Showing 36001 words to 39000 words out of 148334 words

Chapter 13 - SO KO ABOTA BOOK COMPLETE BY Maman Nurool-Huda.doc

27 Sep 2025

2896

Tace"hakane my shaheed but yanzu dai kun shirya da Sameer ko? Ko har yanzu Kuna tab'awa?"

Yace"kina ganin Zan tab'a sonsa nifa duk duniya bani da makiyi daya wuce shi "
. Tace"Wai miye ya had'a ku ne haka"

Yace"Haka kawai Allah ya d'aura min kiyyayarshi "
. Tace"Allah ya kyauta"Hira suka Shiga Yi na masoya sai 1pm yace"muje cafeteria for lunch please Ina Jin yunwa"

Tace"ok muje"
. Tashi yayi ya Kama hanunta suka fita suna fita a elevator Suma su zeenat na fitowa daga office rike da hanun juna kallo d'aya yayiwa hanunsu ya d'auke Kai

Shaheeda ta kwace hanunta tace"Sameer is that you??

Sameer yayi murmushi yace"shaheeda how are you yaushe Kika shigo ne saukan yaushe?"

Tace"jiya da daddare nace Bari in dawo in duba sweetheart dina Kan matar naija su min wuf dashi"

Sameer yayi murmushi yace"ban gan laifinki ba shaheeda duk da nasan kanin nawa Bai damu da Mata ba ya rike Miki Amana"

Shaheed na Jin haka yayi tsaki yayi gaba ya barsu"

Shaheeda ta kalli zeenat dake rakube b?yan Sameer domin tunda ta gan shaheed ta b'oye tace"who is she ko itace kishiya ta?I mean kishiyar farfadata"
. Yace"yes she is the love of my life my baby "

Shaheeda ta Mika Mata hanun tace"sunana shaheeda nice budurwar da shaheed zai aura,nice to meet you dear"

Zeenat ta kakaro murmushi tace"the pleasure is all mine iam zeenat a tare suka jera zuwa cafe din shaheeda ta tafi tebu din shaheed dake cin abinci"

B?yan sun fito daga cafe sai zeenat ta had'u da tasleem ta tsaya suna Hira shikuma Sameer ya shige

Tasleem tace"dear dama Ina son ganin ki yau da misalin 8pm Ina son ki rakani wajen wani birthday party saurayina na ne Hamza zaiyi birthday Kuma yace"in ban Zo ba zamu rabu,nikuma bana son in je ni kadai"

Zeenat tace"no dear bazan iya zuwa ba kema ban so ki je"

Tasleem tace"wallahi Ina sonshi zeenat ki taimakeni"

Da k'yar zeenat ta yarda zata rakata

Ko da aka tashi kin tafiya gida tayi domin tasan baza a Bari ta Kuma fitowa ba ko kad'an Bata so zuwa ba Sameer ne ya Bata goyon baya yace"ta mutunta kawancenta Hira suke tayi da Sameer shima be tafi ba har 6 dinya d'aukesu ya kaisu boutique ya siya musu Kaya masu yawa Kiran Inna tayi ta fad'a Mata yau bazata dawo da wuri ba in an nime ta tasan me zata fad'a,har ta bawa Sameer suka gaisa da Inna,Inna taji Dadi sosai kamar sun San juna Daman da Sameer din


.gidansu tasleem sukayi daman da yayarta mace dake aure anan take Zama domin iyayensu sun rasu

Ce Mata sukayi kawarsu ce zatayi birthday zasu dawo da wuri

Anty rukkaiya tace"karku Kai 9 a waje please "

Tace"inshaallah bazamu dade ba"

Hamza be Zo ya d'aukesu ba sai 7:30 zeenat tayi mamakin ganin Wai shi tasleem take so domin Hamza kallo d'anya zaka mashi ka gane irin yaran Nan ne masu matukar rashin ji,sai kallonta yake Yana lashe baki Amma da shike sakarya ce maimakon ta fasa sai ta bisu

Wani wuri ya kaisu me Kama da club ya paka zeenat tace"miye ya kawo mu club Kuma"
. Yace"so sorry baby wallahi na daiyi hayan wurin ne just me and my friends"

Zeenat tace"a gaskiya bazan Shiga ba"

Tasleem tace"mu dai je zeenat da an yanka cake zamu tafi ai"

