Showing 129001 words to 132000 words out of 180103 words

Chapter 44 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2471

YA HAKURA NGD*
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 49*

Hajara kuwa data fara Dan gyangyadi ihun Safiyya ne yasa ta mik'e a firgice a daidai lokacin da Safiyya ta Isa wajen Bashir din ta kwace ledar hannunsa ganin babu alewar a ciki ta saki ihu Tana "Nashiga uku na lalace Bashir ya Sha alewar"

Ta Danna hannunta a bakin Bashir din Dan ta ciro alewar da Sauri sai dai tana Danna hannunta sauran alewar ya wuce Bashir ya hadiye alewar hankali a tashi ta hau zurmaka hannunta gabadaya a bakinsa tana dukan bayansa Wai duk Dan yayi amai amma a banza Dan kakarin amai yayi kawai baiyi Aman ba hannu Safiyya ta Dora a ka tana "Umma kin cuceni Bashir ya Shanye alewar Sata Umma kina zaune anan fa Bashir ya d'auki. Alewar ya sha Baki Hana shi ba"


"Ta Ina na ganshi nida bacci ya fara daukana ki kwantar da hankalinki ba abinda zai faru gobe da sassafe sai muje wajensa mu Gaya masa

A ranar Safiyya ko kad'an batayi bacci ba hankalinta a balain tashe tana tsoron ta budi Ido taga dan data ci buri akansa ya Zama likita ko Dan siyasa ya zama barawo idan ta tuna yanda bokan yace Zahira zata ringa sata sai cikinta ya murd'a ta tafi bandaki

Sosai taji Haushin Hajara tana ganin har da sakincinta yasa Bashir ya sha alewar Dan tana d'akin Bashir ya d'auki alewar.

Gari Bai Gama wayewa ba ta Sabi Bashir a baya Hajara sanin halin Safiyya da azabar masifa yasa ta bita Dan ita Kuma Haka kawai take shak'ar Safiyya tana Kuma tsoronta.


Sai da suka Dade kafin su samu ganin bokan
Suna Shiga Safiyya ta kunto Bashir daga bayanta tana "ka taimaka min an samu matsala d'anna ne.ya Shanye alewar a taimakamin a rufamin asiri"

"Garin ya ya Shanye alewar"?

Cikin kuka Safiyya ta bashi labari shi kuwa bokan ya girgiza Kai Yana "Ba abinda zan iya Yi akai Dan ke kikace muyi aikin da duk abinda maman yarinya zatayi bazata iya karya shi ba hakane yasa Dana hada maganin na baki Akan ki zuba a cikin ruwa indai ya baje toh Mai karya asirin sai ya iya hado maganin daga cikin ruwan zai karye"

Ihu Safiyya ta ringa zunduma wa.tana ya rufa Mata asiri zata bashi ko nawane

Hajara itama ta hau rokonsa shi kuwa yace musu ba abinda zai iya Yi akai Amma suje zai nema idan ya samu zai Basu.


A Haka suka dawo Safiyya na zunduma.kuka Bata tab'a kawowa Bashir ne zai Sha alewar ba Hajara kuwa sai rarrashinta take Safiyya na daka Mata tsawan Akan laifinta ne sakacinta ne yasa Bashir ya Sha alewar sai rashin kunya takewa Hajara tana neman zaginta Amma Hajara Bata ce Mata komai ba

Ko baccin kirki Bata iya yi Sabida tashin hankali kasan zuciyarta kuwa wani balain tsanar Naeema da zahiran ne ya Kara rufeta tana Jin duk a sanadinsu danta ya Sha alewar Sata ya Zama Dole ta d'au fansa sai ta wahalar da Naeema ta wahalar da Zahira da Bata ji ba Bata gani ba matsawar danta ya tashi da sata abinda zata yiwa Zahira Allah kadai ne ya sani

Hankali dai ba akwance ba kullum cikin Zullumi ta cigaba da fita aikatau da zumar samun wasu kudin ta Kara komawa wajen bokan Dan yanzu zuciyarta Kara taurara yayi wajen San ganin bayan Naeema data Mata Karen tsaye a idonta ma gani take Kamar Hajaran ta fara sanyi da batun Naeeman

Sosai tayi mamaki da ganin Saude Bata Zo musu ba kwana biyu ganin an tafi Wajen wata Bata ganta ba yasa ta shirya bayan ta dawo daga aikatau ta nufi unguwarsu Naeema

Wajen karfe Biyar na yamma ta nufi unguwar tana zuwa tun kafin ta Isa gidan Saude ta hango wani dalellen mota a k'ofar Gidan Naeema.

