Showing 9001 words to 12000 words out of 159134 words
Chapter 4 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
ba,
Sai kamshi ke tashi ta ko ina,
Da sallamah suka shiga har tsakiyar falon in da wata yar budurwa ta amsa wacce ba zata wuce shekara goma sha huɗu ba,sanye da hijabi dai dai guiwa,da fara'a ta tare su"oyoyo yaya Suraj,barka da dawowa,Allah yasa kamin tsaraba "ta faɗa tana dariya tare da isowa in da suka zauna shida Abbu,
Murmushi ya sakar mata wanda ya kara baiyana kamar dake tsakanin su,cikin kwaikwayonta yace" Oyoyo Rabi'ah, Allah yasa kin ajiye min abin daɗi "
Dariya ta saka tana buga ƙafa irin na shagwaba,"ai Ammi ta ajiye maka,"
Dariya suke mata shida Abbu,wanda yace"kinga ƙyale shi Auta wannan karon harda ne sai an ba tsaraba,ɗan mun gaji da kullun mantawa da mu da akeyi"
Karan tafiyar da suka ji ne daga gefen su yasa suka juya,
Mace ce kyakkyawa wacce da ka ganta yanda kasan an tsaga kara tsakaninta da Suraj,da kuma ƙanwar shi,abubuwan Abbu kaɗan ne suka kwasa.
Da sauri ya tashi ya karasa inda take tare bata kyakkyawar runguma"I miss you Ammi"
Shafa bayan shi tayi"baka kai ni ba Baba na,"
Dagowa yayi ya rike hannun ta ya sumbaci hannun,"Ammi na yunwa nake ji"
"Mu je ka ci abinci"
"Ammi bari nayi wanka sai nazo na ci"
Jinjina kai tayi"ok Allah yama Albarka"
"Amin My Ammi" Ya fada yana nufar kofar fita"Abbu sai zuwa anjima "
Hannu ya daga mai,"sai ka shigo "
Yana fita ta bayan shiyansu yabi inda ya ɓulla ta wani boy's quarter,babba wanda daga dukkan alamu anan samarin gidan suke,
Duka kofofin irin wanda zaka saka ɗan kati ne ya buɗe,a kwai kuma inda zaka saka number,
Dan haka da katin yayi amfani ya buɗe ƙofar wanda wani ni'imtaccen sanyi ne ya daki hanci na,nayi mamakin ganin garman dakin domin na ɗauka ɗaki daya ne,sai dai babban falo ne madaidaici mai dauke da manya kujeru sai kayan kallo da man yan labulai wanda suka ƙara kawata falon,
Sai dakin barcin shi mai hade da bayi,
Wanka yayi ya canja kaya,sannan ya fito,sai dai a maimakon ya koma shiyansu sai naga ya shiga daya daga cikin part din dake gidan wanda yake kusa dana farko.
Da sallamah ya shigo,in da wata tsohuwa dake zaune a saman babban darduma tana baran gyada ta amsa,"Me gida na barka da dawo,"
Ya mutse fuska yayi yana zama kusa da ƙafarta "kin min tsufa,ni yarinya karama nake so"
"Kai dai faɗi gaskiya kace ka rasa mai sonka, kaga ni ma manegi nake da kai tunda an rasa meso"
Dariya ya saka wanda bai yi niya ba,"ni har yanzun banga wacce ta min ba,"
"Ko dai Aljana ta aure ka ne bamu sani ba Surajo,kai ko dan irin ƴan matan nan da samari keyi kai ban taɓa ganin ka yi ba,to bari Adamu da Auwalu su zo,dole a fara ni ma maka taimako" (Adamu shine sunan Abbu,mahaifin shi,Auwalu kuma Abba,yayan mahaifinsa,baban Ibrahim)
Ɓata fuska yayi"dan Allah ki daina ɓata min suna wai Surajo,pls ƴan mata,kuma ni bani da wata Aljana data aure ni,kin ga me zan samu a dakin nan"ya faɗa yana mikewa tare da tashi ya nufe firig dinta,buɗewa yayi yana dudduba abubuwan dake ciki,wani kwanu ya dauko ya dawo ya zauna,