Da k'yar zeenat ta amince ta bisu

A cakude wajen yake wasu na shaye-shaye wasu Kuma na rawa sai shafa Yan Mata ake "

Zeenat ta ji wurin be Mata ba tace"ni Zan wuce"
. Yace"please atleast ku bari a yanka cake"

Zuwa yayi ya kawo musu juice a glass cup ya Mika musu zeenat tace"no baxan Sha ba"

Yace"haba keko yanzu sai ki zo birthday Dina bazaki ko Sha ko ruwa ba exotic ne fa ba komai ba


Zeenat ta amsa itama tasleem ta amsa suka Sha

Ba ayi minti 20 ba zeenat ta fita hayyacinta ta hau saman wata tebu tana rawa tana d'anga gown dinta

Hamza yayi dariya tasleem hankalinta ya tashi ta karasa tace"me ke damun ki zeenat what wrong with you Kai Hamza me ka zuba Mata a drinks ta Sha take misbehaving"

Hamza yayi murmushi yace"Dole in gode Miki baby na dade Ina shirya inda Zan huta dake sai Kuma Kika kawo min gidan hutu ni ban tab'a sonki ba na daiyi amfani da son da kike min ne dan in sameki sai Kuma Dana gan wanan cikar naji duk duniya babu wacce Nike kwadayi sai ita karya na Miki babu wani birthday yau Zan huta da dukkanin ku biyu"
. Tasleem tayi ta kuka tace"no Hamza kayi hakuri ka barmu mu wuce me na tab'a maka a rayuwa "

Duk inda tasleem ta so zeenat ta dawo hankalinta abin gagara yayi saima shafata da Hamza keyi Kuma da alamu wajen kowa nata kanshin ne domin babu Wanda ya taimaka Mata"

Abu har 9:pm zeenat na fama hango jug din ruwa tasleem tayi watsawa zeenat,zeenat tayi baya zata Fadi tana layi

Tasleem ta jijjigata tace"zeenat ki bude Ido please muna cikin matsala

Da k'yar ta samu Kan zeenat suka Fara niman inda zasu gudu
. Da k'yar suka fita duk Hamza na ganinsu,da yike yaron babban kusa ne a kasar sai ya Kira boys dinshi akan a busu

Gudu suke sosai har sun rabu kowa yayi ta kanshi tasleem ta yanki daji

Da yike wurin b?yan gari ne babu wani Wanda ya taimakesu

Zeenat na cikin gudu ta hango wani a saman mota tace"Dan Allah malam ka taimaka min please"

Jin an shareta Kuma masu binta sun karaso yasa ta d'anga Kai cike da tashin hankali jikinta na rawa ta kalleshi waye zata gani in ba shaheed ba Yana shaye shayensa

Kuka ta fashe dashi ya turata

Tana kuka ta karasa inda masu binta suke tace"Haka Allah yaso ku tafi Dani"ta rigada ta sadakar tasan gomma su da shi

Kama hanunta sukayi suna janta b?yan tafiya Mai tsawo suka Kai inda Hamza yayi parking suna kokarin sakata a mota

Suka ji an naushi d'anya daga cikinsu zeenat ta juyo ta gan wani gaye ne tsaye sanye da irin hulan armed robbers baka ganin komai sai kwayar idonshi Kuma dare ne

Dambe sosai suke da gayen da ya gan ba zai iya dasu ba kawai sai ya Kama hanunta suka Fara gudu gayun na binsu sosai gayen yake gudu itama zeenatu tayi kokari sosai

Koda suka Kai wajen wani mota sun tarar a bude take ga wani a mazaunin driver Shiga sukayi aka ja motar

Tunda suka Shiga babu Wanda yayi magana dukda zeenat a tsoroce take tayi mamakin ganin sun sauketa a kofar gidansu ta fita tana kokarin Yi musu godiya ta gan an ja motar,bin motar tayi da kallo tana mamaki

Koda ta Shiga ta tarar duk sun shige domin goma ta kusa

Part din Inna tayi ta tarar da ita tana cin namanta da fanta da shinkafa da Miya kallo d'anya Inna ta Mata ta Kau da Kai sai yanzu ta tuna kayan jikinta ya d'an kamata

Toilet ta Shiga tayi wanka fito still Inna Bata kula ta ba a kujera ta kwanta

Washe gari tana idar da sallah asuba ta fita ta Fara aiki dan wanke laifi Amma babu Wanda yace Mata komai

Da appa ya fito ta gaidashi ya amsa yace"bazaki je aiki ba yau?"

