Showing 3001 words to 6000 words out of 180103 words

Chapter 2 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

18 Sep 2025

708

kamar ya rab'e gida biyu ba Yana balain kewarta a zuciyarsa Yana balain San ganinta Amma ya rasa Mai ke sa shi Jin wani irin nauyi da d'ad'aurewar jiki

"Ka tafi d'aki kaje ka watsa ruwa kazo kaci abinci"

Umma tace Tana Kara hararsa sabida yanda taga yana satar kallon d'akin Naeema.

Su Safiyya da suka zubawa tv ido yabi da kallo Yana Jin wani irin Mugun Haushin rashin tarbiyya da basu dashi

A tsawace yace musu "Kunyi Sallah kuka zauna Kuna kallo"?

Da Sauri suka mik'e mahaifiyarsu kuaa tace "Ku koma ku zauna ku cigaba da kallonku sabida na tab'a yar gold yake neman hucewa akanku Banda iskanci irin na Naseer har yazo Yana tambayar 'yarsa taci abinci a gabana"


"Umma wlh ba haka bane gani nayi Ana sallar isha suna zaune suna kallo shiyasa nayi musu magana"


"Dalla rufemin baki bazasu tashin ba sai ka bugesu yanda ka Saba bugunsu akan wancan mayyar matar taka"

"Allah ya baki hakuri"

Naseer yace Yana Kara kallon su Safiyya da suka koma suka zauna har da Kara volume din tv shi kuwa ya wuce d'akinsa Yana Jin wani irin d'aci a makogaransa shi Kuma nashi jarrabtar kenan Mahaifiya bai San Mai yasa take masa haka ba har gida ya Kama Mata tak'i yarda ta dage sai ta zauna dashi da kannensa wajen su uku.

Alwala ya daura ya fito ya tafi massallaci bashi ya dawo gidan ba sai wajen takwas da rabi har a lokacin suna zaune suna kallo.

Ko sallamar da yayi ba Wanda ya amsa masa Inda sabo ya Saba hakane yasa ya kinkimi Zahira da ke bacci a kasan carpet ya Kai ta d'aki ya dawo ya d'auki Nadiya itama ya kwantar da ita a gefenta ya dawo palon ya zauna duk da ba yunwa yake ji ba bai isa yace ya koshi ba dan Umma fad'a zata rufeshi dashi kamar zata Kai masa duka.

Yana zama umman ta mik'e ta nufi kitchen da kanta ta d'auko farantin data jera abincinsa a Kai ta ajiye masa yace mata ya gode.

Yana bud'e abincin yaga baki bakin gari a kwance akan farar Shinkafa a hankali ya saka cokali ya fara jujjuyawa Yana mamakin abubuwan da yake yawan gani a abincin da umman ke bashi Amma bai isa ya tambaya Bismillah yayi ya fara cin abincin.

Umma kuwa tayi Tsaki Tana zabga Mai harara taurin Kan Naseer din na balain Bata mamaki.

Yana gama ci ya koma d'aki ya kwanta ya zubawa Zahira Ido Yana kallon ta tamkar itace Naeema sosai yake so ya tuno ta wani Abu na danne shi har karfe goma sha biyu na dare bacci yak'i zuwar masa hakane yasa ya d'aura alwala ya hau Kan sallaya ya tadda sallah Dan tun Yana shekara goma sha biyu ya sauke al qurani Mai girma Naseer nada ilimin addini sosai Wanda duk mahaifinsa Mallam Ibrahim ya gado Dan shahararren mallami ne
Sosai har almajirai ne dashi da yawa har sai daya rasu.


Har karfe biyu Yana Kan Sallaya a zaune Yana Jan carbi maganar da yake juyowa kasa kasa yasa ya mik'e a Hankali ya bud'e k'ofar d'akinsa ya fito a tsakiyar palon ya hango mahaifiyarsa sanye da jar doguwar Riga har kasa hannunta rik'e da kunnen Naeema.

Sallati ya fara yi dayaji kansa ya balain Sara masa ya koma d'akinsa da Sauri ya zauna akan sallayar ya dafe kansa da hannu biyu Sabida nauyin da kansa ya masa.

"Naseer ka dage da Addu'a mahaifiyarka Tana cikin kungiyoyi da yawa bansan wacece ita ba sai Dana aureta"

Kalaman da mahaifinsa ke yawan Gaya masa kenan a lokacin da yake rayye.

