Showing 6001 words to 9000 words out of 180103 words
adduoi Dan gani yake kamar itama gamo tayi abinda ya d'aukewa Mallam Ibrahim hankali daga Kan Hajara kenan.
A takaice tundaga ranar Hajara ta ringa hargitsa gidan cikin sirri batare da an ganota ba Dan dai kawai Kar Mallam Ibrahim ya samu nutsuwar tunkararta da Sunan rukiyya.
Nan kuwa Mallam ibrahim tuni ya gane Hajara ba Jinnu ke damunta ba ba dai San a wane matsayi zai ajiyeta ba Mayya ce ko matsafiya addua kawai yakewa kansa da sauran iyalinsa da duk sai da Hajara ta tab'asu.
Duk abinda yayi na addua Dan ya kawo karshen abinda Hajara yak'i tasiri akanta Dan yanzu Bata ma Abunta a boye a Sha biyu nayi zata zura jajjayen Kaya tayi ta abubuwanta
Zuwa lokacin an fara gane wacce Mallam Ibrahim ya aurowa kansa.
Waazi da nasiha ba Wanda Mallam baiyi wa Hajara ba Amma duk a banza.
Ana saura sati biyu tayi shekara a gidan ta haifo santalelen danta Mai Kama da Mallam Ibrahim sak.
Mallam Ibrahim na d'aga bakin kofa ta haihu Ana yanke masa cibi Yasa aka mik'o Masa shi ya kafa bakinsa a kunnen jariri ya masa huduba ya lullubeshi ya bar gidan da jaririn Dan ya Sha alwashin Hajara bazata ga kalar jaririn ba ballantana ta shayar dashi.
Tunda yaganta da ciki ya Samu wani amininsa Mallam Hassan dake Jos da sukayi makaranta tare ya zayyana Masa komai Dan har yafi Mallam Ibrahim din ilimi hakane yasa Mallam Hassan yace Masa tana haihuwa ya kawo masa jaririn.
Ruwan zam zam yayi ta bawa jaririn har suka Isa garin Jos Da isarsa Matar Mallam Hassan ta karbi jaririn tayi Masa wanka a cikin matan Mallam Hassan d'in akwai Mai shayarwa aka bata Jaririn ta shayar dashi.
A takaice Kwanan Mallam Ibrahim uku a Jos ya dawo bayan ya bar amanar Jaririn daya sawa suna Naseer a hannun amininsa da yake hazikin mallami ya Kuma ce Masa duk tsafin Hajara Bata isa ta gano Inda Naseer yake ba hankalinsa kwance a dawo gida.
Inda dawowar da yayi yazo ya tada tashin hankali Dan Hajara haukace musu tayi a gida Akan sai an fito Mata da jaririnta Inda tayi ta azabtar da matan gidan akan su fito Mata da jairirnta ko ta kashe su.
Ahaka ta rik'ewa Zinnira da kafa Fatsima kuwa har lokacin bakinta a karkace yake Aisha kuwa ta Mata turen Aljannu
Mallam na dawowa gidan taci kwalar rigarsa akan ya bata danta shi kuwa yace Mata ita da ganin danta sai dai a lahira domin dansa Jinin musulunci ke yawo a jikinsa.
A takaice sosai Hajara ta hargitsa gidan yan kungiyar ta suka ringa tayata
Sai da Mallam Ibrahim ya dage da Addu'a sosai a ranar da yaga abin yaci tura ya yanke igiyar auren dake tsakaninsu.
A takaice silar rabuwar Mallam da Hajara kenan.
Inda rabuwar ma da yayi da ita ya Kara haddasa wani tashin hankalin duka iyalinsa sai data sako su a gaba har Fatsima ta Kai ga rasa ranta.
Hajara sosai ta dage Masa akan idan Yana San ta bar rayuwarsa gabadaya ya bata danta Dan har yan kungiyar su sun kasa gano Inda Mallam ya boye Naseer.
Mallam Ibrahim kuwa tuni ya daina bacci ya dage da Addu'a da Saukar Qurani kafin ya d'an Samu Hajara ta rabu dashi duk da hakan Bata fasa zuwa tambayarsa danta ba.
Koda lokacin da suka rabu da Mallam ibrahim data koma Calaba ta tarar da Sulaiman ya rasu Mahaifiyarta ma haka Dan lokacin ba waya ballantana taji labari Bata wani damu ba Mahaifinta da Hassan da Husaini ne kawai sukayi bakin cikin mutuwar Aurenta tunda Mahaifiyarta ta rasu Mahaifinta bai cika lafiya sosai ba.
