Showing 105001 words to 108000 words out of 180103 words

Chapter 36 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2490

Umma Umma dai Bata dukansu Amma Safiyya kam tana Kai musu duka a labarin ma da Minal ke bani dayake tana da surutu cewa tayi wani kullum.yana zuwa wajen Safiyya zance

Sam bana wani Gane maganar da Minal kemin zuciyata tana can wajen Aunty fatana ta dawo tacemin ta gansu Minal ce Bata San Mai take cewa ba

Raheema kuwa sai wani narke min take tana min kananan shagwaba Humaira kuwa hannuna ta rike Gam a cikin nata tana "Umma Dan Allah karki Kara tafiya ki barmu kinji"?


Aunty kuwa a lokacin data Isa gidan.

Da Sallama ta Shiga gidan

Hajara na zaune tana Shan garin kwaki da Yan canjin da Naseer ya Bata Safiyya Kuma tana can gefe tana cin abinci a farin roba da kana gani kasan na siyarwa ne shinkafa ne da Miya har da lemo taci uban kwalliya.

Ba Wanda ya amsa Sallamar da tayi

Safiyya kuwa har wani yatsina fuska tayi tana wa aunty kallon up and down tare da cewa "lafiya daga Ina"?

Wani irin harara aunty ta watsa Mata ta kalli Hajara da ta karasa kwankwade garin da take Sha tana "shigo Mana daga Ina"?


" Ciki Aunty ta karasa tana kallon yanda gidan yayi gaja gaja ba kintsi

Ta zauna a gefen tabarmar da Hajaran ke Kai ta hau gaida Hajaran

Hajara ta amsa cikin Dan sakin fuska tana jiran Karin bayani

" Sunana Hafsa Matar mallamin su Zahira ce ni kwana biyu bamu ga Zahira da Nadeeya sunje makaranta ba shine Mallam yace Nazo gida naji lafiya suka daina zuwa"

"Dolene sai sunzo makarantar lafiya Lau kawai bamu ga Daman suzo bane"

Safiyya tace tana Harare Harare


"Baiwar Allah ba wajenki Nazo ba ba kuma dake nake magana ba da mahaifiyarki nake magana Dan ita nakewa kallon Mai hankali sanin bakida hankalin yasa ko kallon naki banyi ba

Wani irin Ashar Saffiya ta lailayo

Aunty kuwa ta ja Tsaki ta kalli. Hajara da ke ta juye juye kafin ta saukr ajiyar zuciya ta ce "wlh sati biyu da kwana shidda kenan da b'atan Zahira da.nadeeya tsautsayi daga Dora musu tallan shinkafa da miya su Kai titi su dawo har yau dawowar da basuyi ba kenan ba neman da bamu musu ba

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun kawai aunty ke maimaitawa hankalinta a balain tashe ya tabbata dai su zahiran sun b'ata yau Mai zata cewa Naeema

"Kullum sai babansu ya fita da sassafe nemansu sai daddare yake dawowa sai dai ku tayamu kawai da Addu'a Abu Bai dadi ba"

Aunty Bata iya Kara ce komai ba ta mik'e ta fita Tana hada hanya sosai taji hankalinta ya tashi Dan tasan Yau Naeema sai ta kusa karamin hauka ita ma da nata sakacin da Bata duba yaran akai akai Kamar yanda ta alkawartawa Naeema.

Lokacin data Isa kasa Shiga gidan tayi sai da Mallam ya hangota ya iso wajenta ta ja shi gefe ta Gaya masa yanda sukayi da mahaifiyar Naseer sosai.hankalinsa ya tashi yana mamakin ya Yara zasu B'ata har guda biyu Amma Naseer ya boye musu Anya akwai gaskiya a lamarin Nan kuwa

A tare Suka Shiga gidan

Ina ganinsu na mike da Sauri naje wajen aunty a rude Ina "Kinga su zahiran ko? karya Minal take basu b'ata ba ko"?

