Showing 75001 words to 78000 words out of 180103 words
balain tsana Kamar ta jefata a wuta.
Idan taso yiwa Tijjani hargagi akan zata tsine Masa idan Bai bi umarninta ya saki Murja da ba Yar arzki bace murmushi takaici yake Yana "Tsinuwa Kuma na nawa Umma Kinga fa halin da Kika jefamu akwai masifar da yafi wanan Umma ba abinda matata ta Miki bazan saketa ba.
Daga Haka zai kad'a kansa ya fice
Safiyya kuwa data ga alamar yunwa zai kasheta kudin mota ta nema ta tafi Calabar.
Inda ta nemi Lami da itama taje wajen dangin babanta suka daura Mata aure da wani gurgu tuni ta dawo daga rakiyr Hajara ta tuba.
Kwana uku kawia tayi a gidan lami Suka fara samun Sab'ani Dan Safiyya Bata rik'e girmanta na Yaya ba tuni ta Kara ficewa daga gidan.
Ta koma gidan kanin mahaifinta Dan mahaifinta tuni ya bar garin tunda ya dawo hayyacinsa shi kuwa kanin mahaifinsu ya Riga yaci Dubu sai ceto ba abinda Hajara zata iya Masa hakane yasa bai k'i karbar su ba Dan shima tamkar mahaifinsu ne.
Sai dai itama zuwa gidan datayi sai da sukayita fada da matar kanin babansu a karshe shima yaga bazai iya ba ya Bata kudi akan ta koma Inda ta fito ko ta zuciya ta Nemo mijin aure.
Ahaka ta Kara dawowa gidan Tijjani tare da cin alwashin neman mijin aure.
Sai dai dawowarta yasa Murja ta daura damarar cin ubansu Dan ta balain tsanar Safiyya sabida Bata da mutunci itama.
Kwana biyu da dawowar Safiyya da safe Tijjani ya fita da wuri.
Daren jiya Hajara kwana tayi da yunwa Dan Dan kanzon da Murja ta basu Nan da Nan Safiyya ta cinye hakane yasa yau ta fito da wuri ganin murja bata palon yasa ta nufi kitchen da Sauri jikinta na rawar yunwa.
Ido biyu tayi da katon bredi ta Kai hannu ta d'auka cikin murna ta rufo kitchen tana juyawa suka yi Ido biyu da Murja dake mata wani irin kallo .
Hajara gabanta sai daya Fadi Amma ta maze ta matse bredin a hammatar ta tana hararar Murjan tana "Na dauka nida gidan Dana k'arfi da yaji ki ringa Mana Horan yunwa Dan uwarki wlh kyalleki nakeyi bakisan wacce ce Ni bane Ni nasan baki bar Dana Haka ba asirce shi kikayi Amma wlh zanyi maganinki Bari na samu kudi nayi tafiya na dawo"
Wani irin Dariya Murja ta kece dashi tana "Naji barauniyar bredi kafin kiyi magani na ki bani bredina"
Ta Kai hannu ta fusgo bredin Hajara ta kwace cikin zafin nama kafin kace me sun kaure da kokawa.
Murja Bata duba Wai uwar mijinta bace ta haye ruwan cikinta ta hau Kai Mata naushi ihun Hajara ne ya tashi Safiyya ta fito a guje ta hau kaiwa Murja duka.
Murja kuwa ta tashi daga Kan Hajaran ta jawo safiya ta matse a hammatar ta ta hau dirkarta.........
8/19/21, 10:31 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Wanan Shafin naki ne Ateekah Nagode da soyayyarki a gareni Allah ya bar zumunci*🌹🌹🌹
*Page 29*
Ba karamin duka Safiyya taci a hannun Murja ba ta watsar da ita a tsakar gidan ta shige daki da bredin ta.
Daga Hajara har Safiyya babu Mai rarrash wani duk kamaninsu ya canja.
Allah ya Isa kawai Hajara Da Safiyya Suka ringa jawa Murja Hajara kuwa tayi ta rantsuwa da idan Tijjani ya dawo wlh sai ya saketa ko ta Masa baki.
Haka suka shige daki ga duka ga yunwa dake nukurkusar Hajara Bata tab'a tunanin akwai ranar da Yar cikinta zata iya daga Ido ta kalleta har Wai ta iya kawo hannu jikinta ta haye ruwan cikinta ta Mata duka a gidan danta sabida ta dauki bredi.