Ita kuwa Hajara baje kolinta kawai take cikin shekara Biyu manema sukayi Mata caaa dayake tana da kyanta ba laifi a wanan lokacin.
A cikin manemanta ta zabi wani Tijjani Cikin wata uku sukayi aure lokacin da matansa guda biyu.
Ko wata uku batayi a gidan ba tasa duk ya saki matansa ta ringa ganawa yayansa azaba Tijjani nagani babu yanda zaiyi Dan bashida bambanci da danta Sabida ta riga da ta Mallakeshi sai yanda tayi dashi.
A cikin shekara Shidda ta Haifa masa Yara Uku Danta na fari yaci Sunan Mahaifinsa Tijjani sai Mai bi masa Safiyya Sai Lami har a lokacin ita da yan kungiyarta suna iya kokarinsu wajen ganin sun gano Inda Mallam Ibrahim ya Kai Mata danta Amma Ina abin yaci tura sun kasa gano Inda Mallam din ya kaishi wanan kenan.
B'angaren Naseer kuwa sosai ya karantu ya ilimantu ya tarbiyyantu a hannun Mallam Hassan ya samu ilimin Arabic da Boko daidai gwargwado Mallam Ibrahim na zuwa ganinsa akai akai Dan duk cikin yayansa yafi Jin Naseer a Ransa ya Kuma fi tausaya Masa sabida halin mahaifiyarsa har Misra Mallam Ibrahim ya tura shi ya Karo karatu Sabida Yana so Naseer yayi ilimi Mai zurfi da zai iya na Kare kansa daga sharrin masu sharri duk cikin yayansa babu Mai balain hakurin Naseer ga k'ok'ari Yana da shekara Ashirin ya fara kasuwanci Dan ba laifi Naseer nada zafin nema cikin kankanin lokaci at Age of 23 ya zama successful bussines man duk abinda ya juya sai Allah ya saka Masa albarka.
Har a lokacin Yana wajen Mallam Hassan jefi jefi yake zuwa Modobi wajen mahaifinsa ya Sha tambayarsa game da mahaifiyarsa sai Mallam Ibrahim yace yayi hakuri ya bashi lokaci zai bashi labari wanan kenan.
Naeema
Mahaifinta Lawan yaren Ribina ne dake Kauyen Toro dake jihar Bauchi Shida matarsa Aminat Auren Zumunci akayi musu Mahaifin Naeema maharbi ne Kuma Yana had'awa da noma kyakyawa ne kamar Fulani gasu da gashi har gadon Baya Lawan karfaffan mutum ne Mai balain Zuciya ya tsani raini da wulakanci shiyasa bai fiye huld'a da kowa ba iyalinsa kawai ya sani sai mak'otansa matarsa Aminat Mahaifinta da mahaifinsa uwar su daya ubansu daya wuta ce ta Kama bukkarsu daddare sukayi gobara Inda iyayensu duk suka rasa ransu Lawan da Aminat ne kawai Allah ya tseratar hakane yasa awancan lokacin rukon Amina ya koma hannun Mai gari har ta Isa Aure ya aura Mata Lawan da tun mutuwar iyayensu yake Fadi tashi.
Tunda sukayi aure Amina inta samu ciki sai ya zub'e idan kuwa ta haifeshi sai yazo babu Rai ahaka sukayi shekara Goma da aure kafin Allah ya tsayar musu ta haifi Namiji da suka sawa suna Aliyu bayan shekara hud'u ta Kara haifar 'ya mace Inda aka saka Mata Naeema.
Naeema kyakyawa ce sosai Dan tun tana jaririya take da balain farin jini Sabida kyanta rububin zuwa daukarta sai zata sha no-no ake dawo da ita da kuwa aka yaye ta idan makota suka d'auketa sai dare suke dawo da ita.
Daga Lawan Har Aminat din ba wani ilimi sukayi ba a wancan lokacin balle su saka yaransu masu karatu ma a wanan lokacin sai yan wajen gari haka.
Aliyu ba inda ya baro mahaifinsa a wajen k'arfi da Zuciya hakane yasa Mai unguwa ya shawarci Lawan ya saka Aliyu a makarantar Sojoji da Lawan k'i yayi dak'yar aka samu aka shawo kansa ya amince.
