Showing 132001 words to 135000 words out of 180103 words
jikina na rawa kasa mik'ewa nayi Dana zub'e a tsakiyar dakina.
Kamar Wasa naji shigowrta tare da rufe k'ofar Gidan.
Kitchen naji ta shiga Ni kuwa na hau sauke ajiyar zuciya dawowa da tayi
Shigowa tayi da kwanu a hannunta daya hannun nata Kuma ledar tuwon ne.
Kamshin abinci yasa naji jikina ya Kara kwasar wani rawan
Ina kallonta ta juye tuwon ta zuba Miya a wani kwanun shima ta kawo shi gabana tana "Umma gashi na samo Miki abinci kici Bari na d'ebo Miki ruwa ta Kara yin waje.
Ni kuwa banyi wata wata ba na hau Danna tuwon a bakina Ina hawaye.
Dan inaganin tsaf Zan sume da ban samu tuwon nan ba fada nayi niyyar Mata Amma Ashe abinci taje Nemo min
Kafin ta kawo ruwan ma har na kusa cinye Rabin tuwon
Sai da tuwon ya kusa karewa naji hankalina ya dawo jikina jikina ya bar rawa.
Ruwan data ajiye a gabana na kafa kaina na Sha
Koshin da nayi yasa nayi hamdala a madadin nayiwa Zahira fada sai na hau shi Mata albarka Ashe dai yunwa masifa ce Dan sai yanzu na dawo daidai
Abinan da Zahira.tamin a matsayin ta na diyata Yana cikin Abubuwan da bana mantasu ahaka tana yarinya tasan tausayin iyaye inaga ta girma.
Amma Wai Zahiran Kuma su Umma ke San ganin Bayan ta Mai ta musu da zafi Haka
A dadafe na yi sallah asuba
Na tashi yarana sukayi Zahira kuwa ce Mata nayi kaina ke ciwo badan ta yarda ba ta hakura ta daina min tambayoyi.
Yanzu su suke min komai hakan yasa ban bar d'akina ba Suka had'a hannu Suka Gama aikin komai na gidan suka fara shigomin d'akin Akan sun shirya zasu tafi
Kansu na dafa daya Bayan daya Kamar yanda na Saba na musu addua suka ringa yin waje sai Dana Zo kan Zahira nace "Zahira kiringa addua kinji Allah ya kareki daga sharrin mutum Dana Aljann kiringa karanta ayatul kursiyyu Kafa bakwai idan Zaki bar gidan Nan idan kin dawo ma ki karanta ki kasance a cikin addua kullum Allah ya kareki da karewarsa karkiyi Wasa da Addu'a kinji Zahira Allah ya Miki albarka ban taba nufar Dan kowa da sharri ba insha Allahu ba Abunda zai sameki ki tsaya kiyi alwala sai ki tafi"
Kallona kawai take har na idda maganata amadadin tayi wajen sai ta tsugunna daidai k'afata tana "Umma ko dai wani abune zai sameni dazu da nake shara Naga kwai a cikin kwarya da sunayena"
Girgiza Mata Kai nayi da Sauri tare da mik'ewa.
Ina "ba Abunda zai sameki Zahira Kar ki Kara kallon Inda Kwaryar Nan yake Abbanku nake jira ya dawo maza jekiyi alwala ki tafi karku makara"
Na nufi wajen Dana ajiye Kwaryar da shima yake d'auke da Jan rubutu da sunan Zahira na d'aga katakon gadona na saka a karkashin gadon Dan so nake idan Naseer ya dawo na nuna Masa Yaga shaida wlh bazan d'auki a tabamin Yara ba"
Yanda nake Jin jikina ma kamar na Hana Zahira. Tafiya makaranta Dan sosai nake a tsorace gani nake zasu iya binta har makaranta su Mata wani Abu Amma ba yanda Zan hanata tunda Bai fi sati biyu su zanna jarrabawa Gama jnr secondary ba"
Har waje na rakasu Bayan tayi alwala yanda take Abu jiki ba kwari yasa na kwantar Mata da hankali har na daina hangosu gabadaya zuciyata ba dadi Haka na dawo gida
Ina kukan tashin hankali da nake ji a jikina Yana tunkaroni a da na dauka na samu kwanciyar hankali Ashe akwai wani masifar dake tunkaroni bansani ba
Masifar da nakeji zuciyata bazata iya dauka ba idan har su Umma suka ci Galaba Akan Zahira ga irin abinda nake gayawa Naseer Nan da har yake Jin haushina.
