Showing 3001 words to 6000 words out of 159134 words

Chapter 2 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

27 Sep 2025

9723

in fada maki Hajiya yau babban malamin nan wanda ake ji dashi a kasa baki daya shi ne zai kawo mana ziyara a garin Abuja,kuma ga shi jama'a daga ko'ina a faɗin Nigeria zuwa suke domin halarta wannan taron Wa'azin"

"Ni kuwa waye wannan malamin"

Dariya yayi "Bara dai na faɗa maki sunan da Matasa ke masa laƙabi da shi,wato YOUNG USTAZ"

Lumshe ido tayi sakamakon faduwar gaban da taji haka kawai daga jin sunan da aka kira,dama kuma tun tambayar farko data mai bata kara fadin komai ba duk maganar da suke tare da Ummita suke,

Maimaita sunan Ummita tayi "Young Ustaz kuma malam,maimakon naji kace Shik wani ko Malam wani"

Murmushi yayi"saboda ko ke kika gan shi kinsan ya dace da a kira shi da young din,domin kuwa shi din yaro ne matashi wanda yake ji da ɗanyen ƙuruciya,da kuma baiwar ilimin Addini da Allah ya mashi,hmm young ustaz kenan,duk yanda ake maki bayanin shi to ya fi nan sai dai kin gan shi kawai,yauwa yau ki kasance a gaban talabijin za'a hasko wa'azin,zaki ga yanda tsantsar kyau da kamala ke zuba,za ki ga......

Da sauri ta katse shi saboda ji tayi kamar kanta na juyawa"ya isa haka Malam sauke mu a nan"

Tsayawa yayi kuwa suka sauka a bakin wani gida matsakaici mai matsakaicin ƙyau,
A kwai mai gadi a ƙofar gidan,wanda yana ganin su ya mike da sauri ya buɗe masu karamin kofa yana gaishe su,

Gidan akwai fili sosai ga wurin parking motoci,wanda naga manyan motoci masu matsifar tsada guda uku,kaloli daban-daban,

Tsayawa tayi a bakin korido tana jiran Ummita data je dauko makulli a ƙasan wani tukunyar fulawa,
Tana daukowa tazo ta buɗe suka shiga,

Sake baki nayi ina kallon ikon Allah,domin falon karan kanshi abin kallo ne,dan ba karamin dukiya aka kashe mashi ba,zaka iya yin mamaki ganin irin wannan haɗaɗɗen falon a cikin wannan gidan,

Ko wacce wani kofa naga ta buɗe ta shiga wanda daga dukkan alamu nanne ɗakinta,

Zama tayi a bakin gado tana sauke ajiyar zuciya,
Rinbon ɗin dake kanta ta cire tana ba suman kanta damar zubowa har gadon bayan ta,

Ɗayan wayar ta ciro daga cikin jakkan tana saka Sim card din data cire a bayan wayar ta kunna,kafin ta gama kawowa ne naga ta jawo dirowar dake gefen gado ta ciro wani kwali wanda ban gane me a ciki ba sai lokacin dana ga ta zaro karan sigari ɗaya,zaro ido nayi ina jira inga me zatayi dashi,
Ban gama mamaki ba kawai sai gani nayi ta kyasta mai wani ɗan abu karamin mai dizai wanda wuta ya fito daga cikin shi,
Sakawa tayi a baki ta mishi kyakkyawan riƙo tana zuka a hankali tare da busa hayaƙin ta baki da hanci,

Ummita ce ta shigo ɗakin,kallon ta tayi, sai dai babu wani alama na mamaki data nuna dan ganin tana shan taɓa,sai ma cewa da tayi,

"Biba yau akwai fita ne?