Kokarin mika hannu take zata ƙwace "to ka dawo kenan ko,zaka fara caje min dakin kamar kaban ajiya,bani fura ta nan,damawa nayi na sha anjima"
Kaucewa yayi yana dariya"ke dai faɗi gaskiya dama ni kika ajiye ma,dan ki kara siye zuciya ta,to karki damu ba yanzun zan yi auren ba,"ya faɗa yana yin Bismillah tare da saka ludayi aciki yana kaiwa baki,
Sallamah suka ji daga bakin ƙofa,
Kaka ce ta amsa da karfi tana bada izinin shigowa,shi dai a hankali ya amsa,
Wata budurwa ce ta shigo kyakkyawa wanda ba zata wuce sha tara ba,sanye da jallabiya baki sai karamin hijabi,hannunta riƙe da Basket da kulolin abinci,
Cikin yanga mai haɗe da natsuwa ta shigo,ɗan dukawa tayi"barka da dawowa Yaya Suraj"
Hannu kawai ya daga mata,ba tare daya bata amsa ba,
Basket din hannun ta kai gaban Kaka ta ajiye "Kaka gashi inji Momy"
"To Allah yayi Albarka,je kikai kicin"kallon shi tayi" Surajo ko a zubo maka"
Girgiza mata kai yayi ba tare daya bata amsa ba,yana cigaba da kurban furanshi.
Tana shiga kicin sai ga wasu ƴan mata su biyu suma sun shigo,sai dai su zasu kai ishirin da uku zuwa da biyu,gai dashi suka yi saku gai da Kaka sannan suka shige cikin dakin kaka,
"Yanzun zaka saka a fara min layi a ƙofar daki Sojago,ƙarfi da yaji kasa na samu karin wasu jikokin wanda ba nawa ba,sai dun saboda kai,kai kuma na rasa kanka ace ka rasa wacce ta motsa zuciyar ka sai kace wani Dutse"
Wacce ta kai abinci kicin ne ta fito ta zauna kusa da kaka,"yaya Suraj munga wa'azin ka na Abuja yayi kyau sosai "
Wani mugun kallon daya sakar mata ne yasa ba shiri ta mai da gyadar dake hannun ta wanda ta diba,tare da tashi sumui_sumui ta shige dakin kakan,in da waɗannan yan matan suke.
Kallon shi tayi"Allah raba ka da bakin hali"
Rufe kwanun yayi"dana yi me?
"Kai kenan baka son mace ta rabe ka,,daga harara sai ka dauri yi masu bakin hali,ta yaya mace zata ji daɗin zama da kai"
Hannun ta ya rike tare da sumbatar bayan hannun,"idan na tashi aure sai na baƙi mamaki"
"Allah yasa ba mamakin da zai kashe ni zaka bani ba"
Dariya kawai yayi yana fita daga shiyan,dan yasan in dai ya zauna to fa yanzun zasu shiga yin zirga-zirgar a cikin falon,daga yan matan gidan har na makota masu shigowa,
Shi kuma tsakanin shi da mace sai niman tsari,
Shi sam basu gaban shi,basu burge shi,shi yasa duk wacce tayi kuskuren ya gano kina son shi,to kin shiga uku bashi ba raga maki,tsakanin ku harara,amma in kin iya takunki to zaku zauna lafiya,harma ku yi hira,to duk kuma randa yan iskar nashi ke kai,to ranar kowa a gidan kama kanshi yake hatta masu tsaron shi,ɗan shi mutum ne mai matukar sauƙin kai,bai da saurin fushi,ya nada fara'a,sai dai bai son rai ni,wani lokaci kuma haka kawai ranar sai kaga ya dauke wuta,wato ya gimtse fuska duk wanda ya mai to ranar ya shiga uku,domin ya iya bada punishment wanda duk girman mutum sai yayi kuka,shi yasa duk randa suka ganshi a irin wannan yayi kowa yake kama kanshi a gidan babba da yaro....
Yana fitowa daga part din kaka sai ga Direba, cikin girmamawa ya miko mashi wani karamin pos na mata da waya kiran iPhone"Ustaz gashi a cikin mota na gani"
Bai amsaba sai tsayawa da yayi yana kallon pos din tare da wayar "ina riƙe pos ne da zaka kawo min?