.
A ranar kasa komai nayi zuciyata na wajen su Zahira abincin rana ma ban iya Yi ba karshe dai waje na fita Dan sosai naji na kasa samun kwanciyar hankali sai Dana hangosu hankalina ya kwanta na koma ciki na daura alwala azahar.
Ina iddar da sallah na fito na Dora musu farar taliya Dan inada Miya
Sai a lokacin na daure na saka Abu a bakina shima Dan Kar Zahira ta zargi wani Abun Dan nasan halin ta
A takaice ahaka na ringa dari dari indai su Zahira suka tafi makaranta sai sun dawo hankalina ke kwanciya
Bacci Kam bana Iya yin shi cikin nutsuwa Rabin Daren rayya shi nake Ina kaiwa Allah kukana haka ma nake tashin Zahira tayi duk da Bata iya jurewan tana Yi sai dai na juya naga tayi bacci
Ban iya larabci ba da hausa nake adduoina Dan nasan ba yaren da Allah baya ji Yana jina Yana Kuma ganin duk abinda ke faruwa Dani Allah yasan zuciyata tayi rauni bana Jin Zan iya jure ganin wani Abu ya Samu yarana da nake ganin su kadai ne farinciki na a gidan Duniya a lahira kuma Allah ya bani Aljanna.
Har wani irin Rama nayi Sabida tashin hankali Dan idan dare yyi Haka Zan ta sintiri daga d'akina zuwa kofar gida Wai ko zasu Kara aiko wani.
Duk da ban Kara ganin kowa ba sabida dadewar da akayi hakan bai saka na saki jikina ba
A ranar laraba da bazan manta ba na Kara sanin suwaye Umma Ina zaune a tsakar gida Ina tsince wanke da Zan Mana abinci dashi ba kowa a gidan Dan dukansu sun tafi makaranta Isihu ma ya tafi wajen Aunty matar Mallam zai Kai Mata sako
Sai dai idan anzo siyan Abu na Shiga ta tsakar gida na bada abinda aka zo siyan.
Sallama da naji da yazo daidai da bugun zuciyata yasa na Dago bakina d'auke da Addu'a na amsa Sallamar a daidai lokacin da Wata Saude da take makociyarmu ta shigo makociyata ce data takuramin da karbar kayana Bata bani kudi hakane yasa Dana gaji na daina Bata shima su Nadeeya ne suka cemin tana zuwa wani shagon siyan Abu da kudi shagona ne take aikowa karbar bashi ko a yanzu ma data shigo bazan iya tuna adadin kudina dake wajenta ba.
Cikin sakin fuska na Mata iso dana ga fuskarta a sake tana sanye da dogon hijabi hannayenta a ciki.
Tabarmar danake Kai na Kara bajewa Ina "Zauna Mana mmn maimuna"
Cire takalminta tayi ta hau Kan tabarma ta zauna tana "mmn Zahira Ina wuni"
"Lafiya Lau ya su maimuna"?
"Suna Nan kalau"
Tace tana cigaba da jujuya hannu a cikin hijabi Ni Kuma Haka kawai naji zuciyata na bugawa bansan dalili ba.
Adduoi kawai nake a Zuciyata ita kuwa tayi shiru Bata ce komai ba
Ni kuwa nace Mata lafiya Dan bata Saba shigomin ba balle nace shigowa tayi Dan mu gaisa
Murmushi tayi tana lafiya Lau shigowa kawai nayi mu gaisa
Ni kuwa da zuciyata ke cigaba da bugawa nace mata ta kyauta na mike na Shiga kitchen na debo Mata ruwa a Raina Kuma inata addua fad'uwar gaban da nakeji tunda ta shigo Ina Kuma mamakin dalilin zuwan nata da Sam ban ji na yarda da ita ba
Agabanta na ajiye ruwan Ina "Bismillah ga ruwa"
Girgiza min Kai tayi da Sauri tana ta koshi har lokacin hannunta na cikin hijabi tana Dan kalle kalle
"Ke kadai ce kenan a gidan banji Motsin su Zahira ba"?
