Showing 102001 words to 105000 words out of 180103 words

Chapter 35 - NAGA TAKAINA COMPLET BOOK by Sadnaf.txt

Sadnaf   

17 Sep 2025

2502

Aunty Dan Allah kiyi hakuri karki yanka mu"

Zahira tace tana fashewa da kuka.

"Toh wlh idan Tijjani ya dawo kuka ce na muku wani Abu kukace na Hana ku abinci na rantse da Allah sai na cire muku Ido kunji na rantse muku idan ya dawo kuce Masa kunci abinci Kun koshi ke Kuma da ganinki kin iya munafirci Abu kad'an sai ki hau hawaye wlh ya dawo kikamin wanan kalar tausayin gobe Yana fita sai na yanka ki kunji Mai nace ko bakuji ba"?


Gyada.mata Kai sukayi a tare Dan har ga Allah sun yarda zata yankasun sabida yaran da akwai tsoro ba Kamar na yanzu ba sai a lokacin ta barsu suka zauna a Palo.

Duk a tsorace Suka Kamar su zura da gudu

Ana Kiran Sallah magriba Tijjani ya dawo

Murja tayi sauri ta jawo Nadeeya ta kwantar da kanta a cinyarta

Ta hau shafawa tana "in cigaba da muku tsatsuniyar"?

A daidai lokacin da Tijjani ya shigo Niki Niki da ledoji

A hannunsa

Nadeeya kuwa sai mutsu mutsu take sabida danneta da Murjan tayi a cinyarta tana shafa Mata Kai

Tijjani kuwa washe baki yayi Yana "Uwar biyu keda yaran naki ne kuke Hira"?


Murmushi Murja tayi tana "wlh fa Wai tsatsuniya nake musu ai ba karamin dadi naji ba da zuwansu Dan wlh suna ta deb'emin kewa da sai dai nayi zuru Ni kadai kamar Mayya Nadeeya dai tafi yayarta wayewa Dan ita ta saki jikinta ita kuwa yayarta sai noke noke take Taki sakin jikinta"

Murja ta karashe a daidai lokacin da Tijjani ke amsa gaisuwar da Zahira take Masa kanta a sunkuye
Nadeeya itama gaishe shin tayi a lokacin da Murja ta daina shafa kanta ta mik'e zaune.

Shi kuwa Tijjani cikin Jin dadi ya amsa gaisuwarsu Yana "Ai Zahira Haka take tana da wuyan sabo ko gidansu Kikaje Bai zama lailai kiji maganarta ba har ki dawo

Nadeeya ce dai ba ruwanta.

Kuzo maza kuga kayan Dana siyo muku Tijjani yace Yana janyo katuwar ledar daya shigo dashi.

Murja kuwa kamar ya caka Mata wuka Haka taji a lokacin da ya jawo ledar ya bud'e

Nadeeya kuwa tuni ta Isa wajensa

Zahira kuwa ko dagowa batayi ba ballantana taje Inda yake zaune

Ki taso Mana Kika zauna.

Murja tacewa Zahira cikin murmushi yak'e dayafi kuka ciwo

Zahira kuwa jikinta na rawa ta Isa wajen Tijjani ta zauna a wajen kafarsa

Nadeeya kuwa a gefensa ta zauna

Tana murna da ganin kayan data ke kyautata zaton nasu.ne


Kaya ne masu Dan saukin kudi guda shida shidda iri daya

Sai takalma guda biyu brush biyu har da Mai da Dan turarensu.

Bai tsaya iya Nan ba har da yatsana ya siya musu.

Kamar an cinnawa Murja wuta haka ta ringa ji sai juye juye take ita kadai ita da take d'auke da ciki Tijjani ko pant Bai siya na jariri ba Amma ya laftowa su Zahira uban Kaya

Nadeeya kuwa tsalle tsalle kawai take akan kujeran tana murna yartsana da aka siyo musu shap tama manta da wata Murja a palon balle ta tuna dukan dataci.

Zahira ce ma ta kasa sakin jiki ta ringa satar kallon Murja dake musu wani Irin kallo


Manyan biscuit ya d'auko ya bud'e musu ya bawa kowace guda guda Yana maza suci

Nadeeya da Zahira kuwa sukayi ta mishi godiya

Har wani Dan hawayen bakin ciki ne ya Dan taru a idon Murja

Tana hada Ido da Tijjani ta kakalo murmushi tana "gaskiya ka kyauta Allah ya Kara budi dama dazu nake ta ce wa Basu zo da Kaya ba ko Mai zasu saka"

"Aikuwa gashi na samo musu Wanda zasu ringa Dan sawa Kafin na Karo musu idan na samu kudi.

