Showing 171001 words to 174000 words out of 180103 words

Chapter 58 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2481

kanta ta fara tsayawa tana kulasu

A cikin ma nemanta akwai wani Khalid da ke balain santa mahaifinsa Mai kudine sosai dan sananne ne a lokacin Kuma dan siyasa.

Nacin da yake yiwa Zahira ba dare ba Rana har wajen koyon dinki yake binta yasa ta fara sauraransa duk da ba wani San shi take ba.

Kyautatawa kuwa sai da na sa Zahira da dakatar dashi dan ba karamin kudi yake kashe Mata ba


Ba Kuma iya Zahira ba har kanennta da waleed.

Kayan abinci haka zai jiddo a kurkuka a kawo mana.

Gashi da hankali koni yafi kwantamin akan kabiru zahira ke hana shi turowa dan tana ganin kamar shima zai iya cewa ya fasa aurenta idan aurensu ya kusa har lokacin bata San dalilin daya sa kabiru ya fasa aurenta ba dan data ce mu bata wasikar da kabiru ya rubuto Mata k'in bata mukayi sabida Kar hankalinta ya tashi.

Khalid yana ganin Zahira tak'i bashi dama ya turo ya nemi Naseer da kansa akan Yana san auren zahira.

Maganin kada ayi kar a soma Naseer bai b'oye wa Khalid duk abunda ya faru da Zahira ba na juyar Mata da Kai da akayi tayi rashin ji a shekarun baya ya nuna Masa bai San suwaye sukayi yiwa Zahira haka ba da Karfin Addu'a ta dawo daidai wanan dalili yasa har Wanda yaso Aurenta ya janye dan haka baya so sai tafiya yayi nisa shima ya janye.

Ga mamakin Naseer khalid sai ce Masa yayi ai ko da halin Zahira ne ba juyar Mata da kai aka yi ba Zai iya Aurenta ko haihuwa tayi shi bai had'a San Zahira da komai ba indai aka ga bai Aureta ba toh mutuwa yayi.


Ba ni ba har Naseer a ranar ba muyi bacci ba sabida tsananin murna Zahira ta dace da Mai kaunarta duk fargabar daya cikemin zuciya duk ya kau.

Sati d'aya a tsakani dangin kabirun manyan masu kudi Suka kawo kudin neman aure a shiryensu suke har da akwatunan lefe dozen.

Ni kaina na tsorata da irin dukiyar da suka kawo.

Kanenn Zahira kukan farinciki kawai suke suna wani hanin ga Allah baiwa ne.


Mahaifin Khalid daya kasance dan siyasa a lokacin chairman ne da kansa ya taka yazo gidan Sabida San da yake yiwa Khalid.


Bayan babban sallah da sati biyu aka saka bikin Zahira da Khalid.

Iyayen Khalid sunce basa bukatar a kawo Zahira da komai.

Su zasu mata dan ba Khalid kadai ke san Zahira ba duk dangin Khalid da iyayensa balain San Zahira suke so daga Allah.

Tabbacin ba abinda zai hana auren nan idan dai ba mutuwa ba yasa hankali kwance muke ta shirye shiryen mu Allah kadai yasan farinciki da nake ciki dani da Naseer da inna Amina

Addua kam ba dare ba Rana haka muke yi har da azumin mu sadaka duk alhamis da jumma da kaina nake girka abinci Mai yawa na ciyar da almajirai.

Ana saura sati uku auren Zahira da Khalid mahaifin Khalid ya turo wasu mutane biyu da mukullin sabon gida da takardu akan an bar Mana gidan mu tashi daga wanan gida sabida ya Mana kadan a hidimar biki.

Da alama ta silar Zahira arzikinmu zai farfado.

Kukan farinciki dagani har yarana da shi kansa mahaifinsu haka muka ringayi ga Karin alkawarin
bayan biki za'a nema wa Naseer aikin yi tunda iyayen Khalid su keda gwammnati a lokacin

Cikin farin ciki muka koma sabon gidan da muke ganin kamar duk mafarki muke dan gidane irin na masu kudi Mai gate komai akwai


Dukan mu sai da mu kaje gidansu Khalid muka yi godiya har da Inna Amina.

Da a wajena saninta a rayuwarmu alherine.