Dukar dakai yayi cikin girmamawa yace" Ba haka nake nufi ba,a yi hakuri,ina ganin na wannan yarinyar ce data shiga motarmu "
Ɗan shiru yayi yana nazari dan shi sam yama manta da wata ta shiga motar su dazu,ohh ya tuna,wannan mara kunyar yarinyar,wacce tace mashi maye,harda cewa ya gyara suman kanshi,
"Jeka dashi" Yace ma Direban,har kuma mutumin ya juya yana tunanin yanda zai yi da kayan,ko me ya tuna ohho,sai kuma yace "Kawo"
aikuwa da sauri mutumin ya kawo mai ya juya ya bar wurin cikin sauri dan karma ya canja ra'ayi.
Jujjuya kayan yake a hannu kafin ya nufe dakin shi dasu......
______Bangaren Biba kuwa...
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*08*
*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*
A gigice ya shigo cikin gidan har yana cin tuntube sabar saurin da yake yi,
Ga masu aiki ta ko ina duk in da yabi sai gaida shi suke yi amma sam ba su bane a gaban shi,
Burin shi daya shine ya ƙarasa inda masu gidan suke,
Tunda ya taka ƙafar shi a babban falon gidan wanda daka ganshi kasan naira tayi kuka ya fara kwalla kiran sunan mutanen gidan daya bayan daya cikin tashin hankali,
"Mama! Mama!Abdulrahman! Yaya Abdulmajid! Ina kuke ɗan Allah ku fito! "
Daya bayan daya suke fitowa daka shiya mabanbanta a cikin falon,
Ita wacce aka kira da Mama wacce ke sanye da Hijabi dogo har ƙasa tare da carbi a hannun ta ne ta kalle shi,"lafiya Abdulmalik?
Kallon ta yayi,tare da kallon ƴan uwan shi maza dake tsaye suna jira suji ko lafiya,yake a gargitse haka,
A hankali ya buɗe baki ya kira sunan ta"Mama"
Amsawa ta kara yi tana kallon ɗan nata wanda yake cikakken saurayi kuma matashi wanda zai kai shekara ishirin da takwas,taga ya fashe da kuka tare da rungume ta,
Duk da basu san me ya saka shi kuka haka ba,amma sun san ba karamin abu bane zai saka shi kuka haka,dumin kuwa shine mai ƙarfin zuciya a cikin su,shine mai kwantar masu hankali a ko wani lokaci,tun bayan faruwar wani babban lamari a rayuwar su,wanda shi ne yayi sanadiyar sauya komai na gidan,ya mai da masu da gida tamkar kango wanda babu mutanen dake rayuwa a cikin shi,tun daga lokacin da suna rasa NURUL AINI,wato hasken idaniyar su,mai haska zukatan wannan Alhali gaba ɗaya,sunyi babban saken da ZINARIYAR da suke ji da ita tabar hannun su,wanda suke tunanin da wuya ta kuma dawowa hannun.
Abdulmajid da bai da wuyan kuka wanda shine Babban yayan su,ne ya zo ya rungume shi yana hawaye"Me haka Abdulmalik,so kake ka kara tayar mana da hankali,ɗan Allah na rokeka ka faɗa mana damuwar ka,ɗan uwan mu"
Dagowa yayi ya kalle su,yayin da wasu hawayen ke kara sauko mai a ido,dukar da kai yayi,sannan ya dago cikin matsanancin rauni yace"Mama na ganta,na ganta yau a garin Abuja "
Cikin sauri Abdulrahman ya kara so in da yake"wa ka gani! Wa ka gani yau a Abuja,pls ka faɗa mana"
A jiyar zuciya ya sauke me haɗe da kuka,"Yaya,wallahi na rantse Allah wannan karon naga Ummu Salma a garin Abuja, na....
