Showing 48001 words to 51000 words out of 159134 words

Chapter 17 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

27 Sep 2025

9762

a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*31*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Tun daga farkon shigarsu layin Sultan Road Jami'an tsaro ne ta ko ina wanda hakan ne zai tabbatar maka da unguwar bata ƙananan yara ba ce,
Tunda Direban daya dauko shi ya shigo layin Jami'an ke tsare shi domin duba wanda ya dauko,domin da mota daya ne suke,kuma sun san duk wanda yake layin da kuma number motar su,da ya tsaya ya sauke glass sun hango wanda ke Hakimce a cikin motar suke Sara mai su basu hanya,

A bakin wani haɗaɗɗen bakin Get din wani gida ya tsaya,wanda ni kaina da badan nasan ba yanda za'ayi a ajiye gidan kwali iska bai dauke ba da nace wannan gidan ba hannu ya gina shi ba,
Gani nayi Get din ya buɗe da kanshi kafin direban ya shiga da motar ciki,nan ma Get din ne ya kulle kanshi,

Wurin Parking motoci ya parkar inda a ƙalla a wurin a kwai motoci sama da guda shida wanda in zai tafi wa'azin dashi suke tafiya,a rufe motocin suke daga dukkan alamu ma an jima ba'a yi amfani dasu ba,
Motar su na gama tsayawa wasu mutane su huɗu suka zo suka tsaya suna jiran fitowar sa,yayinda daya daga cikin su ya buɗe ƙofar motar,
Daga dukkan alamu masu tsaron gidan ne sai dai dukkanin su karfafa ne a koshe suke,

"Yallabai mun iso" Cewar Direban shi,

Buɗe Lumsassun idanun nashi yayi wadanda basu da daɗin kallo ko kaɗan,
Sannan ya zuro ƙafar shi waje,sai da ya dauki sekon goma sannan ya fito gabaɗaya,
Duk rusunar da kai suka yi suka shiga gaishe shi cikin girmamawa,
Sai dai ko ɗaga hannun daya saba masu idan ba yajin yin magana basu samu ba,duk randa kuma ƴan arzikin ke kai zai tsaya ya basu hannun su gaisa yana tambayar ya suke,
Amma na yau kam da ban ne,
Dereban ne ya mike ma daya daga cikin wadanda ke tsaye wayoyin shi daya bari a mota,
Amsa yayi ya mika ma na kusa dashi"Bala karɓa ka shigar ma maigida dashi,ka kuma shirya masa abinci,naga kamar yau a gajiye yake,sai dai kabi a hankali karka cika kwaranniya dan yana buƙatar hutu da natsuwa"

Wanda aka kira da Bala ne ya amsa da"an gama sarkin gida"
Cikin sauri ya bi bayan shugaban nasu wanda tuni har ya kusa isa kofar falon kasancewar a hankali yake takawa,
Yana isa naga kofar ya buɗe da kanshi sannan suka shiga ya kulle,

Ko ina a gyare yake tsaf dashi sai kamshi ke tashi ta ko ina,haka kuma idan ana maganar tsaruwa da kayan Alatu to babu abinda babu na more rayuwa na zamani acikin falon,

Haurawa gidan saman yayi ya buɗe wani daki,ba tare da ya kunna wutar dakin ba ya faɗa kan gado yayi ruf da ciki,numfashi kawai yake fitarwa da sauri_sauri,

Ganin bai kunna wutar dakin ba kuma ya kwanta ne yasa ya ajiye masa wayoyin saman durowan dake bakin ƙofa,dan in yace zai shiga ba ganin gabanshi zai yi ba,

Fitowa yayi daga falon gabaɗaya,wurin Sarkin Gida ya nufa,dan sunan da suke kiran shi dashi kenan saboda shi ke kula da harkan komai na gidan tun zaman iyayen Suraj har zuwa yau shi yasa suke kiran shi da haka,
Zama yayi kusa da shi "ina ga fa akwai Matsala"

"Na me kenan,ya kamata kayi ka haɗa abinci"

"Bai da amfani domin ko nayi ba iya ci zai yi ba,kai baka lura da halin da yake ciki bane,kuma wutar dakin a kashe yake ya kwanta,"