Few mutane lokacin suna Dan zuwa karatun allo a lokacin hakane yasa Aminat ta yiwa Lawan Magana ko zaa saka Naeema da take da shekara goma a lokacin bai k'i ba Naeema ta fara zuwa sai dai tana fara zuwa Samari sukayi ca akanta Dan Naeema nada tsayi sosai hakane yasa wasu suke ganin girmanta sosai ga kyaunta daya fita Dan tana da Dan girman jiki she so innocent and Calm Dan haka ma Mahaifiyarta take.
Ko wata uku batayi da fara zuwa makarantar ba Lawan ya cireta dayaga yanda maza ke bi masa ya har gida Inda tuni ya koma Yi Mata kulle.
Tana da shekara Sha uku Lawan ya fara barinta kula Samari a wancan lokacin Dan 13 ko 14 anyiwa yarinya aure a wancan lokacin idan Kika Kai 15 16 haka zaayi ta kanannun maganganu kin tsufa bakiyi aure ba.
One faithful day Naseer ya Kai kayan daya Saro garin Bauchi cikin kwana uku ya Gama abinda ya Kai shi a ranar da zai tafi wani abokinsa mustapha ya nemi ya raka shi kauyen dasu Naeema suke zai Kai Sako ahaka kaddarar Had'uwar Naeema da Naseer ya kasance.
Naseer dake Shirin barin garin Bauchi sai gashi ya fasa komawa a ranar Dan ba karamin kamuwa yayi da San Naeema da itama ruwa taje dib'a suka had'u dashi a hanya Bata wani kula shi ba Amma fuskarsa na Nan daram a kwakwalwarta.
Dayake ba wani fita take ba hakane yasa Naseer bai Kara samun ganinta ba da aka kwana biyu.
Lawan kuwa sosai ya damu da rashin ganin Aliyu da aka ce Masa Zai na zuwa ganin gida duk karshen wata hakane yasa yaje wajen Mai unguwa Akan yaji ko lafiya Dan shi ya had'asu da mutumin daya tafi da Aliyu a lokacin Mai Unguwa ya d'auko letter da aka kawo masa daga birni dayake ba dukansu ne sukayi Boko ba basu San Mai wasikar ya k'unsa ba sai da aka Nemo Wanda ya d'an iya karatun a wasikar ake bayanin baa ga Aliyu ba sun b'ata shi da wasu dalibai da sukaje.
Hankalin Lawan Dana Amina ba karamin tashi yayi ba sosai aka hau neman Aliyu cikin samu ganinsa ba addua kawai suke akan Allah ya bayyana musu shi rashin Aliyu yasa Amina ta Dan fara rashin lafiya a cikin irin wanan Halin Naseer yaje neman Auren Naeema da kansa a wajen Lawan Inda farkon ganin da Lawan yayiwa Naseer yaji Naseer din bai kwanta Masa kamar yanda wani abdullahi yafi kwanta Masa a maneman Naeema ba Dan har a zuciyarsa yafi San Abdullahi ahaka iya shi ya yarjewa Naeema take kulawa sabida yabawa da yayi da hankalinsa Dan Naeema nada manema da yawa daga Samari zuwa manyan masu kudin sai dai ya lura kamar Naeema tafi San Naseer Kuma baya San yayi Mata dole.
A takaice ahaka Mallam Hassan yazo ya nemawa Naseer auren Naeema bisa jagorancin Mallam Ibrahim daya sakarwa Mallam Hassan ragamar komai.
Cikin mutunci akayi komai bayan Lawan ya danyi bincike akan Naseer da a garin Jos yayi binciken nasa bai San suwaye asalin iyayen Naseer ba.
Naeema kuwa kawayenta sai tayata murna suke da samun miji kamar Naseer Dan Naseer San da yake yiwa Naeema baya b'uya.
Wata uku aka saka bikinsu.
Inda matan Mallam Hassan su suka Dan had'a Masa lefe aka Kai lokaci kawai ake jira.
Naseer kuwa tuni ya Gina katafaren gidansa a garin Jos.
B'angaren Hajara kuwa haikan ita da yan kungiyarta suke neman Inda Mallam Ibrahim yaje ya b'oye Naseer Dan har lokacin Hajara na zuwar wa Mallam Ibrahim akai akai akan a nuna Mata Inda danta yake.
A cikin irin wanan lokacin Ana saura wata daya auren Naseer da Naeema .
Naseer da Mallam Hassan suka tafi Modobi wajen Mallam ibrahim.
