Showing 93001 words to 96000 words out of 159134 words

Chapter 32 - YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

27 Sep 2025

9749

tayi cikin jin haushin kyale ta da sukayi tace"Baba yau fa Birthday dina so nake su bani kyautar karin shekara"

Dafe goshi yayi"My gimbiya yanzun fa ƙarfe biyar na asuba tayi,ko sallah ba'a yi ba,ki je ciki idan gari ya waye zasu baki "

"Ba zasu bani"

"I promise you zasu baki"

Juyawa tayi ta shige cikin shiyansu ta bar wurin,
Girgiza kai kawai yayi yana kwankwasa masu kofa sau daya tare da kiran sunan su,
Nan take kuwa sai gashi ko wanne yana buɗe ƙofar dakin shi yana fitowa,
Kallon su yayi"Amma kuna jin kanwar ku ko?

Hamma Abdulrahman yayi"Baba wallahi she is really Stoburn"

"Lokacin sallah yayi sai ku fito mu tafi masallaci"

"To Baba"

Koda suka dawo masallaci da zasu kulle kofa daga mai saka filo ya toshe kunne shi sai mai saka Earpis a kunne, dan kawai kar su ji damun da zata masu,
Sai dai fa duk da haka ƙarfe bakwai na safe na cika ta dauki katon sanda ta shiga bugun kofar su dashi tana kiran sunan su,
Ganin ba su da niyar buɗewa ne yasa da kuka ta nufi cikin gida dakin Mama wacce take kwance tana waya,
Kwantawa tayi kusa da ita tana cigaba da kuka wanda ganin haka yasa ta ajiye wayar"me ya faru?

"Mama su Yaya sun ƙi tashi su ban Happy birthday"

Kallon agogon bangon ɗaki tayi "ƙarfe bakwai yanzun,ki bari idan sun tashi zasu baki"

"Wancan karon ma haka suka min fa Mama,ni dai yanzun sun daina so na"

"Salma pls barci nake ji kin ji Sweet heart"

Sauka tayi akan gadon tana barin ɗakin ta shige nata ta kulle ƙofa,
Komawa tayi ta kwanta kan gado tana jin haushin abinda suka mata,daga haka barci ya ƙara kwashe ta,
Ba ita ta farka ba sai ƙarfe goma saura,banɗaki ta shiga tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na Les ruwan ƙwai da fari,
Ba karamin kyau kayan ya mata ba,sai Mayafin data yafa,ta fito shar da ita yanda kasan wata Ƴar Tsanar Zinari,

Ji tayi an Kwankwasa mata ƙofa,dama kuma tana shirin buɗewa ne dan haka buɗewa tayi,
Ji tayi abu mai ƙyalli ya zubo mata a kai yayin da yannin ta ke tsaye a gabanta suna mata waƙar Happy birthday to you,
Duk irin yanda take jin haushin su ganin yanda suke murmushi da dariya yasa ba shiri itama ta saki dariya tana kama ƙananan fulawar dake sauka a jikin ta,
Hannun ta Abdulmajid ya jawo suka gangaro da ita ƙasa,anan ta tarad da Mama rike da katon cake tana jiran isowar ta an kunna kendu a jikin shi,

Karamin wuƙa ya mika mata ta amsa,suna mata waka ta yanka cake ɗin,
Mama ta fara saka ma abaki kafin ta shiga saka masu daya bayan daya,sai Yusuf dake gefen shima yana murmushi dan ba karamin burge shi suke yi ba ta saka mashi shima a baki.

