Showing 147001 words to 150000 words out of 159134 words
Chapter 50 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
pant da bran,zagayawa yayi ta bayan ta,jin saukar hannun shi a saman maɓallan bran din ta ne yasa ta ɗan ja numfashi,
Daya bayan daya yake ɓalle maɓallan guda uku har ya kammala,
Da sauri ta dafe kirjinta d hannu ta yanda bran din bai faɗi ba,
Zagayowa ya kuma yi ya tsaya a gabanta,ba tare da ya kalli fuskarta ba ya saka hannun shi duka biyu a saman kafadar ya shiga zame hannun a hankali har ya gangaro,ganin bata cire hanun ba,shi kuma bai daga hannun shi a wurin ba ne yasa dole ta zana hannu tana kara yin kasa da kanta,
Cirewa yayi ya ajiye,sai dai tun daga nan kuma sai ya kasa yin komai,sai tsayawa da yayi yana kare mata kallo,ita kuma da gangan ta ki kare jikinta,to me zata ɓoye shi,
Ganin ta fara gajiya da tsayuwar ne yasa a hankali ta raba ta gefen shi ta shige cikin bahon wanka,
Lunshe idanun shi yayi da dan ƙarfi ya buɗe,ba tare da ya kalli in da take ba ya bar bayin,
Ta jima a cikin sannan ta fito,sai dai baya cikin dakin wani irin sanyi ta ji ya ratsata lokaci ɗaya,lokacin data daura ƙafarta a tals din dakin dan ba karamin sanyi ya ɗauka ba,ga na AC dake busowa,
Har cikin kwakwalwarta take jinshi,
Cikin sauri ta haye kan gado ta jawo bargo ta shige ta dungule.
Ya dauki lokaci sai kuma gashi ya shi ya shigo dakin dauke da tiren abinci da kuma ledan magungunan da aka amsu,
Ajiye tiren yayi ya nufi bayi,sai dai bata ciki,fitowa yayi yana tunanin ina kuma ta shiga ne,
Idanun shi ya sauka a kan gado,yanda mutum ke dunkule yana rawar sanyi,
Da sauri ya hau kan gadon yana yaye bargon,
Tallabota jikin shi yayi yana jin yanda jikinta ya dauko wani zafi,"Bebin,upon your Eye"
Ƙara shigewa jikin shi ta yi tana faɗin "Suraj!sanyi na ke ji,ka rufe ni" Cikin rawar murya,
Kankameta yayi"is ok"
Ciro wayar shi dake cikin Aljihu yayi ya shiga Laluben number Farhan,kira biyu ya ɗauka,
Cikin zolaya yake faɗin "Angon Biba bada kanka a sare"
Karamin tsaki ya ja"jikin ta ya kara yin zafi,wani taimako zan bata "
"Ba yanzun kuka dawo Asibiti ba? Ya tambaya saboda sun yi waya kafin farkawar ta,
" Eh"
"Ok ka kwantar da hankalin ka,ba wani abu bane,yanzun ina take?
" Gata nan"
"To samu ruwan sanyi amma ba ina nufin na firig ba,ka saka towel karami kana shafa mata a jiki gaba daya,idan kuma har zuwa lokacin bai sauka ba,kai kayi amfani da jikin ka"
"Kamar ya?
" Kai ban son iskanci"ya faɗa yana sauke wayar,
Kallon ta yayi yanda ta kanainaye shi,a jiyar zuciya ya sauke yana kwantar da ita da kyau,
Kamar yanda yace haka yi mata sai dai har zuwa lokacin idan yayi sanyi sai kuma ya kara zafi,
Karshe rigar dake jikin shi ya cire ya cire mata towel din dake jikin ta ya rungumeta yana jin yanda zafin ke ratsa shi,
Tsayin awanni biyu da ta samu bacci a jikin shi ba karamin jigata yayi ba,dan ko rintsawa bai iya yi ba,ganin lokacin sallah na gabatowa yasa a hankali yayi ƙoƙarin zameta daga jikin shi,sai ji tayi ta kara kankameshi,mai da kanshi yayi ya kwantar na tsayin mintuna biyar kafin ya ƙara ƙoƙarin gwadawa ta hanyar zame hannayen ta data zagayeshi dashi,
A hankali ta buɗe idanun ta wadanda suka sauya sukayi dishi_dishi,"please don't live me"tana kara komawa jikin shi,
Ajiyar zuciya ya sauke,yana shafa kanta,"i will never live you,never "
Dago kanta tayi tana kallon shi"kayi Alkawari"
Sumbatar goshin ta yayi"i promised,na maki Alkawari "
Ajiyar zuciya ta sauki na samun natsuwa,tana sakala yatsun su wuri ɗaya tana juyawa"ina jin kewar Mama sosai,da ace tun a wancan ranar nazo da mun haɗu da ita,har ma muyi magana,sai dai.. sai dai..
