Showing 108001 words to 111000 words out of 159134 words
Chapter 37 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt
basu takardun kammala karatu,in da ta samu kyautuka masu tari yawa kasancewar ta First Class,
Ba zata taɓa mantawa da wannan ranar ba a rayuwar ta,
Abinda ya faru kuwa a lokacin shine Yaya Abdulrahman baida lafiya sosai har yakai ga an saka masa bututun shaƙar numfashi,wannan dalilin ya hana daga gida babu wanda yazo mata, duk da ba daɗi sai dai bata ji haushin su,
Abinda ya ɓata mata rai shine rashin halarta Yusuf wurin har aka gama ta dawo gida,
Kiran number Mama tayi tana tambayar ta mai jiki,
"Da sauƙi ta amsa mata"
"Mama ki gaishe shi idan ya farka"
"Zai ji"
Dan shiru suka yi na sakanni,kafin tace "Mama,dan Allah ko zaki ma Yusuf magana da kanki ko zai yarda muga likita tunda cikin satin nan zamu dawo,"
"Salma ke ma kisan ban cika son shiga harkar mijin ki ba,ki bari idan kun dawo koma dai menene sai mu yi magana"
"Dan Allah Mama,ni dai nafi son kawai ki mai magana mu ga likita anan"
Numfashi ta sauke"to kai mashi wayar"
Dariya ta saka"na gode Mama"
Koda ta shiga dakin shi yana wanka,"Mama bari zan kira ki zuwa anjima domin yana wanka yanzun"
Da to ta amsa tana kashe wayar,
Ita kuma zama tyi anan bakin gado tana tunanin yanda zasu kare da Mama,Allah dai yasa ya amince,ai kuwa da ta ji daɗi,
Hannunta ne taje ajiyewa shine ya sauka a kan wayar shi dake ajiye,
Murmushi tayi tana juyo da fuskar wayar"shi kenan bai da aiki sai kallo a waya,ji yanda ya kife waya salon mutum ya zauna a sama sekrim ya fashe y..........
Sauran maganar nata ya makale ne sakamakon wani irin mugun gani da tayi a rayuwar ta wanda har yau yake mata gizo a kwakwalwarta,har a bada bata fatan tuna abinda ta gani a wannan wayar,
Domin kuwa Video ne hannun ta ya danna ya shiga play,
Fuskar Baba ne a bayyane yana tsaye haihuwar uwar shi tare da Yusuf da ke kwance yana mika mashi hannu alamun yazo gare shi,
Yanda kasan mata da miji,sumbatar juna suke yi suna shafa jikin juna,yayin da lokacin daya Baba ya shiga aikata Madigo da Yusuf ta baya,suna masu kururuwan jin daɗi,
Haka ma video na gaba,wanda sai da tayi playing uku duk su biyu ne a daki mabanbanta suna aikata Luwaɗi,
Daga zaunen da take ne ta ji idanun ta na ƙoƙarin rufewa,jin alamun zai fito ne yasa da sauri ta ajiye wayar tana fita daga dakin a daddafe saboda duhun da take gani,
Da kyar ta iya kai kanta ɗakin ta zauna a kasa ba tare da ma ta san cewar a kasar take ba,
Tunda take a rayuwar ta bata tsammanin duka su biyu zasu iya aikata haka ba,
Mijin aurenta da mahaifinta,
Duk yanda taso ta ƙaryata kanta kasawa tayi,haka kuma duk yanda taso ta gasgata kanta nan ma kasawa tayi,
Tsabar tashin hankalin da ta shiga ko kiran Mama bata iya ɗauka ba,a ranar tai ma kanta buking din jirgin Nijeriya wanda gobe zai tashi ƙarfe tara na safe,
Ranar duk iya sata irin na barci kasa ɗaukarta yayi,domin idanunta kuwa kafin wayewar gari sun kumbura,haka kuma a lokacin da za'a auna jinin ta to zai iya kaiwa ɗari biyu, ji take zuciyarta ya mata wani irin nauyi har numfashinta bai iya fita da kyau,
Sai dai bata damu ba, da halin da take ciki dan haka ko ta kanshi bata bi ba,ƙarfe takwas na safe ya mata ne a airport,ita bata ma kaunar ta ganshi domin hankalin ta tashi zai ƙara yi,nimar wanda zai karyata mata lamarin take yi,dan haka tana buƙatar Mama,tana son tayi magana da ita, dan baza taɓa iya ɓoye mata wannan lamarin mai girma ba.
