Showing 81001 words to 84000 words out of 159134 words
Chapter 28 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
baiyana ka a idanun kowa"
Cikin tsawa mai haɗe da bacin rai yace"ke har wacece ke da kika isa ki bata shirin da ake yi tun kafin ki zo duniya,ke a tunanin ki zaki iya?shin zaki iya wasa da wuta a tsakiyar Teku?
"Idan har kai da wuta kake wasa to ni ruwa ce mai matukar sanyi,wannan wutar da kake takama dashi sai na kashe shi na bi ta kanshi"
"Zamu gani tsakanin ni da ke,?ki jira yi saƙonni na"
Dariya tayi,"babu abinda zaka iya domin ni *YAR TSANAR ZINARI CE* mai tattare da abin mamaki iri-iri,
Idan har ka iya to zaka iya taba ni ka zauna lafiya,idan kuma ka bata rawar ka da tsalle to dafi ne dane wanda yafi na maciji hatsari,idan ka shirya rasa rayuwar ka sai a kafta"Ta karasa faɗa tana sauke wayar domin dama ta tsammace abinda yafi haka daga gare shi,
A nashi bangaren buga wayar da kasa yayi yana wani irin huci kamar zai yi aman wuta tsabar bacin rai,
" Ina son a nimomin duk wani bayani dangane da wannan yarinyar"
"An gama Shugaba" Suka fada cikin girmamawa,
_______a washegarin da zata tafi bata samu damar wucewa ba,saboda dan tsaikon da aka samu daga Airport,dan haka da yamma ta shirya ta tafi Hotel din da ya sauka,in da abun ya faru,
Nuna masu I.D card din ta tayi ta gabatar ma da matar da ke zaune a wurin tarbar baki,"dan Allah ina son in ga footage din 15 ga wannan watan"
"Kiyi haƙuri ba ni da damar nuna maki,sai dai zan kira manager duk abinda ya ce zaki ji"
"Ok ba damuwa"
Daukar waya yarinyar tayi ta shiga kira,
Ita dai tana gefe tana jiranta,tana kuma kallon yanayin yarinyar,daga dukkan alamu ba'a dace ba,
Tana gamawa tazo in da take"ki yi haƙuri domin tun a wancan ranar Ƴan Sanda sun zo sun wuce shi"
"Yan sanda kuma?
" Eh"
Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ƙwanƙwaso,"ko zaki iya haɗa ni da manager naku,dan akwai tambayar da nake son na mashi"
Gyaɗa kai tayi"to bari na kira shi"
Bayan yan mintuna sai ga mutumin ya zo,duk da ta dauka ko Bayarabe zata gani sai dai yanayin sarin na shi da yanayin shi zai tabbatar maka da IBO ne,
Kamar a hassale yake,yanayin fuskar shi ya nuna haka da yake tambayar yarinyar,
Nuna mashi in da take zaune yarinyar tayi,
Yana karasowa ya zauna yana kare mata kallo tun daga sama har ƙasa kamar mai nazarin ta,
Sanye take da riga da siket wanda siket din har kasa,rigar kuma mai dogon hannu mai botiri, sai ta gaban rigar ta hada ta daure leɓe daya,sai dan karamin Baby Hijab,tayi kyau sosai yanda kasan wacce bata cikin damuwa,
Ƙara gyara zama tayi tana daura ƙafa ɗaya kan ɗaya,ita ma tana tsare shi da nata fararen idanun masu matukar han hankali,
"Hi" Ta fada
"Hy"
Nan ta gabatar mashi da kanta da kuma abinda take nima.....