Ita da idan aka hada Ido da ita sai gaban mutum ya Fadi
Take ta hau tuna yanda idan Suka had'a Ido da Naeema jikinta ke kwasar Bari sabida tsoro.
Muryarta ma idan Naeema taji tana ganin yanda tsoro ke bayyana a Fuskarta Amma Wai yau itace Murja da take kyautata zaton Lami ta girmeta itace ta Mata Haka Kai Ina da sake zama a Haka Bai Kamata ba Dole ta koma kauyensu ta nemi shugabarsu tayi ta Bata hakuri ta dawo Mata da Karfin tsafinta a ranar da ta Bata a ranar zata kashe Murja
Naeema Kuma da take daurawa alhakin duk halin da suka tsinci kansu a ciki ta sakata a uku ta Sha bak'ar wuya Kafin ta rabasu da Naseer Dan har gobe tana Nan Akan bak'anta na yak'ine tsakaninta da Naeema ko taci ko Naeema taci.
Muryar Safiyya ne ya dawo da ita hankalinta
"Wlh ya zama Dole mu bar gidanan Umma Dan wlh Tallahi na gaji da zama da tsinaniyar matar Nan da Bata da mutunci gwara mu koma gidan yaya Naseer koda kuwa a daki daya yake.
Akan abinci tsinaniyar Nan ta Mana irin wanan dukan Ni nasan ba ita ta iya Mana wannan dukan ba wlh Aljannu ne da ita.
Dan Haka Umma a yau ba sai gobe ba mu tattara kayanmu mu koma gidan Yaya Naseer kema kinsan Naeema ma ko numfashin kirki Bata iya yi idan muna waje daya ballantana ta kawo Mana iskanci shi kuwa Yaya Naseer sai yanda kikayi dashi Kuma wlh ko Dan wanan matar Umma ya Kamata muje mu roki Shugaba muna bukatar mudubin mu ko Dan gudun Kara faruwar Haka yau da ace da Karfin mu a tare damu ai sai dai wata a yau ba ita ba"
Wani irin girgiza Kai Hajara tayi zuciyarta fal cike da mugunta da San d'aukar fansar abinda Murja ta musu
"Sabida abinda yarinya Nan tamin Zan nemi kudin mota naje wajen shugaba ko da Bata maidamin karfina ba inaso a hukunta min ita inaso a makantar min da ita na dawo na zaneta na saka Tijjani ya saketa bayan nayi aiki a kansa Dan Ni nasan bata barshi Haka ba asiri tayi Masa.
Idan zaman Nan din bai yiwu ba sanan muyi tunanin zuwa gidan Naseer.
"Toh Ina zamu samu kudin motar tafiya"?
"Idan Tijjani yazo sai ya Nemo min kudin motar duk Inda ya shiga kuwa wlh idan yak'i bani sai na tsine Masa Dan bashida amfani a wajena tunda har ya iya fifita matarsa akaina ya ringa toshe kunnensa idan na masa maganar matarsa tashi ki lek'a min kiga ko ya dawo Dan bazan Kara kwana a gidan Nan ba"
Safiyya fitowa tayi daga d'akin da kumburarren baki
A Palo ta tarar da Murja tayi hadin kauri ga kwai ta shimfida tana ci tana gyad'a kai sai murmushi take.
Safiyya da kumburarren idonta ta hau hararar Murja.
Murja kuwa ta saki murmushi tana "Wanda ya ja Dani wlh zai Sha wuya dama idan kun samu kudin motar kun taimaka wa kanku Kun siyi abinci Dan duk Inda zakuje ma wahalar da kanku zakuyi ba Abunda zaku iyamin"
Tsaki Safiyya tayi Dan ta d'auka lab'ewa tayi taji abinda suke cewa
A k'ofar gida ta tarar da Tijjani ashe ya dawo Yana zaune Akan benci kusa da kantarsa.
Safiyya tana Isa wajensa ta fashe da kuka Tijjani ya d'ago ya kalleta ganin jikinta duk a kumbure yasa ya mik'e Yana "Ke lafiya Mai ya Sameki Haka"?
Cikin kuka Safiyya ta bashi labarin abinda Murja ta musu.
Ta Kara da cewa "Yanzu Yaya tsakani da Allah Haka zamu cigaba da rayuwa a gidanka matarka na Mana horar yunwa tana dukanmu da anyi magana sai kace Umma ce ta jawo komai Kai baka San tashin hankali har matarka ta saka hannu ta daki Umma toh kaje tana kiranka Dan ta rantse bazata kwana a gidanan ba tafiya zatayi"
"Murjan ce ta daki Umma Akan abinci"?