Ƙarfe tara jirginsu ya shilla a sararin samaniya.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*66*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Jirgin su na sauka,Adaidaita ta tare ya kawota har cikin unguwar su,
A baki Get tace ya tsaya sannan ta ciro kuɗi ta bashi,ko tsayawa karɓar canji ba tayi ba ta buɗe Get ta shige,
Megadi na ganinta ya taso cikin rawar jiki da murna zai tare ta,sai dai ko takanshi bata iya yi ba sai ma sake mashi aƙwati da tayi ta karasa cikin gida tana kwalla kiran sunan Mama,
Daya daga cikin masu aikin gidan ne take sanar da ita ba kowa a gidan domin duk suna Asibiti wurin Abdulrahman,
Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi da tana ƙoƙarin danne duk wani damuwa dake ranta,sai dai wannan lamarin ba irin wanda zata iya jurewa ba na,Oh shiyasa wato bai da ra'ayi akan mata ko,
Dakin Mama ta shiga ta watsa ruwa sannan ta canja kaya,sai dai a kwana ɗayan nan kawai idan ka ga irin ramar da tayi zaka yi tunanin ko tayi shekara ne tana ciyo,
Ta dauko mayafi tana ƙoƙarin fitowa ta tafi Asibitin sai ga Mama ta shigo,
Tsayawa tayi baki buɗe tana mata kallon mamaki"ke ce kuwa da gaske"
Nan take ta ji komai ya ƙara dawo mata saboda,raunin da take kokarin ɓoyewa ne ya baiyana,
Da sauri Mama ta rungume ta tana shafa bayan ta "ina Yusuf din yake?
" Na baro shi a can London"
"Kika taho nan ke kaɗai?ko dai faɗa kuka yi ne?
Girgiza kai tayi cikin tsananin kuka tace" Mama!na ga Baba da Yusuf a waya"
Kasa karasawa tayi sai yanke jiki da tayi ta faɗi,dan nan take numfashin ta ya ɗauke,
Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana,domin ihu Mama ta fara tana kira sunan ta,abinda ya kuma bata tsoro shine ganin jini na fita daga kasa ta,
Kasancewar Mama mace mai jiki yasa ta dauke ta da kanta ta saka a mota,direba ne yaja suka tafi Asibiti,inda anan ne aka karbe ta aka shigar da ita dakin taimakon gaggawa,
Sai bayan awa daya da rabi likita ya fito,
Anan yake sanar da Mama cewar sai dai suyi haƙuri domin cikin dake jikinta dan sati takwas ya fita,sannan sun mata wankin ciki,yanzun haka tana dakin hutu suna iya zuwa su ganta,
Kuka Mama ta fara tana riƙe hannun Baba wanda isowar shi kenan ya samu likita na wannan bayanin,
Lallashinta ya fara yi "idan har kina kuka haka ita kuma me ya kama tayi kenan,ya isa haka zo mushiga mu duba ta"
Tare suka shiga dakin da take kwance ita kaɗai,idanun ta a buɗe suke yayin da take kallon sama,
Jin an buɗe ƙofa ne yasa ta maida kallon ta kan ƙofa,ganin shine yasa ta lumshe ido tana ƙoƙarin koran abinda ke zuwa mata a cikin ƙwaƙwalwa,
Da sauri suka karasa inda take,rike hannun ta yayi"Salma kina lafiya?ya jikin naki?yanzun me yake maki ciyo?