Ganin ta tafi suuu tayi baya tana ƙoƙarin faduwa ne yasa da sauri suka tare ta suna kiran sunan ta a kidime,tare da taimaka mata suka zaunar da ita kan kushin,
Kiran sunan daya faɗa ta fara"Salma! Salma,dan Allah ku nimomin Salma kamin in mutu,akwai abinda nake son na faɗa mata,"riko hannun Abdulmalik din tayi"ɗan Allah ka taimake rayuwa ta Abdulmalik ka kai ni wurin Salma,waiyo Allah rayuwata bata amfana min komai ba sai aikin dana sani,na bi son zuciya na cutar da rayuwata da ta ƴa ta,na kai kaina ga halaka bayan nasan cewa halakar ce,ya zanyi da rayuwata,waiyo ya Ubangiji ka yafe min,ka yafe min na tuba"
Tsugunawa yayi a gabanta tare da zube guiwoyin shi a ƙasa yana zubar da hawaye mai ciyon gaske,"Mama ina niman gafaranki domin na kasa kawo maki ita,domin kuwa a Traffic na ganta,ko da na kira sunan ta muna haɗa ido da ita ta fita daga adaidaitan da take,na yi niman ta a wurin banganta ba,kwanana biyu a kullum a wurin nake yini ko Allah zai sa na ganta amma banganta ba Mama"ya faɗa yana kifa kanshi a cinyar ta.
Dafa kafadar shi Abdulrahman yayi"karka damu Abdulmalik,ko da ace zamu zagaye garin Abuja,insha Allah in dai anan Ummu Salma take sai mun ne mo ta,"
"Kwarai kuwa" Cewar Abdulmajid,domin kuwa sun san dole zai kasance cikin damuwa,duk cikin su yafi shakuwa da ita sosai,
"Mama ɗan Allah ki bar kuka haka,kin ga kada Dady ya tashi yaga idonki ya kumbura haka zai damu,idan kuma yaji batun Salma kin san me zai iya faruwa, pls"
Hannu tasa tana sharewa wani na zubowa "na kasa tsayar dasu,a ko wani lokaci ƴar uwar ku na cikin rai na,tunda tabar gida dai dai da sakon daya ban taba manta taba,a ko wani numfashi na cike yake da nadama,da dana sani,ji nake da za'a dawo da lokaci baya,da ban haɗu da miji kamar mahaifinku ba,da dana haɗu dashi dana ki amincewa dashi,kila da kaddarata bata zo a haka ba," Dago kai tayi ta kalle yaranta maza dake zagaye dasu,"a lokacin da kanwar ku ta faɗa min damurta,a matsayina na uwa kamata yayi na nima mata mafita na gari,sai na bata shawara akan tabi ta hanyar da nake bi,!a lokacin kun san me tace min kuwa?
Duk kallon ta suke cikin tsananin sanyin jiki mai haɗe matsanancin damuwa irin wanda yake tafiya da kuzari,
A lokacin kuka ta fashe dashi tare da rungumeni,tace min Mama kina ban tsoro,wannan kamar ba Mama na ba,dan Allah ki dai na faɗin haka kina ban tsoro,
Da wannan hannun nawa na ture ta,na ce mata sai ta nimar ma kanta mafita da kanta,amsar da ta ban shine,na yi dana sanin zuwa duniya a matsayin ƴar ku,da Ace Allah yana ba ya'ya zabi su zabi iyaye,Mama da ban zabe ku keda Dady a matsayin iyaye naba,na kwammace a haife ni a cikin ahalin da basu da komai sai sun fita sunyi bara sannan su ci dani,ba zan taba bi ta hanyar da kuka bi ba ke da Dady,Allah ya isa tsakanin ke dani,da kuma wanda yake a matsayin uba a gare ni,Ubangiji shi zai min hisabi daku ta yanda kuka kawo ni wannan duniyar,:
Wannan shine maganar kanwarku dani na karshe,Abdulmalik na tabbatar da haƙƙin ta ba zai bar ni ba,maganarta gaskiya ne,ban cancanci zama uwa ba,dan Allah ku gafarce ni"ta faɗa cikin matsanancin kuka tare da haɗe hannun ta wuri ɗaya.
Dukkanin su rungume ta suka yi suna masu kwantar mata da hankila,domin kar hawan jinin ta ya tashi,
Da kyar dai suka samu ta yi shiru,yayin da kowannensu ke fama da kuka zuci,domin kuwa Ummu Salma farin cikin su ce,ita ce Nurul Kalbi a gare su.