Tace cikin murmushi Nima cikin murmushi nace Mata eee wlh Ni kadai ce.
Sallama ake ta rafkawa ana San siyan Abu Amma fir naki tashi Dan Sam ban yarda da Matar Nan da ta shigo min ba ita kuwa cewa take na tashi Mana na sallami customers Dina Ni kuwa na girgixa mata Kai Ina "ba wani abin arzkik zasu siya ba abinda ma suke nema babu"
Na karasa Ina karantar yanda tayi Jim Bata ji dadin magana ta ba Hakan kuwa yasa na Kara gasgata zargin ba alheri ne ya kawota gidana ba.
Zama na gyara sosai Ita kuwa ta cigaba da kame kame tana surutun ta ita kadai
Ni kuwa jinta kawai nake Ina mamakin abinda yasa ta saka hannayenta a hijabi Sanin Dana Mata ma ba ma'abociyar saka hijabi bace ban dai ce komai ba na cigaba da wayancewa kamar gyara waken nake Amma idona na kanta
Muryata daya doki kunnena da "Mmn Zahira wlh fitsari ne ya matseni Ina bandaki nayi Dan Allah"
Sosai naji kirjina ya tsananta Bugu jikina na kwasar rawa
Sai Dana dau mintina kafin na iya nuna mata band'akin Tsakar gidan
Mik'ewa tayi da Sauri har lokacin hannunta na cikin hijabi ni kuwa nace Mata "Ga buta Nan da ruwa a ciki babu ruwa a band'akin
Wajen band'akin ta nufa da Sauri tana ta mutsu mutsu da hannu
Kafin ta Ciro hannu daya ta sunkuya ta dauki butar a garin ta mik'e Naga wani irin dunkullellen laya ya Fad'o
Yanda layyan ya Fado Haka naji Kamar kirjina xai Fado.
Da Sauri ta tsugunna ta rufe layyar da hijabinta ta d'auka tana k'ok'arin Shiga band'akin
Cikin zafin nama na taso kafin ta karasa band'akin na jawo
doguwar hijabinta da karfi da har sai daya shake Mata wuya na Kara jawo hijabin har sai data zub'e a kasa
Banyi wata wata ba na Kara shaketa da hijabin Dana cukwikuye burinta kawai ta cire hijabin Dana shaketa dashi Sabida matsar Dana Mata
Azaba yasa ta saki layyar
Bansan inada karfi ba sai a ranar saman kanta na hayye har lokacin Ina shake da ita na dau daya hannun nawa dake balain rawa bakina d'auke da Addu'a na Dago layyar da aka caccaka allurai a ciki ga sunayen Zahira Nan a zagaye da layyar.
Ihun sallati na saka na saki layyar Cikin tashin hankali na Kara shaketa da hannu biyu cikin kuka na hau ce Mata "Mai na Miki mmn maimuna da kike San ganin bayana Ashe kece kike San ganin Bayan Zahira Basu Umma ba Mai na Miki da zafi Haka Mmn maimuna da kike San ganin Bayan Yata a iya sanina ban miki komai ba hasali alheri na Miki kika zalunce Ni
Mai na Miki Haka Mmn maimuna Mai Zahira ta Miki"?
Nace cikin kuka Ina Kara shaketa da k'arfi sai kakari take Ni kuwa na hau jibgarta Ina buga kanta da kasa rantsuwar da nake akan wlh sai ta gayamin Mai Zahira ta Mata yasa take San ganin bayanta da irin shakar Dana Mata yasa cikin azaba tace na saketa zata fadamin
Ban cikata ba nace ta gayamin a Haka Ina jinta ko kuma wlh na dauko wuka yanzu nan na kasheta
Dan sosai na ringa Jin Zan iya kasheta yanda nake Jin zuciyata daga makotaka Mai hadina da ita da zata nemi cutarmin da ya
Ganin magana na Mata wuya yasa na sausauta rikon Dana Mata a wahalce tace "wlh bani bace Mmn Safiyya da Safiyya ne Suka Sakani wlh Allah ranan ma da muka zo k'ofar gidan nan har da Safiyya muka zo.