Wannan shine asalin rayuwar su mai ɗauke da farin ciki da annashuwa,

A hankali shakuwa ke ƙara shiga tsanin su da Yusuf wanda take kira da Game partner saboda duk lokacin da yazo gidan suna tare suna buga game yana biye ma duk wani shirmenta,kamar yanda yannin ta ke mata,

Wata biyu da cikar ta shekara goma sha-biyar takardar nima mata jam'i ya fito a London wanda anan zata karanta Lauya na tsayin shekara biyu,

Koda Baba ya kawo mata takardar a maimakon yaga farin ciki shimfide a fuskarta sai damuwa daya hango,yayi tambayar duniya amma sai ce mashi take babu komai,karshe ma sai tashi tayi ta fito daga falon shi wanda a bakin ƙofar fita ne suka haɗu da Yusuf yana ƙoƙarin shiga wurin Baba,

Kallon shi tayi na sakan ni kafin ta ɗauke kai tayi wucewar ta,
A cikin yan watannin nan da yayi tare da su,ta lura ba karamin ji dashi Baba yake yi ba,yanda yake ma Yusuf ko su Yaya baya masu haka,idan har Yusuf zai ce yana son abu to cikin rawar jiki kuwa zai ɗauka ya bashi har ma fiye da yanda ya tambaya,
Shida iyayen shi Baba ya basu wani tankamemen gida wanda babu abinda babu a ciki,sannan ga Mota lafiyayye ya siya mashi,amma su yaya tun yaushe suke bin shi ya sai masu mota yaƙi sai dai duk inda zasu Direba ya kai su,

A babban falo taci karo da Yaya Abdulmajid,rike ta yayi"ke kuma tunanin me kike kina tafiya?

Kallon hanyar data fito tayi "na fara jin haushin Yusuf" Ta faɗa tana tura baki,

Kama baki yayi yana dafe kwankwaso"ke kuma da ya maki me?

"Kalli fa yanda yake shiga dakin Baba kai tsaye yanda kasan wani Baban shi"

Rankwashi ya sake mata a kai"to ai Baban shi ne tunda yaron aikin shine,kin ga ban son gulma je ki faɗa ma Baba masu karɓar sadaka suna waje suna jira "

Dafe kanta tayi tana bata fuska "ba zan je ba ka je da kanka" Ta faɗa tana rugawa da gudu tayi hanyar dakin Mama,

Girgiza kai yayi "kyuya ko?zamu haɗu da ke" Ya faɗa yana wucewa dan sanar dashi,domin Al'adar shine yin sadaka a ko wani yamma,daga wurare ma mutane kanzo karɓar wannan sadakar nashi,shi yasa mutanen unguwar su ke girmama shi sosai,

Dakin Mama ta shiga da sallamah ta same ta a zaune kamar ko yaushe ita kenan yawancin lokaci cikin amsa waya,sam Mama bata gajiya da amsa waya,

Zama tayi kusa da ita "Mama"

Sallamah tayi da wanda take wayar ta juyo kanta"ya akayi Sweet heart?

Miƙa mata takardar tayi,

"Na menene?

" Na makaranta ne a London "

Nan take ta sake murmushi ta jawota ta rungume "Oh Sweet heart congrat yaushe ne tafiyar?

" Nan da sati biyu "

Ganin yanda tayi maganar cikin damuwa ne yasa ta ƙara kallon ta"me ya faru,ya naga kamar you ar not happy "

Ai kuwa kamar dama jira take ai mata wannan tambayar ta fashe da kuka wanda yi take ba kakkautawa,
Duk ta tashi hankalin Mama sai aikin lallashi take yi,
Da kyar ta samu tayi shiru ta natsu,
"Faɗa min meke faruwa"

"Mama ke kika ce duk abun dake damuna a should feel free to tell you"

Jinjina kai tayi"sosai ma faɗa min ko ma menene I will be here for you "

Share hawayen idon ta tayi da yaƙe dai na zuba.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*57*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

"Mama ina ganin ina da karfin sha'awa"

Zaro ido tati cikin mamakin jin abunda yarta ta faɗa "Ƙarfin sha'awa kuma Salma?