Tijjani yace cikin mamaki
Bai tsaya ma jiran Mai Safiyya zata ce ba ya shiga gidan
Sai dai me suna Shiga palon Suka ga Murja a kwance a kasa tana ta numfarfashi kayan jikinta duk a yayyage jikinta ya wani kumbure Yana ta kyalli Kamar wacce akayiwa shegen duka
Shigowar Tijjani yasa ta fashe da kuka ta hau mik'a Masa hannu tana "Zo ka taimakeni zasu kasheni"?
Dak'yar.tayi.maganar tana numfarfashi.
Tijjani kuwa ya saki sallati ya karasa wajenta a guje ya d'ago ta cikin tashin hankali Yana duba yanda jikinta ya kumbure.
Safiyya kuwa mamakine ya kasheta a tsaye ta saki baki tana kallon Safiyya
Hajara ma fitowa tayi daga d'akin dataji muryar Murja kamar wacce aka daka.kafin ma ta fito ta hau addua Allah yasa ruwan zafi ne ya kwarowa Murjan.
Amma abinda ta gani ne ya sa ta kasa motsi daga ita har Safiyya kallon Murjan kawai suke suna Jin Mai ke fitowa a bakinta
"Na shiga uku Tijjani mahaifiyarka da kanwarka zasu kasheni kaga yanda suka dakeni suka had'u akaina sukayita jibgata akan sunce na kara musu abin karyawar bazai isa ba
Shine nace musu bredin guda daya ka kawo babu wani shine Ina ajiye musu kayan shayin suka yi ball da shayi da bredin suka tashi Suka rufeni da duka"
Ta karashe tana matsar kwalla"
Tsabar mamakin makircin Murja Safiyya zub'ewa tayi a kasa.
Tana "Yaushe muka dakeki? A yaushe Kika bamu shayi da bredin" kiji tsoron Allah ke Kika dakemu ko mu muka dakeki"?
Tijjani kuwa tuni idonsa ya kad'a yayi ja halin dayaga Murjan ya balain b'ata Masa rai.
Mik'ewa yayi a fusace Yana "A gaskiya na gaji wlh Nagaji Umma Akan me zaa ringa dukan matata akan abinci kuka had'u kuka Mata irin wanan dukan Umma wlh bazan d'auka ba Dan Ni ba Naseer bane ku barni Mana inji da masifar da nake ciki akan me zaa zo a Kara min wani a ringa dagawa iyalina hankali ahaka kuka sako matar Naseer agaba yanzu Kun bar kanta Kun dawo Kan matata toh a gaskiya bazan yarda ba na gaji Umma ki koma gidan Naseer kawai kasheta kuke so kuyi akan abinci?kunsan da yanda nake Samun ma abinci"?
"Ke Kuma Dan uwarki har wuyanki yayi kaurin da Zaki kawo hannu jikin matata Sa'oinki suna can daga Mai yaya bakwai sai takwas ke kinzo Nan Zaki daga min hankali maza ki shiga daki ki kwaso kayanki Kar na sake ganin kafarki a gidan Nan"
Kuka Safiyya ta fashe dashi tana "Wlh Tallahi yaya karya take Mana Ita ta dakemu fa daga Umma ta Shiga kitchen dinta ta d'auko bredi zata ci shine ta hau Umma da duka na fito Zan ceceta ta had'a Dani haba Yaya Kar San matarka ya rufe maka Ido ka kasa Gane sharri take Mana ka kalli fuskata ka kalli fuskar Umma mu zamu daketa mu Kuma daki kanmu"
"Wayyo Allah kaina wayyo Allah bayana"
Kawai Murja ke cewa tana matsa kwalla Tijjani kuwa hakan ba karamin Kara Masa Haushin Hajara da Safiyya take ba.
Bakin cikin sharrin da ta musu yasa Safiyya ta fara kuka
Hajara da wani irin Abu ya tokare Mata wuya Tama kasa magana sabida sharri da.makircin da Murja ta had'a musu Tijjani ko bincike Bai tsaya Yi ba ya hau Kai ya zauna Yana fadar duk maganar data fito daga bakinsa.
"bani kudin mota na bar maka gidanka a yau Tijjani yau Akan mace ka rufe Ido kake gayamin bakaken maganganu matarka ta daki nida kanwarka ta Kara hada Mana sharri ka goyi bayanta ka k'i bincike kaji daga bakinmu.