"Watarana zaka ganewa idonka watarana zaka San wacece ita Naseer mahaifiyarka Bata bacci daddare"

Kansa ya Kara rik'ewa Gam a lokacin da yaji kansa ya Kara Sara masa daya tuno maganar mahaifinsa.....


Share
8/19/21, 10:30 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 2*

*Naseer*

Mahaifinsa Mallam Ibrahim Dan Asalin Kauyen Modobi ne dake jihar Kano fitattacen Mallami ne a kauyensu har daga wasu garuruwan Ana zuwa d'aukar karatu wajensa manomi ne Yana Kuma had'awa da kiwo tun Yana da shekara ashirin yayi aurensa na fari da wata hindatu a cikin shekara hud'u ya auri Mata hud'u bayan hindatu akwai Aisha akwai Fatsima sai Zinnira Zaman lafiya ake sosai a gidansa Dan matansa sun had'e kansu Mallam Ibrahim a tsaye yake sosai Akansu hindatu nada Yara biyar Aisha nada hudu Fatsima nada hudu itama sai Zinnira dake da biyu

Duk yayan Mallam ibrahim suna da shekara goma sha Suke sauke Al Qurani Mai girma da littattafan addini ya tsaya musu sosai wajen inganta tarbiyyarsu ko kadan bai wani damu suyi Boko ba sai dai idan yaran sun girma akaran kansu wasu suka shiga na Boko wasu Kuma suka rungumi sanaar da mahaifinsu ya dorasu akai wato noma da kiwo a lokacin Mallam ibrahim Yana cikin masu kudin garin Dan Yana da shanaye da yawa gonakinsa ma bazasu kirgu ba

Hakane yasa yaransa maza dukansu suke da sana'ar da sukeyi har da masu Dan fita zuwa birni
Yaya matansa kuwa duk ya aurar dasu Dan suna shekara goma sha yake aurar dasu.


A haka rayuwa take tafiya girma na zuwar wa Mallam Ibrahim da matansa Watarana hindatu uwargidansa ta kamu da rashin lafiya kwana biyu da fara rashin lafiyrta ta amsa Kiran mahallacinta

Sosai Mallam Ibrahim yaji mutuwarta Inda aka ringa zuwar Mai gaisuwa ko ta ina dalibansa da duk sukayi karatu awajensa haka sukayi ta zuwa daga garuruwa daban daban suna Masa gaisuwa da suka ji labarin mutuwar a cikinsu Akwai wani Kabir da ya kasance dalibinsa Dan garin borno kasuwanci ne ya maidashi garin Calabar anan ya had'u da matarsa Sakeena ya Aureta yayansu Hud'u Sulaiman shine na fari sai Mai bi masa Hajara sai Hassan da Husaini duk a cikin yayansa.

Hajara ta fita daban a cikinsu taurin Kai ne da ita da ruk'o gashi ko Yaya kayi Mata Abu ko bisa kuskure ne sai ta nemi hanyar da zata Rama ko mahaifiyarta da mahaifinta Bata barsu a baya ba indai suka yi Mata sai ta San hanyar da ta bi ta rama batare da sun sani ba wani irin bakin haline da ita Kabir da matarsa Sakeena har mamakinta suke a irin haka watarana aka aiketa ta Kai Nikan Massara a hanyar ta tafiya wani yaro ya tsokaneta ta zubar da nikan tabi shi a guje Dan baa Mata ta kyalle Sai data tayiwa yaron lilis ta dawo ta d'auko buhun ta koma gida tace wa Sakeena massarar ya zub'e ta ajiye Mata buhun a gabanta ta nufi d'akinta kamar batayi komai ba Sakeena kasa magana tayi Tabita da kallo Sulaiman kuwa dake palon a zaune ya mik'e a zuciye ya bita a baya ya hau ball da ita sai daya Mata lilis ya fito daga d'akin Dan yana Jin Haushin taurin Kan hajara.

Yana fitowa daga d'akin itama ta fito a guje tayi waje Tana ranstuwa da sai ta rama.