Dan shiru yayi kafin yace"bari na kira Sir Farhan "

"Gaskiya kam,dan ina ga ba lafiya"

Nan take kuwa ya dauki waya ya kira wanda suka kira da Sir Farhan,ban dai san Me ya faɗa masa ba ya dai ce"ok sir"sannan ya sauke wayar,

"Kaje kayi girki amma ka Girka abu mai sauƙi ga shi nan zuwa,"

Tashi yayi ya koma kicin cike da tunanin meke damun Ogan nasu,yasan shi mutum ne mai matukar sauƙin kai da son mutane,shi mutum ne mai taimako duk da aiki suke masa amma yanda yake biyan su yafi karfin kudin aikin su,shi yasa suke matukar jin daɗi zama dashi duk da yana ɗaukar lokaci kafin ya zo,yawancin lokaci a wata sau daya yake zuwa ya duba su ya wuce,wani lokaci kuma idan ya buƙaci hutu to zai yi kwana biyu anan ɗin.

Bayan minti talatin sai ga wani mota ya shigo gidan,
Tashi sarkin gida yayi ya nufe inda yake ɗan tun shigowar shi layin sai da Security suka kira domin tabbatar da ko an san da zuwan shi,
Kyakkyawan saurayi ne shima matashi,zasu zo tsara da Suraj din,
Cikin sauri ya fito motar yana tambayan sarkin gida"ina yake?

"Yana dakin sama"

Bai ce komai ba ya nufi falon,haurawa saman yayi yana shiga ya kunna wutar dakin,
Karasa yayi in da yake kwance yana kiran sunan shi"Suraj,Suraj "sai dai ina bai dago ba bai kuma amsa ba,

Dafa shi yayi,sai dai ji yayi jikin shi yayi zafi gau dan har yana iya ji a hannun shi,cikin sauri ya juyo dashi,yana ƙara kiran sunan shi,
Sai dai a hankali yake buɗe ido shima ba sosai ba,
Kyara mashi kwanciya yayi da sauri ya fito dakin ya nufi motar shi,kayan aiki ya kwaso ya dawo a lokacin ya tadda yana ta faman kwara amai,
Shi da Bala suka taimaka mai sannan ya masa Allurai ya daura masa drip,
Ganin Bala ya fita ne yasa ya kira sunan shi"Suraj,kana jina,in kana jina ka buɗe ido"

Buɗe lumsassun idanun shi yayi wadanda suke nuna halin da zuciyar shi ke ciki,
"Meke maka ciyo yanzun?

A hankali ya motsa Labbanshi" I am fine"

"Ka tabbata?

Nan ma da ido ya amsa mashi,kafin yace " Were is my Phone?

Da sauri ya tashi ya dauko mashi,
Amsa yayi ya shigo wurin kira,sai dai video called ya kira,kuma number bata Nijeriya bane,
Ringin biyu aka ɗauka,sai dai wani Baturen mutum na gani fuskarshi dauke da murmushi,ya kira sunan Suraj din,
Gaisawa suka yi da harshen Turanci,kafin naji yana faɗin"we're is Grandma?

"Do you want to see her?
" Yes "
She is in examination room,give me five minutes "

"Is there any progress? Ya tambaya,

Ajiyar zuciya mutumin ya sauke" We hope so this time,and don't worry everything we'll be all right dear "

"Thank you sir"
"I'm sure your grandma will be very proud of you Suraj,and don't forget anything you're so dear to her"

Wanna ne karon farko tun faruwar wannan lamarin da naga ya dan saki murmushi kaɗan wanda idan baka lura bane ba lallai ka gane anyi shi ba"Thank you Doctor "daga nan ya sauke wayar,

" Akwai abinda baka faɗa min ba,me ke damun ka? Cewar Farhan,

"Im ok"

"No,you not"

Kafin yayi magana ne wayar shi ya shiga kara,sai dai number Dazu ne na kasar waje kuma babu suna dan kamar ba'a yi seving din shi ba,

Video call din ne,dan haka ɗauka yayi,sai dai ba fuskar wannan baturen bane yanzun,wani daki ne lafiyayye irin na ƴan gatan majinyata domin daga dukkan alamu a Asibiti ne,
Wata tsohuwa ce kwance a saman gadon,duk da kasancewar tsufa ya kamata amma hakan bai ɓoye kyawun da take dashi ba,gata a kwance tamkar kace ta tashi,sai dai kuma tana cikin yanayi ne na doguwar suma,