Tace"zanje appa"

Yace"Allah ya taimaka "

Data gaida Abba sai ta gan ya Kau da Kai da mamaki ta bishi da kallo shima baba Haka yayi

Zuwa tayi ta shirya saf ta fito sai taji ana buga gate

Umma tace"duba waye ke bugawa"

Tace"ok daga Nan Zan tafi office sai na dawo"

Umma tace"a dawo lafiya"

Tana zuwa ta gan wani dattijon mutum tsaye yace"Nan ne gidan alhaji zubairu Mai kanti?"

Tace"eh lafiya"

Yace"daga court3 Nike Ina niman zeenat Abubukar zubairu"

Zaro Ido tayi tace"me nayi?"

Yace"ok kece?toh tsanmaci ne na kawo kotu na niman ki domin wani Mai sunan shaheed Mohammed Fulani yayi karar ki Akan kinyi me b'arna yace ki biya Baki dashi kun ajiye agreement Amma zakiyi me aiki for 2years kin sab'a Zaki sa hanun anan"

Jikin zeenat na rawa tasa hanun Yana wucewa ta Ruga a guje tana kuka ta tari me napep

Tana kuka ita ta d'au an wuce wurin tunda kwana biyu yayi shiru Ashe be hakura ba sauri take taaje wajen Salim domin shi kadai gareta

A haukace ta Shiga me office ba tare da tayi la'akari da mutane dake office din ba tace"baby ka taimake ya kaini kotu,in iyaye suka ji na Shiga uku ka taimakeni sweetheart an kawo min tsanmaci"

Yace"baby please give me a minuite Bari in sallami baki

Tace"a minuite is what I don't have baby"

Kallon bakin yayi yace"sorry gentleman I think we will have to do this some other time,sorry for the inconveniences"

Suka ce"no prob call us when you are ready"

Suna fita zeenat tace"ya fa kaini kotu wallahi ya kaini kotu "

Duk inda ya so yayi calming dinta abin gagara yayi kuka take jiki na rawa

Amsa paper yayi ya karanta cike da b'acin rai ya dau makkulin motarshi yayi sai gida domin shaheed na gida ya baro shi kwance a falo

Yana zuwa ya Kai me bugu yace"what the meaning of this nonesense?"

Shaheed ya amshi takarda Yana murmushi yace"the last time I checked kaje makaranta"
. Sameer ya wurga me cheque din 1.5millon yace"this is for the damages ka janye karar

Shaheed yace"wanan tsakanina da ita ne ai mun ajiye agreement akan cewa ko daga baya an biyani bazan amsa ba Dole tayi aiki I gave her chances so ka d'auki chicken change dinka ka b'ace min da gani"

Mari Sameer ya Kai me yace"you are very stupid shaheed ni kake fad'a ma Haka"

Dambe suke sosai,hayaniyar su ya fito da Mami tace"Yaya meya faru ne?"

Mami taje da niyyar rabasu by mistake Sameer ya tureta ta Fadi

Ta fashe da kuka hakan yasa Sameer sakin shaheed ya karasa ya riketa Yana Bata hakuri

Tace"kasheni zakuyi,ku kasheni ku huta "

Hakuri ya Bata ya taimaka ta mike tana dingishi ta koma kujera

Tace"meya faru?meya had'a ku Kuma?"

Shaheed da ya zauna Yana kallonsu yace"Mami wata birgin yariyar ce ta min b'arnan that is worth millions na ce ta biya ni har na Bata chance ta Kira wani tace"Bata da kowa a take na Kira lawyer muka ajiye agreement tasa hanun a condition Dina nace Mata ki daga baya an biya ni bazan amsa ba Dole tayi min aiki for 2years yanzu ta Zo zata min aiki ya Hana nikuma na kaita kotu shine dan kawai Yana Dan latsa ta a office shine zai wani zo y...."

Be karasa ba Mami tame wani kallo Sameer yace"kin ji d'an iska ko"

Mami tace"baba miye tsakaninka da yariyar?"