Kasa karasa fada tayi jin yanda kuka ke ƙoƙarin sarke ta,kokarin cire hanun ta take yi cikin nashi,sai dai yaƙe sakin nata hannun ta,
"Koda ma ace kin zo wancan ranar,kin kuma haɗu da ita,ba lallai bane ta iya yi maki magana kamar yanda kike so,saboda haka Allah ya tsara,yanzun haka babu abinda tafi buƙata daga gare ki wanda zaki nuna mata soyayya har ta san kina yi sana da Addu'a,shi kaɗai zaki dinga mata wanda zai isa gare ta,har da shi Baba,ko ba komai ya raine ki na tsayin shekaru goma sha biyar,ba tare da gajiyawar shi ba,kuma cike da kulawa da tattali,shi ma ya cancanci addu'a daga gare ki,"
Kuka ta fashe dashi,"shi kenan ba ni da kowa "
"A'a ki na da ni,sannan ga yannin ki,ba za mu taba barin wani abu ya same ki ba"
Dago jikakkun idanun ta tayi,cikin kuka ta tace"Amma ba ka so na,ta yaya zan iya rayuwa da mutumin da baya so na,kuma ni ma ba na son shi,ta yaya zan yi farin ciki,ta y....
Haɗe bakin ta da nashi yayi a hankali yake sumbatar ta,
Haɗe goshin su yayi wuri ɗaya suna shakar numfashin juna,"zan kula dake na baki farin ciki na tsayin rayuwata,baki bukatar soyayya domin duk abinda kike buƙata kin samu "harshen shi ya saka ya shiga lashi duk wani ruwan hawaye dake saman fuskarta,sai da ya tabbatar ya kashe komai sannan ya gangaro wuyanta,
Jin yanda yake sun sunar wuyan yana sauke mata numfashi yasa ta dago fuskar shi," Me yasa ka ce bana bukatar soyayya?ni soyayya ita na zaɓa a kan komai,ka mai da ni gida"
Kwantowa yayi a jikin ta,"ki bari zuwa anjima"
Dan ture shi tayi tana ƙoƙarin mirginawa "me yasa kake son mai da jiki na wurin hutawarka,kai ma ɗaukar jiki na kake yi wurin hutu kamar yanda waɗancan mutane suka ɗauka,
Babu soyayya a tsakanin mu,ka kyale ni na tafi,ina son nayi rayuwar natsuwa ne yanzun,ina son na bar komai dana samu a wancan hanyar a baya,ciki har da kai,dan Allah"ta karasa faɗa tana sauka kan gadon,
Kallon mamaki yake mata,da jin irin kalaman dake fitowa daga bakin ta,yanzun har shi Suraj zata faɗa ma haka,har shi zata kalli idon shi tace saboda jikinta yake tare da ita,tana kuma mashi kallon daya daga cikin mutanen da suka amfana da jikin ta,
Ba tare da yace komai ba ya sauka daga saman gadon ya nufi ban ɗaki,ya jima sosai a ciki dan har ta gaji da jiranshi ta zuba abinci ta ci bai fito ba,
Yana fitowa kuma bai kalli in da take ba ya fita,babu jimawa kuna sai ga shi ya shigo da leda babban a hannu,ajiyewa yayi saman gado,fuskarshi a cunkushe take yanda baka isa ka shaida yanayin da yake ciki ba,sai dai idanun shi da suka yi wani iri,
"Ga kaya nan ki saka,idan kin kammala ki same ni a falo,zan mai da ke gida"
"Na gode"
"Umm" Ya fada yana barin ɗakin.......