Kafin ta bata amsa ne wayar dake hannun ta ya shiga ƙara,sai dai bata ɗauka ba sai ma kallon Ummita da tayi" Muna da baƙi anjima,ki tabbatar kin kira Sara tazo ta gyara gidan nan dan yayi kura,ki kuma kimtsa kanki"

Gyada kai tana kallon wayar Biyu da ake ma three miss call,amma bata ɗauka ba"to Biba,bara to naje na fara gyara jiki na"

Bata bata amsa ba sai ɗaukar wayar ta da tayi,wanda tana karawa a kunne naji ta ɗayan gefen ana faɗin "haba Biba ai har kin tayarmin da hankali"

Shiru tayi taki magana sai zukan sigarin da take yi tana busar da iska

"Biba kin dawo lafiya ya aikin,da fatan an samu nasara"

"A ko wani lokaci nasara tana tare da Biba,"

Dariya yayi yana sauke ajiyar zuciya domin ba karamin daɗi yaji ba dajin wannan sanyayar muryar nata,"tabbas maganar ki haka take Biba,to yanzun yaushe zamu zo mu karɓi kayan"

"Ƙarfe goma na dare a gida na"tana gama fadar haka ta kashe wayar,

A nashi ɓangaren kuwa,rungume wayar yayi yana wani lumshe ido,Allah ya gani yana matukar kaunar Biba,duk da yasan yanada ya'ya waɗanda suka girma mata,yana da mata har biyu,kyawawa ga ilimi,
Sai dai kyan Biba na musamman ne,bai damu da Karuwancin da take yi ba,ko kuma wasu harkallolin da take gudanarwa,ko shaye-shayen da take yi,shi dai in har zata amince ta aure shi wallahi yana iya rabuwa da matan shi domin ita,yana iya mallaka mata duk abinda ya mallaka,
Sai dai kash,Biba ba su bane a gabanta,eh dole yace basu bane,domin shi kan shi da yake Minista yasan bashi kaɗai ne ke wannan haukar ba a kanta,
Ita mutum ce wacce baka gane asalen ne burin ta a rayuwa,dan haka take da wuyar fahimta,
A jiyar zuciya ya sauke yana daga wayar shi domin kiran sauran abonkan harkallolin su domin sanar dasu yau zasu haɗu da Biba a gidan ta......
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*05*

Sai da ta ƙarasa zuke sigarin da ke hannun ta sannan ta tashi ta shiga banɗaki,
Ruwan wanka ta tara tafashesshe a bahon wankan sai tururi yake,
Wani loka dake cikin bayin ta buɗe ta dauko wasu goruna sun kai kala biyar sai wasu robobi guda uku,
Wani irin sinadari ne a cikin waɗannan goruna wanda suke ruwa-ruwa,ko wanne sai da ta tsiyaya a cikin wannan ruwan,sanna ta buɗe robobin wanda gayayyaki ne kala kala a ciki,shi ma zubawa tayi,sai roban ƙarshe wanda ta dauko wani busasshen jan ganyen fulawa guda biyu ta wurga a cikin ruwan wanda nan take fulawan ya narke ruwan kuma ya koma wani irin ja mai fitar da wani irin sihirtaccen kamshi mai shiga fata,
Fita tayi daga bayin ta jawo kofar,
Kayan jikinta ta cire tas ya rage daga ita sai bireziya da pant,ta dauki wani mai a karamin gora ta shefe gaba ɗaya jikinta dashi,
Sannan ta dauki wani karamin kafet ta shimfida a zauna,gyaran kumban ƙafarta ta fara yi cikin kulawa,tana shafa masu wani dan mai a kwalba wanda sai da ta kusa minti talatin kafin ta kammala sannan ta koma banɗaki dan tuni ruwan ya huce ya kasance dumi kawai yake dashi,duk wasu tsumin kamshi data saka mashi ya gama jika,dan haka karasa cire ragowar kayan da ke jikinta tayi ta shige cikin ruwan tana nitsewa gaba ɗaya har kanta,
Ta jima sosai a bayin kafin ta fito ta shirya cikin wasu doguwar riga fara tas mara nauyi,rigar zan iya cewa ita da babu duk daya gomin kuwa rigar ta sauka har ƙasa,kuma dogon hannu gareshi,sai dai shara_shara ce yanda kasan lariya,sai dai wani dan yadi mai dan kauri wanda ya rufe daga rabin kirji zuwa haƙarƙari,amma cibiya a waje take,sai kuma daga ƙasan mara zuwa ƙasan duwawu suma a rufe suke da wannan yadin mai dan ƙauri,amma daga cinyarta har kasa ana iya gani,