Mai gidan da take wa aikatau Yana jingine a bakin mota Yana kad'a mukullin motarsa

Wajen shagon Naeema kuwa cike da.mutane masu siyayya

Wani irin bakin ciki ne ya cika kirjinta

Ta jingina da bango tana tunanin Mai Alhajin Saad yake Yi a k'ofar Gidan Naeema ko shima siyayyan yazo shagon Naeema.

Tana tsaye taga yaron daya aika cikin gidan ya fito wajen sa ko Mai ya Gaya masa oho ya Kara aika shi gidan.

Sai gashi yaron ya dawo wajensa da Minal biye dashi

Ji tayi inama.tana Jin Mai suke cewa

Tana kallo Alhaji Saad din ya bud'e bayan motarsa ya fito da manyan ledoji ya mik'awa Minal ta ja da Baya tare da girgiza Masa Kai

Ganin Taki karba yasa ya mik'awa almajirin ya bashi kyautar kudi tare da Shiga motarsa ya tafi

Tsabar bakin ciki har wani dafe kirji Safiyya tayi tana tsaye Naeema ta fito.tana sanye da hijabi ta taso.almajirin da ledar daya Shiga gidan sai Masifa take Sam Safiyya ba jiyo abinda take fada take ba har ta gama ta Kira Isihu dake shagonta ta bashi ledar ta koma ciki.


Safiyya zuciyrta cike da tunani ta Shiga gidan Saude

Inda ta tarar da ba kowa a gidan.

Ta fito daga gidan kenan taci Karo da Saude data shigo gidan itama a firgice hannunta rik'e Dana Maimuna data ci kuka ta gode Allah rigarta duk a yayyage

Saude tana ganin Safiyya ta fashe da kuka tare da rike hannunta suka koma ciki Suka zauna akan tabarma.

Safiyya kuwa ta bi maimuna da.kallo da.kayanta ya yayyage tana "Wai Saude lafiya kuwa yana ganku Haka Mai ya samu maimuna Haka"?

"Safiyya Ashe alewar Nan da muka bawa Maimuna ta bawa Zahira sai data gutsara ta Sha a ciki bamu sani ba tunda ta Sha take jawomin magana
sata
ko ta Ina rabona da cikakken bacci wlh na manta Safiyya shiyasa ma bakya gani na koni Maimuna Bata kyalle ba duk abinda ta gani a gidnan dauka take idan kuwa ta fita waje sai dai azo a kirani ace gata can an Kamata tayi sata.
Yanzu ma Haka wani babban shago taje ta yi sata kafin azo a gayamin shine aka Tara Mata jamaa aka fara dukanta aka yayyaga Mata Kaya har wajen Yan sanda suka Yi niyyar kaita sai danayi ta hadasu da Allah da annabi Safiyya Ina zaman zamana na Kai kaina Halaka na cuci kaina garin tsinannen.kwadayi irin na yarinya Nan taje ta gutsuri alewar Nan ta sha.

Ihun da Safiyya ta saki tana Dora hannunta aka yasa Saude ta tsayar da maganar da take Safiyya ta hau birgima a kasa tana "Na Shiga uku Saude Bashir Nima ya Shanye duk alewar idan har maimuna gutsura kawai tayi take wanan Satan Ina ga Bashir daya shanye duka Na Shiga uku Saude na Shiga uku yanzu Haka Bashir zai ringa sata naje gurin bokan akan ya karya Mana asirin yace bazai iya ba sai dai ya duba"


Kuka take sosai Ita kuwa Saude ajiyar zuciya ta sauke tana Jin Sanyi a zuciyarta da ba iya maimuna ce zata yi Satan ba har da Bashir Amma a fili kuwa kuka ta hau Yi tana sun Shiga uku yanzu ya zasuyi ahaka suka Gama jajjantawa juna suna tunanin neman kudi su nemi wani ya karya asirin