Shiru tayi ta dukar da kai tana murza ƴan yatsun ta,

Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin saisaita kanta" Ta yaya kika san haka,i mean ya kike ji a jikin ki?
Ganin taki cewa komai ne yasa ta riƙo hannayen da take murzawa "ba na ce zan taimaka maki ba,dan haka faɗa min "

Dan rintse ido tayi ta buɗe,tana jin kunyar yanda zata faɗa,sai dai ba ta da wanda zata ni ma shawara ne sai ita Maman,domin duk rashin kunyar ta ba zata iya tunkarar daya daga cikin yannin ta maza ta nime shawarar shi ba,ko yanzun ma abun yana son yafi karfin ta ne "Idan har zan kalli wani namiji na kan ji tsigar jiki na yana tashi,sai kuma in ji ina son in rungume shi,haka kuma idan na kalli film naga mace da namiji sun yi Kiss ji nake kamar na samu wani kusa da ni da zai min,jiki na sai ya dinga kaikayi ta ciki wani lokaci har jikewa nake yi ta cikin pant di na,hankali na tashi yake"

"Har da yannin ki kina jin haka a kansu?

Da sauri ta girgiza kai" Su bana jin komai a kansu ko kaɗan "

Dan shiru Mama tayi tana nazarin maganarta tabbas sha'awar ne,to sai dai ya zata yi da ita,

"Mama baki ce komai ba?

" Salma tunani mafita nake yi"

"Mama ina da mafita"

Kallon ta tafi ta zuba mata ido na wani lokaci kafin tace "wani iri?

" Mama na yanke shawarar aure zan yi"

"Aure!aure fa kika ce Salma?yanzun ke har kinsan aure?

Dukar da kai tayi" Ni dai aure nake so "

Tama rasa me zata ce mata sai ido data zuba mata"shekaran ki nawa ma?

"Goma sha biyar"

"And you want to get marriage at this age?

Shiru tayi bata bata amsa ba,

"Answer me girl"

Kara marairaice fuska tayi"Mama ni dai duk hukuncin da zaki yanke dan Allah kumin aure "

Dafe kai tayi kafin ta kuma cewa"to wa zaki aura?

Kai tsaye ta bata amsa wanda sai da tayi dana sanin faɗin hakan domin tunda suke da Mama bata taɓa yi mata tashin hankali ba irin na yau "Mama Yusuf nake so,shi nake so na aura "

Wani irin zabura da tayi tare da faɗin "What" Sai da ta matsa baya,domin kamar abin yazo ma Mama a bazata ne,

"Yusuf fa kika ce"

Shiru tayi tana zazzare ido,

"Wasa dai kike yi ko?

" Umm um,i Love him i want to married him"

Cikin tsananin faɗa da rufewar ido tace"ba dai a gidan ba,in banda rashin hankali da rashin sannan ciyon kai me zaki yi da wannan yaron,to bari kiji in dai har ina raye ba zaki taba auren wannan yaron ba har a bada ba dai Yusuf ba,wato zaman da yake yi cikin ku bana arziki bane yana zuwa ne dan ya hore maku kunne,to ba dai a gidan nan ba zai koya maku bakin hali da mummunan ɗabi'a ba,kar na kuma jin kin yi maganar aure a gidan nan balle maganar shi,kuma tafiya karatu dole ne,tashi ki barmin daki mahaukaciyar banza"

Da kuka ta tashi ta bar dakin tana mai matukar jin zafin abinda Mama ta faɗa akan Yusuf,

Ranar yi ni tayi kuka a daki wanda sai da idanun ta suka kumbura shi yasa ko abinci dare bata fito ci ba,

*Ban sani ba ashe wannan shine mafarin komai,Ashe Mama ta san abinda ni ban sani ba game dashi,amma a wannan lokacin yarinta da ƙuruciya sun hanani ganin komai sai ma laifin Mama da nake gani* buɗe shafi na gaba yayi.

Ganin har sun kammala cin abincin dare ban fito ba gashi basu ji Mama tayi magana ba yasa Ya Abdulmalik cewa"Mama lafiya banga autar ki ta fito cin abinci ba?

Kauda kai tayi"ƙila ta ko shi ne,idan yunwar cikinta ya isheta zata fito"

Duk kallon_kallo suka shiga yi ma junan su,abinda bai taba faruwa ba,kome Salma tai mata da zaran lokacin cin abinci yayi taga bata fito ba da kanta zata shiga lallashi har sai ta lallabata ta fito ta ci,

"Mama wani abun ya faru ne? Abdulrahman ya tambaya tana ajiye chokalin hannun shi,

" Kamar me kenan?