Na jerowa Aunty tambayoyi Ina rik'e hannunta Gam

"Zauna muyi magana"

Mallam yace Ni kuwa.na zub'e a kasa Ina sallati ta tabbata dai yarana sun b'ata sallati kawai nake Ina ihun kiran.zahira.da Nadeeya Ina nayi nadama Dana tashi tafiya ban tafi dasu ba Ashe kallon.karshe nayiwa zahira shiyasa take ta waiwayena da Zan tafi Mai nayiwa su Umma Haka suka nemi su b'atarmin da yarana mai Zahira da Nadeeya suka musu da zafi haka"


Dak'yar na tsagaita kukan da nake Mallam.yace "ki kwantar da hankalinki a gaskiya bana Jin yaranki sun b'ata dan da sun Bata gaskiya zamu ji labari.ina dai zargin Naseer dai hutun.ya Kai su Dan Ina ganinsa a bakin titi wajen ginin shaguna Nan na bakin titi
da yaranki sun b'ata bana jin zai iy wanan ginin Dan Haka yanzu ki Bari daddare zanje wajen.Naseer da.kaina nace Masa nji a gari ance yaransa sun B'ata dagaske ne ko.karya ne"

Karki damu insha Allahu yaranki Basu B'ata ba

"Sun B'ata Mallam boyewa kawai Naseer keyi Dan Ni bansan Inda zai Kai yaran Nan hutu ba Dan Allah kubarni naje gidan

Dak'yar suka shawo kaina akan na Bari gobe naje gidan Dan dagewa nayi sai naje su Umma sun fito min da yarana.

Su Minal din ma rikesu nayi na dage akan wlh bazasu Kara komawa gidan ba Suma kuka suka ringa Yi wiwi akan bazasu tafi su barni ba dak'yar Mallam ya Basu Baki akan suje gida gobe Zanzo na daukesu da kaina Kuma karsu gayawa kowa sun gani ya hada musu da alewa dak'yar suka yarda suka tafi bayan na musu alkawarin zuwa gobe na tafi dasu

Duk da har ga Allah daga aunty har mijinta Dan sunmin fin karfine da wlh ba abinda zai Kara rabani dasu.

Ko gida ban iya komawa ba sabida har ga Allah gobe da sassafe Zan dira gidan Daga Umma har Naseer wlh sai sun Fito min dasu Nadeeya har wani zazzabi naji Yana neman rufeni.


Alaramma kuwa masu d'aukar karatu Wajen sa ne yasa a ranar Bai samu zuwa gidan ba nikam Dama yanda Naga Rana Haka Naga dare ko ya na Dan rufe idona sai Naga kamar Zahira da Nadeeya na kuka suna cikin wani Hali idan dai wani Abu ya samesu Nima kaina bazan yafewa kaina ba.


Da asuba naso dira gidan Sabida inasan na samu Naseer a gida

Sai dai Mallam.dake waje Zaune da almajirai yasa na koma ciki.


Aunty ma Ni haushinta nakeji da rarrashin da takemin ita kuwa ganin na matsu na fita yasa ta saka Hijabinta ta fita wajen Mallam ba jimawa kuwa sai ga ta dawo tana na tashi mu tafi.

Da Sauri na sab'a Waleed a bayana muka dau hanya bani burin daya wuce na Isa gidan

Muna kuwa Isa gidan ban tsaya wani buga k'ofa ba na hankada k'ofar na Shiga.

Naseer ne a tsakar gidan da tsintsiya Yana shara Umma Kuma tana daga bakin kofarta a zaune

Su Minal Kuma ma Kan tabarma suna Shan Koko da kosai

Naseer tsintsiyar hannunsa ne ya kubce daga hannunsa a lokacin da muka hada Ido dashi

Umma kuwa har tana tuntub'e wajen mik'ewa

Yarana kuwa Suka taso aguje suka rungumeni suna ihun Umma

Ni kuwa Raina a had'e nace "Naseer Ina Zahira da Nadeeya Naseer Ina ka kaimin su"?


Ko kallon.umma banyi ba da ke masifar uban me Nazo nema banma San ta zo kusa Dani ba

Naseer kuwa kamar.mai tsoron magana Naga Yana ta min magana da Ido.
Ni kuwa cikin Jin haushi.nace "Naseer Ina Zahira da Nadeeya nace Wlh Tallahi bazan yarda ba a yau sai an fitomin da yarana Naseer idan ba Haka ba wlh hukuma ce zata rabamu na rantse da Allah"


"Yaranki sun b'ata kiyi.abinda zakiyi Yar iska kaji Mara mutunci ke kadai Kika haifesu Naga shi Naseerun.yafiki iko Akansu shima ya fara d'aukar dangana ballantana ke din banza da baki ma San ciwon su ba kizo Nan kina Mana hauka kin Dade Baki hadamu da hukuma ba idan ma salon da Kika zo dashi kenan Dan ki dawo gidanan wlh bazaki dawo ba muguwa azzalluma daga fitarki Kika je kikayi wa yarona asiri duk ya tsiyace"