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*50*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
"Ina mai baki haƙuri da kuma sanar dake kamar yanda ta faɗa maki haka din ne,domin ƴan sanda sun zo sun tafi da Footage ɗin"
Dan kumbura baki tayi tana busar da isa tare da shafa goshin ta,
"Karki damu da zaran sun dawo dashi zan kira ki,"
"Shi kenan na gode,sai dai dan Allah da zaran sun kawo ka kira ni"
"Karki samu damu,sai dai baki Bani number da zan kira ki ba"
Karamin takarda da biro ta ciro ta yaga ta rubuta mashi suna da number ta bashi,
"Sai na jika" Ta faɗa tana wucewa,
Taso ace ta riga ƴan sanda rike Footage ɗin,sai dai ba damuwa Allah yasa su dawo dashi akan lokaci,
Washegari jirgin London ta bi kwanan ta daya a London ta wuce Germany a nan sai da tayi kwana biyu saboda shirye-shiryen da suka tsaya yi ita da Doctor wanda sai da ta bashi wasikar Suraj ɗin sannan ya yarda suka tafi ITALY kwanan ta daya ta biyo jirgi ta dawo,domin zuwa lokacin hankalin ta ya koma gida ta koma ta harhaɗa wasu hujjojin,
A daren da ta sauka Hotel din ta koma ba tare data ko tsaya ta ci abinci ba ko ta huta duk da irin gajiyar data yi,
Ba wannan matar rannan ta samu ba dan wannan ce mata ta yi bayanan,dan haka number shi ta laluba da tayi seving,
Sai da yayi ringin uku ba'a dauka ba,har ta cire rai zai dauka sai gashi an daga,
Cikin magagin barci yake tambayar waye,
Faɗa mashi tayi har da ranar da suka haɗu ƙwanaki uku da suka wuce da kuma Alkawarin da ya mata,
"Ohh Sorry Madam kiyi haƙuri na manta gashi har nayi tafiya tanzun haka ina Chaina kuma sai nan da kwana biyar zan dawo"
"Har kwana biyar?zuwa lokacin ai an shiga kotu,gaskiya ba ni da wannan isasshen lokacin"
"To yanzun ya kike son nayi?
" Ko akwai dai taimakon da zaka min,idan har Footage din yana kusa kana iya saka wanda kafi yarda dashi ya bani "
"Gaskiya ba zai yuba,kin ga ni bacci ma nake ji,ki bari gobe zamu karasa magana" Dif ya katse wayar,
Kallon wayar tayi tana jujjuya shi a hannun ta,
Yanzun ya zata yi,dole tana buƙatar wani abun na daban,Asalin Footage din kawai zai tabbatar da komai,
Ganin zaman ba zai mata bane yasa kawai tayi ordan abinci sannan ta fito ta shiga mota bayan ta karɓa,
Duk da a lokacin ƙarfe tara na dare ake nima hakan bai sai ta yi gudu sosai ba da mota kamar yanda ta saba duk da ba cikowar abin hawa,
Wani katon Mota irin na kwasan shanaye ne yazo gabanta yana tukin banza,idan ta kauce sai ya kuma shigo ta,
A karo na biyu ta je gaucewa kenan ta ji wani motar ya daketa ta baya da karfi ko karin sai saita kanta take ta rike Sitiyarin motar dake ƙoƙarin kauce mata,sai dai kara dukan Motar na bayan yayi,wanda hakan yasa tayi Losing control motar ta faɗa cikin wani karamin Kwalbati,
Ganin haka ne yasa suka wuce suka bar wurin,
Hanyan mutane basu cika bi ba,wasu dan haka dai_daikun motoci ne masu tafita suka tsaya,sannan aka buɗe motar aka fitar da ita,wanda tun buguwar kanta da Sitiyarin ta Suma,
Fito da ita aka yi aka saka ta a motar wani mutum suka yi asibiti mafi kusa da ita,
___________*Niger State*
Kusan mintunan shi Arba'in kenan a tsaye a ƙofar gidan amma ya ƙasa shiga,
Haɗaɗɗen Namiji ne wanda ya amsa sunan shi,Black Beauty ne dan bakin shi har daukar ido yake,gashi dogo,da ka ganshi kasan cikakken matashi ne mai ji da kuɗi,saboda ko kayan dake jikin shi abin kallon ne dan Farin Shadda ya saka sai daukar ido da walwali take yi,
Jin an buɗe ƙofar gidan ne yasa da sauri ya dan matsa baya yana kallon ƙofar,
Haɗa ido suka yi da juna,sai dai wanda ya fito daga cikin gidan bai ce mashi komai ba ya raɓa ta gefen shi zai wuce,
Cikin sauri ya riƙo hannun shi yana kiran sunan shi tare da marairace fuska "Abdul Majid,dan Allah mana"
Fisge hannun shi yake kokarin yi amma yaki saki sai fadin yake dan Allah,
Wannan karon a hassale ya juyo "wai me kake so ne da ni?dan Allah ka rabu damu ka bar kofar gidan nan dan bamu kaunar ganin ko da inuwar ka ne,ka fita a rayuwar mu dan Allah kamar yanda ka yi a baya"
"Naji amma dan Allah ka bani dama ko sau daya ne na ganta,ina son nayi magana da ita ne"
Wani irin kallon takaici ya watsa mai"wa zaka gani?
