,dan har akwai wata rana da Ibrahim ya taɓa mai gatse,akan cewar mu dai munji ance kun gaji dukiya sai dai ko kadan banga alama ba,ƙila ma faɗi ne irin na mutane,domin meshi ai baya