Dan shima Mallam Hassan akwai wani kanin mahaifinsa dake garin Modobin dayake San duba jikinsa.
Suna zuwa aka musu tarb'a Mai kyau Mallam Ibrahim sai murmushi yake Yana bin Naseer da kallo a Ransa Yana tunanin a yau zai Dan bashi labarin Mahaifiyarsa Amma bazai Gaya Mata wacece ita ba.
Zai dai bashi wasu adduoi ya ringayi na kariya daga sharri duk da Yana tunanin duk hatsabi bancin uwa bazata tab'a danta ba.
Wajen karfe hud'u suna zaune gabadayansu a k'ofar gida har da yayyen Naseer da ke zuwa wajen mahaifinsu haka da yamma duk da ba uwa d'aya ce ta haifesu ba suna da balain had'in kai.
Cikinsu kuwa har da Mallam Hassan
Kamar wacce aka jefota haka suka ga Hajara a gabansu.
Dan shugabarsu ce tagano Naseer ta mudubi shi da Mallam Hassan hakane yasa tayi saurin gayawa Hajara shine ta bayyana gabansu afujajan.
Mallam Ibrahim Sallati ya saki a lokacin da ya ganta ya hau addua a Ransa.
Mallam Hassan shima Yana ganinta yasan itace duk da bai taba ganinta ba.
Hajara kuwa Naseer kawai ta zubawa Ido tana kallonsa tamkar yanda yake kallonta yanajin wani iri a jikinsa
Hajara kuwa da Sauri ta dauke idonta daga kansa data ga katon tabon Sallah Goshin Naseer nata shigar Mata Ido haka kawai taga kamar kallonsa na neman haddasa Mata ciwon Kai.
Ranar wanka ba a boye cibi inji Mallam ibrahim "wanan itace mahaifiyarka Naseeer"
Naseer mik'ewa yayi da Sauri ya Isa gabanta ya tsugunna har kasa ya fara gaisheta Hajara kuwa kamar ta Kama da wuta sabida tsananin bakincikin ilimin addinin data ga ya ratsa Mata d'a Dan har ga Allah hakan na iya zame Mata barazana.
A takaice a ranar Hajara ta kebbe da Naseer tana Masa masifa bai tab'a nemanta ba hakuri kawai yake Bata Yana shima bai San dalilin daya sa Mahaifinsa yak'i Basa labari game da ita share maganar tayi ya hau Masa fadan da yanzu basu had'u ba sai dai yayi aure batare da sanin ta ba.
Anan mmaki ya rufe Naseer Dan yasan bai mata zance aurensa ba Kuma tunda tazo bai ga ta kebb'e da wani ba ballantana yace anan taji labari.
Hakuri kawai ya bata
Ita kuwa tayi murmushi tana "Ai matar da zaka aura kyakyawa ce ba laifinsa"
Kara dagowa yayi cikin mamaki Yana "Kinsanta ne"?
"Sosai ma nasanta dazu duk naji labarinta da zuwanka gurin mahaifinka Kai yanzu dai kafisan mahaifinka akaina ko shiyasa baka tab'a nemana ba Dan haka yanzu gobe zanzo na d'aukeka muje gidana ka Kuma ga 'yan uwanka"
"Murmushi Naseer yayi Bai ce komai ba Yana Dan Jin wani iri a jikinsa kasancewarsu waje daya data zo tafiya kuwa sai data bi Mallam Hassan da wani irin kallo tayi kwafa tayi tafiyarta.
Bayan sallar isha Mallam Ibrahim ya d'an fara yiwa Naseer hannunka Mai sand'a da Naseer ya bashi labarin Hajara zata zo gobe su tafi yaga gidan da take zaune.
"Naseer ka dage da Addu'a mahaifiyarka Tana cikin kungiyoyi da yawa nima bansan wacece ita ba sai Dana aureta zama Bai Kama ka ba Dan kaima baka wuce ta sako ka a gaba ba Dan su ba basu San Allah bama balle suji tsoron sa a zuciyarsu basu San Mai tausayi ba ballantana suyi Imani"
Watarana zaka ganewa idonka watarana zaka San wacece mahaifiyarka tun sanin Dana Mata Bata baccin dare bansan a wane matsayi zan sakata ba Mayya ce ko matsafiya Allah kadai ya barwa kansa sani Allah kadai ke kareni sanin wacece ita yasa na dauke ka tun kana jariri na kaiwa aminina Sabida ya kularmin da Kai Ina tausayinka Naseer a cikin yarana kafi kowa hakuri Kaine Kuma bakayi dacen uwa ba tun a yanzu ka dage da Addu'a Naseer.