A hankali ta zame hannun ta a cikin nashi,"Mama ina Yusuf "
Ajiyar zuciya ta sauke"karki zamu yana hanya,sun riga sunyi magana da Baban ku,ya shaida mashi kina nan"
"Me likita yace" Ta tambaya yayin da maganarta ke fita a hankali,
Kallon juna suka yi sai dai sun kasa faɗa mata,ba tare data ce masu komai ba ta juya baya yayin da take jin hawaye masu zafi na ƙara wanke mata fuska,
Ganin haka ne yasa suka mike suka fita tare da jawo mata ƙofa dan ta samu ta huta,
Ganin sun fita ne yasa ta fashe da kuka sosai ko zata ɗan ji sanyi,ita a rayuwar ta bata San wani irin so take ma Yusuf ba,wannan abun da ta gani koda ace na karya ne yaci ace ta tsane shi,amma ta kasa,sai ji ma da tayi tana son ganin shi,ita ta san wannan shine babban jarabawar ta soyayyar Yusuf,
Ta jima tana kuka kafin barci mai nauyi ya ɗauke ta,
Ƙarfe hudu na yamma aka sallame su suka dawo gida,dan Mama ce ta tsaya da ita sai Yaya Abdulmajid,
Da taimakon Mama ta zauna a kan gado,tana ya mutse fuska,dan har yanzun tana jin murdawar ciki,
Har Mama zata fita ta kira sunan ta,"Mama"
Juyowa tayi, nuna mata kusa da ita tayi alamun ta zauna,
Dawowa tayi ta zauna kusa da ita,
"Mama,kinsan me na gani a wayar Yusuf?
Girgiza mata kai tayi,
" Video Baba na gani tare da Yusuf suna aikata barna,dukkanin su babu kaya ajikin su Mama,Luwaɗi suke aikatawa "share hawayen daya zubo mata tayi" Na kasa yarda,Baba ba zai taɓa aikata haka ba ko Mama?abu ne da Allah ya ya tsine ma masu yi,kuma duk mai yi Allah zai haɗa sa da mutanen Annabi Lut,aci gaba da azabtar dasu har ranar tashin kiyama,Mama saboda Luwaɗi Ubangiji kan iya juya kasa ya kife ta,Nasan Baba ba zai yi haka ba,balle da Mijina "
Rungumeta tayi yayin da taji wani irin tashin hankali na karyo mata,abinda take mata gudu kenan a wancan lokacin amma ita bata fahimtaba,
Dago fuskarta tayi suna fuskantar juna"kina jina ba?
Jinjina kai tayi tana ƙoƙarin rike kukan dake ƙoƙarin kucce mata,
"Kina son mijinki har yanzun?
" Mama na kasa daina son Yusuf,duk da baya kyauta ma rayuwata na kasa tsanar shi,gani nake idan har babu shi ba zan iya rayuwa ba"
"Bansan wani irin so kike mashi ba,in da ace zaki iya hakura dashi da sai nace ki hakura dashi Allah ya zaɓa maki wanda ya fi shi"
Girgiza kai tayi"ba zan iya ba Mama"
"Allah ya riga yayi ki mai ƙarfi sha'awa,shi kuma bashi da ra'ayi akan mace,zamanku akwai cutarwa mai tarin yawa Salma,sai dai hanya daya ce wacce za ku bi daga ke har shi ku zauna lafiya cikin kwanciyar hankali ba tare dakun rabu ba"
Dago jajayen idanunta tayi tana kallon mahaifiyar nata"wani hanya ne Mama?
"Zan faɗa maki,amma ki bari sai gaki gani ga kuma Yusuf"
"To yaushe zai zo?
" Ai na faɗa maki yana hanya na tabbatar zuwa anjima zaki ganshi,bari na hado maki shayi sai ki sha kafin a kammala abinci,ni zanje na duba yayan ki a asibiti"
"Ki ce Ina gaida shi Mama,sannan yayi sauri ya ji sauki gobe Birthday dina"
Murmushi tayi tana shafa kanta"baki manta ba"
"Umm"
A ranar ma koda Yusuf din ya iso da wuri bai zo ya duba ta ba duk da Baba ya faɗa mashi batun zubewar cikinta,sai ƙarfe tara na dare,
Duk da bata jin daɗin jikinta a haka ta ƙara yin wanka ta dan shirya sannan ta fito falo in da yake zaune,
Hmm jama'a kuɗi yayi,domin kuwa idan kasan Yusuf ada yanzun in ka ganshi ba lallai bane ka gane shi,
Zama tayi kusa dashi,tana ƙoƙarin ɓoye damuwar dake fuskarta "barka da isowa"
Ko kallon inda take be yi ba"Baban ki ya faɗa min abinda ya faru dake,Ashe ciki gare ki,to Allah ya kyauta,sai dai ki sani nayi farinciki zubewar shi domin ban tashi ajiye yara ba"
"Yanzun duk wannan tafiyar da kayi dan ka faɗa min haka ne?