Zama tayi kan kushin tana kallon tashoshin waƙoƙin turawa hankalin ta kwance,dan lokacin ma ƙarfe takwas ta wuce,

Ji tayi ana ta faman ƙwanƙwasa ƙofa,amma ko kallon wurin ba tayi ba,
Ummita ce ta fito daki da sauri ta zo ta buɗe ƙofar tana tambayar waye,

Ba tare daya kula ta ba ya shigo cikin falon yana kalle kalle,hango ta da yayi a hakimce saman kushin ne yasa da sauri ya karasa in da take zaune,
A kasa ya zauna ya kwashi ƙafafunta ya daura saman cinyarshi yana dan mammatsawa a hankali tare da shafawa,sannan cikin marairaice murya kamar zaiyi kuka yace"Biba ina kika tafi kika barni,kin saka na koma tamkar mahaukaci a garin Abuja ina nimanki,amma kin dawo ko ki nime ni"ya karasa fada yana sumbatar tafin ƙafarta,

Bata bashi amsa ba kamar yanda bata hana shi shafar ƙafarta ba,
"Biba na yi kewar ki tamkar rayuwa," Matashin saurayin ya faɗa yana tasowa tare da kara tsugunnawa sosai a gabanta yana shakar wani ni'imtaccen kamshi wanda yake ƙara tashi daga jikin ta,
Tana kallon shi ya matso da kanshi a hankali ya sumbaci lebbanta,
Nan ma bata hanashi ba,

Lumshe ido yayi yana sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya,ƙara sumbatar bakinta yayi a karo na biyu yana daura hannun shi a saman kirjinta ya shafa,

Hannun shi ta cire daga kan kirjinta sannan ta kauda kanta daga kumbatar da yake mata,
Kamar mahaukaci haka yake ƙoƙarin hawa jikin ta,dan wannan kamshin da yake shaka ji yake kamar zai zauce,

Dakatar dashi tayi"ya isa haka Habib,ka tafi gida gobe zamu yi magana "

Girgiza kai ya shiga yi"dan Allah,dan Allah Biba ki taimaka min,wallahi a matse nake,mayi kewar ki Biba ki taimaki rayuwa ko da romancing dinki ne ki bari nayi,nayi alƙawarin kome kike so zan baki,na maki aikawari "

Mikewa tayi tsaye"kayi abinda nace ko kuma kai da ganina sai nan da sati ɗaya"

Da sauri ya juya ya bar gidan domin yasan tabbas zata iya aikata abinda tace,

Habib ɗa ne ga wani Senator,iyayen shi masu kuɗi ne sosai,shi kuma yana aiki ne a Central Bank,ba karamin kuɗi yake dashi ba,
Sun haɗu da Biba ne a wurin wani party a club,ranar tayi shaya_shayen abinda yafi karfin kanta,shine ta bishi gidan shi suka kwana a can,tun daga lokacin yake haukan binta yana mata barin kudi sai dai ko akai bata kawo shi,wani lokaci ne ma in yaci sa'a takan ɗan kula shi,

Ɗakinta ta shiga bata tsaya ko ina ba sai durowan dazu data buɗe wannan karon wani sacet din magani naga ta ciro,
Daya ta balla ta zauna tana tattaunawa kafin ta kora da ruwa,
Ko minti biyar ba ayi ba ta fara jin kanta na juyawa sakamakon kwayar data ci,

Wani Albom naga ta jawo a ƙarƙashin gado irin wanda ake saka hotuna a ciki,
Buɗe shafin farko tayi,wanda naga tana shafawa hawaye ya fara saukowa daga cikin idanun ta,
Taba ta kuma kunnawa,yayin da ta tsayar da idonta a kan hoton wanda bana iya ganin ko fuskar waye,
Ta ɗauki lokaci mai tsayi a haka kafin Ummita ta shigo "Biba sun iso tun dazu ke suke jira,

Wurge ta kuma yi da Albom din kasan gado kafin tasa hannu ta share hawayen idonta,ta ɗauki wayar ta da hannu daya hannu ɗayan kuma na riƙe da karan sigari ta doshi wani karamin hanyar dake cikin falon ta wanda ya sadata da wani madaidaicin falo hadadde in da wasu Dattijai ke zaune su huɗu suna kiranta,
Kallo daya zaka masu ka shaida cewa kuɗi sun zauna tare da hutu.