Safiyya kuwa ta hau yiwa Saude tambayoyi akan Naeema


Saudee kuwa ta hau Bata labarin yanda manyan masu kudi suke Neman Zahira masu nemanta har da Yan siyasa ta had'a da Gaya Mata taga Alhaji Saad ma Yana zuwa gidan shima Wai San Zahira yake

Wani irin abune ya tokare zuciyar Safiyya Dan so tayi Zahira ta ringa sata tayi bakin jini a wajen Samari Amma tunda abin ya koma kansu ya zama Dole su sake wani shirin Akan Zahira Dan sai ta samu cikar burinta zata samu kwanciyar hankali ahaka suka Kara kudurta mugayen Abubuwa akan Zahira Saude ta raka Safiyya ta tafi


Naeema

Maneman Zahira tuni suka isheni da sintirin da suke min a k'ofar gida Zahira yanzu tana da shekara Sha shidda tana Kuma jss 3 Sam ban shirya ta kula wani saurayi ba Dan inada burin tayi karatu Mai zurfi ba ita kadai ba har sauran yarana Ina burin suyi karatu Mai zurfi tunda Ni bansamu wanan damar ba

Amma ga mamakina ko secondary Zahira Bata Gama ba masu nemanta da Aure sun Sako mu a gaba suna Santa da aure akwai wani Alhaji Saad danaga yafi matsawa da zuwa har aikowa yake akan Yana Sallama da Naseer a ranar Dana fita.

Dan na bashi hakuri Akan ba yanzu Zahira zatayi Aure ba Yana ganina ya tsugunna ya hau gaisheni Ni kuwa na bashi hakuri akan ba yanzu zaayi yiwa Zahira Aure ba yayi hakuri.

Daga Haka na koma ciki sai dai ga mamakina Bai fasa cigaba da zuwa ba

A ranar daya zo na karshe ya Bata min Rai Dan Yana aikowa nace ace Bata zance ya Kara aikowa na tura Minal Akan ta bashi hakuri sai dai suna dawowa Naga Almajirin daya fara aikowa da Niki Nikin Kaya Wai a bawa Zahira

Ban Bari ma ya karasa shigowa ba na wafci hijabina na fita dan na Masa kashedi sai dai Ina fitowa Naga har ya tafi.

Hakane Yasa na bawa Isihu Ledojin akan ya Ajiye duk ranar da Alhajin Nan ya dawo a bashi kayansa.

Na koma ciki Ina Shan alwashin idan Naseer ya dawo ya zama Dole muyi shawara dashi Dan abinan ya isheni.

Bayan tafiyar Naseer da wata biyu sai gashi ya sake dawowa da Niki Nikin Kaya na Kuma ji dadin yanda Naga ya fara samun kwanciya hankali Dan ba laifi ya samu alheri daga labarin daya bani


Kamar dai wancan lokacin sai daya kwana biyu kafin yaje wajen Umma da Saude har ta isar mata da labarin zuwansa har da Karin gisihirin da sai da Hajara ta ji tazo wuya tsanar Naeema na cike Mata wuya.

Duk da Naseer ya tafar Mata da abubuwa har da kudin.

Sam hakan Bai faranta Mata ba burinta kawai taga bayan Naeema Saffiya kuwa abinda take so kenan ta hau zuga Hajaran har sai data rabata da kudin da Naseer ya Bata ta had'a Dana wajenta ta kwashi Saude Suka koma wajen boka suka hau Gaya musu abinda suke so ya musu cikin tsananin mugunta.

Shi kuwa ya d'auko kwai guda biyu ya bawa Safiyya ya fada mata yanda zasuyi da Kwan a bayan Kwan kuwa sunayen Zahira ya rubuta kaca kaca

Jiki na rawa suka koma gida Safiyya ta Adana Kwan ta hau neman Wanda zai Mata aikin batare da an samu wani matsala ba.