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*89*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Tana kammala shiryawa ta fito,a falon ta same shi yana amsa waya,zama tayi a gefen shi har ya kammala,
Juyowa yayi fuskar shi dauke da dan murmushi "muje ko?
Jinjina nashi kai tayi tana mikewa,
Tare suka jero hannun shi na zube cikin aljihun wandon shi,
Idan ka kallesu yanda suke taku a hankali yanda kasan wata da zara,sun bala'in dacewa da juna,
" Akwai in da ke miki ciyo ne?
Kallon shi tayj"Umm um,naji sauki yanzun sosai "
Ajiyar zuciya ya sauke "that is good"
Buɗe mata gidan gaba yayi ta shiga sannan ya zagaya ya zauna a mazaunin direba,
A hankali yake tuka motar ba tare da gudu ko garaje ba,"Kasan gidan mu ne?
Ba tare da ya kalli in da take ba yace "um"
Jin haka yasa ta ja bakinta tayi shiru,dan ta fahimce ƴan miskilancin suna kusa,
Cikin kankanin lokaci sai gasu a bakin Get din gidan su,mai gadi na ganin shi ya buɗe masu Get suka shiga,
Tare suka fito sai dai ita gaba tayi ganin ya tsaya da Yaya Abdulmajid suna gaisawa,
Tana shiga falo Turus ta tsaya ganin mutanen da bata taba tsammanin gani ba,wato yan Group din Yar Tsanar Zinari Fans group,
Da gudu ta karasa ta rungume Ummunas tana fashewa da kuka,ita ma rungume ta tayi tana shafa bayan ta,cikin taushin murya ta shiga lallashin ta tana mata nasiha "ni ba zan hana ki kuka ba,domin duk wanda kaji yace yi ma mamaci kuka babu kyau to bai rasa wani mukusanci nashi bane,abinda kawai ba a so shine yin na fitar kima,kiyi haƙuri wannan wata jarabawa ce data same ki,kuma muna maki fatan zaki cinye ta"
Dagowa tayi daga jikin ta tana share hawaye,"Addu'ar ki shi suka fi bukatar a yanzun"cewar Ummuhaidar,
"Gaskiya ne komai yayi zafi addu'a ne magani,ki duba ki ga dukkan mu saboda ke muka zo nan" Cewar Bareerah Umar,
"kalli ga Salma,ga DeejAysh,ga Ummu husna,kin ga harda Rx_Aryamn tana nan,duk da aiyukan da suke dashi haka suka ajiye domin ke saboda suzo su sanyaya zuciyar ki,"
Murmushi mai dauke da hawaye ne suka sauko mata,"Ummunas banga Salmancy da A.I Bauchi da Fatety ba,ko dai basu samu zuwa bane?
"Sun zo,ina ga suna waje suna magana da Suraj ne dan sunce shima ya cancanci gaisuwa"
Sallamar da suka ji ya saka su juyawa,fara'ar fuskokin su ne ya karu ganin tawagar Kungiyar Moonlight writers,wato kungiyar su na Marubuta tare da yan fans group dinsu,
Queen Nasma ce a gaba,domin ita ce shugaba kuma jagoran wannan kungiyar mai Albarka,wanda ya hada manya kuma haziƙan marubata,
Cikin girmamawa da mutunta juna aka shiga gaisawa tare da musayar ta'aziyya,
Ko gama zama ba su yiba sai ga sallamar yan Fans group din FAKIRI yayin da shugaban su Khadijah Umar ta jagorance ce,tare suke da Fans din Sardauna,Allah sarki ƴan Amana,
Wannan zuwan nasu ba karamin farin ciki da daɗi ya mata ba,domin mutane ne da suka zo daga mabanbanta yanki a fadin kasar,har ma da wajen kasar,kuma duk saboda ita suka zo,gaskiya in bata gode ma Allah ba bata san Me zata yi ba,
Aunty Fati Uwar Abulkhairi ita ta fara lura da babu Uwar mijin ta,dan haka mikewa tayi tana dan lekawa tare da fadin"wai jama'a ina Jiddarh Umar?