Abu kamar Wasa har Sha biyun dare Hajara Bata dawo gidan ba anan hankalinsu ya tashi suka hau nemanta

Hajara kuwa Tana fita daga gida ta nausa cikin daji ta samu wani katon bishiya tayi zamanta a wajen Tana ta kuka alwashi kawai take akan sai ta Rama dukan da yayanta sulaiman yayi Mata har dare ya farayi Bata motsa daga wajen ba mugayen abubuwa kawai take ayyanawa a ranta tsabar rufewar da idonta yayi da San d'aukar fansa akan yayanta Bata San dare ya Yi ba wajen karfe Sha biyun dare ta fara Jin wani irin busa da tafiyar mutane sun kunna acibalbal sun Dodora Akansu sunyi layi suna ta tafiya sunyi daurin kirji da jajjayen yadi da tukunyar kasa a hannunsu dukansu Mata ne sunfi su Ashirin.


Hajara kuwa Ido ta zuba musu ko kadan Bata tsorata da ganinsu ba

Su kuwa mamakin ganin yarinya a gindin bishiya yasa shugabarsu tayi musu magana da idan sunje wajen bishiyar su tsaya haka kuwa akayi suna Isa wajen da Hajara take zaune suka zagayeta suna kallonta.

Zubinsu bai saka ta tsoro ta ba illa mik'ewa ma da tayi ta kakk'ab'e rigarta ta fara k'ok'arin matsar da d'aya daga cikinsu tayi wucewarta.

Shugabarsu kuwa dariya ta kyalkyale dashi ta jawo Hajara Tsakiyar su da karfinta ta wancakalar da ita Tana tambayarta wacece ita.

Tsaki Hajara tayi ta Kara mik'ewa ta zabgawa shugabarsu harara Tana "Ina ruwanki Dani"?

Mudubi shugabarsu ta ciro daga tukunyar kasar ta zuba masa Ido bayan yan sakanni ta dago ta kalli Hajara Tana "Kinaso ki dau fansa akan yayanki daya dakeki Sabida kin zubar da Massara"?

Da Sauri Hajara ta gyada kanta ta matsa kusa da ita Tana "Inaso na dau fansa inaso nima na zaneshi kamar yanda ya zaneni"

Dariya shugabarsu ta kwashe dashi tana "matso Nan kigani wanan shine"?


Jiki na rawa Hajara ta matsa kusa da ita ta lek'a mudubin Tana lek'awa taga yayanta a tsaye da mahaifinsu a k'ofar gida suna ta dube dube almar dai ita suke nema.

Da Sauri tace mata "eee shine yayan nawa"

"Ungo Nan Rama dukan da yayi Miki"

Hajara da Sauri ta karbi bulalan da shugabarsu ta mik'o Mata ta daddage da iya karfinta ta fara laftawa mudubin Sulaiman dake tsaye da Mallam Kabir kuwa ya hau zunduma ihu Yana burgima a kasa.

Sai da bulalan duk ya karye Hajara ta jefar da bulalan Tana Jin wani irin farinciki na ratsata rungume matar tayi tana "Nagode Ina sanki"

Wani irin dariya shugabarsu ta kwashe dashi tana "Nima Ina sanki shiyasa nake so ki zama daya daga cikinmu sabida ki ringa taka duk Wanda ya taka ki karbi ki shanye"

Hajara da Sauri ta karbi kwaryar da ta mik'a Mata da Bata San ko menene a ciki ba ta kafa Kai ta shanye tas ta mik'a Mata tana "Yanzu kina nufin duk Wanda ya tab'ani zan iya dukansa ta irin mudubin nan"?


"Sosai ma kuwa cire kayanki ki tsaya a tsakiyar mu "


Da Sauri Hajara ta hau cire Kayanta cikin murna

suka hau zagayeta suna Mata wani irin hayaki bayan sun saka Mata Jan yadi a jikinta

A takaice a ranar Hajara sai karfe biyu ta koma gida fuskar ta a had'e

Gidansu kuwa Sakeena da Mallam Kabir hankalinsu a balain tashe yake da suka ga Sulaiman na birgima jikinsa ya tatashi lokaci guda tuni Mallam Kabir ya hau totofa Masa adduoi Yana tunanin ko Aljannu ne suka shige shi.

A lokacin da Hajara ta dawo kasa Mata magana sukayi gabadaya suka ringa binta da Ido Sabida yanda suka ga ta canza kamar ba ita ba Sakeena kuwa tsigar jikinta har wani tashi ya ringayi idan suka had'a ido.


A takaice tundaga lokacin Hajara ta fara wasu irin Abubuwa daya dasawa Iyayenta tsoranta Sulaiman kuwa tunda ta zaneshi bai Kara samun cikakken lafiya ba .