Tiryan tiryan ta hau bani labarin komai batare da ta rage komai a ciki ba har alewar da suka so bawa Zahira na sata da Abu ya juye ya koma Kan Dan safiyya da Maimunan
Sosai jikina ya dauki rawa na hau sallati........
8/19/21, 10:32 PM - My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*
*NA SADNAF*🌸🌸
®? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 51*
Rawar da jikina keyi yasa na cikata na zub'e a kasa Ina juya Kai na danake ji kamar zai fado kirjina kuwa sama da kasa.kawai yake ita kuwa numfashin wahala kawai ta ringa saukewa tana "kiyi hakuri mmn Zahira Safiyya ce ta ringa zugani wlh a yau din ma kamar bazan zo ba taje har gida ta sakoni agaba Akan Nazo da kaina"
"Da kin shiga da layyar band'akin Nan Ina Zaki saka layyar Kuma Mai zai biyo baya ki gayamin mmn maimuna"?
Nace Ina tsareta da idona Dan Naga alamar tsorona take ji sosai har yanzu hannunta na rik'e da wuyanta
Mutsu mutsu ta hau yi Ni kuwa Ina ganin Haka na mike na je na kulle k'ofar Gidan na dauko wani sharbaben wuka a d'akina na fito dashi daga gidansa tana ganin Haka ta gwallo Ido ni kuwa nace "Na rantse da Allah idan Baki gayamin ba sai na yanka ki mmn maimuna karki dauka bazan iya ba Dan tunda har a matsayinki na wacce itama take da Yara ta Haifa ta san zafin haihuwa xaa iya had'a Baki dake Dan kawai a cutar mun da 'ya toh Dan na kasheki wlh banyi asara ba Zan iya komai Akan yarana ki bude baki ki gayamin Mai zakiyi da layyar Nan da ace kin Shiga band'akin Nan asirinki Bai tonu ba"
Na nufi wajenta na Kara jawo hijabin jikinta da k'arfi cikin azabar tsoro yanda na Dora wuk'ar a wuyanta ta hau min bayani.
"Dama a ranar da muka zo gidanan da Kika bud'e kofar muka gudu nida Safiyya sabida karki Kama mu sosai muka ji takaicin da bamu idda nufinmu Akan ki ba Kika bud'e kofa a nesa da gidanki muka labe muna hango yanda kika rik'e almajirin da muka so Yana kwankwasa gidan kina bud'ewa ya jefa Kwan a tsakar gidan indai ya fashe toh yanda rubabben Kwan xai ringa wari Haka za a ringa toshe hanci Zahira na wari har ta Rasa Mai Aurenta Dan Safiyya tace Bata so Zahira ta samu miji Mai kudi ta aura har ki Huta
Gudun da almajirin yayi da fad'a Mana da yayi kin kwace Kwan yasa Safiyya taji kamar ta haukace zaginki tayi tayi tana tsine Miki Akan Bata yarda.dake.ba kema akwai wajen bokan da kike xuwa yake Gaya miki duk abinda zai faru dake.
Haka ta kwana a gidana ko bacci batayi ba muna Kara Shan alwashin komawa wajen bokan namu washegari kuwa da sassafe mukaje Muka Gaya masa duk abinda ya faru ya Kara cajar mu wani kudin.
Dan dai ta Sakani a gaba ne banyi niyyar zuwa ba sabida banida kwanciyar hankali tunda maimuna ta Sha alewar Nan kullum cikin jawomin magana take.
Ahaka taje.tayi buga buga bansan Inda ta samo kudi ba tazo ta sameni shekaranjiya na Rakata wajen bokan muka Kai Masa kudin shine ya d'auko layyar Nan ya bani yace ayi kokari a jefa a masan gidanan yanda Kashi keda wari Haka zata ringa Yi a wajen Samari Haka zatayi bakin jini
Wanan Abu yasa hankalin Safiyya ya tashi Dan bamu San Mai zuwa gidanki har ya Shiga band'akin ki ba ahaka muka dawo gidana muna naziri a karshe tacemin Ni Zan Mata aikin Nan Zata bani Dubu daya
Dayake Ina cikin bukata a Haka na karba ta bani kudin shine yau ta zo akan tana zaune a gidana tana jirana nazo na saka layyar a masai ai bakida wayo indai nace Miki inajin fitsari bazaki hanani shiga bandaki ba
Nidai Dan Allah kiyi hakuri mmn Zahira sharrin shaidan ne nayi nadamar biyewa Safiyya"
Ta karashe tana fashewa da kuka.