Daya daga cikin su yana dariya ya tashi ya rungume ta a jikin shi "na san zaki iya Biba, shi yasa nace ba wanda ya dace da wannan aikin sama dake Biba"

Ita ma dariya tayi tana zama a kan kafar shi bayan ya jata sun zauna saman kushin,
Shafa gemun shi tayi"kai dai faɗi gaskiya kawai dai kasan babu wanda zai iya irin wannan kasadar sai Biba shi yasa dole dai aka nime ta"

Amsar karan sigarin dake hannun ta yayi ya ajiye a saman wani karamin plate yana shafa bayanta tare da shinshinar hannunta zuwa dokin wuyar ta,

Daya daga cikin su ne wanda zuwan shi wurin na biyu kenan ya ce"Haba Alhaji Mansur,wani irin zubar da girma ne haka,wannan ai tayi sa'ar yar cikin ka,ni gaskiya bana son haka,
Kawai ta bamu abinda zata bamu mu ce"yana faɗa yana kallon inda Alhaji Abubakar ke zaune yana ta faman dariya suna zolayar Ummita wacce ita ma ke saman jikin shi dare_dare,shida Alhaji Rabi'u,

Tashi tayi ta kunna wani karamin talabijin dake jikin bango a wurin,tare da soka wannan Memory din a jikin wani ƙaramin na'ura,ta daddana sai gashi ta kamo wani video,
Wani katon mutum ne zaune a bakin gado daga shi sai ɗan garen wanda wanda har ta shafin gabanshi kana gani,babu riga a jikin, ga kuma manyan kwalaben giya a gaban shi sai sha yake yana dariya yana kallon wasu yan mata dake gabanshi,daya daga ita sai pant irin wanda turawa ke sakawa mara amfanin nan da bireziyarshi,daya kuma sikect ne a jikinta irin na Indiya mai faɗi,sai dai yanda kasan lafiya haka yake ɗan kana kallon komai na jikinta ga shi kuma siket din ya nada tsagu ta cinya har Kwankwaso,
Sun kunna wata waka na yaren garin sai wani irin rawa take tana guyi tana karkada mashi kirji,sai dai kuma su ƴan matan ba a ganin idon su,sai dai bakinsu kawai kake iya gani,
Sai shasshafa tsohon suke har suke cire mashi wannan guntun wandon dake jikin shi ya zamana babu komai a jikin shi,
Inda video ya tsaya kenan,

Abinda ya faru kuwa a can Gambia,bayan sun gama mai wannan rawar ne Biba ta bashi lemu yasha wanda ta zuba kwaya a ciki,
Nan ya tuntsire yana barcin Asara,su kuma suka cire kemera suke wuce,
To in da aka samu akasi shine washegari da managan ya zo duba abubuwan da suka faru a dakin manyan bakin su,dan suna yin haka wanda za'a goge a goge wanda za'a barshi a barshi,to anan ne mutumin yagani ta cctv, dace babban Hotel din sun ga abinda ya faru,ɗan shi mutumin babban VIP din su ne,domin kuwa ya fito takaran niman kujerar Shugaban Ƙasa a Gambia,

Shine sukayi saurin sanar dashi shi kuma tamkar yayi hauka dan ya tabbatar in wannan video ya fita ya shiga uku,ko fita kofar gida sai ya gagare shi,
Shine yaba yan sanda dama su kamo mashi Biba idan kuma sun ga zasu gudu su sake masu wuta,ya masu Alkawarin kome suke so zai basu,har balle Ogan su,

Ita kuma Biba tuni tayi amfani da kyakwalwarta wurin fecewa daga Gambia da wannan kemeran..

Kallon su tayi" to gashi dai kamar yanda kuka buƙata aikinku ya kammala,"ta cire Memory ta damka ma Alhaji Mansur,

Dukkanin su fuskar su dauke yake da maɗaukakin farin ciki domin kuwa bata san irin Alheri da Alfarma da zasu samu ba saboda wannan video,

Kallon ta Alhaji Abubakar yayi"Biba me yasa tunda muke saka ki aiki baki taɓa tambayar mu akan me muyi dashi,ko kuma wani dalili yasa muke haka ba?