Gani nayi ya tsura mata ido,kafin wani lokaci kuma hawaye ya fara saukowa daga ramin idanun shi,wanda ya kyale su suna zuba ba tare daya goge ba,
A hankali bakin shi ke motsi kafin ya furta"Grandma "

Dafa hannun shi Farhan yayi"she will be ok In sha Allah "

Hannu yasa ya share hawaye idunshi "when?when will she wakeup,?yanzun shekara goma sha ɗaya kenan,har yanzu bata tashi ba"

Cikin tsananin tausayi ya kara damke hannun nashi,domin koma menene ya saka shi a cikin wannan yanayin ba kaɗan ba ne,yasan ada yakan yi kuka,amma yanzun ya daina,ba zai iya tuna zanar da ya ganshi haka ba"na San kasan Allah ya kan jarabci bayinsa ta hanyoyi masu yawa ina fata zaka ci wannan jarabawar ta hanyar haƙuri da juriya "

Kashe wayar yayi ya ajiye a gefen shi sannan ya dauki dayan,wurin Massege ya shiga ya buɗe sannan ya mika ma Farhan,

Amsa yayi yana karanta abin da ke rubuce:i hope you like my present:
"Me haka ke nufi? Ya tambaya

Lumshe ido yayi ya kara buɗewa tare da furzar da iska daga bakin shi" Yau za'a Daura min Aure"ya karasa faɗa can kasan makoshi,

zaro ido yayi sai kuma ya ɗan saka dariyar zulaya "wasa dai kake min?
Ganin bai ce masa komai ba,ya kuma cewa" Hi I know you ar joking right?

Kauda kai tayi,

Hakan ya tabbatar masa ba wasa yake ba"da gaske"ya faɗa da karfi wannan karon "how?when? Where? Who is she?
Matsowa inda yayi yake " Dan Allah Suraj ka faɗa min meke faruwa,kasa kaina ya kulle duk ban fahimta ba"

Juyowa yayi yana fuskantar shi"idan ka natsu sai na faɗa maka komai "

Numfashi ya shiga ja yana busarwa sai da yayi haka sau uku sannan yace"na natsu yanzun faɗa min,"

"Fassarar abinda wasikar ke nufi,ya samu nasara a kaina wannan karon"

"Ta yaya suka samu nasarar ka Suraj,nasan kai mai matukar kiyayewa ne, Allah yasa basu da haɗi da wannan auren daka faɗa?

" Shine ma babban matsalar Farhan,wannan karon da hatsabibiyar yarinya na haɗu,ba kamar waɗancan sauran take ba,tana shan Segret ba kaɗan ba,abinda na fi tsana a rayuwata,tsabar saurin ido irin nata yau da safe yarinyar nan har daki na ta biyo ni,and do you no what she did?

"What? Ya tambaya,

Shafa fuskar shi yayi yana busar da iska"she kiss me"

Duk da ganin halin tsananin damuwa da aminin shi ke ciki,da kuma shima damuwar da yake ciki,hakan bai hana shi bushewa da dariya ba,har yana buga katifa,saboda yanda ya faɗi kalmar She Kiss me kamar zai fashe da kuka,

Tsabar takaici tsaki kawai yaja yana kauda kai.


🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*32*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Tsabar takaici tsaki yaja yana kauda kai,

Ganin kamar ranshi ya baci ne yasa ya saisaita kanshi "Sorry ba wai ina nufin yin dariya ba ne,gaskiya bata yau ta ba,yanzun shi kenan ta rage maka daraja ta maida kai karamin bazawari"

Da sauri ya juya "kamar ya?

Haɗiye dariyar shi yayi" First Kiss,first Night,to ta kwace maka first Kiss dinga,kaga ko a tarihi idan aka ce waye ka fara kissing sai dai c.....

Cikin jin haushi ya dauki filo ya wurga mashi,a zuciyar shi yana tsine ma wannan Kiss din,domin kuwa ta cuce shi,

"Faɗa min ya akayi daga yin Kiss da karfe goma na safe sai kuma batun Daura aure,ina ita mejiddarh,?