Tun aurenku da ita ban saka albarka ba nace maka Bata min ba sabida ba matuniyar arziki bace kak'i ji a karshe ta ringa Mana horon yunwa sabida na Shiga kitchen na dau bredi ta rufeni da duka kazo ta Mana sharri ka yarda da maganarta.
Tijjani a yau Ina umartarka da ka saketa saki uku ko na maka baki"
Tijjani kallon Hajara kawai yake cikin mamaki Yana "Da tamin me Zan saketa Umma kawai Dan matata ba ta kwanta Miki ba sai ki dage na saketa yanzu idan na saketa ke Zaki Nemo min wacce Zan aura wai.mai yasa bakida burin daya wuce ku watsa rayuwarmu ne ki hanamu sukuni da zaman lafiya Umma karki manta fa akwai hakkinmu akanki Haka zalika hakkinki akanmu Umma bakida burin daya wuce ki cutar damu muna yayanki Haka kika Sako Naseer a gaba sai da Kika Hana shi sukuni Umma yanzu Nima din baki kyalleni ba sai kin rabani da matata toh a gaskiya bazan iya rabuwa da ita ba Dan babu abinda tamin matsayinki daban matsayinta daban"
"Au Haka kace ko toh shikenan gata Nan na sallama Mata Kai Tijjani daga Yau Murja ta zame.maka uwa karka Kara doso.inda nake tunda ka k'i bin umarnina sai ka tagayyara ka wulakanta Sai wanan tsinaniyar matar ta zama ajalinka"
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha Umma yanzu akan naki rabuwa da matata kikemin baki Haka"?
Hajara Bata kulashi ba ta koma daki ta d'auko buhun Kayanta Ta fito tayi waje.
Safiyya itama ta mik'e ta shiga d'akin ta d'auko Kayanta tabi bayanta.
Tijjani kuwa tsananin mamakin kalmomin Umma ya hanata motsawa.
Murja kuwa cikin makirci tabi bayansu tana "Umma Dan Allah kiyi hakuri ki dawo ya sakeni.
Tana Isa Dab dasu ta Sha gabansu ta saki murmushi tana "Kar na sake na Kara ganin kafarku a gidana duk Wanda ya ja Dani wuya zai Sha Dan Baku San wacece ni ba Kuma danki auren zobe mukayi mutuwa ce zata rabamu karki wahalar da kanku wajen yimin wani Abu Dan Babu abinda zai sameni.
Daga Haka ta matsa daga gabansu ta sakar musu murmushi fitowar Tijjani yasa ta zub'e a kasa da Sauri ta rik'e kafar Hajaran tana "Umma Dan Allah kiyi hakuri ki koma Zan saka ya sakeni."
Tsabar bakin ciki Hajara kasa magana tayi har Tijjani ya karaso wajensu.
Ya mik'awa Safiyya kudi
Safiyya ta d'auke kanta ya daka Mata tsawa kamar zai Kai Mata duka tayi saurin juyowa ta karbi kudin
Shi kuwa Tijjani yace "Allah ya kiyaye hanya Umma idan kin huce zamuzo"
Daga Haka ya juya ya koma ciki.
Murja kuwa ta musu gwallo ta bi bayansa.
Daga Hajara har Safiyya ba Wanda ya iya magana har Suka Isa Tasha suka hau mota.
Sai da motarsu ta d'au hanya Hajara ta rufe fuskarta ta fara kukan bakin cikin abinda Murja ta musu yanda take Jin zuciyarta da zata samu wuka daga Murja har Tijjani zata iya kashe su.
Sai a yanzu ta Gane Naseer Dan halak ne Yana kuma Mata biyayya Naeema ce dai data tsana yak'asa bin Umarninta Karo na farko da tayi Nadamar abinda tayiwa Naseer.
Naeema ta tsana ba Naseer ba da ta sani tun farko Naeema tasan yanda akayi ta kau da ita duk da Naeema duk abinda take tayi dan ta cimma burinta ta kasa samun Galaba a kanta Bata San Mai yasa yaran nata maza suke k'in Mata biyayya Akan matansu ba.
Tuna Naseer da Naeema ya Kara taso Mata da tsanar Naeema da take ganin ita ce silar dayasa idonta ya rufe tayiwa Naseer abinda tayi Masa.