Naseer kuwa Dana Masa maganar takuran da akewa Zahira cemin yayi kar na damu na Bari idan ta Yi placement sai a Mata transfer ta tafi boarding inyaso sai ta cigaba da ss dinta a wajen Dan shima.yana so yaga yaransa sunyi ilimi har ga Allah banasan yarana sumin nisa ballantana Wai su tafi boarding Amma ganin Naseer ya dage yasa na hakura

Yaje makarantarsu ya musu bayanin idan sun Gama placement Yana so ayi Mata transfer zuwa makarantar boarding.


A ganinsa a boarding ma anfi karatu.

Tafiyarsa da kwana goma

Ina cikin bacci nayi mumumann mafarki daya Sakani farkawa

Bakina d'auke da sallati na kunna fitilar d'akin tare da haska yarana Naga duk bacci sukeyi cikin kwanciyar hankali

Ajiyar zuciya na sauke na fito da zumar nayi alwala Dan Dama lokacin tashina yayi biyun dare har na Saba

Dayake dare ne sosai buta na dauko daga bandakina Dan na Debi ruwa Dan na bandakina ya Kare.

Sai dai maganganun danake ji kasa kasa yasa a bakin k'ofata yasa na tsaya cak gabana na fad'uwa.

Muryar namiji da mace nake ji

Hakan ya sa na nufi bakin kofar jikina na rawa

Kasa kunnena nayi naji macen na "ka buga k'ofar tana bud'ewa ka jefa Kwan cikin gidan

Shi Kuma Yana shi tsoro yake ji Idan aka kamashi fa

Bansan lokacin Dana bud'e k'ofar ba matar ta dib'a a guje.

Ni kuwa na rik'e Namijin Gam dake k'ok'arin guduwa saan Isihu ne ya ringa k'ok'arin kwacewa hannunsa d'auke da wani kwarya

Cikin rawar jiki na kwace Kwaryar Ina rik'e da yaron da hannu daya.......

*TOH SAI KUMA BAYAN SALLAH IDAN ALLAH YA KAIMU RAI DA LAFIYA*
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

*Dafatan munyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana Ina muku fatan alheri Nagode da so da.kauna*

*Page 50*

Sosai ya ringa k'ok'arin kwacewa na rikeshi Gam Dan burina na ajiye Kwaryar da Naga kwayaye biyu a ciki na tambayeshi wacce matar data saka shi wanan aikin har lokacin jikina rawa yake.ina Jan innalillahi wa Inna ilaihi rajiun


Cizon daya kaiwa hannuna da balain k'arfi yasa na cika shi ba Kuma zafin cizon yasa na cikashin ba bana San Kwaryar hannuna ya Fadi Kwan ya fashe tunda daga maganar Dana ji matar nayi so take Ana bud'e gidan a jefo Kwan tsakar gidan ya fashe

Da mugun gudu ya dib'a Dana sake shi

Ni kuwa na tsaya kamar mutum mutumi nabishi da kallo har sai Dana Diana hangosa.

Dak'yar naja k'afata na koma ciki adduoi da nake tayi ya Dan sama min nutswa

Ajiye Kwaryar nayi na kulle gidan.na Kara d'aukar Kwaryar na nufi dakina jikina na rawa

A Gefen gadona na zauna na Dora Kwaryar a cinyata bakina d'auke da Addu'a na dauko.kwan guda daya na hau jujuyawa Ina kallon jan rubutun da akayi a jikin Kwan da Sunan Zahira ko ta Ina Sallatin da nakeyi ne yasa Zahira ta bud'e Idonta Dan Bata da nauyin bacci Sam

Hawaye kawai nake Ina cigaba da jujuya Kwan a hannuna bansa lokacin data ma taso ta iso gabana ba sai muryarta naji tana "Umma lafiya kike kuka Mai ya faru"?


Dagowa nayi na kalli Zahira da nake ganin kamar Jiya jiya nan na haifeta duk da ta girma ta zama budurwa.hakan Bai saka na daina Mata kallan yarinya ba Amma Wai Zahiran makiyana ke San ganin bayanta

Sai a lokacin na tuna kallon da Safiyya tayiwa Zahira daya saka gabana tsinke wa ta Kara da na jira Naga balain da zata jefomin sai a lokacin na fashe da kuka.mai karfi Dan na d'auka ba abinda zai biyo baya tunda an kwana biyu Ashe suna kan bakansu


Kuka nake sosai Ina kallon Zahira da Abu kad'an ke sakata kuka itama tuni ta hau kukan tana cigaba da tambayta abinda ya faru nake kuka.