"Tunda ta fita daga dakina bansan me ya faruba,sai kira daga Kaka,daga nan ne komai ya canja," Nan ya shiga bashi labarin duk abinda ya faru har zuwan shi nan.

"Amma Suraj a ganin ka waye ya dauki wannan hoton sannan har ya kai ma Kaka,kenan hakan na nufin bibiyar ku ake kuma wannan shiryayyen lamari ne?

" Tun daga farko shiryayye ne,sannan sanin waye mai daukar hoton bashi bane mai muhimmanci,daga shi mai daukar har wanda ya kai ma Kaka dukkan su yan aike ne,matsalar anan shine suna na da ya bata a gidan,ya cire duk wata yardar dake tsakanina da mutanen da nake kallo a matsayin nawa,ya saka mummunar fahimta a tsakanin mu,abinda ke min zafi Ammi! Idan da Ace Pa yana raye,ko kuma Grandma tana nan da hakan ba zai faruba,da ba akai wannan matakin ba,nima da ina da nawa ahalin,
Wani lokaci Farhan mutane suna da mantuwa,Amma babu komai lokaci ne zai tunatar dasu komai "

Dafa kafadarsa yayi"juriya shine ya kamace ka,ina fata ba zaka taɓa nuna gazawarka a idanun magauta ba?

Dan murmushi yayi"cikin juriya nake tsayin shekaru goma sha ɗaya,idan har zan iya z
Durewa na tsayin wannan lokacin me zai hana ni juriya har yanzun,na dai san duk abunda yake ma ba zai taba samu ba,"

"Hakan na nufin kasan waye kenan? To me yasa baza kaishi kasa ba lokaci ɗaya"

Wannan karon mamaki ne ya kama ni ganin irin murmushin daya saki,duk tsauri irin na mayunwacin Zaki,idan har zai yi farautar habin harin shi koda yana gabanshi dole ne sai ya fara dukar da kai kafin yakai cafka,"

"Kana nufin..

Katse shi yayi" Lokaci bai yi ba"

"To yanzun ya zaka yi da wannan auren?

Kallon Agogon dakin yayi wanda ya nuna ƙarfe biyar da rabi na yamma" Bayan sallah Magrib za'a daura,sai dai bansan yanda suka tsara abin ba,sai dai koma me suka shirya I will accept it,domin hakan ma wani mataki ne na nasara ta wanda su basu san haka ba amma ni na sani"

Cikin mamakin abokin nasa yace"me kake nufi da matakin nasarar ka,bayan kace baka son auren kuma ba sonta kake ba,ama ajiye batun so gefe,kasan ita din yar aikin makiyanka ce,ta yaya samunta zai zamar maka matakin nasara"

Dan karamin dariya yayi duk da bai fito ba haƙoran shi ne kawai suka bai yana "ka sa ido ka gani,domin yanzun ne Asalin wasan zai fara"

Shiru kawai yayi domin gabaɗaya ya rasa gane ina ya dosa,Sallamar Bala ne ya katse su,
Shigowa yayi da tire dauke da bowl na abinci da chokali sai goran ruwa da kofi,
Amsa Farhan yayi ya mai godiya sannan ya fita,

"Yaushe ruwan zai ƙare?ya tambaya.

" Zai kai ƙarfe takwas"

"Idan lokacin sallah yayi ka cire min idan mun dawo ɗaurin aure sai ka maida min"

Kallon mamaki yake mai"zaka je ne?

Bai bashi amsa ba sai ma cin abinci daya fara.

_________

Kaka ce ta shigo dakin rike da wani leda mai dan girma a hannun ta,ajiyewa tayi a gefen ta tana zama kusa da ita,
Ganin bata da niyar yi mata magana ne yasa tace"Kinji haushin hukuncin da muka yanke ne?