Khalid shi ya dau nauyin komai duk da muna ta hana shi ni kaina nasan bazan iya fassalta San da Khalid yake yiwa Zahira ba ga kyau ga kudi dan Zahira ma bazata gaya masa kyau ba duk da tana mace Ya ma fita fari.

Saura kwana goma bikin Zahira da Khalid da yamma ya kawowa zahira dinkunanta da ya kai Mata dinki da kansa ba iya nata ba har da nasu Nadeeya.

Suna hira a waje bayan ta shigo da ledojin ta koma wajensa.

Yana saman motarsa a zaune suna cikin hirar Zahira tace Masa "Wai ni ya Naga kamar baka da lafiya ne sai ramewa kake yi"

Murmushi yayi yana "Nima bansan Mai ke damuna ba Zahira kwana biyun nan bana Jin dadin jikina ne ga mugayen mafarki da nake fama dashi ayita tsorata ni daddare ban gayawa kowa ba idan bake yanzu da nake gayawa ba kema dan bana iya b'oye Miki komai shiyasa na gaya miki da Alhaji da hajiya sun San maganar Nan da sai sun daga hankalinsu amma ni nasan ba komai kila haka akeji idan an kusa aure"


Ya karashe da murmushi Zahira kuwa hankalinta ya balain tashi

Amma ta daure bata nuna Masa halin da take ciki ba yanzu tayi girman da tasan muna da makiya masu San ganin bayanmu tasan komai akan dangin babanta.

Haka sukayi hirar sama sama ta shigo gida.

Ta sameni a d'akina ta zub'e akasan carpet cikin kuka ta hau bani labarin abinda khalid yace Mata ta Kara da "Umma Ina tsoron umman Abba ko Aunty Safiyya suyi wani Abu ya wajen Hana auren Nan Umma kiji fa wai ana tsorata shi daddare.

Tunda ta fara min magana nake sallati.

Bansan ma na mike ba sai tsintar kaina nayi a d'akin Inna Amina Zahira na biye dani.


Yanda ta ganmu a firgice ya sa ta mik'e zaune dan a kwance take

Kuka na fashe dashi na hau bata labarin da Zahira ta bani ina "Mama Ina tsoron sharrin bayin Allah nan Ina tsoron suyi abinda zai saka a fasa auren nan ba abinda bazasu iya yi ba dan suga bayana dana Zahira kin San irin tsanar da suka yiwa Zahira sabida kawai tana Kama dani kinsan irin wahalar da suka bata Kar yanzu da suka ga ta dace da Mai kaunarta su cutar dashi"

Na karashe Ina fashewa da kuka


"Haba Naeema ki kwantar da hankalinki wlh basu Isa su hana abinda Allah ya kaddara ba ki mik'awa Allah lamuranki zai isar miki insha Allahu mu dai mu dage da Addu'a shima Khalid din idan yazo ta turomin shi Zan basa adduoi ya ringa yi ba abinda zai faru insha Allahu dan Allah ku kwantar da hankalinku idan dai kuga baayi auren Nan ba toh wlh dama Khalid ba mijinta bane haba Naeema kiringa amfani da hankalinki Mana yawan tsoron Nan naki ma na iya sawa Allah ya jarrbaceki Abu kad'an sai kice zasu Miki wani Abu kenan duk abinda zai sameki sune bazaa jarrabceki ba"

Naseeha ta min nida Zahira

Nayi k'ok'arin boye damuwa na ne kawai Amma hankalina a tashe yake.

A haka lokacin biki yayi ta matsowa daga ni har Zahira jikinmu a sanyaye yake


Naseer Dana gaya masa ma cemin yayi ba abinda zai faru insha Allahu dan baya bacci tunda bikin ya matso


Ana saura kwana hudu daurin Auren Khalid da Zahira khalid yazo gidanmu a firgice bai tsaya neman iso ba ya fado palon ya zub'e a gabanmu ya hau bamu hakuri duka Muna zaune a Palo

"Dan Allah kuyi hakuri na fasa auren Zahira wlh sunce idan na dage zan Aureta sai sun kasheni

Ido bud'e Ido rufe haka suke biyoni da wuka.