Sallamar Mama ne ya kase shi daga amsar da zai bata,
" Yusuf video dana gani a wayar ka kai da Baba na menene?
Dagowa yayi ya kalle ta ta kuma kalli Mama da ta zauna"me abinda kika gani?
Share hawayen da ya sauko mata tayi,"Mama ki fada mashi ya min ƙarin bayani "
"Ai ba sai na maki karin bayani ba,itama tana iya maki tunda ta san komai"
"Kunga yanzun ba wannan maganar ba,ke Salma ki bar dauko wannan maganar,domin ba na son na sake jin shi a bakin ki,ni da nake son na samar maki mafita ta yanda zaki zauna da mijin ki lafiya,dan Allah ki natsu ki ban hankalin ki"
Shiru tayi kawai tana kallon Mama,domin ita ta ma rasa me suka maida ita,
"Kuna jina,hanyar da naga zai fi maku shine mai zai hana ke Salma ki yarda da wani namiji,ina nufin a duk sanda buƙatar ki na ɗa namiji ya taso ki ni me wani namijin ya sauke maki,tunda shi mijin ki bai da sha'awa,ko ya ka gani Yusuf?
Dariya ya fashe dashi sosai har da tafa hannu"kai lallai Mama ƙwaƙwalwar ki na ja,ni tuntuni da wannan shawarar kika ba mu ai da abin bai kai haka ba,gaskiya in dai ni ne wallahi ba matsala na amince da wannan shawarar "
Ji tayi kamar bugun zuciyar ta zai fito tsabar yanda yake harbawa,ji take kamar bata fahimce in da zancen su ya dosa ba"Mama me kuke nufi,Zina fa kenan,so kuke ke da Yusuf nayi zina da auren shi a kai na,?
"To me a cikin,ba gashi shi ya amince ba,ko kina da wata hanyar ne bayan wannan?
" Inna'lillahiwainna'ilaihirajiun"abinda take ta maimaitawa kenan,domin ji take kamar kanta na juyawa,
"Mama keda bakinki kuke cewa na aikata zina da aurena,?Yusuf da amincewar ka,?" Kara kallon su take da kyau dan so take ta tabbatar ko da gaske sune ɗin a gabanta,
"Ke ba Mama ta ba ce,ba maman dana sani bace! Nayi dana sanin kasancewarki uwa a gare ni,Gara ace wasu matsiyata ne iyayena baku ba,na y......
Saukar lafiyayyen mari ta ji a saman fuskarta,, nuna kanta tayi cikin tsananin bacin rai"do you think is easy for me na fada maki haka? Ni fa mahaifiyarki ce,y......
Wani Envelop ya ciro a Aljihun shi ya wurga mata"idan har ba zaki bi wannan hanyar ba,banga anfani zaman mu ba,domin ba na son takura,gashinan takardar saki ne,na sake ki saki biyu"
Daga zaunen da take ba ta san sanda ta zamo kasa ba,ta ma saka cewa komai,sai binsu da ido da take yi har ya juya ya bar dakin,
Cikin jin haushi Mama tace"ai yanzun sai ki samar ma kanki mafita"ta juya ita ma ta bar dakin........
Hmmmm.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*67*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Ta ma kasa yin kuka,zuciyar ta nauyi ya mata,yayin da idanunta ke ganin dishi_dishi,
Da kyar ta iya mikewa,da bin bango ta isa shiyan mazan gidan,
Ganin falon su a buɗe ne yasa ta shiga,Abdulmajid ne zaune yana cin abinci,
Ganin yanda ta shigo ne tasa ya Mike da sauri yana isa in da take "me ya faru,ke da bakida lafiya da sai ki kirani a waya,
Mika mashi takardar hannun ta tayi,amsa yayi yana fadin" na menene?