Ga ayabar da kikace na siyo Miki ga Kuma balangu Nan Leda biyu ki dau babbar ki bani dayan

Murja Haka ta mik'a Masa ledar kamar ta kurma ihu

Tijjani kuwa ya bud'e ledar balangu ya Ajiye Agaban Zahira Nadeeya ta sauko ta hau CI

Zahira kuwa sai juye juye take tana satar kallon Murja a tsorace sai da Murja ta tafi dauko abincin ta iya Kai Naman bakinta.

Nadeeya kuwa ko kallon murjan batayi ba tayi ta Loma balangun

"Murja kuwa abincin ta d'auko ta zuba Masa faten wake da doya Dan Tijjani Yana balain san faten wake da doya

"Aaa Yau Mai dadin Kika Mana kenan"

Zahira maza ku tashi ku wanko hannun ku muci abinci"

Caraf Nadeeya tace "Ai bamu iya cin wake ba"

"Mun koshi Abba dazun Nan mukaci abinci"

Zahira tace cikin rawar murya

"Shaf na manta fa Baku iya cin Wake ba laifina ne da ban gayawa Auntynku ba"


"Ai sun gayamin Dama danake girkin hakane yasa na dafa musu taliya sukaci

Kallon da tayiwa Zahira ne yasa Tijjani na tambayarsu sukayi saurin cewa sunci.taliyar.

Nadeeya kuwa ta maida hankali ta cinye biscuit din da balangu Zahira kuwa tsatsakura tayi sabida tsoro.
Ahaka lokacin kwanciyarsu yayi sukayi shiga daki suka kwanta

Murja kuwa dak'yar tayi bacci sabida bakin ciki.
Washegari Tijjani na fita

Tayi wa Nadeeya mugun duka ta Kara saka su aiki kamar Jiya har dasu wanki Wanda a tunaninta wahala take basu Bata San sun Saba da aikin ba .

Kayan ma kwacewa tayi ta karya ita kadai batare da ta Basu komai ba

Zahira kuwa bredin da suka boye na jiya Suka ci a boye Dan guntun biscuit din ma ta kwace.

Sai data Kara turasu debo ruwa Dan duk a tunaninta a makabartar suka je jiya Nan kuwa Inda suka je jiya Nan suka debo ruwan

Jamilu kuwa Mai shago daya gansu Basu tambayeshi ba ya Basu kyautar biscuit da lemo suka boye a jikinsu

Suna zuwa suka ga ta d'ebo wake ko tsincewa batayi ba ta Dora waken Mai uban yawa ta daka attaruhu ta zabga a ciki

Sai daya dahu ta d'auko Sabulun Canoe data jika tun safe ya narke "(nasan mutanen da zasu Gane koren sabulu Canoe Zahira da wayonta lokacin ita ke bani wanan Labarin Nadeeya ma Bata manta komai ba)

Juye canoe din tayi a cikin waken ta gwamutsa ta d'auko wani farin roba Mai Dan Fadi ta juye a ciki ta saka a fridge ta kalli Zahira da Nadeeya tana "Daga yau wannan shine abinci ku Badai bakwa cin wake ba shegu tsinanu Zakuci ubanku ke Kuma na rantse da Allah idan kina wanan rawar Kan Agaban mijina kina surutu da wanna shegn bakin naki sai na yankaki ta karashe tana rankwashin Nadeeya

A takaice karfe shidda ta zubo musu waken

Akan suci

Zahira kuwa ta ki ci tace ta koshi
Nadeeya kuwa duk da Zahira nata Mata Ido Akan Kar taci

Nadeeya a Haka ta zauna taci waken Nan Yana d'ade Mata harshe tare da soya Mata zuciya
(Wani ikon Allah ba abinda ya samu Nadeeya tana Nan da ranta har yanzu har da yaranta ma )

A takaice sosai Murja ta bud'e babi babi na mugunta tana ganawa su Zahira Tijjani Bai taba Sani ba Dan idan ya kusa dawowa sawa take suyi wanka ta dauko musu kayan da ya siya musu da Yar tsana akan su ringa Wasa dashi shi kuwa Tijjani idan ya dawo Baya ganewa sam

Sosai take musu horar yunwa Zahira ta ringa wani irin Rama.