"Ummu Salma,dan Allah ka bani wannan damar"
Daga bayansu suka ji an buɗe ƙofar gidan an kuma fitowa,
Ture mai hannu yayi"ka bar kofar gidan nan kafin ka saka na maka abinda zaka yi dana sani"
Wanda ya fito yanzun ne yace"me haka ka keyi Abdul Majid?so kake ka tara mana mutane a ƙofar gida ?
Sake Abdul Majid din yayi ya karaso wurin ɗayan "yau sati na daya kenan kullun sai nazo amma sun ƙi bani dama na ga Ummu Salma,ka taimaka min Abdulrahaman"
Kallon dan uwan nashi yayi"ka tafi in da zaka ni zan shiga dashi"
Juyawa yayi ya wuce abinshi ranshi na kuna,
Kallon matashin yayi yana tura ƙofar gidan "mu shiga *YUSIF* "
"Na gode Abdulrahman"
Har cikin babban Falon gidan suka shiga da sallamah wanda ba kowa a cikin shi sai sanyi da ƙanshi dake tashi,
Nuna mashi daya daga cikin kushin din yayi"zauna bari na kira Mama ku gaisa "
Da sauri ya dakatar da shi cikin yanayin tsoro "A'a ba sai ka kira taba,kawai Ummu Salma nake son gani"
Bai bashi amsa ba ya shiga wani kofar daya buɗe,
Ƙare ma falon kallo yake yana nan kamar yanda ya san shi,sai dai kuma gidan ya mai shiru kamar ba kowa a cikin shi saɓanin da,duk da ƴan aikin da ya gani amma da abin da kamar da ba,
Zuba ma makeken hoton ta dake makale a bangon falon ido yayi,
Fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon wani wurin kamar bata san sanda aka yi hoton ba,amma duk da haka ba ƙaramin fita yayi ba,sai sauran da take tare da yannan ta,su Uku maza ita kaɗai mace,duka suna dariya,
A zuciyar shi ya raɗa Happy Family,
Jin an buɗe ƙofar ne yasa ya maida kallon shi ƙofar,cikin sauri ya sauka daga saman kushin din ya tsugunna kasa kanshi a ƙasa,
Muryanshi har rawa yake wurin gaida ita,"Mama ina wuni barka da fitowa"
Bata bashi amsa ba sai ma tsayawa da tayi dan nisa da shi tana ƙare mai kallo yayin da zuciyar ta ke zafi yana tafasa aduk kallon da take ma shi,
Danne zuciyar ta tayi ta amsa mashi "Lafiya"
Dan shiru suka yi na ƴan mintuna kafin tace"Lafiya dai ko?
Ƙara dukar da kai yayi"dan Allah Mama ina son nayi magana da Ummu Salma ne"
"Kana iya shiga duniya ka duba mana ita idan har ka ganta ka rukar mana ita ta dawo gida haka" Tana gama fadar haka ta shige dakin ta bar shi,
Dago kai yayi ya kalli Abdulrahman "me Mama ke nufi da shiga duniya?