Yayi shiru,sai tayi murmushi tace"balarabe ka janye maganan nan a kotu "

Yace"nifa gaskiya Mami ba wani janyewa da zanyi in kin gan na janye toh aiki ta min ko Kuma in kaita kotu"

Mami ta jinjina Kai tace"hmmm ai da baka min musu ba balarabe da an canza ma sunan ni ai na dade da sanin ban Isa in sa ka ko in Hana ka ba Allah dai ya shirye ka"

Yace"amin"

Kallon Sameer tayi tace"babana in Roke ka wata alfarma?"

Yace"Mami ni nasan ai cewa zakiyi ayi inda yake so ni kullum sai abinda yake so za ayi"

Tace"toh nuna me zakayi Nima ban Isa da Kai ba baba?Dan girman Allah kayi hakuri baba ka Bari tayi aikin ni bana son rigimar balarabe kasan shifa wiwi da totulin ya juya me Kai baya ganin kowa da gashi"

Sameer yace"ba komai a gaskiya in yace zai Masa Mata za a samu matsala"

Mami tace"Allah yayi maka albarka baba yaushe zaka tafi Ghana ne kofi ya kirani Wai business dinka na can na suffering Wai ya Kira ka ka ce zaka zo shiru Kuma ana bukatar ka"

Yace"next week inshaallah"Yana Gama magana ya mike ya bar musu falon

Shaheed ya fashe da dariya"

Komawa yayi ya tarar da zeenat na kuka ya lallashe ta yace"karki damu zai janye karar on condition that Zaki me aiki for 2years na kyaleshi ne saboda mami

Jikin zeenat sai rawa yake yace"karki damu ni zanyi ta biyanki from my pocket "

Zeenat ta d'au Jakarta tace"nagode Allah ya saka da alkhairi na yarda zanyi aikin",
Bata jira cewar shi ba ta tafi office dinshi ta Fara aikinta

B?yan sati d'anya

Ranan lahadi

Zeenat na zaune a gindi fanfo gidansu tana jira bucket ya cika inuwan mutum ta gani yanayin hairstyle dinshi kamar shaheed saurin juyawa tayi sai ta gan ba kowa tayi tsaki tace"mema zai kawo shi Nan"

D'aukar ruwar tayi ta Kai ciki tayi wanka ta kwanta

Sai wajajen 3:30 ta tashi bacci ta saka hijabi ta tafi gun Inna

Kafin ta Shiga taji muryar Sameer suna Hira da Inna labewa tayi taji Inna na cewa"toh in ka tafi yaushe zaka dawo?"

Yace"bazan dade ba Inna bana son bikin ya wuce wata d'anya ,Kuma Inna banso tasan Ina zuwa Ina son in Bata mamaki ne Inna"

Inna ta gyra Zama tace"karka damu ai ko wancan zuwan ban fad'an Mata ba,Amma ka dage kasan a rayuwa in baka iya bada mamaki ba sai Kai a baka kayi ta addu'a Allah yasa itace mafi alkhairi"

Yace"Amin Inna"

Tace"baka ci Naman ba itama Fanta baka tab'a ba zatayi zafi fa"

Yayi murmushi ,zeenat ta koma baya tana murmushi tace"Nima Ina jiran ka masoyi,ina son in rayu da Kai har abada"

Washe gari Monday

Zeenat aiki takeyiwa shaheed kamar zata me sujjada saboda tsoron karya kaita kotu tana zaune tana aiki ya shigo har kasa ta duka ta gaidashi,Amma be amsa ta ba ya shige ciki,abubuwan da zasuyi fad'a da Sameer yakeyi har lunch ya hanata Zuwa Amma Sameer yayi banza dashi saboda Mami in an tashi shi ke kaita gida ya dawo da ita,gashi kullum zeenat sai ta kamashi Yana romancing shaheeda a office

Mami ce zaune Sameer dake dining yace"jirkin 4pm zai tashi Mami"

Tace"babana da ka hakura da tafiyar Nan har a tsaida date din bikin kasan fa rana d'anya yace shi aure zaiyi"

Yace"ah'ah gaskiya bazan jira ba Allah ya Sanya alkhairi in an sa ranan na Zo ai Kuma ai ba dadewa zanyi ba"

Tace"toh ba komai kaima ka musu bayanin zakayi tafiya ko?"

Yace"eh na fad'an musu ai mutane kirki ne Basu da matsala Nima ai bikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login