Indai ta saka wani abu a bakinta jamilu Mai shago ne ya Bata Nadeeya kuwa haka take dirkawa kanta faten wake Mai Sabulun Canoe tayi ta Kashi
Ga uban duka da take musu da sun danyi wani kuskure.

Kullum mak'ota sai sunji ihunsu Zahira.

Tana dirkarsu

A Haka har jamilu Mai shago da abin ya ishe shi sabida tausayinsu Zahiran.yaje har gidan ya kwada Sallama Murja na fitowa ya hau Mata masifa Yana "Kiji tsoron Allah ki daina zalintar yaran Nan idan babu idon iyayensu Allah daya hallicesu Yana kallonki Banda mugunta Mai yaran Nan suka tare Miki da kike musu irin Haka "


"Ina ruwanka Shugaban munafikai ko kashe su nayi Ina ruwanka ka Shiga uku da munafirci wlh ka ficemin daga k'ofar gida kafin na debbo ruwan zafi na watsa maka"

Murja tace cikin masifa

Jamilu zaginta ya cigaba da yi Yana rantsuwar akan sai.ya hadata da hukuma ya kaucewa ruwan data watso Masa ta rufe kofarta

Tana Shiga ciki tayi.kan Zahira da Nadiya ta hau duka Akan sun Kai kararta wajen Jamilu.

A ranar Kuma jamilu yayi ta jiran dawowar Tijjani Dan ya Gaya masa sai Tijjani Bai dawo da wuri ba har ya tashi

Washegari Kuma daya fito Tijjani ya fice.

Karfe takwas yaga Zahira ta fito ita da Nadeeya da bokitan ruwa Akansu

Shi kuwa ya kirasu

Suna zuwa yace "idan na Baku kudin mota zaku iya komawa gidanku"

Da Sauri Zahira ta gyada Masa Kai tana "a gadon Kaya gidanmu yake indai aka saukemu a junction xamu iya xuwa gidanmu a kafa Dan Allah ka taimaka Mana da kudin motar"

Naira Hamsin Jamilu ya d'auko ya bawa Zahira Yana ta ajiye bokitin ma yanzu ta rik'e hannun Nadeeya su gudu.

Ai Zahira da sauri suka dire bokitin ta rik'e hannun Nadeeya suka fara tikar gudu suna wuce gidan Murja ta bud'e kofa Dan ta siyo Madara aikuwa ta hango su Zahira na tikar gudu.

Itama binsu ta fara Yi agujen Taji kafarta ya rik'e.

A daidai lokacin da wani mai vespa yazo wucewa tayi saurin tsayar dashi Akan ya taimaka Mata subi bayan wadancan yaran guduwa zasuyi

Da Sauri ta haye vespan Zahira kuwa Tana ganin Haka ta Kara rike hannun Nadeeya suka cigaba da tikar mugun gudu suna zuwa titi wani bus na k'ok'arin tafiya Zahira.kuwa ta daga hannu biyu ta hau tsyaar da kwandastan

Yana tsayawa suka Shiga motar da Sauri a daidai lokacin da Murja ta sauka itama daga Kan vespan ta hau tsyaar da kwandastan Zahira kuwa ta hau rokansa Kar ya tsaya kashe su zatayi basu kuwa tsaya ba driver ya ja bus din Suka tafi

Murja kuwa ta tari wani bus din tabi bayansu.......



Wlh biki muke wata danake Jin kunya sisi mama ta roki nayi typing ko ba yawa to gashi Nan nayi da yawa
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 39*



*Naeema*


Wani irin rashin lafiya Waleed ya ringayi daya dagamin min hankali duk yanda naso zuwa gadon Kaya gidan Aunty Dan Naga yarana sai ban samu zuwa ba sabida zaryar asibitin da nake fama dashi wani irin kuraje ne suka feso Masa kananu ga Kashi da yake yawan yi.

Ko no-no sai nayi dagaske yake Sha shima Yana Sha wani zubin Haka zai ta kwara amai daddare kuwa Haka nake zaman dirshan Ina jijjiga shi Dan kuka yake kwana yi duk magangunan da nake bashi Banga alamar Yana Jin sauki ba sosai hankalina ya rabu gida biyu ga na rashin lafiya Waleed ga na yarana danakeji Kamar na mutu sabida kewansu.

Idan bacci ya saci daukana kuwa Haka Zan hau mafarki dasu Zahira suna kuka suna mikomin hannu wani zubin Kuma Wai sai Naga suna gudu wata Mata na binsu da wuka.

Sosai nakejin Kamar yarana suna cikin mawuyacin Hali ya zama Dole naje Koda kuwa Waleed din bashida lafiya.