"Tsakanin ke da Salma"

Itama ajiye nata chokalin tayi"ku saurare ne,daga yau sai yau bana son na ƙara ganin ku tare da wannan yaron "

"Wani yaro" Cewar Abdulmajid,

"Yusuf,bana son na kuma ganin ku tare,ko a gida ko a waje,"

Duk shiru suka yi suna mata kallon mamaki,
"Mama dan Allah idan har wani abu ya faru ne ki faɗa mana"

Mikewa ta yi "na dai faɗa maku,idan ana son zaman lafiya a gidan nan sai a kiyaye" Tana gama faɗa ta yi shigewar ta daki ta barsu nan zaune baki sake,

"To me yake faruwa"

"Wa ma ya sani,ku tashi muje mu duba Salma"

Mikewa sukayi suna masu bin shawarar Abdulrahman,

Sai da suka ƙwanƙwasa ƙofar har sau uku suna sallamah ba'a amsa ba,jin shirun yayi yawa ne yasa suka tura ƙofar suka shiga,
Tana zaune a tsakiyar gado rungume da filo tana sauke ajiyar zuciya irin na wanda yayi kuka ya gaji,
Da sauri suka ƙarasa inda take cikin tashin hankali suke tambayar ta me ta faru,me yasa take kuka,

Rungume Abdulmajid tayi tana ƙara fashewa da wani sabon kukan,

Shafa bayan ta ya hau yi"Ya isa haka nan,yayi,kinga jikin ki har ya fara zafi,"

"Yaya me laifi na ma Mama,kawai ɗan nace ina son shi?

Kallon juna suka yi" Waye kika ce mata kina so?

"I am just feeling somehow,I want to get married and I tell her cewa Yusuf nake son aure,shine Mama take ta yi min ihu tana faɗa wai Yusuf ba mutumin kirki ba ne,in dai tana raye ba zata taɓa bari na aure shi ba" Ta kara fada tana saka sabon kuka,

Duk shiru sukayi suna tunanin wannan lamarin,
Abdulrahman ne yace"but the Yusuf I know is not a bad person, ko kuwa?
Ya tambaya yana kallon sauran ƴan uwan nashi,

"Gaskiya ne" Dago ta yayi yana share mata hawaye "kin ga ki kwantar da hankalin ki insha Allah zamu samar maki mafita"

"But Mama tace sai dai bayan ranta,ya ya zan yi?

"But Girl I think you are to small for marriage,domin abinda na sani there are so many complications about marriage,sannan a wannan kananan shekarun naki how are you going to handle them, ta yaya,ni fa ina ganin Mama ta na da dalili"

Duk shiru suka yi suna sauraren shi,
"But Abdulrahman tana son shi"

"Is doesn't matter ko tana son shi,abun nufi shine ya rayuwar ta zai kasance,bancin haka makaranta fa zata tafi London nan da sati biyu,ta yaya zata dauko zancen aure bancin shekaranta sha biyar"

Karfin kukanta ta kara tana maida kanta saman filo "Ku fita I don't wanna see you,"

Dafa ta Abdulmajid yayi"tunda dai har kina son shi ni dai ina bayan ki,tashi ki faɗa min dama kun jima kuna soyayya ne?

Tashi tayi zaune tana girgiza kai"a'a is one side love "

Duk zaro ido suka yi"Uhhh "

Jinjina masu kai tayi "Yes,I never get a chance to tell him"

"Amma shine kike cewa zaki aure shi,kin faɗa mashi ne? Abdulmalik ya tambaye ta wannan karon,

"Kawai ni Mama na faɗa ma kafin na fada mashi"

Dafe goshi Abdulrahman yayi "ohh God,gashi nan bay this your stupid action kinsa Mama ta tsane yaro,to yanzun sai ki faɗa mana me kike son ayi"

Kai tsaye tace"Aure,auren shi nake son yi"

Zuba tagumi yayi yana sauraren wannan haukar na yar uwar tasu"zuwa yaushe kike son auren?