Nikam na rasa Mai nayiwa Umma da Safiyya a rayuwata mai na musu da zafi Haka da zasu bar kaina su dawo Kan yata da Bata musu komai ba.

Wane irin kiyayya ne wanan suke min da Bai tsaya iya kaina ba har da diyata da muka Haifa da Naseer daya kasance jinin Umma ban taba kwokwanto a Raina na Umma ce ta haifi Naseer ba Amma zuwa yanzu na fara kwokwanto Dan ba iya Ni Umma ta tsana ba har da Naseer tunda ba Ni kadai na haifi Zahira ba

Allah ne kadai yasan Mai Suka so yiwa Zahira Allah ya karemu na fito har na samu kwace Kwaryar daga hannun yaron da suka turo.

Sosai hankalina ya tashi a Daren.

Sallah ma ba a nutse nayi ba zuciyata na cike fal da tunani da tsoro tunanina ya rarrabu gida biyu jefi jefi nake dagowa na kalli Zahira dake gefena itama sanye da hijabi tausayin yata na Kara Sakani zubar hawaye duk cikin yarana babu Mai sanyin halinta da tausayin iyaye idan na tuna abinda Zahira tamin a lokacin da nake d'auke da cikin waleeed da muke cikin tsananin talauci har kuka nake nayita Mata adduar samun nagartacen miji lokaci bamuda komai a gidan dak'yar na samo musu garin kwaki Suka Sha suka kwanta itama sai Dana tilasta Mata Tasha Dan dagewa tayi sai dai Nima na Sha Wanda Ni nasan ko Ni na Sha garin Nan ba Inda zai kaimin ni xan iya hakura tunda yarane duk da balain yunwar da nakeji da ke Sakani Jin jiri

Da wuri suka kwanta Ni kuwa bacci yak'i zuwarmin sai.juye juye nake Ina Dan hawaye Dan yunwa nake ji ba kadan ba ga jikina dake balain rawa.


Ashe duk halin da nake ciki Zahira na kallona magana ne.kawai batamin ba.

Mik'ewa nayi Ina bin bango sabida rawar da jikina keyi na fita kitchen Dana San babu abinda Zan samu na sawa cikina bansan lokacin da Zahira ta fita ba sai motsin bud'e kofa naji daya sakani.fitowa daga Kitchen da Sauri nayi wajen.

Ban hango.kowa ba hakane yasa na dawo d'akina da Sauri anan nagane Zahira ce ta fita waje

Ciikin tashin hankali nayi waje.

Ina dube dube Ina mamakin Ina Zahira ta fita daddare Nan


Sunanta na hau Kira da k'arfi


Zahira kuwa Ashe data fita gida gida ta ringa bi tana rokonsu abinci wasu kuwa har zaginta suke Akan me zata buga musu gida suna bacci

Wasu Kuma Haka zasu zageta ahaka ta cigaba da bin gida gida har ta iso wani gidan data ganshi a bud'e


Tana Shiga ta zub'e a kasa cikin kuka ta hau ce musu "Dan Allah ku taimaka Mana da abinci ummana yunwa takeji ta kasa bacci"


Daga Mai gidan har matar gidan tausayin Zahira ne ya rufesu duk da basu Santa ba.
Abincin da matar ta kawowa Mai gidan da shima Bai Dade da dawowa ba suna Dan tab'a hirane hakane yasa Bai ci abinci ba


Magana ya yiwa matar Akan ta Nemo Leda ta juye mata abinci shi Kuma zai Sha shayi da bredi

Matar mik'ewa tayi ta d'auko Leda ta juya tuwon dake da Dan yawa a bak'ar Leda ta juye miyar yauki shima a wani Leda ta hadasu a wani Leda ta mik'awa Zahira data mike da Sauri ta wafci ledar tana ta gode.

Ta fita a guje cikin murna duk da tsoronta da karnuka Haka ta ringa tikar gudu tana murna samo min abinci

Ni kuwa hankali a tashe na koma ciki na Sako hijabi na Dan na nemota sai dai jiri kawai ke d'ibana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login