A takaice ire iren kalmomin Nan ya koma Yiwa Naseer da Naseer ya haddace Gam a kansa Amma a akaran kansa ji yayi ya kasa gasgasta zancen mahaifiinsa a wajensa mayyu apperance dinsu daban yake Dana mutane Amma zai dage da Addu'a kamar yanda mahaifiyansa ya bashi shawara....
Share
dis page is fiction gaskiya Dan wacce ta bada labari Bata San ya mahaifiyarsa ta zama matsafiyya ko Mayya ba but tunda novel ne hakane yasa zamu Nemo yanda ta zama mayyar
Next page zamu tsunduma cikin labarin gdan gadan insha Allah ur comments give me strength d more u comment d more na samu kwarin gwiwa tnk u
8/19/21, 10:30 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 4*
Washegari Naseer suka d'au hanyar Calabar shi da Hajara da a fad'arta tazo ne Dama Wajen wani kawunta a modobi taji labarin zuwansa.
Kwana biyu Naeeer yayi a Calabar a cikin kwana biyun da yayi ya ga abubuwan mamaki da Al ajabi daya d'aure Masa Kai ya Kuma kasa tunkarar Hajara da tambayar daya dank'are Masa a zuciya.
Farko suna Isa gidan ya tarar da kannensa Tijjani Wanda yake da shekara Ashirin a lokacin Sai Safiyya da take da Sha bakwai sai Lami da take da Sha uku a palon gidan a zaune Hajara batayi Sallama ba da suka gidan hakane yasa shi Kuma yayi Sallama ga mamakinsa babu Wanda ya amsa mishi sallamar da zaiyi magana sai ya fasa Hajara kuwa cikin washe baki tace musu ga yayansu Nan da take basu labarinsa kadaran kadahan suka gaishe shi shi ma ya amsa musu Yana Dan karewa palon da aka rataya wasu irin Abubuwa a kowane kusurwar palon har da su Kaho haka.
Muryar Hajara dake kwallawa Tijjani Kira yasa ya maida hankalinsa kanta har Yana mamakin ya za'ayi ga Tijjani a gabanta Kuma ta ringa kwalla Masa Kira haka.
Da Sauri yaga wani datijjo ya fito daga wani daki dake Gefen palon kallo daya zaka mishi kasan Yana balain Shan wuya har wani irin furfura ne suka yayame fuskarsa.
Yana isowa gaban Hajara ya zub'e Yana Mata sannu da zuwa.
Naseer kuwa tsananin mamaki yasa ya saki baki Yana kallon ikon Allah.
Hajara kuwa Bata amsa gaisuwar da yake Mata ba tace "Naseer ga Babansu Tijjani Nan ku gaisa"
Da Sauri babansu Tijjani ya isa wajen Naseer yana neman durk'usa Masa.
Naseer kuwa ya mik'e cikin tashin hankali da Alajabi ya taro shi ya kalli Hajaran Yana "kina nufin Wanan shine Mahaifinsu Safiyya ma'ana mijin da Kika Aura da kuka rabu da Abbana"?
Hajara d'auke idonta tayi daga kansa ta watsawa Tijjanin wani irin kallo.
Shi kuwa jiki na rawa yayi waje da Sauri har Yana tuntub'e Yana zuwa Dab da kofa tace Masa ya shiga kitchen ya tuka musu tuwon Massara da miya.
Da Sauri ya gyada Mata Kai ya fice yana sharar hawaye.
Tunda ya Auri Hajara yasan ya aurowa kansa balai bashida ilimin addini da zai Kare kansa daga Sharrinta baya iya ketara umarnin ta Yana ji Yana gani ya rabu da matansa biyu Yana ji Yana gani ta watse Masa Yaya suka shiga duniya Banda biyu da suka rasu da yake zargin itace ajalinsu ya Riga da yasan wacce ya aura ya Sha yunk'urin guduwa tana kamoshi sosai suka d'aure shi da tsark'a har addua yake mutuwa ta d'aukeshi da irin rayuwar da yakeyi da ita.
Naseer kuwa bayansa yabi da kallo har ya fice ya dawo da kallonsa Kan Hajara data balain had'e Rai hakane yasa ya kasa Maganar dayake da niyyar Yi ya koma ya zauna tunani barkatai na zuwar Mishi