Daga bakin kofa suka ji ta amsa da "gani nan"
Masha Allah kake jin yana fitowa daga bakin mutane,domin sanye take cikin leshi dinkin doguwar riga na bubu wanda ba karamin kyau ya mata ba,gata dama doguwa mai dogon gashi har gadon baya,ga dogon hanci har baki,ido farare tamkar madara,dan ko Biba da take mace sai da ta juya ta kara kallon ta tsabar kyau yanda kasan ba a duniyar mutane ba,kamar dai a duniyar Novel (ni ma na ɗana,ehe basu Biba kadai suke da kyau ba😜)
Cikin tsananin farin ciki ta kara so ta rungume Biba tare da mata gaisuwar rasuwa,sannan cikin girmamawa ta gaida shugaban kungiyoyi da manyan su,
Abinci lafiyayye Biba ta saka aka kawo masu,cikin har da su farfesun kaji da kayan shaye-shaye kala_kala,
Dukkan su kowa yana ji da kanshi domin mutane ne masu aji da class,
Nikam ganin basu da niyar taba komai ne yasa na juya na kalli Maman Abu,"Sirika idan zaki ci Bismillah idan kuma zaki tsaya yanga ni dai na yi nan"kafin su ankara sai ganin Jiddarh Umar suka yi ta zauna tare da takwashe kafa tashiga buɗe plate,duk wanda ya mata shi take jawowa gaban ta,
Ganin da gaske ci take hankali kwance ya saka masu sha'awar ci suma suka fara ci,
Queen ce ta danja gefen mayafin ta "Jiddarh"
Juyowa nayi"umm "domin ba zan iya amsawa ba saboda baki na cike yake da namar kaza,
" Me haka,dan Allah karki bada ƴan Moonligh mana"
'Gaskiya sai dai kiyi haƙuri Queen,ba zan iya ma kai na bakin ciki ba,haka kawai kana kallon abu kana son ci sai ka tsaye kana hadiye miyau saboda wani abu wai shi aji,gaskiya ni dai in kan abinci ne ba ni da aji,domin duk in da naje aka ba ni in har yamin zan ci ne,babu ruwa na ehe "
"Dama nasan you ar very Stoburn"
Tura baki nayi na ci gaba da kwasan girki na,
Rx_Aryamn ce tace"Jiddarh ki bar naman nan haka,kin san ba lafiyar kirji gare ki ba,kuma likita ya hana ki cin soyayyen abu,salon ki ci yanzun an jima ki kama nishi da faɗin zaki mutu"
"Ai sai dai ki yi hakuri likita,domin rayuwa bashi yuwa sai da soyayyen abu,ta yaya za'ayi in gani in kyale,gaskiya ci zan yi idan ciyo ya taso a sha magana asha wahala,idan an warke a ɗaura daga in da aka tsaya"
"To karma dai ki nime ni anjima idan abun naki ya motsa"
Sahibar Moonlight ce ta katse mu ta hanyar fadin "jiddarh naji ance ke yar Kano ce?
" A'a ni ba yar Kano ba ce,ni yar Niger state ce"
"Niger?
" Ni fa bance Niger ba,ina nufin Niger State a garin Minna "
"Wow abun mamaki,wai dama a Minna a kwai marubuta?
" Akwai mana,ban san me yasa mutane wani bi suke raina baiwar da Allah yama dan adam ba,sau da yawa sai kiga mutane suna fadin ai gabaɗaya marubuta a Kano suke,alhalin basu san a garin da suke ma akwai ba,dan haka nake Alfaharin kasancewata yar Niger state "
Murmushi ne dauke a fuskar su "gaskiya ne Jiddarh,yanzun dai tunda kin gama ya kamata a kira mana Ammi da Aunty Hulaira mu masu gaisuwa,daganan sai mu fita mu ma Suraj shima gaisuwa"
"Haka ne" Duk suka amsa,
Ammi ma ta ji dadin zuwan su sosai dan malama Amina Jibrin ta group din Fakiri ita ta bayar da Addu'a sosai tare da wa'azi mai ratsa jiki,
A waje ma gaisuwa suka ma Suraj da su Ya Abdulmalik,har bakin Get Biba ta raka su kafin ta dawo,
Ganin ta wuce ne Salmancy ta kalle mu"ni kuwa sai nake ganin kamar a kwai damuwa a idanun Suraj,ko baku lura da haka ba?
"Ke dai Salmancy Allah ya shirye ki,baki iya gani ki yi shiru" Cewar Bareera Umar,
"Allah da gaske nake ji"
Girgiza kai Ummunas tayi,bata dai ce masu komai ba ita da Ummuhaidar,
"DeejAysh baku gani ba?