Kamar ba zai bashi amsa ba" Tun faruwar wancan lamarin tsakanin ka da Baba komai ya wargaje,kai ka tafi bayan ka rubuta mata takardar saki ba tare daka duba komai ba,ba tare data duba barnan daka aikata ba,ba tare daka duba irin soyayyar da take maka ba,bayan duk abinda kuka aikata wanda shi yayi silan tarwatsewar Ahalin mu,Baba ya samu bugawar zuciya,mukuma mun san tsirrin daya tarwatsa namu zuciyar wanda haka yasa ita Salma kasa jurewa ta bar gida,yau tsayin shekara biyar kenan da faruwar haka,yanzun kana iya tashi kabar mana gida domin ganin ka kaɗai yana taso mana da wani miki ne,kai ne silar faruwar komai dan Allah ka fita rayuwar mu"
Hawaye ne ke zuba daga idanun shi yayin da jikin shi yayi sanyi "Na yi danasani yafi a kirga, Nadama nake a kowace safiya a ko wani lokaci,sai dai ɗan Adam bai isa ya mai da hannun agogo baya ba,idan lokacin ya wuce koda da awa daya ne bai isa ya mai da shi baya ba,ina dana sani akan komai dana aikata a wancan lokacin,ina son Salma so mara misaltuwa,a wancan lokacin bam san Me ya shiga kaina ba,son abin duniya da ƙuruciya su suka ja min,ina kallon irin son da take min kamar irin wanda ba zata iya rabuwa da ni ba ne,shi yasa na aikata komai, amma nayi Alkawarin duk in da take zan nimota,zan tabbatar na dawo da ita cikin rayuwar mu koda nawa zan kashe sai na nimo ta"
Bai bashi amsa ba yasa kai ya fita dan jin waɗannan maganganun na Yusuf kona mashi rai suke yi,ko da aman wuta yake yi idan har ta dawo ko inda take ba zasu bari yaje ba balle yayi tunanin mai da ita rayuwar shi Kazantacciya.
___________*LEGOS*
Koda aka kaita Asibiti bata cikin hayyacinta dan haka da sauri likitoci suka karbe ta,ta samu rauni akai sai da aka nannade kan,sai hannun data samu Targaɗe shima aka daure aka sakala hannun da wani abu mai haɗe da Belet har ta wuyanta hannun ya tsaya a kirjinta,
Sai washegari da safe ta bar Asibitin bayan Direban da Alhaji Mansur ya haɗa ta dashi ya gama biyan komai,ba yanda basu yi da ita ba ta zauna ta ƙara hutu amma taki yarda saboda tana ganin aikin dake gabanta,
Gida ta koma tayi wanka sannan ta sha magunguna ta dauki jakka da takardun da take buƙata ta fito,
Ce ma direban tayi ya kai ta gidan yarin da Suraj yake,
"Hajiya ya kamata ki huta" Ya faɗa,
Dan wallahi ba karamin jin jiki tayi ba,har fuskarta ta faɗa saboda stress yawan tafiya da rashin natsuwar zuciya,
"Idan na dawo zan huta" Ta bashi amsa,
Ya ya'iya dole ya tuka ta har in da take bukatar zuwa,nan ma sai da aka dan bata mata lokaci kafin a bata damar ganin shi....