Takawa take cikin wani irin salo tana juyi tamkar tarwada ta karasa kusa da shi,hannun ta tasa ta ɗan ture shi ya koma ya jingina da jikin kushin ta haye saman ciyarshi,kafinma ya samu damar yi mata magana ta haɗe bakinta da bashi ta shiga sumbatarshi cikin wani salo yayin da hannun ta daya ke bayan kanshi tana shafawa daya kuma ta tura a cikin wandon shi tana juyawa,
Ai kafin ka sani sai ga Alhaji Yahuza ya shiga sakin nishi yana ƙara jawo ta,yana lumshe ido,

Minti biyu tayi a jikinshi ta sauka gabaɗaya har yana mika hannu yana ƙoƙari riƙe ta,

"Ban damu dame zaku aikata dashi ba,domin ni tsarin aiki na kenan indai har zaka biya ni,ya rage naka kasan yanda zakayi da sauran"

Wani irin shigiyar dariya gabaɗaya suka kwashe dashi,Alhaji Mansur har da nuna shi,

"YAR TSANAR ZINARI kenan me saka Yara shedewa,Tsofaffi kuma ta saka su Suman daɗi,"

Cikin nuna ko in kula da halin da dattijon ya fara shiga na sha'awa tace"ko da kamar ƙaramar yar da ka haifa ne idan har kasan zaka samu natsuwa da ita sai ka ajiye tsufan ka koma yaro domin ka more sauran lokacin da suka rage maka Alhaji Yahuza"

Kallon ta Alhaji Abubakar yayi"Ki bani dama na cikashe maki duk wani gurbi dake zuciyar ki,na aure ki,zan nuna maki gata irin wanda baki taba samu ba"

Lumshe ido tayi ta buɗe su akan shi wanda yaji ta ƙara tafiya da zuciyar shi"Ni ƴar tsanar Zinari ce wacce take zagaye da mugayen kunamai masu mugun dafi,duk wanda ya yayi gigin daukar wannan Yar tsanar zinari,to fa wannan dafin ba zai barshi ba,domin mai shiga ciki ne ya lalata zuciya,,shi yasa gara ka bar Yar tsana a inda ka ganta,a kuma matsayin daka ganta,domin ita din ba mai taɓuwa ɓace"
Kiran sunan shi tayi"har yanzun ina ga Allah ba hallici wanda zai ciki zurbin zuciya ta ba,kuma ina ga har abada babu,
Kuna da Account number na ku turomin sauran kuɗi na"

Tana gama faɗar haka ta tashi ta wuce ciki ta barsu a nan idan sun gama tattaunawa su tafi Ummita ta rufe mata kofa,idan kuma tabi daya daga cikin su kwana ne babu abinda ya sha mata kai.......
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*06*

Babban ɗakin taro ne wanda yake daukan mutane sama da dubu,amma duk da haka a cike yake har ma wasu na niman wurin zama,saboda tsabar cika da akayi domin halartar wannan wa'azin,
A kwai wurin zama na Malamai da ban sannan kuma akwai babban TV na bango wanda yake hasko ko wani malami dake wurin dakuma wanda yeke wa'azi alocin,dan kusan Malamai uku ne,
Sannan a wurin akwai wurin zaman mata daban na maza daban,
Sai dai kuma a bangaren matan abinda zai baka mamaki shine yanda wasu daga cikinsu suka ci ado da kwalliya yanda kasan wadanda zasu je wurin bikin ko kuma gasar kyau ta ƙasa,
Lamarin ya ban mamaki,wanda hakan ne ma yasa na shiga wurin matan na zauna dan naji me ke faruwa dasu haka,dan tunda nake halartar wa'azi ban taɓa ganin inda mata suka cika irin na yau ba,kuma suka yi irin wannan kwalliyar.

Wata ce daga bayana naji tana ce ma yar uwar ta"waini Allah wallahi zafi ya ishe ni,gashi kwalliyar dana bada kuɗi har dubu biyar ta fara narkewa saboda zafi,shi kuma wanda nayi domin sa ko shigowa bai yi ba"

Tsaki wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login