Sai dai abinda ya hanani zuwa gidan aunty shine wani Mai maganin gargajiya da aka hadani dashi da ke hanyar Zaria da akace na Kai waleed wajensa zai Samu lafiya idan dai na Kai shi Dan Kamar cutar tasa Bata asibiti ba.

Banso zuwa ba sai da hassana ta dagemin akan naje suna da dangi acan na sauka a gidan

Har mai maganin ya Gama duba waleed Dan idan dai kaje baya Bari ka taho sai yaga alamar maganinsa ya maka aiki.

Baa San Raina ba Haka muka je kauyen da Waleed da kwatancen da Hassana tamin na Isa gidan yan uwansu


Da wata a gidan ta rakani wajen Mai maganin yana duba waleed kuwa ya hau hadamin magangunan gargajiya Yana a cikin kwana uku insha Allahu zanga canji na ringa kawo shi safe da yamma.


Cikin Ikon Allah kuwa da fara amfani da maganin Naga Waleed ya fara samun sauki

A madadin kwana uku Dana so yi sai gashi sai danayi satin

Sati dayan Nan danayi Allah yasan baa nutse nake ba ba kuma a hankalina nake ba sabida tunanin yarana Dan ban fasa mafarki dasu ba.


Ni nasan mafarkina wani zubin yana Zama gaske duk da Ina Taya yarana da Addu'a ya zama Dole Ina komawa naje na gansu.
Haka kuwa akayi Ina dawowa washegari da sassafe na goya Waleed na saka nikab na nufi gadon Kaya

Gidan aunty na Isa kaina tsaye.

Lokacin zuwansu makaranta baiyi ba hakane yasa muka ringa dan tab'a Hira da ita hankalina gabadaya Yana Kan agogo uku na yi kuwa Yara suka fara cika k'ofar gidan

Ni kuwa tsabar matsuwa San naga yarana haka na saka nikaf naje na tsaya a bakin kofa Ina kallon duk Yan makarantar da suka ringa zuwa .

Duk yanda aunty tayi dani Akan na zauna na ci abinci Kar na damu har cikin gida zata kirasu k'in saurarenta nayi ahaka nayi tsayuwar awa daya kafin na hango Minal Humaira da Raheema sun nufo makaranta hannunsu rik'e Dana juna.

Uniform dinsu yayi wani irin dati ko wankewa baayi ba bana Jin ma ko wanka sunyi Raheema ma sai tsince tsince take a kasa tana kaiwa bakinta Minal na hanata.
Hawaye.ne Suka hau zubomin kirjina na bugawa da Sauri wai da Raina yarana Suka Zama Haka toh Ina Zahira da Nadeeya

Na Kara dage wuyana ko Zan gansu daga bayansu sai dai Banga Mai Kama dasu ba har su Minal din Suka karaso suka zauna Akan tabarma sosai naji hankalina ya tashi na fara k'ok'arin fita wajensu.

Aunty dake gefena a tsaye ta rikemin hannu tana na koma ciki Bari ta fita ta kirasu.
Da sauri na Shiga palon aunty na zauna sosai na matsu da su shigo gashi aunty ta Hana ni cire nikaf din fuskata


Tunani kawai nake mai ya Hana su Zahira zuwa makaranta ko Aiki Safiyya da Umma suka saka su shiyasa Suka Hana su zuwa.ko dai Kuma dukansu ma Safiyya ko Umma keyi amma idan Naseer ya Bari aka ci zallin yarana bazan yafe masa ba sosai hawaye ya jika nikaf Dina Waleed kuwa na Kan kujera Yana ta baccinsa

Shigowar Aunty dasu Minal ne yasa na Kara Jin bugun zuciyata ya Karu ahaka na ringa rarraba idona Akansu tausayin yarana na rufeni sunyi wani cirko cirko dasu Kamar basu ba

Kamar na Isa wajensu Naga Aunty ta girgiza min Kai

Na daure na zauna na cigaba da kallonsu Ina adduar Aunty ta musu tambayar dake Raina

Abinci Aunty ta d'auko musu a faranti


Tana direwa suka hau ci Kamar wayanda Basu tab'a cin abinci ba aunty a gefena ta zauna ta Dan matsa hannuna sabida sheshekar kukana dake fitowa Ana ji Dan sosai naji zuciyata ta karye da ganin yarana a yanayin Nan


Dubi yanda Raheema ta zama bak'a yarinyar da duk yayana ba Mai farinta

Dayake cire hijabinsu sukayi kitson kansu ma ya balain tsufa ko tsagan baa gani

"Minal Dama Baku ci abinci bane"?