Duk maganar da take min sama sama nakejinta sabida tashin hankali Dana shiga Ashe duk Inda nake tunanin su Umma sun Kai wajen mugunta ashe sun wuce nan"
Wuk'ar hannuna na ajiye na cika mmn maimuna cikin rawar murya nace " Mmn maimuna akwai wani Abu Dana Miki da kike ganin na cancanci kiga bayana haka?idan nayiwa maimuna yarki Haka Zaki ji dadi ?mmn maimuna iya alewar da yarki ta Sha take sata Bai Isa yasa kigane Allah ke kareni da yarana daga sharrin su Safiyya ba iya sanina ba abinda na Miki Dana cancanci Haka daga wajenki mmn maimuna kudadena dake wajenki bazasu lissafu ba kema kinsani ban taba Miki Aiken ki bani kudina ba ban taba daga Miki hankali Akan ki bani kudina. Ba ban taba canza Miki fuska ba na daina Baki bashine sabida na lura bakyaso na karu dake ta gaban shagona yaranki zasu wuce wani shagon su siyi Abu da kudi Amma idan bashine sai ki taho wajena
Dan Kuma na daina Baki bashin mmn maimuna sai kiga laifina ko kece inaga matakin Dana dauka Zaki dauka tunda kayan Nan ba kyauta nake samowa na zuba a shagona ba
da kudi nake siyan kayan Nan mmn maimuna bayan hanaki bashi danake mmn maimuna akwai abinda na Miki Wanda bansani ba"?
Girgiza min Kai tayi Tana "Kiyi hakuri mmn Zahira sharrin shaidan ne wlh ki yafe min"
"Kiji tsoron Allah Mmn maimuna karki biyewa San zuciyarki kizo ki aikata abinda Zaki zo kina nadama daga baya ki fita daga abinda Bai shafeki ba Umma da Safiyya Allah yasan ba abinda na musu Suka tsaneni na rabu da Naseer ma basu kyalleni ba kiyayyar har ya tashi daga kaina ya koma Kan zahira da Bata ji ba Bata gani ba a iya sanina ba abinda Zahira ta musu kema Haka Amma tunda abinda kuka zab'a kenan. Mmn maimuna wlh station zamuje ayimin katangar karfe daku gabad'aya duk abinda ya sameni da yarana wlh kune"
Ina fadar Haka na dauki layar da Addu'a a bakina na Shiga d'akina na daga gadona na dauko wanan Kwaryar na jefa layar a ciki na zura hijabina na dauki mukullin gidan nayi waje.
Mmn maimuna a guje tayo wajena tana na rufa Mata asiri Kar na Kai su station ni kuwa hankadata nayi ta Fadi na fita tare da kulle gidan ta waje.
Na dauki hanyar station Ina kuka Kamar karamar Yarinya Dan Nagaji da abinda su umma sukemin bansani ba ko matakin Nan da Zan d'auka shi zai saka na samu kwanciyar hankali gwara ayimin tsakani dasu tun kafin su shirya abinda yafi wanan tunda Ashe sau uku kenan suna gwada cutar min da 'ya Allah na Kare mu.
Wanan shine karshen abinda zanyi da zai saka kila na samu Salama sai dai Naseer Yaji Haushin na Kai karar mahaifiyarsa da kanwarsa wajen yan sanda
Da kafa na karasa station din da kyar na tsagaita kukan da nake na musu bayanin abinda ke tafe Dani
Take kuwa wani daga cikin Yan sanda ya tambayeni Ina ita mmn maimuna take yanzu nace Masa tana gidana na kulleta
Gyada min Kai yayi ya Kira wata Yar sanda da kallo daya zaka Mata gabanka ya Fadi sabida girmanta ga kib'a ga tsayi iya hannunta idan ta damke mutum dashi sai yaji a jikinsa ce Mata yayi su dau mota ita da wasu Yan Sandan guda biyu su bini gidana a d'auko mmn maimuna ta Kai su gidan su Safiyya a d'auko Safiyya da