A yanzu Kuma ba wacce take San ganin ta aikata barzahu sama da Murja da take Jin kowacce fitar numfashinta da tsanarta take fita.
Bata da burin daya wuce ta Isa Calabar.
Tsabar b'acin Rai ma neman yunwar tayi ta Rasa.
A lokacin da suka Isa Calabar sanin babu Inda zasu sauka yasa Suka nufi gidan Lami.
Lami Bata ma iya musu magana ba sabida yanda suka had'e rai.
Bata San da zuwansu ba Amma abincin data girka Haka ta juye ta kawo musu
Daga Safiyya har Hajaran Loma kawai suke kaiwa bakinsu har suna neman fada akan abincin.
Sai da suka nutsu Lami ta hau tambayarsu abinda ya faru tagansu Haka.
Cikin bakincki Hajara ta hau Bata labari tana cin alwashin irin Abubuwan da zatayi wa Murja Naeema da Tijjani.
Safiyya kuwa cewa take Banda dai Tijjani tunda nasu ne Kuma ita tasan bayin kansa bane.
Lami girgiza kanta tayi tana "Umma a gaskiya shawarar da Zan baki shine ki hakura ki koma ga Allah Ni yanzu nasan asiri da tsafi duk karyace Umma a sanadin tsafi Umma bayana ya koma haka Umma shekara nawa muna had'awa Naeema abubuwa tana tsallakewa kin taba tunanin da wa Naeema ta dogara take neman fin karfinmu nidai Umma Dan Allah ki hakura ki dawo hanya"
"Kimin shiru Lami zan sauke fushina akanki idan bazaki tayani ba karki soma hanani"
Ta Inda Hajara take Shiga Bata nan take fita ba.
Lami kuwa d'akin ta baro musu tana musu adduar Shiriya
Karfe Sha biyu Hajara da Safiyya suka nausa daji.
Duk yaren tsafin da suka ringayi Shugaba bata bayyana gabansu ba .
Sai da suka Sha bak'ar tafiya ko tsoro basaji suka iso wani wawaken waje Mai dauke da wani gini a tsakiya shi kadai wanda na shugabarsun ce.
Suna Isa wajen suka ganta a zaune ta daura Jan zani Ido ta zuba musu har suka zube a gabanta.
Hajara kuwa cikin kuka ta hau rokonta ta yafe Mata ta maido Mata mudubinta ta tuba bazata Kara ba tana San daukar fansar abinda Murja ta Mata.
Sai data Gama tsaf
Shugabarsu ta jawo wani katon mudubi Mai dauke da wani irin zanne ja
Tayi surutai ta ajiye a gaban Hajaran da Safiyya.
Sai ga wata Mata ta Bayyana sanye da bakakken Kaya Fuskarta gwanin ban tsoro.
"Wannan itace mahaifiyar Murja ko ni ban Isa Naja da ita ba Dan Haka ki bar zancenta Dan idan ta gano daga ke har Ni sai ta kashemu idan kina da wani Abun ki fada kawai Banda wanan"
"Yanzu Bazan iya d'aukar fansar abinda Murja tamin ba kenan mahaifiyarta sabida babba ce itama a kungiya Mai zaman kanta"?
"Abinda nake nufi kenan"
Hajara tsabar bakin ciki kuka ta fashe dashi sai data gaji dan kanta tace
"Dan Allah ku maidamin karfina Shugaba Ina bukatarsa"
"Bazai yiwu ba Abu daya Zan Miki karbi Nan.
Duk Inda kike idan Kika turara Zan bayyana ki fadamin abinda kikeso"
Sai a lokacin Hajara ta Dan ji sanyi a ranta
"Dan Allah inaso a dubamin Inda Naseer yake yanzu shida matarsa Naeema"
Wani Abu ta watsa Akan mudubin sai ga Naseer ya bayyana a cikin mudubin Yana zaune a benci a k'ofar wani katon gida ya zurawa waje daya Ido ya rame sosai Kamar bashi ba rigar jikinsa har ta Masa yawa"
"Ga danki nan ya zama driver a garin Abuja Yana neman kudin da zai dawo wajen iyalinsa.
Matarsa ita Kuma tana Nan a gidansa na gadon Kaya tana d'auke da ciki har ya tsufa"
Shugabarsu ta hau kwararawa Hajara bayanin komai
"Wanan yarinya anyi shegiya tana so ta kashemin d'a da Ransa in Banda balai suna cikin wanan matsin zata Kara k'unsar wani