Ganin bata bashi amsa bane yasa ya buɗe yana karantawa,sai kuma ya saki murmushi"kai amma na ta yaki murna,at list yanzun zaki dawo hankalin ki,gaskiya naji daɗi "
Hawayen da suka kasa fitowa ne suka sauko "Yaya,Yusuf yaci amana ta, y.....
" Kinga dakata,ai kome ya maki ke kika ja,wani irin bayani ne ba mu maki ba a kanshi,karki manta na faɗa maki komai zai faru tsakanin ke da shi karma ki nufoni da batun dan haka ke ta shafa,ina fatan yanzun zaki yi hankali"
Juyawa tayi inda take jin motsin Abdulmalik,
Shima girgiza kai yayi"kinga je ki kwanta zamu yi magana da safe,dan ni yanzun ta lafiyar Abdulrahman muke ba naki ba"
A haka ta juya ta fito sai dai ba ta shiga cikin gidan ba,domin ji take gabaɗaya duniya ya mata zafi,bata taɓa tsammanin zata haɗu da irin wannan lokacin a rayuwar ta ba data roki Allah ya dauki ranta tun kafin yau.
Ta kusan kai ƙarfe biyu na dare zaune a wurin,ta ci kuka har ta gode Allah kafin ta tashi ta koma cikin gidan,
Ko da ta shiga daki ma kasa kwanciya tayi,sai zama da tayi a kasa,da tayi tunanin zata iya samun sauki a wurin Ƴan uwanta,sai gashi sun nuna mata sabanin tunanin ta,ita kuma wanda take gani tamkar majingina a wurin ta,sai gashi ita ke kokarin turata wuta,yanzun Hope din ta daya ne shine Baba,so take ta ganshi ta faɗa mashi komai ko zai karya ta mata,ya kuma samar mata mafita,
Jira kawai take gari ya waye, ta san ƙarfe takwas take dawowa.
A haka ta zauna idanun ta a bushe ar garin Allah ya waye,ganin ƙarfe tatwas da mintuna goma ne yasa ta fito,babu kowa a falon nasu masu aiki sun kammala gyara,dan haka dakin shi ta nufa kai tsaye,
Har ta kai hannu zata tura kofar dakin ta ji hayaniya na tashi yana fitowa daga cikin dakin,
Dakatawa tayi sai kuma ta juya zata koma,dan ta san Mama ce a dakin,yanzun kam bata shirya haɗuwa da ita ba,
Sai dai jin an kira sunan Yusuf ne yasa ta daka,
Baba ne ke faɗin"dan ya sake ta me na bacin rai a ciki,bai mata ƙoƙari ba,saboda ni ne fa ya amince ya aureta har yake zaune da ita, "
"Amma shine zai sakar min yarinya a gaba na,wallahi karya yake bari mu haɗu dan abin ba zai mai daɗi ba"
"Karma ki fara,domin kin San yanda nake son Yusuf ina iya yin komai akan shi,har ta ke ina iya rabuwa dake"
"In dai akan waɗannan ƴan iskan abokan harkallanka ne ai kasaba"
"Ni bansan in da yarinyar nan ta gado irin wannan jarabar ba na tsiya,ke me yasa ba zaki koya mata irin yanda kike yi ba"
"Me nake yi?
" Kin dai san ba zan taba bari Yusuf ya haihu ba,ki bata shawara tabi ta hanyar da kike bi,idan tana son yara ko nawa ne taje ta haifa zamu karba "
"Wai me yasa baka da adalci ne a rayuwar ka,kana son yanda ka bata min rayuwa na bata rayuwar yata,saboda ba kai ka haifa min ita ba,na tabbatar ubanta ba zai taba son haka ba"
Dariya ta ji ya fashe dashi sosai kafin yace"sannu,yanzun ke a yanda kike idan aka ce ki faɗi waye uban Abdulrahman zaki faɗa,balle na