zasu kasheni har da micizai yanzu haka gasu Ina kallonsu da manyan micizai wlh tunda na had'u da Zahira suke tsoratani suke min kashedi nak'i ji yanzu naga da gaske neman rayuwata suke dan har hatsari suka saka nayi yanzu bansan Zan tsira da rayuwata ba dan Allah kuyi hakuri inasan Zahira wlh Amma bana so na mutu na fasa aurenta ne dan na tsira da rayuwata"

Tunda ya fara magana muke kallonsa Muna zuba sallati

Zahira kuwa Ashe ta Dade da sumewa


Naseer ne yayi karfin halin cewa ba komai Allah yasa hakan shi yafi alheri

Khalid daya jike da gumi idonsa duk hawaye

Ya kalli wajen da Zahira ke kwance kamar zai karasa wajenta kuma.ya fasa ya fita waje da Sauri yabi ya rame Kamar bashi ba

Wani mugun ihu na fasa na zub'e a kasa

Kamar wayanda aka Mana rasuwa Muka hau kuka Naseer ya mik'e ya shige dakinsa ya rufo kofarsa da mukulli

Zahira na farfadowa ta hau ihun kuka tana "Mai nayi haka a rayuwata nake ganin irin wanan jarrabawa sai ana dab da bikina sai a fasa Umma Mai nayi musu Abba Mai nayi laifine nazo a yarku?Mai yasa laifin wasu zai shafeni ?Umma a garin yaya Kika auri Abba kinsan basa sanki gashi yanzu ni da ban musu komai ba suna ta watsa min rayuwa kenan ni bazan yi Aure ba?daga wanan sai wanan Umma ban musu komai ba suka min turen Aljannu suka saka ban karasa makaranta ba iya haka bai Isa ba suka fitar dani a hayyacina nayita abubuwa yanzu Kuma na dawo daidai sunce bazan yi aure ba"?

Kuka Zahira keyi kamar zuciyarta zai fita


A fasa auren Khalid da Zahira nayi jinyar fiye da wata biyu a asibiti Allah ne yayi bazan yi ciwon B'arin jiki ba.

A takaice a haka shima Khalid ya tafi.

Yata aka cigaba da zuwa neman aurenta ana dab dayi sai a fasa bayan Khalid mutane biyu Suma.

Daga haka.zahira tace ta cire rai da aure

Ta rokeni.mu bar mai San Nadeeya ya turo neman aurenta Kar mu Hana shi sabida ita.

Tunda kamar ya matsu haka kuwa akayi saurayin Nadeeya Umar ya turo manyansa neman auren Nadeeya aka saka Rana wata uku



Calabar....
8/25/21, 9:59 AM - Alhmdllh: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

Page 63

Safiyya


Fadar tashin hankali da damuwar da take ciki b'ata bakine dan ko baccin kirki bata iya yi Sabida masifar da yaranta ke ciki.

Asmau yanzu duk daurin da zata Mata sai ta kunce ta fito daga d'akin ta fita waje.

A haukacen ma haka maza ke nemanta idan ta daureta ta karfi da yaji haka maza ke biyota gidan ba kunya ba tsoron Allah ga tsokanarta da sukeyi da uwar mahaukaciya.


Abinda ya Kara daga Mata hankali bai wuce Bashir daya dawo gidan da Zama gabadaya ba ya Kori Asmau daga daki dayan data kulleta yayi zamansa a d'akin da macen da itama kana ganinta kasan Yar bariki ce ta ma girmi Bashir nesa ba kusa ba amma haka ta biyo bashir cikin gidan take zuba mulki San ranta Safiyya bata isa tayi magana ba.
Har wajen Oban taje akan a Mata maganin budurwar Bashir din da aka cewa hajiyayye Ashe itama hajiyayyen tana zuwa wajen Oban ya Kuma Santa karya yayi wa Safiyya akan idan yayi aiki akan hajiyayye zata iya hauakcewa akan dole ta hakura.

dan aikatau din da take zuwa yi ta samo abincin da zata saka wa cikinta da hauwa da tana Nan Kamar d'abba Kamar mutum tana samowa Bashir zai nada Mata duka ko shi ko budurwarsa hajiyayye.

Safiyya takwararta itama data gama barikin tsarabar ciki tayo Mata ta dawo gidan ta zauna.

Ga Yar Asmau Nana da Rabia yarta.