Dago idanun ta da suka kumbura tayi tare da girgiza kai"kawai dai auren ne bana so,dama ace korata kika yi da hakan yafi min"

Rike mata hannu tayi"na yarda da wannan hukuncin ne badan in cutar dake ba,na tabbatar da cewa wata rana sai kin yi alfahari da wannan hukun namu"

Shiru kawai tayi bata ce mata komai ba,
Mika mata ledar tayi"ki saka wannan kayan domin ƴan awoyi suka rage a ɗaura auren,sannan mahaifiyar ki ta iso munyi magana da A'i ba baza su jimaba zasu iso"

"Na gode"
"Allah ya Albarkaci rayuwar ki"

Dole ne idan har ina son kaiwa karshe na kwantar da hankali nabi komai a hankali, sai dai kuma hankalin nawa yaki kwanciya saboda rashin sanin wani hali Ummita ke ciki,ƙara share hawayen daya sauko mata tayi,wanda hakan ya jawo idanun suka kumbura sosai,
Da yar ta iya lallashin zuciyar ta sannan ta sauki lafiyayyen Les din da yaji aiki ta saka,a cikin kayan harda ƴan kunni da Sarkar wuya na zinari,sakawa tayi da takalmim,kayan ruwan Orange color ne da fari,shi yasa kayan ya bala'in yi mata yau,duk da yanda fuskantar babu ko da digon kwalliya amma ta fito yanda kasan ba ita ba,dan dinkin riga da zani ne Bubu irin na yarbawa wanda ake daura zanin a ciki,ɗaurin ɗan kwalin kuma data daura sai ta sauko da suman kanta ta baya,wanda har ya kusa gadon bayanta,
Wannan ne karo na farko da tayi shiga mai kyau mai kuma ma'ana tunda ta zo gida,
Zura ƙafarta tayi a takalmin wanda yake flat shoe ne fari da kuma madaidaicin mayafi fari,shi kuma a gefen kafardar ta na hagu ta rataya shi,sai turaren data feshe kanta dashi tun daga sama har katsa,

Jin yanda aka buɗe ƙofar aka shigo sannan aka maida aka kulle ne yasa ta dago kanta tana kallon ta,
Zama tayi kusa da ita cikin sauri ta ce "ina fatan ki zama mai wayau mai kuma rike sirrikan kanki,karki taɓa yarda da kowa koma waye,ki yi taka tsantsan sosai domin ta ko'ina za'a saka ido a kanku" Jin an murda kofar ana ƙoƙarin shigowa ne yasa da sauri ta canja magana"haba ke kuwa Biba wani irin kuka ne haka kika yi,kinga yanda idanun ki suka kunbura kuwa"

Wasu mata ne su biyu suka shigo ɗakin,mikewa tayi tana jawo wata acikin su"yauwa Maman Biba kinga yanda idanun ta suka koma kuwa "

Kallon matar da aka kira da Maman Biba tayi"Da kaganta kaga zubin yan duniya,sai dai ba tada wayewa sosai,tana isowa rungume Biba tayi"Haka kuma lamari ya kansance Habibatu,me yasa zaki aikata irin haka"ta faɗa tana saka kukan munafirci,

Ganin Goggo ta zo tayi tsaye ne yasa dole ta kakaro hawaye"Mama ki yi haƙuri ki yafe min,duk laifi na ne"

Ita dayar da suka taho tare nan ta shiga sharan hawaye harda fyace majina,

Ganin Goggo ta wuce ne yasa ta saki matar da sauri dan warin zufa take yi irin kuma mai ƙarnin nan,
Dan matsawa baya tayi kaɗan tana bata fuska,

"Ki ce min Biba ko Habiba,amma banda Habibatu"

Washe baki tayi"in dai baki so ai an gama,ni inama ni aka ba wannan aikin in auri dan gidan masu kuɗi ai da kullun da namar kaza zan dinga brush "ta karasa faɗa suna saka dariya.

Kaka ce ta saka Nafisa ta kawo masu lafiyayyen Abinci da ta saka aka shirya masu,nan suka shiga ci hannu baka hannu ƙwarya,

Jin Ana kiran sallah Magrib ne yasa gabanta faduwa,har aka idar da sallah tana zaune,ba ta iya tashi ta dauro Alwallah tayi sallah ba,ko a sujada kuka take yi,domin wannan lamarin so yake yafi karfin zuciyar ta,a tsorace take,ido rufe take niman wanda zata iya faɗa ma halin da take ciki,
Ta idar tana saman darduma sai ga A'i ta kuma shigowa tana rangaɗa guɗa tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login