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*51*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Tunda ta shigo cikin wurin ya kafe ta da idanun shi yana ƙare mata kallo tun daga sama har kasa,
Turo baki take yi domin irin kallon da ta tsana kenan a cewarta duk masu irin wannan kallon gulma gare su,
Jan kujera tayi ta zauna sannan tayi sallamah,
Ba tare daya dauke kai ba ya amsa mata,
"Ni bana son irin wannan kallon kamar za'a cinye mutum"
"Idan har kinsan baki da kwarin gwiwa jurewa me na zuwa"
Kauda kai tayi tana hararan gefe "ba sai ka kore ni ba" Ta fada a hankali,
"Ina jin ki"
Daura jakkan hannun ta tayi saman teburin wurin ta ciro wayar ta,
Ƙoƙari take ta kunna amma ta kasa saboda bata saba amfani da hannun hagu ba,hannun dama kuma shine mai ciyo wanda aka nannade,
Dagowa tayi ta kalle shi,har yanzun kallon ta yake bai da alamun ma zai yi magana,
Haushi ya fara ba,amma tunda har bai ji tausayin ta ba yace ta kawo ya taimaka mata ita kuma ba zata taba cewa ya taimaka mata ba,
Dan haka ta Daura wayar a saman teburin ta shiga latsawa dai daya har ya buɗe ta shiga in da take buƙata sannan ta tura mashi a gaban shi,
Mai da hankali kan video dake magana yayi,likitan Grandma ne yake mai bayani akan tafiyarsu har kuma garin da suka isa wato ITALY,sai video fuskarta da aka yi tana kwance amma ya tabbatar mashi daga dukkan alamu za'a dace saboda babban Asibiti ne kuma akwai ƙwararrun likitoci a wurin suna kula da ita yanda ya dace,
Ganin video ya ƙare ne ya turo mata wayar ta gabanta,
Wani karamin takarda ta kara tura mashi"ga address din Asibiti ko da zaka je idan an kammala wannan case din"
"Wani tabbaci kike dashi akan za'a gama?
" Eh to har yanzun gaskiya ban samu abinda nake nima ba,amma ina saka ran komai zai iya juyawa har yanzun muna da sauran kwana biyu a ƙasa "
Lumshe ido yayi ya buɗe bai ce mata komai ba,
Zazzage tarkacen dake cikin jakkan ta tayi sai dai ba takardun data kawo domin ya saka hannun,
Karamin tsaki taja "ina ga na baro su gida,yanzun dole na dawo gobe"
Mikewa yayi yana ƙoƙarin wucewa,
"Ina kuma zaka tafi?
Juyowa yayi kaɗan" Akwai abinda zan maki ne?
"Amma! " Sai kuma tayi shiru"Anyway babu komai "
Har yayi taku uku taji ba zata iya jurewa ba dan haka cikin jin haushi ta dauki bairon dake gefenta ta wurga mashi da karfi,ai kuwa cikin sa'a ya sauka a keyar shi,
Ko daga kai ta kalle shi ba tayi da dan ita bata masan ya same shi ba tsabar masifar da take yi ita kaɗai "mutum ko tausayi bai da shi,ba zai ma iya cewa me ya same ni ba,sai dai kawai ya kureka da idanun shi kamar wani kunkuru,mtwss ko kunkuru na da ido ne ma oho"ta karasa fada tana daukar jakkanta ta fita ba tare data juya in da yake ba dan ita a tunanin ta tuni ya shige,
Ganin ta wuce ne yasa ya sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya,
Yasan koma menene ya same ta baya rasa nasaba da wannan case din,shi yasa tun farko yace ta ajeye case din saboda yana mata gudun irin haka,sai dai tunda ta fara ba shida damar da zai dakatar da ita sai dai kawai ya bita da addu'a Allah ya kare ta,
Dukawa yayi ya dauki Bairon ya shige dashi.
_________*KANO*
"Kaka ya kamata ki saka Biba ta dawo in ya so sai a daukar masa ƙwararre lauya "
"Wai idan ta dawo Uwar me zata maka Ibrahim,ni fa ban gane ba,shin zaka samar masa wani lauya a ina,ko ubanka bai iya samu ba sai kai?ni fa bana son haka ka barmu muji da abinda muke ji"
"Kaka nifa tsoro nake ji kar ta saka yaya na ya ƙare a gidan yari,Biba fa a matsayin yar aiki take a gidan nan yanzun kuma wai lauya,duk ta ina hakan ya kasance,ko dama dai tana da wani manufa ne na zuwa wannan gidan"
Gabaɗaya falon shiru yayi yayinda zuciyar kowa ya koma kan kiyasta masa wacece ita din,
Ammi ce ta katse tunanin nasu