"Umma ba abinda zai Kara dawo Dani gidanan kince bakya Sona na rabu da danki na Kuma tafi Dan Haka a bani yarana na tafi dasu Kar a sake a yarda wani Abu ya Samu Nadeeya da Zahira Dan ba Abunda suka muku"


"Muje waje muyi magana Naeema "

Naseer yace a hankali kamar Mai ciwon makogaro

Tirjewa nayi Umma tayi ta auna min zagi

Aunty kuwa Taja hannuna mukayi waje Dan ta lura kamar akwai maganar da Naseer yake so yamin Amma baya so yayi maganar a gaban Umma.

Su Zahira kuwa kwandastan tambayarsu yayi Ina zasuje Suka ce Masa gadon Kaya sukayi shi kuwa yace ba Nan sukayi ba su dorayi sukayi Amma zasu dorasu a motar gadon kayan.

Zahira da Nadeeya kuwa sai juyawa suke suna kallon motar da Murja ta hau dake bin bus dinsu bumper to bumper

Sai da.suka iso junction bus dinsu ya tsyaa sabida su Dora su Zahira a motar gadon kaya Wanda Murja Kuma ta hau ya wuce

Sai da sukayi nisa ta lura da motarsu Zahira ya tsaya tayi saurin cewa akwai na Nan ta sauka da Sauri

Ta dawo Baya sai dai kafin ta Isa wajensu zahiran har sun samu motar gadon Kaya sun hau driver ma ko karbar kudin baiyi ba yace su barshi

Ahaka Murja ta Kara tare wani bus din tabi bayansu fatanta kawai ta Isa wajen su kafin suje gidan su su tona Mata asiri.

Sai dai duk Inda suka so tadda bus din su Zahira sai days Dan musu nisa.

Suna Isa junction din gadon kayan su Zahira Suka sauka da Sauri suka hau gudu

Murja dake ankare dasu tana ganin kwanar da suka Shiga ta cewa kwandastan akwai na Nan ta sauka da Bakin Sauri

Tana bawa.kwandastan kudi

Ta tari machine akan ya Shiga kwanar Nan ga wasu Yara can suna gudu Dan Allah ya ta dosu.

Su Zahira kuwa gudu.suke.suna fad'uwa.dan sunga hawanta machine

Ta kusa ci musu

Nadeeya ce ma Bata iya gudun sosai sai Zahira ta Dan jirata ahaka machine din Murjan ya taddasu ta Kai.hannu ta daki bayan Nadeeya tana Daga Bayan machine din duk da Yana tafiya.ce wa take su tsaya

Amma Ina Zahira da Nadeeya Kara gudun suka sa Dan sun fara hango k'ofar gidansu.

Murja kuwa sai kaiwa.mai machine duka take Akan yayi Sauri.

Ni kuwa Ina fita waje Naseer ya.jani gefe Yana k'ok'arin min magana Umma kuwa ta fito daga gida tana zagina tana surfamin zagi akan na bar Mata k'ofar Gidan da Ni kuwa na dage bazan bar k'ofar gidan ba wlh sai an fitomin da Nadeeya da Zahira.

Dukanmu ba Wanda ya lura Dasu Nadeeya dake nufomu suna tikar gudu

Tun kafin su iso naji suna kwalla Mana Kira Abba Umma

Muna juyowa suka iso a daidai lokacin da Naga wata Mata itama ta sauka daga Kan machine din ta damko Kafadun zahiran data cala wani uban ihu...........
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 40*

Idon Murja sosai ya rufe da San ta damke Zahira ta faffala mata Mari ko kad'an Bata lura da su Naseer dake tsaye ba ta daga hannunta da zumar wanka Mata Mari

Ni kuwa tundaga yanda nagansu a firgice hankalina ya tashi yanda ta damke kafadar Zahira yasa nayi wani super na Isa gabansu tana daga hannunta na tare Marin tare da rike hannunta na wancakalar da Karfin tsiya

Zahira kuwa ta taso aguje ta buya a bayana tare da kankameni jikinta na balain rawa.

Sai a lokacin Murja ta lura dasu Naseer da jikinsa ke rawa shima cikin tashin hankali ganin su Nadeeya da Zahira dake tikar gudu Murja na binsu a Baya


Jikinta ne ya dau rawa cikin tsoro ta zub'e a kasa tare da fashewa da kuka

Ni kuwa nace "Ke jahilar inace da Zaki biyo yara har gidan ubansu a gaban iyayensu Kuma ki nemi dukansu Mai suka Miki"?