Busar da iska tayi ta baki" Ta ya za'ayi in gani bayan hankalina yana kan kallon baiwar kyan da Allah ya mashi"
"Kuka sani ko damuwar mutuwar ce har yanzun a ran shi" Cewar fatity,
"To me zai hana mu tambaye Jiddarh Umar"
"Dadi na dake kanki na ja Salma" Ummuhusna ta fada,
Jawo ni baya suka yi "faɗa mana meke damun Young Ustaz ne haka?
Kallon su take ita ma kamar yanda suka zuba mata ido,dan har dariya sun so bata" To ta yaya zan sani,kawai dai ku jira ku gani koma dai meke damun shi ai da kanshi zai faɗa ko,ni ta yaya ma za'a yi in sani"
"Saboda ke ce Alkalin wasan"
Gira daya na daga,"a naku ganin ba,ni kuma a nawa bangaren hannu na shine Alkalin wasan,domin ban isa yanke hukunci ba sai lokacin da nake kan buga wasan,ma'ana sai lokacin dana dauki waya,dan haka mu jira mu gani,Allah sarki gaskiya Biba ta ban tausayi "
Karamin tsaki sis Khadijah taja"ai ke kika sani,ni kunga tafiya ta ga Baban Hamnat can ya zo daukata "
Sallamah suka mata ta wuce,
A takaice dai da dai_daiya matan auren mazajen su ke ta zuwa suna ɗaukar su har ya rage daga ni sai Fatity,
Ganin yanda ta yi shiru be yasa na dafa ta"ya dai mutuniyar"
"Jiddarh aure zan yi"
Ba karamin dariya maganar ta ya ba ni ba,ai kuwa sai da na dara"me yasa sai yanzun?
Kafin ta ba ni amsa ne sai ga kiran Sultan di na ya shigo waya,dan haka ba tare dana saurare ta ba na daga mata hannu ina daukau wayar tare da shigewa cikin Adaidaita sahun dana tare,
Murmushi tayi itama tana ɗaga min hannu........
*wannan shafin na sadaukar dashi ga yan group din Yar tsanar zinari,da Moonlight writers,sai group din Fakiri,wadanda na kira da wadanda ban samu na kira ba,ina matukar Alfahari da ku*
*Love you all* 😘
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*90*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
*Sadaukarwa ga*
Mummys Girl
Maman Amira(Kaduna)
Maman masoyi
Hassana Muhammad
Ummeeh
Maman Ummi
Khadija Barau
~Chawa
Madame Anass
Nana Aisha
Maman Abdul,
Na sadaukar da wannan shafin gare ku,Allah ya Albarkaci rayuwarku dana Ahalinku.
Ko da ta koma falo har ma'aikatan gidan sun kusa kammala gyaran falon,dan haka kai tsaye dakin da Ammi ta sauka ta shiga,
Tana ganin ta kuwa ta mika mata hannu,amsa tayi ta zauna kusa da ita,
"Ya jikin naki?
Dan dukar da kai tayi" Naji sauki sosai Ammi"
"Alhamsulillah"
Dan shiru ne ya ratsa dakin na sakon ni,kafin tace"ki yi hakuri haka Allah ya kadar ta ba zaku haɗu ba "nan ta shiga yi mata nasiha mai matukar sanyaya jiki,tana kara tsoratata akan tsoron Allah da bauta masa,cire damuwa da maida komai ba komai ba,muhimmancin hakuri," Ina fata zaki yi aiki da abinda na faɗa maki?
Share guntun hawayen ta tayi tana jin yanda zuciyarta ke sanyi tana kara samun natsuwa"na gode sosai Ammi insha Allah zan yi iya ƙoƙari na"
"Allah ya maki Albarka,ya baki zuri'a na gari"
"Amin"cikin sanyin murya tace" Ammi ina Abbu,kin koma Kano ne,yasu Kaka?
Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi,"ayanda naji Kaka tana kwance a Asibiti,amma jikin da sauƙi yanzun,Ashe tun randa ake shari'ar Nurudeen ya kwasa ya tura ma mahaifiyarshi,shine ita muka ta je ta nuna ma Kaka,wacce nan take ta yanke jiki,ita ma