Duk dare mahaifiyarta idan ta shiga d'akin Hajara haka zata ga tayi d'aura kirji da Jan yadi Wanda hakan ke haddasa Mata tsoron Hajara sai ta fito daga d'akin da Sauri.


Ahaka ta tari Mallam kabiru da zancen Hajara Akan kila ba ita kadai bace Hajara nada Aljannu.

Tuni Mallam Kabir ya gasgata zarginsa akanta Inda ya bazama Nemo Mata magani a wajen mallaman addini Idan ya kawo Mata a gabansa zata zubar dashi bai Isa yyi magana ba hakane yasa ya shiga matsanacin damuwa ya fara tunanin hanyar da zai bi Dan ya raba Hajara da Aljannun dake jikinta a cikin irin wanan yanayin yaji labarin rasuwar Matar Mallam Ibrahim da yake ta San zuwa wajensa akan Maganar Hajara.

Da Wanan damar daya samu yazo bayan anyi Sadakar Bakwai ya samu Mallam Ibrahim da zancen Hajara da Abubuwan da takeyi dake nuni tana da Aljannu Inda ya roki ya taimaka masa ya rabata dasu.

Mallam Ibrahim kuwa ce Masa yayi yaje ya taho da ita zai rabata dasu insha Allahu.


Hakan kuwa akayi bayan sati daya da komawarsa Calaba ya zo da Hajara wajen Mallam.

Mallam Ibrahim da karfinsa ya dagewa Hajara da addu'a da manyan ayoyi Al Qurani Wai Nan duk so yake ya raba Hajara da Aljannun jikinta Nan kuwa bai San Shugabarsu d'auketa takeyi idan an fara rukiyyar ahaka yayi mata rubutun kwana bakwai

Washegarin da suka cika sati yacewa Mallam Ibrahim zasu iya tafiya Yana kyautata zaton insha Allahu Hajara ta rabu da Aljannun.


Mallam Ibrahim kuwa gefe yaja Mallam Ibrahim cikin sunkuyar da Kai ya nemi alfarmar da ya auri Hajara Dan a ganinsa in Yana tare da ita sai tafi samun lafiya.


Mallam Ibrahim kuwa bai k'i tayin da Mallam Kabir yayi Masa ba a cikin Sati d'aya aka daura auren Hajara da Mallam Ibrahim washegarin da aka daura auren Mallam Kabir ya dauki hanyar Calaba cikin tsananin farinciki Yana tunanin auren mallam Ibrahim da Hajara shine zai saka Hajara ta samu lafiya.

Hajara ko kadan Bata damu ba a lokacin da mahaifinta ya Gaya Mata ya aura Mata Mallam Ibrahim da zai iya jika da ita Dan tasan akwai abinda ta taka.

Shi kuwa Mallam ibrahim ganin yarinya sabuwar jini yasa ya Dan fara rawar kafar zai angonce da yarinya lafiya Lau yayi mata kwana bakwai dinta cikin doki a ranar da zai bar d'akinta a ranar ya fara dasa zargi Akan hajaran tunda tazo gidan bai tab'a ganin ta kalli gabas ba gashi indai zasu kwanta sai ta daura Jan yadi.


Kuma idan dai zaiyi adduar Daren daya Saba tashi take ta bar d'akin ta koma waje har sai ya Gama


Hakane yasa washegari ya shirya zama a d'akin Dan ya gasgata zargin da yake Mata na ko da sauran Jinnu a jikinta.

A ranar bai fita Waje karatu ba wajen karfe Takwas na safe ya kalli Hajaran da ke ta sharar bacci Sabida bata baccin dare.

Ido ya zuba mata Yana ganin yanda ta rambada kwalli a goshinta da idonta.

Matsalar Karfe Hud'u yake fita massallaci da asuba sai karfe shidda na safe yake dawowa gida hakane yasa baya sani ko tayi sallar Asuba ko batayi ba Azahar da sauran salllolin kuwa Yana k'ofar gida da dalibai da suke d'aukar karatu hakane yasa baya sanin tana sallah ko batayi.

Hannu ya Kai ya fara bubbuga pillon data Dora kanta akai.

Hajara ta bud'e idonta da suka kad'a sukayi ja Dan meeting suke a cikin baccin da take Mallam Ibrahim ya tasheta.