Nace wa wacce ta biyo su zahiran da bansan dalilin dayasa ta biyosu ba banma San daga Ina suke ba

"Murja lafiya kuwa"?

Shine abinda naji Naseer yace Mata ita kuwa sai rizgar kuka take"

Tana k'ok'arin magana naji muryar Nadeeya data rungume kafafun Naseer ta Baya ta lek'o da fuskata tana "Allah ya isa tsakaninmu dake muguwa Azzalluma sai Allah ya saka Mana bazamu tab'a yafe Miki ba
Abba muguwa ce kullum sai ta dake mu ta d'auko wuka Wai sai ta kashemu Bata bamu abinci sai dai Wake da sabulu"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Nadeeya Mai na Miki da zakimin wanan Sharrin Yaya Naseer wlh karya take min tunda ka Kai su kullum sai sunyi kuka Akan suna San su dawo kullum sai na rarrashe su shine yau daga Shiga wanka na fito mak'ota sukace min gasu can sun gudu shine fa na biyosu har Nan Dan bana San wani Abu ya samesu Amma wlh ban musu komai ba"


"Wlh Abba karya take yi kaga shattin tsintsiyar kwakwan data dakemu dashi kaga Gefen fuskar aunty Zahira wlh muguwa ce yanzu ma sai data dakemu Wani Mai shago ya bamu kudi Akan mu gudu kafin ta kashemu"


Murja na k'ok'arin Magana

Hajara da tunda ta ga Murja ta daskare a tsaye

Ganin irin sharrin data kula musu Kafin su har gidan Tijjani irinsa take kulawan yanzu yasa ta daka wani uban tsalle ta tsaya Agaban Murja tana "Karya kike wlh shegiya munafika kafira makira Yar wuta duk abinda yarinya Nan tace wlh Zaki aikata tsaf Yau kinzo har inda nake kin sameni kin rabani da Dana kin sa ya koreni hakan Bai isheki ba sai kin taba jikokina toh wlh yau sai na Rama abinda kikamin"


Hajara tace tana cakumo rigar Murjan tare da ware murya ta hau kwallawa Safiyya dake daki tana bacci batare da tasan duk abinda ke faruwa ba yanda ta ware murya ne yasa Safiyya ta jiyota ta kuwa fito a guje.

Murja kuwa irin cakume mata Riga da tayi yasa ta mik'e tana "Umma Mai na Miki Dan Allah Mai na Miki kika tsaneni"


"Allah ya tsinewa bakinki albarka da kike KIRANA Umma dashi Ni da kika zaneni wanan Bai isheki ba Kika hada da makirci sai da muka bar gidan nida gidan Dana k'arfi da yaji Kika hanani abinci dayake bakida ta Ido ni Zaki kalla kicewa Umma Allah ya tsine Miki Murja Nan ma makircin zakimin kenan duk da babu idon Tijjani?

"Murja sosai.ta ringa Kai zuciyarta nesa Dan ji take kamar ta daga Hajaran ta maka da kasa Amma Bata San ta kwafsa sabida Naseer da ya saki baki Yana kallonsu

Hawaye ta hau yi cikin shesheka tana "Haba Umma kiyayar da kikemin har ya Kai Haka da Zaki min sharri"

Ke Amma bakida kunya Yanzu anan ma makircin Zaki mana"

Safiyya tace tana nada hannun rigarta


"Haba Umma"

Wani irin Mari Hajara ta d'auke Murja dashi sabida bakin cikin yanda Murja ke neman nunawa ita ta Allah ce

Murja kuwa ta dafe kumatunta tana Jin zuciyarta na zuwa wuya tana k'ok'arin Kara magana ta Kara kwashe Murja da.mari

Murja kuwa zafin Marin Yasa ta manta da wani Naseer da ke tsaye ta daga Hajara sama duk da uban cikin jikinta ta makata da kasa

Safiyya tayi Kan Murja ta hau Kai Mata duka

Naseer kuwa dake sallati

Ya nufi.kansu aguje Yana ihun Kar a tab'a Murja ciki ne da ita adaidai lokacin da Hajara ta samu ta mayar da.murja kasa ta d'ebo kasa.ta cusa a bakin Murja

Naseer kuwa ya wancakalar da safeeya ya ruk'o Hajara da k'arfi da itama kamar karfin aka Kara Mata sai ma k'ok'arin tak'e cikin Murja dake kawo Mata duka itama take.