Taurin zuciya yasa Zuciyata bata buga ba.

Bashir haka zaiyi sata a biyoshi har gida Ana nemansa hajiyayye budurwarsa kayan mayye take siyarwa wani zubin aka ma su biyun wani zubin su tsere a kamata

Duk jikinta tabon dukan ne na Bashir takan tsine Masa ta Kara tsine Masa har ta ringa ayyanawa da irin rayuwar Nan da take da yaran da basu Mata albarka ba gwara duk mutuwa sukayi.

Bakin ciki daya Mata yawa ta nufi wajen Oban dan ya binciko mata halin da su Naeema suke ciki da take jinsu a kahon zuciyarta ba yanda zatayi tana Shan gararin rayuwa su Kuma su Sha iska Mai dadi.

Gani take duk Wanan masifar Naeema da Naseer su Suka jawo Mata ta Kuma yarda da zancen Oban da ta fara ganin kamar bai iya aiki ba daya ce Naeema itama ba zaune take ba tana zuwa wajen Mallamai suna Mata aiki shiyasa duk abinda suka Mata yake dawowa kanta.

Amfanin da Oban yake dan Mata yasa bata bar zuwa wajensa ba amma duk lokacin data samu kudi dole ta nemi wani bokan da zai mata mugun aiki ko ba Akan Naeema ba yarta Asmau ta samu Lafiya da hauwa da shi kansa Bashir din.

Bata da burin daya wuce su samu lafiya.

Jikewa tayi da gumi a lokacin da Oban ya nuna Mata wani yazo auren Zahira rashin Jin da tayi ne yasa aka fasa auren

Yanzu haka ga wani Dan shahararen Mai kudin ya fito neman aurenta har an kusa ma auren an mallakawa Naseer gida.

Oban ya Kara da "Yayanki zai dawo da arzikinsa har yafi na da ta silar Wanda zai auri yarinya Nan Dan aiki Mai kyau suke so su bashi.

Matarsa Kuma zatayi kudi itama har ta fita waje

Ba iya Kuma Zahira ba duka yaranta ba Mai auren karamin mutum"

Kasa magana tayi tsabar kad'uwar da tayi da tashin hankali Taya tana nan na abinci na neman gagararta Naeema da Naseer su Kuma suna neman zama masu kudi?
Taya yaranta daga mahaukaciya sai Mai bin maza da kungurmin barawo yaranta data ci mugun buri akansu ba Wanda ya mata albarka Amma yaran Naeema gasu Mai kudi ke nemansu ta silar Zahira ma har ana neman mallakawa Naseer gida

Ita tana nan a wulakance ta Zama kamar zararriya
Auren Zahira na nufin samun kwanciyar hankali Naeema da farincikinta

Ita Tana Nan tana Shan duka awajen bashir yaranta mata ba ma na kwarai ballantana ta sa Rai suma zasuyi aure inaaaa

Tace da k'arfi ta matsa kusa da Oban tana ruk'o hannayennsa tana "Yarinya Nan bana so tayi aure yanda yarana Suka wulakanta a gabana haka nake so yarinya Nan ta wulakanta a gaban Naeema bana San Naeema ta samu kwanciyar hankali daidai da second daya inaso yarta Zahira ta dauwwama a gabanta ba aure yanda naga alamar yarana haka zasu dawwama a gabana.

Inaso kayimin aikin da zaa ringa tsorata shi a nemi ma ransa har sai ya janye daga neman aurenta

Duk Wanda zai nemi Aurenta a ringa tsorata shi ko sai yaje wajen Zahira dab da aurensu ya ga Zahira na bashi tsoro har sai ya janye

Ba iya Zahira ba duka yaran naeema haka nakeso su dawwama a gabanta taji abinda nakeji a Zuciyata

Naseer a Kara saka Masa tsanar Waleed idan Zan samu ne Naseer nakeso ya Zama ajalin Waleed.

Duk wani Abu da zasu samu ta silar yaransu ya lalace ko gidan ma da kace Ana shirin basu idan an basu Kar yayi albarka har sai sun koma wanan karamin gidan.

Inaso Naeema ta Shiga ukunta ta lalace wanan shegiyar tsohuwar dake taimaka mata inaso!!!