Aunty tace tana Kara Dan tattab'a hannuna alamar Kar nayi magana

"Munci bamu koshi bane"

"Waye ya Baku abincin"

"Mama ce ta bamu"( Haka suke cewa Umma )


"Ina Abbanku"?

"Baya Nan ya fita da sassafe "

"Bakuje makarantar boko bane"?

"Eee bamuje ba an koremu kudin makaranta"


"Ina Zahira da Nadeeya ya Banga sun zo makaranta ba sai ku kadai"?

Kirjina wani irin bugu yake a lokacin Dana ga Minal ta kalli Aunty tare da cire hannunta daga cikin abincin tana "Abba da Mama sunce sun b'ata mun daina ganinsu Aunty
Ummanmu ta tafi ta barmu Aunty zahira.ma da Nadeeya sun tafi sun barmu ba Mai Mana wanki da wanka kullum sai abbanmu yayi kuka daddare"?


"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aunty nashiga uku na lalace yarana sun b'ata Zahira da Nadeeya sun Bata fa"

Nace cikin azabar tashin hankali Ina mik'ewa tsaye

Muryata dasu Minal sukaji yasa suka Mik'e a tare cikin ihu sukace "Ummaaaaa"


Bansan lokacin Dana fashe da wani irin kuka ba na fusge nikaf din fuskata na durk'ushe na fara kuka

Yarana suka debo aguje suna ihun Umma Suka zo suka rungumeni gabadaya.

Minal kawai na iya rik'ewa Ina "Minal Mai kikace Kika ce Zahira da Nadeeya sun b'ata kamar ya sun b'ata Minal kinsan.mai kike cewa kuwa tun yaushe suka B'ata"?

"Umma sun Dade da b'ata mama ce ta Dora musu talla abinci shine Basu Kara dawowa ba Naji Abba yace an sace su"



Wani irin mik'ewa nayi na fara k'ok'arin nayi waje da gudu Aunty kuwa ta rik'eni Gam Ina "Ki cikani Aunty wlh yau sai dai su kasheni kina ji Zahira da Nadeeya sun B'ata aunty ta yaya yarana zasu B'ata wlh bazan yarda ba sun Dade suna min Abu Ina kyalesu Amma wlh bazan yarda su b'atarmin da yarana ba Mai na musu Haka suka tsaneni wlh gidan zanje aunty ki cikani"


Nace Ina ihun kuka Aunty kuwa ganin dagaske nake Yasa ta Kira alaramma mijinta


Ina balain Jin nauyi da kunyarsa Yana shigowa na nutsu Amma ban fasa kukana ba sai Kiran nashiga uku na lalace nake ko Waleed dake kuka ban kalla ba sai aunty ce take jijjiga shi su Minal kuwa manne min sukayi suna tsoron Kar na Kara tafiya na barsu

Aunty ce ta Kora Masa jawabin abinda ke faruwa

Shi kuwa cikin mamaki yace "Sun b'ata fa sukace Amma ai muna gaisawa da Naseer din Bai taba cemin sun b'ata ba Dan ko shekaranjiya Dana Kara tambayarsa yasu Zahira suka daina zuwa makaranta cemin yayi hutu ya Kai su Banga Kuma alamar tashin hankali a fuskarsa ba

Cikin kuka nace "wlh b'oyewa yake bayaso aji labarin sun b'ata Dan yasan zan iya jin labari Mallam nasan wacece uwar mijina wlh zata iya b'atarmin da yarana Dan Allah ku barni naje gidan da kaina su fitomin da yarana Haka ma Suka tab'a batar da Nadeeya dak'yar aka ganta Dama sun tsanesu Dan Allah Mallam kubarni naje da kaina"


Na karashe cikin ihun kuka Ina dafe kirjina Dana ji Yana min suya Wai yarana sun b'ata da Raina aka dorawa yarana talla Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun

"Ki kwantar da hankalinki Naeema Bari na tura mmn Sadiya ta je gidan da kanta mubi komai a hankali insha Allahu Ina kyautata zaton hutun ya Kai su basu b'ata ba Bari taje ta dawo Muji ya sukayi da Yan gidan

Nidai Dan yamin Dole ne da tuni na kusa Isa gidan.

Aunty kuwa Hijabinta ta zura tayi waje.
Yarana kuwa Suka hau bani labari irin rayuwar da sukeyi da su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login