Mallam Ibrahim da Sauri ya k'au da kansa a lokacin da suka had'a ido da ita.

Hajara kuwa tace Masa "Mallam lafiya baka fita karatu ba yau"?

"Kinyi Sallah Asuba kuwa?

Cikin mamaki Hajara ta Masa wani irin kallo tana "Nayi Mana Mai yasa kake tambayata"?


Mallam Ibrahim baice komai ba ya tashi daga Kan gadon a zuciyarsa Yana zargin har yanzu Hajara Tana da Jinnu a jikinta Alwala ya dauro ya dawo d'akin ya shimfida Sallaya ya d'auko Al Qurani ya bud'e Yana gyaran murya Hajara ta duro daga Kan gado da Sauri tana "Mallam yau Kuma karatun a daki zakayi"?


Wani irin kallo ya Mata ita kuwa tayi waje da Sauri.

Mallam kuwa ya girgiza Kai Yana gasgata zarginsa ya fara karanta Suratul Baqarah.

Hajara k'in dawowa tayi d'akin ta fita zaure tayi Zamanta

Sallamar da ake tayi da Mallam Ibrahim ne yasa akan Dole ya fita bayan ya shiga d'akin Fatsima da suka koma zaman d'aki tunda aka d'aura auren Hajara da Mallam Ibrahim Dan sosai suke ganin wani Abu a tattare da ita indai suka had'a ido sai gabansu ya fad'i sosai sukejin tsoranta hakane yasa duk suke zama a daki abinda ke fito dasu kawai girki ne da alwala Mallam Ibrahim kuwa bai tab'a lura ba Dan shi ba zama yake ba.

Fatsima tsugunnawa tayi ta gaishe shi daya shigo shi kuwa yace Mata "aiki nake so kimin naso nayi aikin da kaina Amma Ana ta zuwa nemana Ido nakeso ki sawa yarinya Nan Hajara akwai zargin da nake akanta inaso kiga idan Tana sallah kinsan Ni ba zama nake ba ballantana nasan ko tanayi ko batayi har yanzu akwai wayanda ilimin addini bai je musu ba a zub'e kawai suke suna rayuwa"

Fatsima kamar zatayi magana Kuma ta fasa Dan a cikinsu ba Wanda ya tab'a sa Abu tak'i yi

Ko kallon Hajaran dake zaune a zauren baiyi ba ya fice Dan a yau zai rabata da bakaken Jinnun dake jikinta.

Hajara kuwa Yana fita ta nufi d'akin Fatsima kanta tsaye ta bankad'a labulen d'akin Fatsima dake kwance akan Gado ta tashi zaune gabanta na balain fad'uwa da ganin Hajara a d'akinta Dan Bata tab'a shigo Mata ba.
A haife dai ta haifi Hajara Dan zata iya cewa ma zata iya jika da ita.


Wani irin kallo Hajara ta Mata tana "Wato kece munafikar gidanan kece Zaki sakamin Ido kenan toh sai Naga da bakin da Zaki Gaya masa nayi Sallah ko banyi ba.

Daga nan Hajara ta juya ta bar d'akin.

Fatsima kuwa ta hau sallati Tana adduar duk daya da yazo bakinta.

Mallam Ibrahim bai shigo gidan ba sai karfe Tara na dare.

Yana shiga gidan d'akin Fatsima ya shiga da Sallama.
8/19/21, 10:30 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 3*


Fatsima da kanta ke balain ciwo tunda Hajara ta shigo Mata daki ta tashi zaune dak'yar.

Bata tab'a Jin tsoron mutum kamar yanda take Jin na Hajara ba ta tsorata da maganganun da Hajara tazo tayi mata dazun hakane yasa ko kad'an Bata samu nutsuwar saka Mata Ido ba

"Ina aikin Dana saka ki"

Fatsima murza hannu ta fara yi ta rasa ta Inda zata fara Masa bayani kamar ance ta dago ta kalli bakin kofa aikuwa ido biyu tayi da Hajara ta zubo Mata Ido"

Inda Fatsima kuwa ta daka tsalle ta tsaya tana Shirin magana bakinta ya karkace.

Sallati Mallam Ibrahim yayi ya ajiye jarkokin rubutun da ya shigo dasu yayi Kan Fatsima dake ta zabure zabure.

Sosai hankalin Mallam Ibrahim ya tashi a ranar yayi ta totofawa Fatsima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login