Jin wani ɗan ƙara ne yasa duk suka dago,
Mikewa tayi tsaye,tana ɗan share fuska,"ina ga mahaifinku ya tashi,muje ku duba shi"
Duk bin bayanta suka yi,suka bi ta cikin wani korido a falon in da yasa dasu da wani karamin falon wanda akwai wani dakin a cikin sa,dakin suka shiga,in da wani farin mutum ke kwance a kan gado an daura mai abun jawo numfashi a hanci,sai na'urorin dake zagaye dashi masu nuna blood pressure,da temperature,sai respretion,din shi,
Duk zagaye shi suke yi suna mashi sannu,da ido kawai yake iya amsawa,yana bin su da kallo daya bayan daya,kafin ya saida idanun shi akan matarshi,
A hankali ya daga hannun shi ya mika mata,
Matsowa tayi tare da kama hannun shi ta riƙe,
Cikin dauriya ya ɗan daga abin zukar numfashi,a hankali ya furta "Salma,ta dawo"
Da sauri Abdulmalik ya maida masa abin a hancin shi,"Dady ka kwantar da hankalin ka zata dawo,insha Allah zata wo"
Mai da ido kawai yayi ya lumshe,bai ƙara ce masu Komai ba har suka bar dakin...
*Abuja*
Sai da ta sauka a Adaidaita sannan ta shiga niman pos ɗinta,
"Ohh, ya Allah,ina ganin na barshi a motar wannan mutumin," Tsaki taja,sannan ta karasa inda me gadi ke zaune,"Audu ka bashi dubu daya idan nashiga ciki kazo ka ansa"
"To Hajiya an gama" Daki kuwa ya shiga ya dauko dubu guda ya ba mutumin.
Ita kuma tuni ta shiga gida,
Dakin ta shige kai tsaye tare da ciro wani madaidacin akwati ta shiga zuba kayanta a ciki,
Ummita ce ta shigo,dan su gaisa,sai dai ganin yanda take haɗa kaya a akwati cikin sauri ne yasa ta tsaya tana kallon ta,"tafita zaki yi ne Biba?
ba tare data juyo ba ta bata amsa"Eh"
"Zuwa ina,ko wani aikin ne ya taso"
"Legos zan je,ina ga daga nan zan tafi England ba yanzun zan dawo ba"
Cikin sauri ta ƙarasa in da take tare da karɓar takalmin data dauko tana kokarin sawa a jakka,"Biba amma lafiya,tafiya cikin gaggawa haka,kuma ba aiki ba"
Dauko wani tayi ta saka"sauri nake yi,"
"To zan biki"
Kafin ta bata amsa ne wayar ita Ummitan yayi kara,
Dubawa tayi,wanda ganin me kira ne yasa da sauri ta saki hannun Biba data riƙe tana danna wayar tare da ƙarawa a kunne,
Kafin tayi makaga sai cewa aka yi"idan kina tare da ita ki bata "
Cikin sauri ta mika ma Biba wayar,tare da faɗin "VIP ne"
Bata yi niyar karba ba sai dai jin sunan da aka kira yasa ta amsa tare da karawa a kunnen ta,"ina jin"abinda tace kenan.
Daga ɗayan gefen kuwa sai cewa akayi"ki shirya a yau da yamma zaki bi jirgi domin zuwa Kano,akwai aiki mai muhimmanci da za ki yi a can"
"Akan waye? Ta tambaya.
" YOUNG USTAZ "............
*sai mun haɗu a paid group*
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*10*
*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*
"Akan waye" Ta tambaya,
Ta ɗayan ɓangaren ne aka bata amsa da "YOUNG USTAZ"
Shiru tayi yayinda ta shiga tunanin ina ta taɓa jin wannan sunan,
Bata son tayi Stressing brain ɗin ta shi yasa ta kara tambayar"waye shi"
"Idan kin isa Airport akwai wacce zata baki wani envelope mai dauke da duk wasu bayanai na mutanen gidan wanda ya kamata kisani har da na shi"
"Zan iya tafiya da Ummita? Ta tambaya tana kallon Ummita wacce ke haɗe hannun ta alamun roƙo akan zata bita,
" A'a domin wannan karon aikin ya banbanta da wanda kuka