"Kafin na tafi London,idan ya so sai mu tafi tare dashi"

Mikewa tsaye yayi daga saman gadon nata"Abdulmajid jeka ɗebo mata abinci taci,ke kuma ki kwantar da hankalin ki zamu fara shawo kan Mama kafin mu tunkare Baba da maganar,sannan zuwa anjima zanje gidan su Yusuf din sai mu yi magana dashi a can"

Ai kuwa nan take farin ciki ya mamaye duk wani bacin rai na fuskarta "Na gode ya Abdulrahman"

Ko kulata bai karayi ba ya fita,
Abdulmajid ne ya kawo mata abinci tana ci suna hira har da Abdulmalik har saida suka tabbatar da ta ko shi kafin su bar dakin.

A falon su suka same shi zaune yana waya wanda daga dukkan alamu da Yusuf din yake waya,sai da ha kammala sannan ya ajiye wayar ya kalle su"Abdulmajid kai zamu tafi gidan su Yusuf da kai,
Kai kuma Abdulmalik ka zauna har mu dawo"

"Ba damuwa sai kun dawo amma dai karku daɗe domin kun ga takwas da rabi ya wuce"

"Ok" Kawai suka ce mai suja fita,

Ba da direban gida suka je ba,dan basu ma son Mama ta san sun fita,dan haka suna barin Get din gidan suka tare Adaidaita suka shiga,
Har kofar gidan Yusuf ya kai su sannan suka sallame shi ya wuce,

Me gadin gidan ya san su dan haka ko da suka Kwankwasa ya buɗe yaga sune bai hana su shiga ba sai gaida su cikin girmamawa da yayi,

Suna shiga ciki a ƙofar falon su wurin da aka zuba kujeru dan hutawa suka same shi,
Sai da suka ja kujera suka zauna sannan suka shiga gaisawa kamar yanda suka saba,

Dariya yayi"yau kune a gidan namu da daddare,hala daga wani wuri kuke?

"A'a daga gida dai"

"Wow kace today was my lucky day,to bari na kawo maku abun motsa baki"ya mike yana faɗin "ina Game partner di na da Abdulmalik suke ke?

"no bar shi kawai dama akwai magana mai muhimmanci daya kawo mu,su suna gida"

Komawa yayi ya zauna yana tunanin wani irin magana ne da zai fito dasu gida yanzun haka,shi yasa yayi mamakin daya gansu a wannan lokacin,"ina jin ku"

Furzar da iska Abdulrahman yayi kafin yace "Me tsakanin ka da Ummu Salma?

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*58*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Maimaita tambayar yayi "meke tsani na da ita?

" Umm"

Dan shiru yayi yana nazarin wani irin tambaya ne wannan sannan da wani amsa ya dace ya basu,"maganar gaskiya ban gane inda wannan tambayar ta dosa ba,dan nasan babu komai tsakanin ni da ita,kawai dai ina mata kallon kanwata ce kamar yanda kuke mata,that's all"

Kallon Abdulmajid yayi"That's so bad "cewar Abdulrahman

Jinjina kai yayi"nan da sati biyu zata wuce karatu London"

"Wow that's Nice,gaskiya na taya ta murna sosai"

Ƙara kallon juna suka yi,kafin yaci gaba da faɗin "sai dai akwai ɗan matsala"

Shiru yayi yana sauraren su,"matsalar me?

"Taki yarda da batun tafiyar domin wai aure take so,idan har ba'a mata aureba ba zata tafi ba"

Dan waro ido yayi"aure fa,da yaushe ta isa aure bayan shekar ta goma sha biyar,kai gaskiya Salma da rigima take,yanzun ita wa take so ta aura,ko dama tana da saurayi ne?ya faɗa yana tsare su da ido,

"Maganar gaskiya bamu sani ba sai yau a dazu,sannan da muka tambaye ta sai cewa tayi kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login