"Cikani munafiki Ashe Dama gidan Tijjani ka Kai yaran Nan shine kacemin sun b'ata ka dagamin hankali Naseer Ni zaka yaudara Naseer Akan na Mori yaranka mu samu na rufin asiri gabadaya ka gwammace ka Kai su gidan azzalluma Nan makira har kazo kamin karyar sun B'ata Naseer Dan kawai Kar na Dora musu talla?

Tallan Dana Dora musu Dan wa na Dora musu Naseer ba Dan mu samu abinda yaran naka Zasu ringa ci bane tunda ka kasa Nemo Mana kudin kirki tunda shegiya matar Nan taka itama.ta bar gidanan ta asirceka komai naka ya tsaya cak daga Kai har Tijjani kun auro shegu tsinannu"

"Wlh Ni ba shegiya bace Umma kuma danki da kike magana ai na bar.miki shi tunda bana gidansa yanzu Yara Kuma da kike magana wlh a yau Zan kwashe su na tafi dasu Dan bazan Kara barinsu a gidanan ba Ni Zan iya kula dasu ke D'an naki ya kula dake kedai Umma ki nemo masa wacce ta kwanta Miki ki aura Masa"


Nace Ina rik'e da hannun Zahira Dana Nadeeya daga abinda ya faru.nagane Murja ce matar Tijjani tunda Naseer ya rik'e Umma.ta kwashi takalmanta tare da furzar da kasar da Umma ta cika Mata bakinta dashi.

Da sauri.ta hau tafiya tana rufe fuskarta da mayafi Safiyya kuwa har da diban dutse ta jefa Mata

"Karki sake Kimin rashin kunya in Banda kaddara Mai Naseer zaiyi dake Yara Kuma da kike magana ba Inda Zaki tafi dasu ko kwaki ya samo ya Basu suci so kike ki tafi da yaran sabida ya biyoki ko toh na Gane wayonki ba Inda zakije da yaran"?

"Wlh sai na tafi dasu Umma Banga uban da zai Hana ni tafiya dasu ba"

Nace Rai a bace tare da rike hannayen yarana nayi gefe dasu Nadeeya kuwa Naga ta Dan tirje

Naseer da idonsa ya kad'a yayi wani irin ja dak'yar ya bud'e bakinsa yana "ki tafi dasu Naeema Allah ya musu albarka"


Ameen nayi saurin cewa na fara k'ok'arin juyawa hannuna rik'e Dana yarana Zahira kuwa har tayi gaba.

Aunty ita Kuma tana rik'e da hannunsu Raheema.

Umma kuwa tace "Kace ta tafi dasu kana da hankali kuwa"?

Naseer Bai ce Mata komai ba

Illa ma hannunsa da ya mikomin Yana "Dan Allah Dan bani Waleed Naganshi Naeema"

Ban ma saurareshi ba duk da tausayinsa na nukurkusar zuciya ta


Aunty kuwa ganin na ma share shi na dau hanya zan tafi yasa ta saki hannunsu Raheema ta karaso wajena ta kunto Waleed Ni kuwa nace Mata "Kar fa ya hanani Dana"
Bata saurareni ba ta mik'awa Naseer Waleed

Waleed kuwa ya karbe shi da hannu biyu ya rungumeshi a kirjinsa adaidai lokacin da hawaye suka zubo Masa yayi saurin d'auke hawayen ya sumbaci Waleed a goshi Yana "Allah ya maka albarka Naseer"

Daga Haka ya mik'awa Aunty shi

Ya kalli Zahira da har sunyi gaba Yana "Ba Sallama Zahira Raheema.humaira bazaku zo kumin Sallama ba"

Da Sauri duk.suka nufi wajensa ya sunkuya ya rungumesu ya shafa kansu gabadaya har da Nadeeya dake gefensa yace "Maza kubi ummanku ku tafi kunji Allah ya muku albarka kuringa yiwa Abbanku addua Allah ya bashi kudi kunji"?


"Abba bada Kai zamu tafi ba"?

Nadeeya tace hawaye na cika Mata Ido adaidai lokacin da su Zahira suka.dan Kara yin gaba Dan suna tsoron Naeema ta tafi ta barsu

Murmushin karfin hali Naseer yayi Yana "badani zaku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login