"Kullll Oban yace da Sauri Yana Karki soma kiramin tsohuwar nan dan na gwada aiki akanta komai.nawa lalacewa zaiyi nadai San Tana gidan ban Isa na Mata komai ba.
Duk abinda kikace ayi yafi komai sauki zaayi Amma fa sai kin kawo kudin aiki dan iya jikinki bazai iya biyana ba"

"Duk Inda kudi suka Shiga Zan Nemo Oban kwanciyar hankalinta ne dai banaso"

Safiyya sai data had'a da satarwa hajiyayye kudinta data Shiga bandaki dan.tayi wanka ta kaiwa Oban ya Mata aikin.

Kullum tana hanyar zuwa dan taga halin da suke ciki ahaka har Khalid ya fasa auren Zahira da ranar zuciyarta ya kasance fess tana Jin inama Safiyya batayi cikin shege ba da tayi aiki akan khalid yazo ya aureta.

Duk halin da su Naeema ke ciki tana sane tana kuma da labari ta wajen Oban hakane yasa ta Kara dagewa wajen ganin Zahira batayi aure ba har dasu Nadeeya.

Hajara

Bata tab'a sanin haka ake samun kudi idan ana bara ba sai data fara daga fara baranta zuwa yanzu har ta Tara kudade masu yawa da Bata tab'a mafarkin samunsa ba.

Ko kad'an bata yi tunanin kama haya ba ta cigaba da zama a rumfar mahaukatan da ta Riga da ta saje dasu

Ciwon kafar da take fama dashi daya dan kumbura yasa mutane ke Kara tausayinta tana fita bara zasu hau Tara Mata kudi har da masu bata kayan sawa.


Sai data tabbatar da ta Tara kudin da yawa daddare ta hau shiga mutane tana neman Wanda zai mata aiki akan Naeeema da Safiyya da take ganin sune manyan makiyanta a duniya.

Tsohuwar unguwar da suka zauna ta nufa ta Kara da nausawa daji ko zata samu ganin shugabarsu ta matsafa da takejin da tana Nan da duk matsalarta ta Kau

Sai dai ta karaci bullayinta a dajin bata sameta ba a wajen fitowa ta hadu da dattijuwa da zasuyi saani da ita ta kada baki ta tambayeta ko tasan Wanda zai iya taimaka Mata Wala mallami ko boka

Dattijuwa kuwa cikin murmushi tace itama Nan tayi su tafi

Silar haduwar Hajara da kawarta kenan Mai irin halinta da ita Kuma kishiya take San taga bayanta.

Bokan shima bayarabe ne da suka Samu dan sunfi yawa acan garin

Duk kudaden baranta ta zub'ewa bokan.

Ta fara da "Inaso naga bayan matar Dana ta wahalar dani shekara da shekaru Muna Abu daya da ita ban taba cin Galaba a kanta ba sai da tayi ta tsallake duk abinda na mata iya haka bai isheta ba sai data rabani da d'ana har a cell yarinya Nan ta kullemu muka kwana inaso a tura Mata cutar da zaiyi ajalinta tayi mumunan rashin lafiya da zaa rasa maganinsa har sai ta mutu.

Dana Kuma ayi.min aiki da arzikinsa zai dawo ya sake aure na Mori arzikinsa.

Safiyya yata Kuma Ina so a watsa rayuwarta idan har ni Dana tsugunna na haifeta zata kora har tayi dambe dani inaso yaranta su Zama ajalinta ta rasa kwanciya hankalinta ta ringa Neman mutuwa ma mutuwa tak'i daukarta.


Wani mugun dariya ya kece dashi yace mata "An gama amma duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki"

Hajara kada Kai kawai take cikin farinciki a duk abinda tace ayi Mata idan har ta samu cikar burinta akan Naeema gani take burinta ya gama cika.

Bata damu da yanda bokan ke ta nanata Mata duk abinda ya biyo baya tayi kuka da kanta ba.

Cikin farinciki ta baro wajen bokan tazo ta cigaba da baranta dan bayan kwana biyu bokan yace ta koma

Wanan kenan

(A labarin naeema wlh Tallahi na rage abubuwa da yawa ba sai dai na ringa rantse muku ba amma dai na kusa zuwa Inda muka tsaya a labarin)

Naeema

Tausayin yata nake sosai dan ta cire rai daga auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login